Daudar Gora Book 1 Page 13

Latest Posts

6/recent/ticker-posts

Ad Space

Daudar Gora Book 1 Page 13


13_*

 

………Ta ko’ina bayine masu hidima ga wannan basarakiyar daula. Yo basarakiya mana, dan itace masarauta dake mulkin Æ´an Æ™asa dama sarakunan Æ™asar baki É—aya. Sun sake wuce gate na biyu inda anan É—in ma dai katafaren wajene da misaltasa babban aikine ga mai hasashe. Ta ko’ina hadimai ne ke kaiwa da komowa maza da mata. Ga wasu irin gine-gine na alfarma da É—aukar hankalin mai kallo tamkar ba’a cikin Æ™asar Ruman ba. dogayen gine-gine ne da abaya sai dai su hangosu daga nesa tamkar yanda suke iya kallon jirgi yayinda yake keta giza-gizai. Ga wasu irin korayen shukoki tako ina tare da shimfiÉ—aÉ—en lafiyayyen titi da za’a iya rantsewa yafi kowanne titi dake a cikin Æ™asar Ruman. Kasancewarta farin shiga a ganin wannan shimfiÉ—aÉ—É—iyar daula saita fara tunanin anyama kuwa a duniyar mutane take? Kokuwa dai mafarki takeyi ne? Dan sam inda take yafi kama da anguwanin Æ™asashen turawan da a tv ne kawai suke iya ganinsu cikin film ko labarai da makamantansu…
Har motocin suka samu wajen tsayawa aka fito da ita sam ba’a hayyacinta take ba, bawai Æ™awatuwa da tarin Æ™yale-Æ™yalen da aka zubane kawai ke É—ibar hankalinta ba, akwai wani É“oyayyen tunani acan Æ™asan ruhinta da Æ™ahon zuciyarta mai alaÆ™a da tabbatar da abinda mutane ke faÉ—a akan Daular Ruman É—in…… Saukar sautin busar sarewa mai zaÆ™i da daÉ—in saurare da ya fara tashi a cikin daular Ruman ya sauka cikin kunnenta tare da katse tunaninta ya maidota hayyacinta. Wannan saÆ™one dake isa zuwa kunnen duk wanda ke a cikin masarautar cewar an iso da _Zawjata almilki_.
Tsawon lokaci sautin na tashi har sai da saÆ™on ya isa ga kunen kowan da ake buÆ™ata. Daga Iffah dai bata san ma’anarsa ba, dan haka bata É—aukesa komai ba. Sai ma share hawayen fuskarta data cigaba dayi, dan har yanzu fuskar tata na lulluÉ“e ne da hular Æ™awatacciyar rigar jikinta da zamu iya kira alÆ™yaba. Sai dai zuciyarta cike take da alwashi mai ban tsoro ga duk wanda zai iya jinsa a kunne. Ta sadaukar zata mutu, amma ba ita kaÉ—ai ba harda Shahan-shan na Daular Ruman, idan an hanata damar bayyanama duniya a Æ™wato musu Æ´ancinsu, sai ya mutu aga wanda zai cigaba da kashesu. A karan farko ta saki murmushi mai Æ™ayatarwa, irin murmushin data jima batayiba kuwa……..
Babu wanda ta É—aga kai ta ko kalla a cikinsu har suka gama bushe-bushen algaitunsu dana sarewa. Cikin girmamawa É—aya daga cikin matan da suka É—akkota ta matso gab da ita.
“Ran Zawjata-almilki ya daÉ—e, nan shine sashen Malikat Bushirat. Mahaifiya ga Zakin wannan daula Shahan-shan, Uwa ga duk wani É—an Æ™asar ruman”.
A karo na farko Iffah ta É—an É—ago idanu ta dubeta kaÉ—an daga cikin alÆ™yabar, kanta a Æ™asa yake ita a dole bazata iya ko haÉ—a ido da ita ba domin girmamawa. komai batace da ita ba, sai dai ta dubi katafaren ginin da ya tabbatar mata da maganar matar. Idanunta ta maida ta risinar kawai batare data nuna alamar tama jita ba. Abin mamaki bai nema tsaida bugawar zuciyar Iffah ba sai da suka shiga wannan katafaren gini, bayi sai zubewa suke akan gwiyawunsu tamkar wasu masu neman gafara ko kuma Tajwar Eshaan É—inne da kansa. Zaman faÉ—a muku daula da dukiyar dake a wannan sashe ma ai É“ata lokacine, dan haka na baku damar Æ™iyastama zukatanku kawai…. (Lol)

