Daudar Gora Book 1 Page 10

Latest Posts

6/recent/ticker-posts

Ad Space

Daudar Gora Book 1 Page 10


10_*

……..Kamar wasa Iffah na shigowa gida ta zube kwance tana rawar sanyi, ga jikinta ya É—auka matsanancin zafi. Ummu bata kawo komai a ranta ba game da ciwon Iffah sai tunanin ranar da ake Æ™wallawa ce ta washeta. Da Æ™yar ta tilastata tai wanka, taci abinci kaÉ—an ta ajiye. Maganin zazzaÉ“i Ummu ta bata tasha, daga haka ta koma ta kwanta ranar ko Islamiyya bataje ba.
Da dare firgita data dingayi saboda munanan mafarkai ya sa kusan kowa bai rintsa ba a gidan sai gab da asuba. Da barci yaÉ—an figeta saita tashi a firgice har sai sun rufeta da addu’oi take samun nutsuwa ta sake komawa barci. Al’amarin ya tsayama kowa a rai, sai dai ganin ta tashi ragal da asuba tai salla sai sukaita mamaki. Dan bazaka taÉ“a tsammanin itace a daren jiya ba.
Da safe koda tace zataje makaranta hanata Babiy yayi, acewarsa ma asibiti zasuje da Hanash. Kasancewar Iffah da rashin son asibiti sai ta turje akan itafa ta warke, dama jiyan rana ce (ta fake da abinda Ummu tace). Ganin harda Æ´an kwallanta Babiy yace to inhar zazzaÉ“i ya sake dawowa a yinin yau dole suje asibitin nan. Da sauri tace ta yarda. Bayan wucewar Babiy tai ta É—an Æ™arfafa kanta harda taya Ummu aiki, duk da yanda takejin yanayinta babu daÉ—i haka tai Æ™udirin shirin Islamiyya idan lokaci yayi, tana É—aki kwance bayan idar da sallar azhar sai ga kiran malaminta Fawzan, wayar kawai ta tsurama ido tamkar bazata É—auka ba harta katse, wani kiran ya sake shigowa shima harya katse bata É—aga ba. Duk da zumuÉ—in son ganin kiran nashi da take ciki a kusan kwanaki uku sai taji hanunta ya mata nauyin É—agawa a yanzu daya kira… Shigowar saÆ™o ya katse mata tunani, ta kai hannu kan wayar ta É—auka kamar mai tsoro…
_“Fareedah ga dama ta biyu ta sake samuwa, Idan kinga saÆ™ona kiyi Æ™oÆ™arin fitowa kafin Four”._
A zabure ta miƙe jikinta na tsuma ta hau shirin Islamiyya, tare da tattare dukkan takardun bayanan da take ta faman adanawa harma da waɗanda ta ƙara haɗawa a kwanaki ukun nan.
“Ummu zan wuce Islamiyya”. Ta faÉ—a lokacin da take Æ™oÆ™arin saka takalmi a Æ™afarta Ummu na tsakar gida tana alwalar sallar la’asar.
“Ke da baki da lafiya auta”.
“Ummu naji sauÆ™i wlhy, kinga saukarmu ya kusa babu buÆ™atar na fara wasa ai. Malam nata mana gargaÉ—in hak……”
Sauran maganar ya maÆ™ale a harshenta sakamakon tashin sautin busa mai nuni da isowar jama’ar masarautar Daular Ruman. Tamkar an daki kan Iffah da guduma haka taji wani dummm! A cikin kunnenta har suka Æ™arasa shigowa cikin gidansu jinta bai dawo ba. (Shin tsoro ne? Ko firgici?) bata san wanene ya risketa ba…… TaÉ“ata da Ummu tayine ya sata jan kakkauran numfashi tare da kallonta. Jikin Ummu ne ke rawa, idanunta kam tuni sun tara Æ™walla. Iffah ta shiga girgiza mata kai alamar kar tai kuka, ta sake damÆ™e hanunta cikin nata tare da maida kallonta garesu rai É“ace, dan ta É—auka alwashin a wannan karon komi sukazo da shi sun tara sun samu, sai dai a kasheta…
“Mi kukazo yimana a gida kuma? Ko kun dawo muma ku idasa kashemu tamkar yanda kuka halaka min Æ´an uwana da tsafink……”
Da sauri Ummu ta danne mata baki da tafin hannunta tun kan ta Æ™arasa faÉ—a. Kai take girgizamata cikin rawar jiki. Da ace ba Ummu bace babu abinda zai hanata ta ture hanunta ta Æ™arasa abinda ta fara faÉ—a ko zata samu salama a ranta. Sai dai kuma bazata iya ba, dan haka ta shiga yima Ummu alamar roÆ™o da magiyar ta barta amma taÆ™i yin hakan…
Basamuden nan ne na kullum mai riÆ™e da bulala ya daka mata tsawa. Da sauri Ummu ta sakemata baki, sai dai ta jawota jikinta ta Æ™anÆ™ame. Iffah jitai zuciyata ta Æ™ara hautsunowa, a matuÆ™ar zabure ta sake buÉ—e baki zatayi magana ya dakatar da ita…
“Ke Æ´ar talakawa lura da inda kike. Bakin rijiya ba wajen wasan makaho bane. Idan taÆ™amarki tsageranci tamkar Æ™iftawar ido za’a sauke miki shi, a kuma shafe babinku daga ke har iyayen naki a doron Æ™asa”.
Hasala iya hasala Iffah tayi, Kukan da Ummu ta fashe da shi ya hanata cewa komai ta juya gareta jikinta na rawar shiga tsananin É“acin rai, kanta take juyamata alamar karntace komai…..
“Umm….”
“A’a Iffah! Ina umartarki karki ce komai”.
“Kibarta tace É—inma yanzu harshenta ya zama datsatstse a gabanki.”
Kafin Ummu dake girgiza kai tace komai Babiy ya shigo tamkar an jehoshi, da alama dai wanine ya sanar masa da zuwan jama’ar masarauta gidan nasa. Ko sau É—aya basu bashi damar cewa komaiba suka isar masa da saÆ™on kira daga daular ruman.
“Innalillahi…..” Iffah ta shiga ambata ita da Ummu, dan sunaji a ransu tarihine dai yake Æ™oÆ™arin maimaita kansa, hawaye masu tsananin Æ™una da É—aci na gangarowa bisa Æ™yaÆ™yÆ™yawar fuskata Babiy da shima dai yasan labarin gizo bazai wuce Æ™oÆ™i ba. A gaban idonsu aka wuce da Babiy Daular Ruman a karo na uku, tare da barin wasu dakaru a Æ™ofar gida ta hanyar hana duk wani mai yunÆ™urin fita daga gidan. HaÉ—e kai kawai Iffah da Ummu sukai suna kuka, dan shi kaÉ—ai suke da damar yi É—in..

