Daudar Gora Book 1 Page 11

Latest Posts

6/recent/ticker-posts

Ad Space

Daudar Gora Book 1 Page 11


*_11_*

……….Iffah taci kuka matuÆ™a da ko maÆ™iyinta ya dubeta sai ya tausaya mata. Sai dai kuma iya juyawa su Babiy sun mata akan su gudu ta kafe akan itafa ta yarda zata aura *_Tajwar Eshaan ibn Haysam Abdull-Majeed_*. Sosai hankalinsu yake Æ™ara tashi da tirjewarta. Gashi gaba É—aya ta bikice musu ko isashen lafiya babu a tare da ita. A cikin wannan halin Babiy ya sake samun saÆ™on kira daga masarauta. Yana shirin tafiya sai ga Kaka. Duk sunyi matuÆ™ar mamakin zuwan nasa, dan abune mai wahalar gaske a garesa zuwa inba da wani dalili ba. Sun tarbesa kamar yanda suka saba matsayinsa na uba. Bayan gama gaisawa ya kai dubansa ga Iffah dake kwance cikin bargo duk ta rame ta sake komawa fayau da ita, dama tun rasa Æ´an uwanta É—an jikinta ya zube, dan sam ba siririya bace. Iffah nada jiki murjajje daba za’ace mata siririya ba kuma babu mai sakata a sahun masu Æ™iba. Duk da shekarunta har yanzu sunada Æ™aranci ALLAH ya bata jiki na manyan mata da’a yanzu komanta yake ciff dai-dai da halittarta. Kaka ya É—auke idanunsa a hankali tare da maidasu ga Babiy.
“Muhammadu Zayyanu ka sakama ranka nutsuwa ka cire batun barin gidan dan bashine mafita ba. Hasalima tun randa ka amsa kiran masarauta wannan gidan zagaye yake da dakarun daular ruman harta inda baka zata ba. Ko’a tunaninka zasu tunkareka da wannan maganar su baka damar kanka sannan su koma gefe da tunanin kai bazakayi wani yunÆ™uri ba”.
Daga Babiy har Ummu da Hanash kallon tsoro da mamaki sukema Kaka. Ya É—an jinjina kansa alamar tabbatarwa. “Karku damu da yanda akai nasan wannan, kai dai kawai kaje ga kiran da sukai maka. Karka kuma nuna wani ja’inja kace ka amince musu suzo neman auren”.
Kuka Ummu ta fashe da shi tana kallon mahaifin nata. Yay É—an murmushi da É—auke kansa tamkar bai fahimci mitake nufi ba. Ganin haka Hanash da idanunsa sukai jajur cikin cinkushewar harshe yace, “Amma kaka miyasa ka zaÉ“a itama mu sake rasata? Wlhy nayi alÆ™awarin in har itama ta salwanta sai na salwantar da ran Shahan-shan da wannan hanun nawa wajen É—aukar fansa koda nima za ai gunduwa gunduwa da naman jikina!!”.
“Ba kai ne zaka salwantar da ruhinsa ba, ni nan Fareedah bint Zayyan nice zan karya Æ™arfin ikon azzalumi da hannuna, zan masa shaÆ™a irin wadda har sai ya mutu yana mai kallon tsakkiyar cikin Æ™wayar idanuna Hanash Akhi”.
Su duka zuba mata idanu sukayi, dan a yanda take maganar babu alamar tana a cikin hayyacinta. Babiy zaiyi magana Kaka ya girgiza masa kai alamar kar yace komai yaje kawai….

