Daudar Gora Book 1 Page 14

Latest Posts

6/recent/ticker-posts

Ad Space

Daudar Gora Book 1 Page 14


14_*

 

………Wannan dare darene na tarihin da har abadan Iffah bazata taÉ“a mantawa da shi ba. Badan wani abu ya faru bayan wanda ya faruba, wanda ya farunne bazai taÉ“a zama shiÉ—aÉ—É—e a zuciyarta ba. Kwana É—aya tak ta kasance cikin É—imuwa da tsananin kewar ahalinta. Wanda ta riga ta gama sallamawa ta rabu dasu kenan har gaban abada. Sai dai bayan mutuwarta suzo jana’izarta batare da ko kan gawarta an barsu matsawa ba. Sam babu wani barci koda É“arawo da yaci galabar É—aukarta a wannan dare. Hakama abincin da aka biyo bayanta da shi na buÉ—a bakin azumin da tace batacisa ba. Kuka taci ta Æ™oshi har kusan rabawar dare kafin ta miÆ™e zuwa bayi tayo alwala ta nutsu gaba É—ayanta gaban UBANGIJIN talikai maji roÆ™on bayinsa. Duk da tsananin tsoro da take a ciki na kasancewa ita kaÉ—ai a katafaren sashen haka ta dinga jarumtar son dannewa a zahiri. Sai dai duk Æ™anÆ™antar motsi yakan saka zuciyarta harbawa da tunanin anzo kashetane.
Tana idar da sallar asubahi barci yafa ce ya shirya, dan duk yanda take faman turesa da son Æ™in yinsa sai da yakaita Æ™asa, dole takai kwance kan lafiyayyen kafet É—in dake gaban gadon kafin Æ™iftawar ido ta fara sauke numfashi….

Barci sosai Iffah tasha na tsahon lokaci mai tsayi da har sai da aka tadata ta fahimci hakan. Ƙyawawan idanunta dake cike da barci ta buÉ—e da Æ™yar akan matar dake tsaye a gabanta kanta a rissine. Babbar mace ce mai shekaru sosai, sai dai shigarta ta tabbatar da cewa ita É—in bakomai bace sai hadima a masarautar. Amma kuma da alama hadima ce mai babban muÆ™ami da matsayi….
“Barka da safiya ya Zawjata-almilki”.
Ta katse tunanin Iffah ta hanyar gaisheta. YunÆ™urawa tai ta tashi zaune idonta na a kanta, kanta ta gyaÉ—a da faÉ—in, “Mama ina kwana”. Dan shekarun girma na matar ya wuce ta zauna saita gaisheta. Sosai ta ga ruÉ—ewa da kiÉ—ima a idanun matar. Cikin yin waige-waige na tsoron kar wani yaji ta zube Æ™asa da rawar harshe. “Ranki ya daÉ—e na roÆ™eki dan ALLAH wannan sunan yabar fita a bakinki. Kece uwa a garemu, ke kika cancanta mu kira da sunan bani Æ™asÆ™antacciyar baiwa mai miki hidima ba. Sunana shine Diwa, zaki iya kiran Ama (baiwa), ni shugabar hadimai masu kula da tsaftar sashen Malikat ce. An kawo miki abin karin kumallone tare da wanda zasu shiryaki da hadiman da zasu kasance masu hidima a gareki”.
Idanu kawai Iffah ta tsura mata cike da tausayawa. Sai dai komai bata iya cewa ba ta kauda idanunta zuciyarta na ƙuna na raɗaɗin ƙasƙancin da su talakawan ruman ke fuskanta a ƙarƙashin waɗannan masarautu. Hadima Diwa miƙewa tai da sauri ta fita. Mintuna kaɗan sai gata ta dawo tare da wasu mata guda biyu.
“Ranki ya daÉ—e, waÉ—annan matan sune zasu shiryaki a yanzu”.
Yanzun ma iyakarta É—ago ido ta kallesu kawai, sai dai batayi musu ba wajen basu damar fara aikinsu. Amma a zuciyarta ta cigaba da yin addu’a sakamakon harbawa da Æ™irjinta keyi da sauri-sauri tamkar mai tsoron tunkarar wani abu. Tsaf suka kwance kitson dake kanta, dogon gashinta da mafi yawan Æ´an Æ™asar ta Ruman keda ya bayyana.
“ALLAH ya Æ™ara miÆ™i tsahon rai da lafiya, wannan lokacine na wanka”.
Komai Iffah batace musu ba ta miƙe, dan tanabin huɗubar Kaka ne daki-daki. Da zata shiga bayi dakatar da su tai daga ƙoƙarin binta da suke.
Hadima Diwa dake gurfane gefe tai saurin faÉ—in, “Ranki ya daÉ—e ki basu dama dan ALLAH, dan zasu nuna miki yanda zaki amfani da kayan wankan da aka shirya dominki a ciki, su kuma gyara miki kai kawai su fito”.
“Karki damu zanyi da kaina”.
Ta faÉ—a tana mai shigewa kafin ma ta sake cewa wani abu, sai dai bakinta É—auke yake da addu’a. Wani irin harbawa zuciyarta tayi, tareda sarawar kai lokacin da take sanya Æ™afa cikin toilet É—in sai kace ba dashi tai amfani ba da asubahi, yanzu kuma da su Diwa suka shikago sun gyarasa da ajiye kayan wankan da suka shigo da shi tare da matan, hannu takai saman kanta tana karanto addu’a bayan ta shiga toilet da tayi sannan ta Æ™arasa shiga. Shi kansa bayin abin kallone a yanzu fiye da É—azun, dan yanzu an Æ™awatashine da wasu irin fure da candles ta gefen jakuzzie É—in. Sai wasu nau’inkan ruwan turare da aka ajiye domin tai amfani da shi, sam zuciyarta taÆ™i aminta da hakan, atake ta dinga É—aga tasoshin da suke a ciki tana maidasu gefe guda ta hau wankanta tana mai zubda hawayen tausayin kanta dana iyayenta da batasan halin da suke ba a yanzun suma….

