Bamagujiya 11-12

Latest Posts

6/recent/ticker-posts

Ad Space

Bamagujiya 11-12

Free Page 11-12*

★★★~~~★★★~~~★★★

 


Ankai ruwa rana kafin su fita daga Hayin Fulanin Saida aka shigar da jami’an tsaro sannan suka samu suka fita da Habeeb daga garin da sharraÉ—in Habeebah zata zauna a gdan Liman zuwa wasu kwanaki kafin mijinta ya dawo ya É—auketa.
Inda su Jimo sukaci alwashin muddin suna raye wannan aure bazashi ko inaba shidai Habeeb bai bawa mgnrsu muhimmanci ba yaja ƙafafunsa suka bar ƙauyen cike da kewa shauƙi da ƙaunar matarsa.
Itako Habeebah lkcn da taji hukuncin da aka yanke da kuma furucin da mahaifinta yayi akan aurenta sai duka jikinta yayi sanyi bataso aurenta ya kasance a haka ba bataso ace ta samu matsala da iyayenta ta dalilin aurenta ba Shikenan sun sallamata babu su babu ita saboda Habeeb?”
Hawaye ne ya sulalo mata ta zauna a shimfiɗar da Hajjo matar Liman tayi mata ta zuba uban tagumi hawaye wani nabin wani zuciyarta tayi ƙunci duniyarta tayi duhu.
Tunda ta taso takejin iyaye mata suna cewa duk matar data É—auki namiji uba saita mutu marainiya! Yanzu ita meye ribar da zata samu data amince tayi baram baram da iyayenta akansa? Waye shi??Meye yake ma nufi da aurenta??? Meye yasa ya tsallake matan dake birni yace sai ita?.

 

Tambayoyi barkatai marasa amsa tunanin Jumme ya faɗo mata ta kuwa rushe da kuka me gigita tunani da taɓa zuciya yanzu Shikenan bazata sake ganin Jumme ba? Ta rabu da mahaifiyarta me ƙaunarta da ƙaunar farin cikinta har abada?
Kuka takeyi sosai me taÉ“a zuciya, a haka Hajjo ta ishe ta ta tafa hannu tana salati tace “Haba yarinya Meye kuma abin kukan ai gdy ya kamata kiyiwa Allah daya baki mijinki me sonki da tausayinki gashi Allah ya É—aga darajar ki zaki tafi birni”
ÆŠagowa tayi ta dubi Hajjo fuskarta taf da hawaye tace “Waye Allah?” Da sauri Hajjo ta kalleta da mamaki tace “Allan ne baki sani ba Æ´ar nan tab to wannan wanne irin aure ne shi mijinki naga ai musulmi ne….”
Har yanzu idanunta nakan Hajjo ta kuma cewa “shima kina nufin yasan Allah?” Jinjina mata kai tayi tace “tabbas yasan Allah domin kuwa alama ta nuna bayan sanin Allah har tsoron azabarsa yanaji Habeebah kinason sanin Allah?” Saurin É—aga mata kai tayi tayi murmushinta ta dafa kanta tace “Zakisan Allah harma ki bauta masa yanzu Meye abin da kike bautawa?” Sunkuyar da kanta tayi tace “Uwa me tsarki ita nake bautawa kuma ita ce abar dogaro na itace take bani nasara akan komai nawa sannan yanzu itace tayi fushi dani harma tasa iyayena sukayi fushi dani yanzu Shikenan rayuwata bazatayi albarka ba…..”