★Kamar yanda Kaka ya umarci Babiy ya amsa kiran masarauta kasancewar a wannan karon an bashi damar zuwa ne shi kaÉ—ai batare da dakaru sun taho da shi ba. A yanda ya samu tarba zai tabbatar maka dama a jirace ake da zuwansa. Kamar ko yaushe a wannan karon ma baiga Tajwar ba, amma dai a karon farko na tarihin rayuwarsa an kaisa har cikin fadar Shahan-shan. Inda yaga tsantsar dukiya da ainahin karagar mulki ta Shahan-shan da akayita da zallar zinare. Hakan ba’abin mamaki bane ba, saboda girman Shahan-shan koda da diamonds akai kujerar mulkinsa bazai zama wani babban al’amari ba, sannan zinare arziÆ™in Æ™asar su ta ruman ne da bare ma kanzo ya ci balle su Æ´an Æ™asa musamman Shahan-shan. Karo na farko da Babiy yaga karramawa daga dattijan daular Æ™asar ruman. WaÉ—an da ko’a mafarki bai taÉ“a tunanin gani ba dan su É—in ma ba’abune mai sauÆ™i ga duk wani talaka ganinsu ba kai tsaye haka. Duk da a birkicen da yake ALLAH sai ya saka masa nutsuwar yi musu bayani babu ko rawar harshe a tare da shi. Sun masa godiya da tabbacin a gobe idan ALLAH ya kaimu masu neman aure zasu zo. Karramawar da sukai masa ta matuÆ™ar basa mamaki da tsayawa a ransa, sai dai ta wani gefe na zuciya ya tabbatar da sabuwar hanyar yaudarace kawai. Cikin danÆ™areriyar mota aka maidasa har gida badan yaso haka ba, yayi shiru ne kawai domin bin unarnin mahaifin matarsa, dan duk da bai taÉ“a ambatawa ba ga kowa ya jima da tsanar duk wani abu daya shafi masarautar daular ruman..

★A wannan dare Babiy yayi zaman kuka irin wanda ake kira kuka a zahiri da baÉ—inin rayuwa. Har yanaji bazai iya cigaba da yima kaka biyayya ba shikam, zai É—auke Iffah su gudu daga ruman koda daga shi sai ita ne. Sai dai wani É“angare na zuciyarsa na tunatar da shi maganar Kaka, yasan gaskiya ya faÉ—a, dan daular ruman bazata zuba ido na barinsa sakakai ba. Ajiyayyun dakarun dake a Æ™ofar gidansa ma kawai tabbaci ne….
A É“angaren Ummu ma bata runtsa ba, sai dai saÉ“anin Babiy ita kwana tai tsaye tana gayama UBANGIJI damuwarsu da roÆ™onsa kariya da kuÉ“uta ga yarinyarta. Shi kuwa Hanash kwana yay Æ™ulla ta yanda zai halaka Tajwar Eshaan ibn Haysam Abdul-majeed da kansa. Hakama Iffah nata shirin nada alaÆ™a dana Hanash. Ta gama yankema kanta koda zata mutu itama sai dai su mutu tare da Tajwar Eshaan. In yaso a binne gawarta a tsakiyyar ruman matsayin tarihin da za’a dinga tunawa…….