★Karan farko na tarihi, karan farko na rayuwa, yau ga Iffah gaban *_Malikat Busheerat_*. Mace ta biyu ga tsohon Tajwar Haysam ibn Abdull-Majeed. Mahaifiya ga Tajwar Eshaan ibn Haysam Abdill-Majeed Shahan-shan na wannan Æ™arni. HamshaÆ™iyar mace mai tsananin Æ™yau tamkar itace ta zaÉ“ama kanta Æ™yaÆ™yÆ™yawar surar jikinta da zubin halittar ta. A kallo É—aya da Iffah tai mata daga cikin hular alÆ™yabar jikinta ta kasa sake É—aga idanu ta Æ™ara saboda kwarjininta. Ta tabbatar ta isa a kirata _Malikat_ (Sarauniya), Uwa ga fir’aunan sarki kuma. KishingiÉ—e take a É—aya daga Æ™ayatattun kujerun katafaren falon daya amsa sunansa daular duniya, wanda kafin isowarsu cikinsa sun wuce manyan faluka da suma suka amsa suna daular duniya bama ta ruman ba kawai. A gefe da gefenta wasu matanne cikin shiga ta alfarma suma har su huÉ—u, sai hadimai dake zagaye da ita kowanne da hidimar da yake a gareta cikin matsanancin taka tsan-tsan da kai. Dan ko wadda ke tare da ita suna shigowa zubewa Æ™asa sukai jikinsu har tsuma yake yi, ita Iffah har tsoroma suka bata tare da mamaki mai girma na wannan Æ™arfin iko.
Iffah dai na tsaye har sai da É—aya daga cikin matan nan dake tare da Malikat ta miÆ™e ta kamota ta zaunar Æ™asa bisa lallausan carpet É—in dake a falon saitin Malikat Bushirat da har yanzu tana a kishingiÉ—enta kuma ko sau É—aya bata É—ago ta kalla kowaba tunda suka shigo. Kusan minti biyu falon yay tsitt babu wanda ya sake koda motsin kirki, sai Æ™arar na’urar sanyi dake tashi kaÉ—an-kaÉ—an da wani Æ™amshi na musamman.

(To masu karatu inhar Malikat na’a haka, yaya shi kuma Tajwar É—in zai kasance kenan akan izza da mulki?.)

