Daudar Gora Book 1 Page 1

Latest Posts

6/recent/ticker-posts

Ad Space

Daudar Gora Book 1 Page 1


*بِسْÙ…ِ اللَّÙ‡ِ الرَّØ­ْÙ…َٰÙ†ِ الرَّØ­ِيم*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_ÆŠan É—ano daga Zafafa biyar_*

………Kwanakin mako uku kenan da shuÉ—ewar komai amma komai ya kasa mantuwa a zukatansu. Kuzari ya samu rauni kamar yanda dukkan karsashi ya gujema gangar jiki. Duniya ta masu Æ™unci, Æ™unci irin wanda har Æ™arshen numfashi da wahala su manta. Farin cikinsu ya zama fansar damuwar wasu, wasun da kansu kawai suka sani basa kallon na Æ™asa da su. Da ace Æ™arfin iko a hanun kowanne ruhi yake a zahirin rayuwa, da ita ce zata zama mace ta farko a duniya mai Æ™arfin ikon da zai girgiza zukatan kowaÉ—anne irin azzalumai. Kafin shuÉ—ewar makwanni uku masu É—auke da kundun baÆ™in ciki rayuwar ahalin Mal. Zayyan tamkar dutsen lu’u-lu’u suke a cikin tsakkiyar zinare. Ba magana ake akan dukiya ba, dan tana a cikin jerin abu mafi rauni da suke É—auka ko amsa sunan ko kallo farin ciki. ana magana ne akan kammaluwar ahali masu matuÆ™ar Æ™aunar juna zunzurutu mara gauraye. Masu kuka a yayin zubar hawayen É—ayansu, masu dariya a yayin farin cikin É—ayansu, masu jiyya a yayin ciwon É—ayansu, masu zama komai a lokacin da komai yake abu É—aya a hanunsu.
babbar Æ™asace a tsakkiyar wani babban tsibiri a wani Æ™arni daya shuÉ—e kafin yau, Æ™asace mai yawan arziÆ™in zinare yankin nahiyar Africa. Ƙasar Ruman nada babbar Daular mulki data Æ™unshi manyan sarakuna masu É—unbin tarihi kala-kala da labaransu bazai taÉ“a kasancewa shuÉ—aÉ—É—e ba a duniya. Ba arziÆ™in zinare ne kawai suke da shi ba, sunada nau’i-nau’in kayan itatuwa da wajajen noma harma da kiwon dabbobi da akan fita da su Æ™asashe daban-daban ko’a shigo cikin Æ™asar a saya. Al’ummar wannan Æ™asa sun kasance wasu irin Æ™yawawan mutane masu kwarjini da cikar haiba, sai dai duk da Æ™yawun da mafi rinjayensu ke da shi hakan bazai hana a samu masu Æ™arancin Æ™yawun ba. Sunada yawan addinai da Æ™abilu tamkar kowacce Æ™asa, sai dai mafi rinjayen Æ™abila sune masu yara yaren rumanci, sannan addinin musulinci yafi kowanne addini Æ™arfi da rinjaye. Abu mafi mamaki a Æ™asar ta Ruman shine, duk da Æ™arfi da rinjayen da addinin musulinci ya samu suna girmama al’adunsu na kaka da kakani musamman Æ™arfin iko. Ƙarfin iko nada matuÆ™ar tasiri a Æ™asar Ruman ainun, hakama al’adu da girman masautunsu na taka rawar ganin hana dukkan abinda turawa suka zo musu da shi taka rawar gaban hantsi a garesu bayan ilimin boko, duk da suma sun shiga cikin Æ™angi na mulkin mallakar turawan a Æ™arnin daya shuÉ—e. Babu wani mulki dake da tasiri sama dana sarautunsu tun a farkon Æ™arnikan baya har zuwa yau É—in nan da suke rayuwa bisa mulkin mallakar sarakunan dake mulkin mallakar su.
itace babbar masarauta da dukkan masarautu ke Æ™arÆ™ashin ikonta bama su talakawa kaÉ—ai ba. Itace tamkar fadar shugaban Æ™asa a wasu Æ™asashe. A maimakon mulkin siyasa, su itace babbar masarauta mai faÉ—a aji akan komai da kowa na Æ™asar Ruman, komai yana tabbatuwa ko akasinsa da Æ™arfin ikon sarki mai mulki a kujerar wannan daula. Bama gasu talakawa ba, babu wata masarauta a cikin kasar Ruman data isa koda É—aga murya a bayan idon Daular Ruman saboda karfin ikon mulkin – (King of kings). Ƙarfin mulkin wannan Daula yakai a duk faÉ—i da Æ™asar Ruman ke dashi babu wani mahaluki da zai iya faÉ—ar siffa kai tsaye ko kamanni na sarkin da duk zai mulki daular ruman tun zamanin Æ™arnikan baya, saboda tsantsar girmamawa da akema sarakunan wannan Daula ko iya É—aga kai a musu kallon Æ™urulla na kusa babu maiyi, daga nesa kuwa fuskokinsu ababen kwarjinine irin na masu mulki da a ranar wasan al’ada na kowanne shekara ake iya ganinsu a zahiri daga nesa bisa keken doki. A tsari da Æ™a’idar daular ruman dukan yarima mai jiran gado daya shiga shekaru bakwai na girma za’a É—aukesa kowa ya daina ganinsa, a sirrance zaiyi ilimin zamani dana addini dama duk wata rayuwarsa irin ta kowa. Bayan cikar shekarun girma a