 

Murmushin tausayinta Hajjo tayi ta mike ta zari buta tace “bari naje nayi sallar magaruba sai mu zauna” nan ta zauna tana kallon yanda Hajjo take sallarta kamar yanda ta taba ganin É—an birni yanayi, bayan Hajjo ta idar ta sako musu tuwo da man shanu suna ci Hajjo na bata labaru masu ban dariya sai gashi ta saki jiki tana ta dariyarta da haka Liman ya shigo ya taddasu yaji daÉ—in yanda ya samu Habeebah tanata dariyarta abin ya matukar faranta masa rai ya mika mata wayar hannunsa yace.
“Mijinki ne yakeson mgn dake” Æ™asa tayi da kanta cike da kunya Hajjo ta karÉ“i wayar tace “kekam da a cikinmu akayiki bansan irin halin da zakiyi ba kawai daga mijinki na kira sai kiyi Æ™asa dakai to ko yaranmu ai sun daina wannan kunyar”
Tana mgnr tana kara mata wayar a kunnenta tayi shiru tana jinsa yanata mgn taki cewa komai har ya kashe ya sake kira Hajjo ta tashi ta nufi garken shanu hakan ya bata damar cewa “ÆŠan birni….” Ajiyar zuciya yayi yace “har yaushe zaki daina cemin É—an birni kike kirana da sunana Beebah?” Ajiyar zuciya tayi tace “kaje gdane?” Gyara kwanciya yayi yace “ina kwance a gadona inajin dama kina kusa dani da kin ragemin kewa ko tausa kyayi min….”

 

Wani gwauron numfashi ta sauke daya sanyashi tambayarta “Meye” a kunyace tace “Kunya kabani ai babu kyau sashi ya rinÆ™a taÉ“a sashi” dariya sosai mgnrta ta sanyashi yace “Har yanzu?” ÆŠaga kai tayi tace “Eh” murmushi yayi yace “idan nazo É—aukanki nan da sati biyu zaki maimaita min am kinsan me?”
Girgiza masa kai tayi tace “Aa” yaja fasali yace “Hajiyata tana gaisheki na sanar da ita komai daya faru ta sanyawa aurenmu albarka sosai tayi mana fatan alkhairi” dariya tayi tace “Hajiyanka mahaifiyarka kenan?” Jinjina kai yayi yace “Eh tayi murna da samuwarki cikin alhinta Habeebah mahaifina Sarki ne a garinmu Sarki Khalil na Æ™asar Dutse shine ya haifeni mahaifiyata kuwa Hajiya Kilishi wato Ummusalma haifaffiyar Masarautar Daura ce mu bakwai mahaifiyarmu ta haifa maza biyar mata biyu nine Æ™arami a maza a dakinmu sai mata biyu da suke Æ™anne a gurina matan mahaifina uku Hajiya Zulai wato Hajiyan soro tanada ya’ya Hudu uku mata É—aya namiji Nasir kenan sa’anni muke dashi sai Hajiya Hauwa Hajiyan Æ™ofa yaranta biyu dukka maza Fahat da Salim gidanmu bamuda matsalar Æ´an ubanci duk da dai ba’a rasa shi ko yaya ne tunda ya shiga gidan Annabi ma bare mu bayin Allah, abu É—aya ne matsalar family É—ina munada Æ™abilanci duk wata mace da yayyuna suka aura to ta fito ne daga tsatsonmu haka matan ma ba’a kaisu ga waje a cikin dangi akan auraddasu kasancewar mahaifinmu da Æ´an uwansa sunada yawa sannan suna Æ™yamar talauci wannan yasa musu gudun bare saboda sunce daga bare za’a samu musu musakai a gwamutsa musu zuri’a da datti”
Numfashi yaja ya sauke yaci gaba da cewa “Habeebah nasan zaki fuskanci Æ™alubale zama da zuri’armu domin kece kika fara shigowa wannan zuri’a tamu matsayin mata kuma kika zo a wani yanayi da mai Æ™aramar Æ™waÆ™walwa bazai mawa rayuwa uzuri ba”

 