Koda ta fito da tunanin samun matan data bari sai taci karo da akasin haka. Domin kuwa wayam ɗakin babu kowa, sai ƙamshi mai daɗi na turaren wuta da aka ajiye ke tashi. Numfashi ta sauke a hankali, badan samun nutsuwa na abinda ke gudana ba. Sai dan samun sassaucin nauyin da zuciyarta tai mata. Kusan mintuna biyar da fitowarta ta gagara tsinana komai, hasalima bata san ta ina zata fara ba.
Knocking Æ™ofar da neman izinin shigowa ya sakata É—aga idanunta manya takai dubanta, kafin ta bada izinin shigowa tana mai janye idanun nata. Hadima Diwa ta shigo sallama kanta a Æ™asa, tun’a bakin Æ™ofa ta zube bisa gwiyawunta. Cike da tsantseni irin na tsakanin yaro da uban gidansa murya cike da rauni tace, “Ya Zawjata-almilki! Yanzu lokacine na shiryawarki da taimakon waÉ—an nan mata”. Ta Æ™are maganar da nuna bayanta.
Iffah dake saurarenta tare da zuba mata ido kallonta ta kai bayan nata, kamar zatai magana sai kuma ta fasa. Tai É—an shiru na wasu sakanni tamkar mai tunani kafin taja numfashi. “Ai zan iya shirya kaina su barshi kawai”.
Ƙasa Diwa ta sake yi da kanta da sake gurfana Æ™asa sosai. “Ki gafarceni ya Zawjata-almilki. An basu umarnine, saÉ“awa kuma a garesu tamkar bijirewa ne?”.
Tsantsar tausayinsu da takaici mai gimtse maƙoshi ya sake baibaye Iffah, ta nisa tare da haɗiye abinda ya tokare ƙirjinta tana mai jin-jina kai wa hadima Diwa kawai. Tamkar ƙyaftawar ido matan suka shigo su biyu. Suma dai kallonsu kawai Iffah take cike da tausaya wa. dan cike da girmamawa a gareta suka zube gwiyawunsu a ƙasa domin gaisuwa a gareta kasancewar bana ɗazun bane.
“Dan ALLAH ku miÆ™e”.
Ta faɗa cikin wani irin yanayi daya saka matan ɗan ɗagowa suka dubeta. Su ɗin ababen tausayine, amma sai sukaji itace suke tausayi fiye da kansu. Umarninta sukabi duk suka miƙe ɗin, suna maiji da kallonta da matuƙar girma a idanunsu duk da ƙanƙantar ta, dan kuwa itace mafi ƙarancin girma a cikin Zawjata-almilki da aka kawo daular ruman.

Sun mata shiri irin na Zawjata-almilki data isa a kirata da wannan sunan. Dan ƙwalliyar tata ta dace da halittar ƙyaƙyƙyawar surar jikinta da ƙyawunta. Ta cancanci a kirata Malikat Fareedah bayan Zawjata-almilki duk da ƙanƙantar shekarunta. Saboda duk da damuwar dake shimfiɗe a ƙyaƙyƙyawar fuskarta hakan bai hana bayyanar fitar kwalliyar ƙawata kwarjininta da cikar haiba ba. Su kansu hadiman dake zagaye da ita sai faman satar kallonta suke. Bawai dan tafi duk sauran Zawjata-almilki da suka shuɗe ƙyawu ba, kawai natan ya matuƙar ƙayatar dasu ne batare da sun san dalili ba. Ita a karan kanta kallon kanta take dajin tamkar ba ita ɗin bace, bawai dan ƙyale-ƙyalen gold da diamonds da aka ƙawata adon jikin nata da shi ba. Hasalima sune abu na farko da takejin tsantsenin gani a jikinta.
Hadima Diwa data sake neman izinin shigowa ta shigo a gabanta ta sake zubewa tana mai satar kallonta itama. Cikin jinjina girma irin na UBANGIJI mai halittar abinda yaso a yanda yaso ta isar da saÆ™onta kamar haka….
“Ya Zawjata-almilki! Yanzu shine lokacin karin kumallonki”.
Iffah da takurar ta fara gundurarta ta saurin tarar numfashinta, “Bana buÆ™atar cin komai nikam Mama”.

 

Post a Comment

0 Comments