garesa za’a fara bayyanasa ga sarakunan sauran masarautu cikin shigar da Æ™wayar idonsa kawai zasu iya gani. Nuna yarima mai jiran gado ga sauran masarautu na nufin alamar mahaifinsa zaiyi murabus kenan ya É—aurasa a karagar mulki basai bayan ransa ba. Sarkin kuma da baya buÆ™atar hakan bazai taÉ“a bayyana yarima ba ga kowa har sai bayan mutuwarsa. – shine sarkin daular ruman daya shuÉ—e aka É—ora É—ansa É—aya tilo bisa karaga. Shi kaÉ—ai ya haifa a duniya, shine kawai magajinsa sai mata huÉ—u da saÉ—aka daya bari. A yanda tarihi yazo ba’a taÉ“a – mai Æ™arfin iko da daularsa ta gagari duk wani jar fata nunawa yatsa ba kamarsa, ya shimfiÉ—a mulki a Ruman dama yankin Africa gaba É—aya, izzarsa da Æ™arfin mulkinsa yasa ba masarautun Ruman kawai ba, dukkan masarautun Africa na biye da shi da girmamawa da tsoro mai Æ™arfi. Ya tara arziÆ™i mai ban tsoro da ban mamaki, ya kuma shimfiÉ—a ayyuka da ba Ruman kawai ba, Africa gaba É—aya bazasu iya mantawa ba. Kaf Æ™asashen jajayen fata masu faÉ—a aji na tsoro da shakkar -. Sarki Haysam ya raini É—ansa É—aya tilo tamkar sauran shuÉ—aÉ—É—un sarakuna koma fiye da su, dan saÉ“anin sauran yarima da tarihinsu ya shuÉ—e shi wannan yariman tun a shekara uku na haihuwarsa babu wanda ya sake ganinsa kojin labarin inda yake rayuwa. Sai dai a kullum akanji sunansa a bakin Tajwar Haysam fiye da sau goma, ambaton sunansa shine mafi yawan magana dake fita a bakin Tajwar. Hakan kan saka razani da tabbatuwar shi wannan yarima zai kasance na daban a dukkan sarakunan da suka shuÉ—e kenan. Tabbas hasashen mutanen Æ™asar ruman ya rabbata, dan kuwa dai kam da gaske – ya zama sarki na daban a cikin dubban sarakuna, tare da labari mai ban tsoro da razani fiye dana mahaifinsa. Kamar yanda Æ™a’idar daular ruman take bayan cikar shekara talatin da biyar yarima Eshaan ya bayyana a Æ™asar haihuwarsa ta Ruman, sai dai kamar kowane yarima na baya babu mai iya ganin fuska ko suffarsa ta ainahi, hatta da idanunsa ma shi babu wanda zai iya ganin koda Æ™wayar cikinsu sakamakon glass dake sakaye da su. Bayan gama bayyanashi ga masarautu da wata É—aya kacal Tajwar Haysam bin Abdul-Majeed yay murabus aka É—aura yarima mai jiran gado bisa kujerar mulkin daular ruman tare da auren mata huÉ—u galla-galla daga mabanbanta masarautu masu Æ™arfin faÉ—a aji a kasar ruman. Kwanan bakwai akan karagar mulki Tajwar mai murabus Haysam bin Abdul-Majeed ya kwanta jiyya, jiyya ce data girgiza kowa ta kuma bada mamaki, dan kuwa kwanansa É—aya tak yace ga garinku nan. Kwatanta tashin hankalin da Æ™asar Ruman ta shigama a lokacin bazai lissafu ba. Ƙura bata lafa ba mutuwar É—aya daga matan ta sake bayyana, kwana É—aya da mutuwarta watama ta sake mutuwa a washe gari amare suka rage saura biyu. Al’amari ya fara saka zukatan jama’a hasashen da babu damar cewa komai. Wata biyu tsakani É—ayar matar ta uku ta sake mutuwa saura É—aya. Tofa babbar magana. Abu mafi girgiza zukata shine mutuwar É—ayar data rage a shigar sabon wata. Kenan matan Tajwar da mahaifinsa sun gama mutuwa kaf a cikar wataninsa uku da hawa karagar mulkinsa da kuma aurensa. Abun ya taÉ“a zukata aynun, sai dai babu wanda ya iya ko tari saboda tsoro. Sai dai abu mafi tsayawa arai a cikar wata na shidda aka sake É—aura auren – da wasu matan biyu daga gidajen masarautun kasar ruman. Labarin bai canja ba, dan kuwa suma sun mutu É—aya bayan É—aya kafin cikar shekararsa guda da hawa mulkin. Abin al’ajabi aka kuma sake aura masa wasu biyun daga wasu masarautun, suma É—in dai kamar Æ™iftawar ido nasu labarin ya shuÉ—e a cikin shekara É—aya. Haka aka sake É—aurama Tajwar Eshan aure da wasu mata daga mabanbanta masarautu da tsoro bazai barsu hana auran Æ´aÆ´ansu ba, haka kuma suka mutu suma ya kasance duk ya auri yarinyar kowace masarauta goma da suke da su.
Zuwa yanzu ba shakka da tsoron ɗaga murya bane kawai a zukatan mutanen ƙasar Ruman, hatta numfashi suna yinsane tamkar ɓerayen dake a ƙarƙashin tsaron maguna. A tunaninku yaya sautin fitar numfashin zai kasance?.