*_WASHE GARI_*

Washe gari data kasance safiyar laraba da misalin Æ™arfe biyar na yamma sai ga manyan baÆ™i daga masarauta ruman. BaÆ™i masu ban mamaki, dan kuwa wasu manya ne a cikin dattijai masu faÉ—a aji a daular ruman. Sannan iyaye ga Shahan-shan ta É“angaren jini makusanta sosai ga mahaifinsa. Tamburan masarauta da É—unbin tawagar hadimai da jibga-jibgan motoci da suka Æ™oshi ne suka tabbatarma da jama’ar anguwa dama maÆ™waftan anguwar wace tawagace. Tuni mutane suka fara Æ´ar rige-rigen fitowa daga gidajensu bama idanunsu abinci.
Sun tarbesu bisa jagoranci Kaka daya tsara komai tare da shimfiÉ—a kakkauran gargaÉ—i ga su Babiy. Bayan an musu masauki a cikin lambun Babiy ta É“angaren garden É—in da yayi domin farin ciki ga iyalansa aka cika musu gabansu da Æ´aÆ´an itatuwa duk da babu tunanin ko zasu ci. Babiy, Kaka, da wasu dattijai biyu, É—aya ta É“angaren Babiy, É—aya ta É“angaren Ummu É—an uwa ga kaka kenan suka zauna da su. Sun miÆ™a gaisuwa a garesu cikin mutuntawa da nuna tabbacin su É—in masu Æ™arfin iko ne a garesu talakawan Æ™asan ruman. Hakan yayima dattijan matuÆ™ar daÉ—i da yabama su Kaka. Dan haka suma suka nuna mutuntawa a garesu da basu Æ™arfi matsayin waÉ—anda sukazo neman iri wajensu. Hakan ya É—an bama su kaka mamaki amma sai babu wanda ya nuna. Sun gabatar da buÆ™atarsu, tare da bada duk wani abu na al’adar aure da Æ™asar ruman ta tanada ninki wanda akanyi sau goma. Hakan sai ya Æ™ara firgita Babiy da bashi tabbacin yanda za’a salwantar da rayuwar Æ´arsa É—aya tilo data rage masa zai zama Æ™ololuwar girma fiye da Æ´an uwanta kenan. To inbaice hakaba mizaice, dan dukiyar da suka kawo kawai tamafi Æ™arfin ma sayen Iffah idan sayarwar zaiyi. Bai samu damar cewa wani abu ba, yadai cigaba da kukan zucinsa yabar su Kaka dayin abinda ya dace.
A wannan zama aka Æ™arÆ™are komai har ranar É—aurin aure dama inda za’a É—aura auren. Daga haka sukai addu’a suka tafi bayan an shigo da tarin kayayyakin da sukazo da shi. Daga Babiy har Ummu tagumi kawai sukai suna kallon kayan da aka baza a tsakar gida. Hakama Hanash da dattijan nan guda biyu da sai gobe zasu koma tare da kaka. Kaka kuwa na gefe zaune abinsa tamkar baima san mike faruwa ba a gidan. Yayinda Iffah ke can Æ™uryar É—akin Ummu kwance cikin zazzaÉ“i data yini da shi…..
Washe gari su kaka suka wuce batare daya sake cewa uffan ga su Babiy ba akan komai. Yadai gargaÉ—i Babiy akan karya kuskura yace zai yi wani yunÆ™uri. Ya kuma sakasu killace dukkan kayan da aka kawo daga masarauta…..