★Bayan cikar awanni biyu da tafiyar Babiy sai gashi ya dawo, dawowa irin wadda ya saba a duk lokacin da makamancin kira irin wannan ya samesa daga daular Ruman. Yanda ya kafe Iffah da idanunsa dake zubda hawaye ya saka Ummu zubewa Æ™asa cikin kuka. “Abu Hanash itama zamu rasata ko? Itama ka É—aura mata aure da Tajwar…..?”
Hawayene masu É—umi da Æ™una suka ziraro a idanun Babiy, ya girgizama Ummu kansa a hankali alamar a’a, tare da girgiza kan nasa kuma alamar tayi shiru. Hawayen nata ta share kamar yanda ya buÆ™ata, sai dai jikinta bai bar tsuma ba. Kamar yanda Iffah data kafesa da idanu bata iya ko Æ™yaftawa ba. Ummu ta sake gyara zamanta da fuskantar Babiy da Æ™yau….
“Idan ba abinda muke tunani bane to minene ya faru?”.
“Ki kwantar da hankalinki babu komai f…..”
“Bazan taÉ“a yarda babu komai ba. Sai dai idan kana so ka rufeni ne. Hakan kuma shine mafi Æ™ololuwar kuskuren da banajin zan iya yin afuwa gareka a kanshi. Dan inaji a jikina zuwanka masarauta nada nasaba da rayuwar yarinyata data rage min, idan har zuciyarka ta iya É“oyewa Æ™wayoyin idanunka basu lulluÉ“e komai ba, garama ka sanar min”.
Babiy ya fahimci idon Ummu ya rufe ta manta Iffah na wajen, dan haka ya cigaba da Æ™oÆ™arin ganin ya kufcema faÉ—ar abinda yazo da shi har sai sun keÉ“e amma ta dage akan itafa ya faÉ—a mata a yanzu. So yake ya buÉ—e ido amma bashi da sauran Æ™arfin zuciya a yanzu, dan haka a sanyaye ya rumtse idanunsa da launinsu yay matuÆ™ar komawa ja. “Ba’a É—aura mata aure da shi ba. Sai dai….” ya kasa Æ™arasawa.
“……Sai dai me? Dan ALLAH ka faÉ—a min”. Ummu ta faÉ—a tana mai sake fashe masa da kuka mai matuÆ™ar sake É—aga masa hankali. MiÆ™ewa yay yunÆ™urin yi tai saurin riÆ™e masa Æ™afa. Babiy ji yake shima kamar ya fashe da kuka ya huta kawai. Ya dawo ya durÆ™usa gaban Ummu tare da riÆ™o mata hannu, “Akan abinda suka faÉ—a munada mafita tunda yasha ban-ban dana baya Jumaima. Dan haka na gama yanke shawarar zamu bar garin nan dama Æ™asar gaba É—aya a daren yau insha ALLAH. Dan sun buÆ™aci izinin neman auren Iffah ne a gareni, sun kuma bani damar zuwa nai shawara daga nan har zuwa Æ™arshen makon nan”.
Kafin Ummu ta samu damar cewa wani abu sulalewa da faÉ—uwar Iffah a lokaci guda ta riski kunnuwansu. A tare suka zabura kanta jikunansu na matuÆ™ar rawa da tsuma. Ummu ta fashe da kuka dai-dai tana É—ago Iffah dake wanwar a Æ™asa taga ta koma yaraf alamar babu rai a tare da ita…..