★★_________★★

Sunanta shine na yanka, sai dai iyayeta da dukan jama’a na mata alkunya da . Su huÉ—u iyayensu suka haifa, itace auta a cikinsu. Hanash! Shine namiji babba. Arfa! ita ke bi masa, Fariha! Itace ta uku, sai ita auta . Sunan mahaifinsu Zayyan!, amma suna kiransa Babiy, mahaifiyarsu Jamaima! Suna kiranta Ummu. Ƙasar Ruman Æ™asarsu ce ta gado tun iyaye da kakanni, nan kaÉ—ai suka sani, anan kuma kaÉ—ai suke rayuwa. Kamar yanda na faÉ—a muku a tun farko Æ™asar Ruman Æ™asace mai tarin arziÆ™i nau-i daban-daban da ake kaikawo da su a cikin Æ™asa da wajenta, tun daga kan zinare, noma, kiwo, Æ´aÆ´an itatuwa dama wasu daban lissafo ba. Sai dai duk da wannan tarin arziÆ™i da ALLAH ya basu hakan bai hana kasancewar wasu a cikin matsayin talakawa ba. Kamar dai su , mahaifinsu talaka ne mai rufin asirin ALLAH. Manomi kuma makiyayi, a nomansa harda noman zuma yakeyi. Dukkan wani nau’in zuma zaka samesa a hannunsa, wannan yasa yake mu’amula da daular Æ™asar Ruman. Duk da ba masu arziÆ™i bane su mahaifinsu mutumne mai tsantseni da taka tsantsan, sannan ya tsaya tsayin daka wajen ganin sun samu ilimin addini dana zamani irin na yara Æ´an gata. Gidansu gidane mai ban sha’awa da birgewa a É“angaren mu’amulantar juna mai cike da soyayya da Æ™auna. Basu da wani buri sai na faranta ran juna, a koda yaushe zaka samesu cikin nishaÉ—i dan talaucinsu bai taÉ“a kasancewa damuwa ga rayuwarsu ba ko nakasu ga farin cikinsu. Idan É—aya na ciwo sukan kasance tamkar su duka suke ciwon, idan É—aya na farin ciki sukan kasance su duka cikin farin ciki. Sune abokai kuma kawayen junansu harda iyayensu. Sunada tarin burika na rayuwa dana kai da kai, wasu a rubuce, wasu a Æ™ayyade a cikin zuciya, wasu a bayyane, wasu a adane a Æ™asan zukata. wasu sun cika, wasu Æ™addarorinsu masu É—aci da saka zubar hawaye dake gudana a halin yanzun sun yanke igiyar kaiwa ga samun cikarsu. Labarin sauyawar tasu, da yankewar tasu ya farane daga wata rana dake dai-dai da cikar sauran kwanaki huÉ—u na zagayowar bikin al’ada da Æ™asar Ruman ke gudanarwa. Ranar da tarihinsu bazai iya gogewa ba, zukata bazasu iya mantawa ba, lissafin faruwarsu da shuÉ—ewarsu bazai taÉ“a daina maimaita kansa ba koda a bayan rai ne.