★★★_______★

Tamkar da gayya cikin kanÆ™anin lokaci gari ya É—auka Shahan-shan zai yi aure, alamu kuma sun nuna ana shiryama auren da shiri na musamman duk da amaryar bata kasance Æ´ar kowa ba. Hasalima ahalinta nada tabon Shahan-shan a dalilin salwantar Æ´aÆ´ansu biyu kafin ita. Dukkanin waÉ—an nan Æ™ananun magana na faruwane a bakunan mutane da Æ™aramar murya, yayinda a kafafen Æ´aÉ—a labarai da fejikan yaÉ—a zumunta babu mai iya É—aga murya yayin faÉ—a sai fatan alkairi kawai. Mutane sun sake samun tabbacin wannan aure na musammne daya sha banban dana baya sakamakon fara shelarsa a kafafen yaÉ—a labarai domin gayyatar manya-manyan Æ™asar kamar kowane Tajwar da jama’ar majalissarsa da talakawan garinsa. Da yanda ake wasu Æ´an gyare-gyare a daular ruman wai duk na tarbar zuwan ranar É—aurin aure ne. Humm abin faÉ—a taf bakunan mutane sai dai babu damar faÉ—ar. Idan kuma suke ganin zasu sami wani Æ™arin bayani an toshesa dan babu mai ikon shiga gidan Babiy a halin yanzu kasancewar zagaye yake da dakaru tako ina, acewarsu suna bama *_Zawjata-almilki_* tsaro ne. A cikin gidan kuma babu mai fita hatta da Hanash dake zuwa babbar makaranta…
A haka kwanakin biki da suka rage suka cigaba da shurawa batare da wadda ake iƙirarin zama amaryar ta sake tada kai ta dubi wani abu daya shafi auren nata ba koda da kallo. Ta dake matuƙa tamkar ba itaba, hatta da ciwon dake cinta a tsaitsaye taki bada damar da su Ummu zasu fahimta. Ta ƙeƙashe idanunta ƙam ta hana hawaye zuba daga cikinsu. Ta tattare gaba ɗaya hankalinta ta maida ga rubuce-rubuce da babu wanda ya fahimci na minene a gidan, dan bata bari kowa ya duba mata shi. Sai dai ga duk mai hankali a duba ɗaya da zai mata zai fahimci tana cikin matsananciyar damuwa, mai busar da zuciyar mai ita da zai iya aikata komai da zai iya zama komai akan komai..
Kamar ko yaushe yau ma bayan ta kammala ayyukan gidan da take taimakawa Ummu da su ɗaki ta koma tana kukan zuci daya zame mata abokin rayuwa. A idaniyarta kam babu alamar ɗigon hawaye, sai dai raɗaɗin wanda ke kwaranya a zuciya ya maida launin idanunta sirkin ja har kana iya ganin jijiyoyi a cikinsa. Duƙufe take akan littafinta tanata rubutu da sakin ajiyar zuciya akai-akai. Ummu data shigo ɗakin takai zaune a kusa da ita tana mai tsurawa rubutun idanu na wasu sakanni.
“Ibnati!”.
Karan farko Iffah ta ɗago ta kalla Ummu duk da tun shigowarta ta jita sarai. Wani irin miskilin murmushi ta saki tare da maida kanta a hankali ta duƙar..
“Kina ganin laifinmu ko?”.
Cak ta tsaya da rubutun data cigaba, sai kuma ta saki murmushi. Tsahon sakkani uku kafin ta É—ago ta dubi Ummu. Ta É—an girgiza kanta da ajiye biron hanunta. “Ummuna idan har zanyi zargin wani akan wannan al’amarin to kaina ya dace na zarga. Ku É—in nagartattun iyayene abin alfaharin kowane irin É—a. Ni ya dace nazo muku da wannan maganar, domin nice na saka zukatanku a damuwa da É—unbin fargaba. Na tabbata a kowane sakan, a kowane minti, a kowane awa, a kowane kwana na waÉ—an nan kwanakin kunayinsa ne cike da fargabar shuÉ—ewarsu da gabatowar su. Kuyi haÆ™uri ku Æ™ara haÆ™uri ku gafarceni. Koda baku faÉ—amin ba, baku faÉ—ama duniya ba nasan irin raÉ—aÉ—in da kukeji a zukatanku domin nima makamancinsa nakeji. Sai dai ina muku albishir Ummuna, koda zakuyi kuka a wannan gaÉ“ar bazakuyi irin na baya ba. Na muku alÆ™awarin kukan ku zai kasance tare da dariyarkune a lokaci guda. Dan ruhina sai ya amso muku diyyar su Nina Arfa kafin yabar gangar jikina. A duk randa saÆ™on mutuwata zai riskeku insha ALLAHU zai riskekune tare da na mutuwar azzalumai. Dan haka ina roÆ™onku kar kuyi baÆ™in ciki a wannan karon, zaku sadaukar da ruhin da zaije muku yaÆ™in neman Æ´ancin kai ne ku da al’ummar Æ™asar ruman…..”
Kai Ummu ta shiga jujjuyawa hawaye na kwaranya a idanunta, “Ibnat…”
“Na roÆ™eki kar kice komai Ummuna, albarkarki itace mafi Æ™ololuwar buÆ™ata ga ruhin daya daÉ—e da zama cikin tahin gawa. Ƙaddarata rubutacciya ce tun daga alÆ™alamin da idan yay rubutu babu wani duster dake iya gogesa”………..✍

ALLAH sarki Iffah, ALLAH ya baki damar yaƙi irin wanda ya dace da fatanki na alkairi

*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*

*DAUDAR GORA Billyn abdul*

*KI KULANI hafsat xoxo*

*A RUBUCE TAKE Huguma*

*RUMBUN K’AYA Hafsat rano*

*IDON NERA Mamuh ghee*

_LITTAFI DAYA: 400_
_LITTAFI BIYU: 600_
_LITTAFI UKU: 800_
_LITTAFI HUDU :1000_
_LITTAFI BIYAR: 1200_

_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_

_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_

_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_

_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_

_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_

_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_

ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN

MARYAM SANI
ACCESS BANK
0022419171

SAI A TURA SHAIDAR BIYAN

09033181070

IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA

09166221261

*ƳAN ƘASAR NIGER. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*

+227 90165991

Books biyar 1250CFA
Books hudu 1050CFA
Books uku 850CFA
Books biyu 650CFA
Bookk daya 450CFA

KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.

MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.

 

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*

✨ÆŠ ✨
( )

 

Post a Comment

0 Comments