Iffah da shirun ya isheta kaÉ—an ta É—ago idanunta ta cikin hula ta saci kallonsu. Sai taga su duka har Malikat É—in ashe ita suka zubama idanu. Haka kawai tasha jinin jikinta, dan kallone bana a santa ba, kallone dake buÆ™atar nutsuwa kafin a bashi fassara. KaÉ—an taja numfashin dake neman maÆ™ale mata a maÆ™oshi da Æ™ara yin Æ™asa da kanta hular ta sake rufe fuskarta ruff. A hankali, cikin son É“oye rauninta da hawayen dake neman kwace mata ta furta “Barka da yamma ranki ya daÉ—e”.
“Malikat ta amsa miki, tare da maraba a gareki”.
Ɗaya daga cikin matan ta amsa a maimakon Malikat da har yanzu batako motsa daga kishingiɗar da tayi ba. Sai dai ta ɗago ƙyawawan idanunta farare tas ta sake zubasu akan Iffah, idanun ta juya a hankali ta dubi ɗaya daga cikin matan nan dai dake kusa da ita.
“An gama ranki ya daÉ—e”.
Matar ta faÉ—a da girmamawa alamar ta fahimci mi take nufi. Tsam ta miÆ™e zuwa inda Iffah take, ta kai hannayenta biyu ta kama hular alÆ™yabbar tai baya da ita, Æ™yaÆ™yÆ™yawar fuskar Iffah datai jajur saboda kukan da tasha abinka da farar fata ta bayyana. Idanu Iffah ta rumtse sakamakon jin al’amarin a bazata, ga wani irin harbawa da Æ™irjinta yayi har sai da ta ambaci (Hasbinallahu wa-ni’imal wakil) a zuciyarta sannan taji numfashinta da yay sama yay Æ™asa a lokaci guda ya daidaita. Kaf hadiman Æ™asa sukai da kansu, dan haramunne a garesu kallon fuskar *_Zawjata-almilki_* kai tsaye. Yayinda Malikat Bushirat ta motsa a karo na farko daga kishingiÉ—ar da tai idanunta akan Iffah. Kusan kallon mintuna biyu tai mata kafin ta janye idanun cike da Æ™asaitar masu isa, yatsun hanunta ta É—an murza suka bada sautin (É—ass! ÆŠass!!!) har sau biyu. Tamkar Æ™iftawar ido hadimar dake tsaye riÆ™e da wani Æ™asaitaccen bowl kalar gold da adon stones masu É—aukar ido ta iso gaban Iffah da kanta ke Æ™asa har yanzu tana ambaton ALLAH a zuciyarta ta zube tamkar mai neman gafara. Kanta a Æ™asa alamar bazata iya kallon Iffah ba ta miÆ™a mata bowl É—in hannu biyu bayan wata a cikin sauran hadiman ta matso da sauri ita kuma ta janye farin Æ™yalle da aka yana a saman bowl É—in tare da murfinsa, tatacciyar madara fara tas ta bayyana. Cikin rawar murya da tsantseni hadimar ta furta,
“Ya Zawjata-almilki! Wannan madara ce mai daraja daga hannun Malikat domin nuna maraba da zuwa a gareki cikin DAULAR RUMAN”.
Shiru Iffah bata da alamar motsawa, har hakan ya bama duk wanda ke gurin mamaki har Malikat Bushirat. Tsahon sakanni goma kafin ta É—ago. Manyan idanunta da sukaci kuka har suka gode ALLAH ta zubama bowl É—in tare da hadimar dake gurfane a gabanta tamkar mai neman gafara. Kanta ta girgiza a hankali tare da sake maidashi ta risinar. Cikin motsa laÉ“É“anta a hankali tace, “Wannan karamci abin alfaharine a gareni da nuna tsantsar godiya ga Uwa gareni dama Æ™asar Ruman baki É—aya. Sai dai ina mai neman afuwar jinkirtamin shan wannan madara sakamakon azumtar wannan yini da nakeyi batare da nasan yau zata kasance rana mafi daraja da alfarma a gareni ba”.
Kalaman Iffah da tasirinsu tamkar saÆ™ar Æ™udan zumace cikin kuttu a zukatan duk wani mai numfashi dake a wannan falo. A zahiri da baÉ—ini kuma babu wanda mamaki bai bayyana akan fuskarsa ba, saboda abune da bai taÉ“a faruwaba a cikin daular ruman. Malikat Bushirat tai Æ™yauta a jinkirta amsa tare da biyo jinkirin da sharhin da babu gargada akan harshen mai furtashi. Wannan abu yakai a kalla Iffah a sake kallonta dan ko Æ´aÆ´an gidajen sarauta goma cif da aka kawo daular a irin matsayinta basu samu Æ™warin gwiwar Æ™in shan irin wannan madara ba. Hasalima kowaccensu da rawar jiki take amsa ta shanye tas ta bada bowl É—in tana mai gurfana a gaban Malikat domin yin godiya. Ba’a matsayi kuma kawai ba hatta a shekaru Iffah itace mafi Æ™anÆ™anta a cikin Zawjata-almilki goma sha huÉ—u da aka kawo gidan.
Ɗaya daga cikin matance ta zabura idanunta dake nuna ɓacin rai akan Iffah. Sai dai abin mamaki Malikat Bushirat da idanunta ke kan Iffah ko ƙyaftawa babu ta ɗaga mata hannu alamar ta zauna tare da sakin wani ƙasaitaccen murmushi. Nuni tai akan a rufe madarar. Ruf aka maidata yanda take hadimar ta miƙe daga gaban Iffah da tunda ta sake maida kanta ta rissinar bata ƙara ko motsawa ba.
A karo na farko Malikat ta motsa laÉ“É“anta, cike da izza da Æ™asaita irin ta manyan masu mulki. “A kaita masaukinta”. Ƙasaitacciyar muryarta ta ratsa zuciyar Iffah tare da girgiza gaÉ“É“anta cikin ikon harbawar jini. Sunan ALLAH ta Æ™ara tsarkakewa a zuciyarta dan tabbas Malikat ta cika Malikat É—in babu tantama. Saboda muryar tata kanta barazanace ga duk mai yunÆ™urin kawoma girmanta wargi da saka tsantseni a zuciyar duk wani talaka dake a Æ™arÆ™ashin mulkinta.
“Ki huta lafiya, cikin aminci da farin ciki”.
Iffah ta faÉ—a cikin risinar da kanta alamar girmamawa lokacin da take miÆ™ewa bisa taimakon É—aya daga cikin matan nan. Yin hakan ya sake saka zukatansu a mamaki, ita kanta Malikat Bushirat da kallon Æ™asan ido ta bisu har suka fice. A Æ™asan ranta tana mai jin farin cikin samuwar Zawjata-almilki data dace da gudan jininta tilo kuma Shahan-shan na Æ™asar Ruman gaba É—aya. A ganinta lokacine daya dace tai yaÆ™i da maÆ™iyanta masu yaÆ™ar Zakinta a yanzu dake zagaye da su…..