A kowane karshen wata Babiy ke kai zuma tulu uku daular ruman, amma a duk bikin shekara na al’ada tulu goma yake kaiwa dan shi kaÉ—ai ne yardajje a manoman zuma da sarki ke iya amfani da zumar dake zuwa daga hanunsa tun zamannin Tajwar Haysam. Koda ya mutu kuma bai daina amsa ba. Sai dai kuma duk da wannan yarda a kullum zagaye suke da tsaro ta fannoni daban-daban duk a dalilin zumar da Babiy kan samarwa Tajwar. A ranar data rage sauran cika kwanaki huÉ—u na bikin al’ada rashin jin daÉ—in jiki ya saka Babiy bama Hanash damar tafiya dasu duka cikin Æ™aton gidan gonat da yake noman zuma domin É—urasu a sabbin tulunan da za’akai daular ruman. Da’ace yasan anjimarsa ko Æ™addararsa data ahalinsa da bazai taÉ“a barin wannan lokaci zuwa ba koda a mafarki. Sai dai kash, Æ™addara ta riga fata inji masu iya magana. Cike da farin ciki suka fita, dan kuwa a shekara sau uku kacal Babiy ke barinsu shiga cikin lambunsa. Ba lambun kawai ba, hatta fita koda ta zuwa makarantace suna yintane cikin shiga mai lulluÉ“e dukkan kamanni, domin kuwa Æ´aÆ´an nasa na É—auke da wani irin sirrin Æ™yawu mai É—aukar hankalin duk wanda zaiyi tozali da su, dan haka kullum cikin shigar larabawa suke harda niÆ™abi, idanunsu kawai ake iya gani da tafukan hanunsu, a yau kam sai suka fita a asalinsu batare da sanin iyayensu ba duk da kuwa suna dai sanye da abayoyin, sai dai babu niÆ™abin. Su kansu da’ace sun san abinda ke biye da rayuwarsu da zasu ninka niÆ™abi kan niÆ™abi ne har sama da sau sittin idan zai nisanta zuwan almakashin daya datse walwalin zinaren farin cikin zukatansu.
Sun isa lambu sun gudanar da ayyukan da Babiy ya umarcesu cike da farin ciki da nishaÉ—i, suka tsinko tarin Æ´aÆ´an itatuwa kowa da nasa da burin abinda zaiyi dashi a ranar bikin al’ada dake tunkarosu. shigarsu gida dai-dai da isowar tambura da bushe-bushen algaitu masu ban mamaki da al’ajab a cikin kunnuwansu dama dukkan sauran talakawan gari, dan abune da ba’a sabaji ba sai a wasu lokuta na gittawar Tajwar daga can kan hanya bawai a cikin anguwa kamar hakan ba………..✍

 

*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*

*DAUDAR GORA Billyn abdul*

*KI KULANI hafsat xoxo*

*A RUBUCE TAKE Huguma*

*RUMBUN K’AYA Hafsat rano*

*IDON NERA Mamuh ghee*

_LITTAFI DAYA: 400_
_LITTAFI BIYU: 600_
_LITTAFI UKU: 800_
_LITTAFI HUDU :1000_
_LITTAFI BIYAR: 1200_

_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_

_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_

_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_

_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_

_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_

_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_

ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN

MARYAM SANI
ACCESS BANK
0022419171

SAI A TURA SHAIDAR BIYAN

09033181070

IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA

09166221261

*ƳAN ƘASAR NIGER. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*

+22799643131

Books biyar 1250CFA
Books hudu 1050CFA
Books uku 850CFA
Books biyu 650CFA
Bookk daya 450CFA

KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.

MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.

 

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*

✨ÆŠ ✨
( )

 

 

Post a Comment

0 Comments