Numfashi ta sauke hawaye ya zubo mata tabbas wannan shine an gudu ba’a tsira ba anyi gudun wuya an haikewa wuya har ta fara kukan tausayin kanta na kasancewa matar Habeeb tun yanzu wannan wanne irin dangi ne da basa Æ™aunar bare?
Muryarsa ce ta katseta da cewa “kiyi hÆ™r da yanayin da zamu É—an samu kanmu nasan zamu fita babu wani yanayi da yake dawwama Beebah da wasa nake Miki bazan iya barinki kiyi dogon Zama a garin nan ba zuciyata bazata nutsu ba gobe xansa Azo a tafi dake” zaro ido tayi tace “gobe?” Murmushi yayi yace “ko baki shirya ba?” Sunkuyar dakai tayi tace “Amm….” “Shetttt” yace mata sannan yace “amma me? Banson jayayya karki fara kinji?” “to” ta amsa da ita sannan yaci gaba da janta da hira tana Æ´ar dariyarta har zuwa wani lokaci sukayi sallama Hajjo ta nuna mata makwanci ta kwanta bacci ya É—auke ta cike da mafarkan ÆŠan birni.
Washegari da wuri batama tashi daga kwanciyar safe ba Liman yazo yace tazo tanada baÆ™i taja ajiyar zuciya ta miÆ™e ta É—auki hijjab É—in da Hajjo ta bata jiya tasa ta fito tun daga nesa ya kafeta da manyan idanunsa tayi masa kyau da shigar Muslim women sai yaji ta Æ™ara shiga ransa ta Æ™arasa gabansa kanta a Æ™asa ta tsugunna tace “barka da hanya” numfasawa yayi ya sanya hannu ya É—agota ya sanya hannu ya lakaci hancinta yace “Sannu matar Prince Habeeb kina lfy?” Sake sunne kanta tayi tana ajiyar zuciya yajata ya shigar da ita motar yaja suka bar gurin a guje.

 

Yanda ta É—ago da alamun firgici yasashi kallonta yayi mata murmushi yace “zaki koma rayuwa a inda aka halicce ki don gurin” nandanan jikinta yayi sanyi ta mayar da idanunta ta lumshe tare da kwantar da kanta a kujerar wani zazzafan hawaye ya zubo mata yabita da kallo hakanan yaji ta bashi tausayi.
Sun jima suna tafiya tana rera kukanta batare daya ce mata ƙala ba bawai don kukan baya damunsa ba sai don bashi da kalmar dazai iya rarrashinta da ita, dole tayi kuka rabuwa da dangi ƙawaye da garinka rabuwa ta har abada batare daka shirya ba dole ne ya taɓa zuciya da gangar jiki.
Bai nufi gdansu da ita ba wani Unguwa ya nufa yayi parking ya fito ya buÉ—e get na gdan ya shiga da motarsa yayi parking sannan ya kamo hannunta yaja fasali yace.
“Kiyi hÆ™r Beebah nasan kinajin ciwon rabuwa da makusantanki ne wlh ban rabaki da danginki don cutarwa ko zalumci a gareki ba sai don hakan shine yayi daidai da tsarin rayuwarki,
Dukkan wata mace a duniya a Æ™arÆ™ashin haka take ko yanzu ko gobe ko jibi sai kinbar gdanku kin tafi gidan aure so ki kwantar da hankalinki insha Allahu nayi alÆ™awarin baki kulawa saikin zama abar alfahari ga danginki baki É—aya”

 