…..Sosai kukan Iffah ya sake É—aga hankalin Babiy. Dan tunda aka zuba mata ruwa ta farfaÉ—o ta haÉ—e kai da gwiwa. Suma idanu kawai suka zuba mata suna hawayen zuci, rikicin yana a kantane kawai, amma sune suka fita jin raÉ—aÉ—in a zuciya saboda ita akwai Æ™uruciya tare da ita. A ganinsu bai zama lallai ma tana hange irin wanda su suke matane ba.
Kusan mintuna talatin suna a haka, kafin Babiy yay ƙarfin halin miƙewa suma yay musu umarnin su tashi su koma ciki. Sai da taimakon Ummu Iffah ta iya miƙewa, har sun kusa shiga ɗakin ta tsaya, ɗagowa tai ta dubi Ummu ta juya ta dubi Baby hawaye na sauka da gudu bisa ƙyaƙyƙyawar fuskarta.
“Bazamu gudu ba Babiy, zan aure shi….”
KaÉ—an ya rage Babiy yaci uban tuntuÉ“e saboda firgitaccen furicin Iffah mai kamanceceniya da gawurtaciyar sautin saukar aradu cikin tsakkiyar duhuwar dare. Ummu ma dai da taima Iffah sakin bazata Æ™irji ta dafe dukanin idanunta na firfitowa…..
Iffah ta share hawayenta da sakin murmushi a karo na farko. “Ummu! Babiy! ku kwantar da hankalinku, kar kuma ku É—auka ba’a cikin hayyacina nake ba. Nasan burinku shine ku kuÉ“utar dani daga mutuwa, sai dai kuma a duk inda zanje ku sani tana tare da nine. Wannan azzalumin ba guje masa ya kamata ayi ba, tunkararsa ya kamata ayi. Kamar yanda kaka ya faÉ—a, a wasu lokutan gujema Æ™addara ba mafita bace sake kirawowa kai halaka ne. Amma tunkararta gaba da gaba Æ™arfafa imani ne sannan jarumtace. Shin idan mun gudu kunada tabbacin zamu iya tsere musu bayan Æ™asar a hanunsu take? Sannan idan mun tafi ina zamuje bayan babu inda muka sani sama da Æ™asar Ruman. Fir’auna ma da yay nasa zamanin mulkin da ko kama kafarsa wannan shaiÉ—anin baiyiba UBANGIJI maida ANNABI MUSA (A.S) yay cikin gidansa ya rayu bisa Æ™udirarsa da tabbatar masa shine mai iko akan kowa da komai. Azzalumin nan ba gudun masa ya kamata ayi ba, daÆ™ilesa ya kamata ayi, domin idan ni kun kuÉ“utar dani, su sauran iyayen da zasu iya fuskantar makamancin halin da kuke ciki fa bayanku?. Babiy zanyi biyayya kamar yanda Æ´an uwana sukayi, kuma ku sani da iznin ALLAH nice zan kashes……..”
Cikin rawar jiki Ummu ta zaburo tare da toshe bakin Iffah. Sai faman waigen bayansu take domin sanin dakarun Daular Ruman na ƙofa gidan har su biyar. Babiy ma gaba ɗaya kalaman Iffah sun sake rikitashi. Sai dai kafin wani cikinsu ya samu damar cewa wani abu ta shige cikin ɗakin. Idanu suka tsirama juna shi da Ummu harna tsahon mintina biyu, kafin Babiy yay ƙarfin halin janyewa yana mai jan nannauyan numfashi da barin wajen ya shige ɗakinsa. Da ƙyar itama Ummu ta sauke numfashin, har zatabi bayan Iffah sai kuma ta fasa ta nufi ɗakin Babiy ɗin itama.