★★Kamar yanda Malikat Bushirat ta bada umarni amarya Iffah (Zawjata-almilki) an isa da ita sashenta dake gab da sashen matan Tajwar Eshaan su biyu da har yau suke raye, sannan kuma kusa da katafaren sashen Tajwar Eshaan da yafi kowanne gini É—aukar hankali da kayan kyale-Æ™yale da tsagwaren dukiya a cikin Daular Ruman harma da tsantsar tsaro… Sashen Iffah ya kasance shima sashe dake É—auke da nau’in kayan more rayuwa da a kallo É—aya mai karatu zai tabbatar da sai dai Zawjata-almilki É—ince kawai kam ta dace da zama a cikinsa. Kamar yanda al’adar take anyi rakkiyar Iffah dake kan keken doki tare da busar sarewa mai daÉ—in saurare har zuwa sashen nata. Iya masu hurumin shiga kawai suka shiga har cikin bedroom da suka kira matsayin master bedroom nata. Sai dai suna fita ta miÆ™e daga zaman É—ofanar da tai a gefen gadon, cikin ambaton sunan ALLAH da zubar hawaye ta jaye hular alÆ™yabar ta ta Æ™arema É—akin kallo na tsahon mintuna uku. Komai batace ba ta É—auka akwatinta da aka shigo da shi ta fito a É—akin tare da jawo Æ™ofar. Bata wani tsaya kallon falon data fito ba, sai dai tabi kowace kusurwa na cikinsa domin lissafa adadin Æ™ofofin dake a cikin. Ƙofar da lissafinta ya tabbatar mata ta nufa, cikin É—an jimami da tausayin kai ta murÉ—a Æ™ofar mai kalar ruwan gold. ÆŠakin ta shiga bayan ta leÆ™a kanta cikinsa. Shima É—in dai a Æ™ayace yake da komai na alfarma. Sai dai komai nasa ya banbanta da kalar na wancan É—akin. Amma shima duk abinda ke cikinsa royal ne irin kayan da suka dace da gidan hamshaÆ™an masarautu kamar Daular Ruman. Ajiyar zuciya ta sauke bata samun nutsuwa ba, sai ta son rage nauyi mai danÆ™arewa a Æ™irji kawai har numfashi ya gaza samun damar fita yanda ake buÆ™ata. Jikkar ta ajiye tare da zama bakin gadon ta rushe da sabon kuka………✍

_To ko burin Malikat Bushirat zai cika kuwa? Kokuwa dai itama Iffah zata suÉ“ucema Æ™warin gwiwar tata tamkar Zawjata-almilki na baya da suka shuÉ—e ta hanyar kisan da har yanzu ba’a san wanene sanadinsa ba?. Idan Shahan-shan ne da kansa yaya Malikat zata kasance a wannan yaÆ™in kenan? Dan masu iya magana kance fa DAUÆŠAR GORA CIKI KA SHATA.._

*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*

*DAUDAR GORA Billyn abdul*

*KI KULANI hafsat xoxo*

*A RUBUCE TAKE Huguma*

*RUMBUN K’AYA Hafsat rano*

*IDON NERA Mamuh ghee*

_LITTAFI DAYA: 400_
_LITTAFI BIYU: 600_
_LITTAFI UKU: 800_
_LITTAFI HUDU :1000_
_LITTAFI BIYAR: 1200_

_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_

_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_

_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_

_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_

_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_

_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_

ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN

MARYAM SANI
ACCESS BANK
0022419171

SAI A TURA SHAIDAR BIYAN

09033181070

IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA

09166221261

*ƳAN ƘASAR NIGER. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*

+227 90165991

Books biyar 1250CFA
Books hudu 1050CFA
Books uku 850CFA
Books biyu 650CFA
Bookk daya 450CFA

KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.

MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.

 

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*

✨ÆŠ ✨
( )

 

 

Post a Comment

0 Comments