Hannunsa yasa ya share mata hawayen yace “kukan ya isa haka muje na baki ruwa kiyi wanka ki canza kaya ki bani lbrn kuruciyarki”
Fitar da ita yayi a motar suka nufi ƙofa ya buɗe suka shiga ta tsaya tana ƙarewa falon kallo sake da baki da kuma bayyanannan tsoro ta dubeshi yayi murmushi ya sake riƙe hannunta yakai bakinsa ya sumbata ya ɗago idanunsa da suke lumshewa kamar me jin bacci ya zubasu akan fuskarta yana ayyana abubuwa da yawa a ransa saidai shi kansa baya ƙarfafawa zuciyarsa gwiwa wajen aiwatar da abinda take muradi.
Zubewa yayi a kujera kallon Beebah na saukar masa da wata kasala me narka lakar jiki ya miÆ™a mata hannu da nufin tazo gareshi ta noÆ™e cike da tsoro yayi wata miÆ™a ya miÆ™e yace “ok muje bamuda lkc” batayi masa musu ba suka nufi wata Æ™ofa ta buÉ—e É—akine harda gado kato na alfarma ta kuwa lalace a kallon gadon bataji sanda ya zare mata hijjab dinta ba saijin hannunsa tayi a Æ™irjinta ya sanyata cikin jikinsa ya rungumeta da wani salo me narkar da cikakkiyar mace, itakam Beebah yanda taji yana sama da hannunsa saman Æ™irjinta yasa Æ™irjin nata dukan uku² tayi saurin juya masa baya ya kasance Æ™irjin nata ya koma Æ™irjinsa hakan ma daÉ—i yayi masa yasa hannu ya tallafi mazaunanta.
Nan take jikinta ya Æ™ara É—aukar rawa ta janye da sauri zatayi mgn yasa hannunsa kan bakinta ya lumshe idanunsa da suka kada sukayi jawur yace “Mijinki ne ni Beebah akwai bambanci da irin mazan da kike tsoro muje na nuna Miki yanda zakiyi wanka bamuda lkc na faÉ—awa Hajiya na daukoki idan munje don Allah kada ki bani kunya duk abinda kikaji na faÉ—a a matan gda da Mai martaba ki gasÆ™ata hakan kinji?”

 

 

ÆŠagansa kai tayi ya jata suka shiga bathroom É—in dake batada duhun kai batasha wahalar gane komai ba ya fita ya barta tayi wankanta dama jiya da dare Hajjo ta tsefe mata gashinta tasa klin ta wankeshi tas gashinta yanada muguwar cika ga tsayi ta sharceshi da matajin data gani a gurin ta sake shi ta fito sanye da hijjab É—inta yana kwance a gado ya rungume hannunsa a Æ™irjinsa ya lula sama jannati yaji ta shafa fuskarsa ya sauke ajiyar zuciya me Æ™arfi ya sauke idanunsa akanta tayi masa murmushi tace “Tunanin me kakeyi?” Tashi yayi zaune ya kuranta ido har Saida ta tsargu sannan ya janyo ta ta zauna kusa dashi karon farko data fara zama a abu me laushi dangin katifa ya tallafi fuskarta yace “A matsayin Æ´ar aiki zan kaiki gdanmu….”
Wani kallo tayi masa na sosai tace “Ƴar aiki baiwa fah kenan?” Numfashi ya sauke yace “Hakane zaki tsaya iya bangaren mahaifiyata Hajiyata tasan matsayinki a gurina Habeebah bawai don kaskanci ba a’a saidon kareki daga duk wani abu da ka iya faÉ—owa bayan bananan zan kaiki matsayin Æ´ar aikina karki damu shekara É—aya kawai zanyi na dawo kasar nan gabaÉ—aya nayi Æ™oÆ™arin tafiya dake na hasaso asirina zai tonu domin babu wanda yasan da aurena dake sai Hajiyata nabarki gurinta amana kuma zanyiwa Khalisa da Hudah kashedi akanki bazaki samu matsala da kowa ba kiyi hÆ™r kinji…..”

 

*share please*
[4/16, 7:49 PM] AM OUM HAIRAN: *BAMAGUJIYA*
*(HOT LOVE AND DESTINY)*

NA

*FAUZIYYA TASIU UMAR*
*OUM HAIRAN*

https://youtube.com/channel/UCZ5Vt2–iGyJfTwItSzAnGg

*Paid book*
Kunata cewa promo ɗin dana baku yayi kaɗan to gashi nan na ƙara daganan zuwa jibi zaku sameshi a 200 PC 500
Ki biya ta waɗannan hanyoyin acct details 0255526235 Fauziyya Tasiu gtbank ko ku turo katin waya MTN ta WhatsApp number na kamar haka 09013718241 ƴan Niger kuma zaku tuntuɓi wannan number don biyan kuɗinku +227 95 04 58 22.

Post a Comment

0 Comments