Shigowarta dai-dai dayin sallamarsa waya manne a kunensa. Zaune takai a bakin gadon dake ɗakin dan inba haka ba zata iya zubewa ƙasa saboda yamutsawa da jininta ke mata. Jin sunan Baba da Babiy ya ambatane ya sata maida hankali garesa itama. Komai sai da Babiy ya zayyanema Kaka kafin yay shiru alanar saurarensa.
Daga can Baba yaja nannauyan numfashi bayan gama sauraren surukin nasa mijin Æ´arsa tilo data rage masa a raye. Sai kuma yay murmushin Æ™arfin hali mai sautin daya isa har cikin kunnen Babiy. “Ni ma ina goyon bayan maganar Fareedatu. Da ace wani rai nada ikon hana tabbatuwar wasu daÆ™iÆ™u na gaban rayuwarsa masu tafe da Æ™addara da mutane da yawa sunyi rigakafi kafin cikar adadin waÉ—an nan daÆ™iÆ™u Muhammadu Zayyanu. Amma inaso ku tuna muÉ—in talakawansu ne, masu rayuwa a Æ™arÆ™ashin mulkinsu, bamu da wani Æ™arfin iko akan hukuncinsu garemu ko kan Æ´aÆ´anmu. Dan haka ku bita da addu’a kawai itama.”
Tamkar yana gabansa ya jinjina masa kansa, tare da Æ™oÆ™arin danne hawayen da yake na zuciya da Æ™unarsu gara ace a zahiri suke zuba bisa Æ™yaÆ™yÆ™yawar fuskarsa. “Shikenan Baba, amma furucin Iffah ya girgizani, ina tsoron kar zuciya ta ingizata tai yunÆ™urin aikatawa. Kisa fa! Koda bata aikata ba fitar wannan furucin zuwa kunen wani bayan mu ba Æ™aramar magana bace”
“Kar komai ya dameka Muhammad Zayyan. Ta faÉ—ane kawai saboda raÉ—aÉ—i da takeji da kuma Æ™uruciya, kai dai ka sanar dasu ka amsa daga nan zuwa kwanaki uku. Zan zo a amsa kuÉ—in auren da ni dama wasu a cikin zuri’an ka insha ALLAHU………✍

ALLAH sarki Iffah kin bani tausayi

*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*

*DAUDAR GORA Billyn abdul*

*KI KULANI hafsat xoxo*

*A RUBUCE TAKE Huguma*

*RUMBUN K’AYA Hafsat rano*

*IDON NERA Mamuh ghee*

_LITTAFI DAYA: 400_
_LITTAFI BIYU: 600_
_LITTAFI UKU: 800_
_LITTAFI HUDU :1000_
_LITTAFI BIYAR: 1200_

_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_

_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_

_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_

_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_

_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_

_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_

ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN

MARYAM SANI
ACCESS BANK
0022419171

SAI A TURA SHAIDAR BIYAN

09033181070

IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA

09166221261

*ƳAN ƘASAR NIGER. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*

+227 90165991

Books biyar 1250CFA
Books hudu 1050CFA
Books uku 850CFA
Books biyu 650CFA
Bookk daya 450CFA

KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.

MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.

 

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*

✨ÆŠ ✨
( )

 

 

Post a Comment

0 Comments