Daudar Gora Book 1 Page 17

Latest Posts

6/recent/ticker-posts

Ad Space

Daudar Gora Book 1 Page 17


17_*

………..Dare yayi nisa, bakajin motsin kowa a daular ruman sai sassanyar iskar dake kaÉ—a bishiyoyi kaÉ—an-kaÉ—an. Sai kuma Hadiman da ake kira Ghazi a masarautar ne kawai ke faman kaikawo domin bada tsaro ta kowacce kusurwa ta gidan musamman a sashen Tajwar Eshaan.
Iffah dake kwance samÉ“al a katafaran gadon alfarma na Malikat Bushirat idanunta a rufe kai kace batama numfashine ta fara zabura a hankali kamar wadda ake mintsini. Jasrah ce kawai tare da ita a É—akin, tana daga gefe barci ya É—an figeta mai cike da wani irin mummunan mafarki. Wata gigitacciyar Æ™ara da Iffah ta fassa tare da girgizar data saka gadon shima rinÆ™a girgizawa yasa Jasrah farkawa a kiÉ—ime. Tsalle tai gefe jikinta na rawa ganin yanda Iffah da gadon ke girgiza, hatta shi kansa É—akin ji Jasrah keyi na mata rawa shida fitulun da suka haskesa, dan sai daukewa suke suna kawowa. Wani irin tari Iffah ta farayi mai tahowa da aman jini ta baka ta hancinta harda ta kunne. Jasrah ta fara Æ™wala kiran sunan Malikat Bushirat a matuÆ™ar firgice tana sake manne jikinta da bango hanunta na laluben Æ™ofa amma ta kasa buÉ—eta…
Malikat Bushirat da dama ba barci take ba saboda tsabar damuwa ta buÉ—e idanunta a hankali jin sautin muryar Jasrah tamkar a sararin samaniya tana yawo. Cigaba da jin sautin ya sata miÆ™ewa zaune ta sauka a gadon baki É—aya. Babu wani hadimi dake da damar shigowa sashen É—akunan barcinta sai masu gyarawa kawai suma da safe ne, hakan ya sata É—ora abaya kawai a saman kayan barcinta ta fito…. Jasrah da ta gama fita hayyacinta gaba É—aya ta faÉ—a jikin Malikat Bushirat, rungume Æ´ar uwar tata tayi, a hankali ta shiga hura mata iska a kunne tana bubbuga bayanta. Jasrah da Æ´ar nutsuwa ta fara zuwa mata tai lamo tana sauke numfarfashi a jajjere, sai kuma ta É—ago a hankali hawaye wanke da fuskarta…
“Mike faruwa?”.
Malikat ta faɗa a hankali. Ɗakin Jasrah tabi da kallo, kafin ta fara mata bayanin komai har yanzu hawayenta sun kasa tsayawa. Sosai hankalin Malikat ya ƙara tashi, sai dai kamewarta yasa ba lallai ka fahimta a kan fuskarta ba. Cikin takunta na ƙasaita ta isa gaban gadon inda Iffah take. Kwance take samɓal tamkar ba itace ta gama buge-buge ba yanzun. Idanu ta tsura mata a karan farko, yarinya ce ƙarama sosai kuma ƙyaƙyƙyawa matuƙa, duk da halin ciwo da take ciki da canjawar fatar jikinta ƙyawunta da kwarjininta basu gushe ba, tausayinta mai tsanani da ƙaunarta suka sake ratsa zuciyarta. Zaune ta kai gefen gadon ta kai hannu ta shafa yalwataccen gashin Iffah daya gama bajewa a kan filon.
“Ibnati kiyi haÆ™uri zaki samu lafiya bazasu taÉ“a samun galaba ba kinji”.
Iffah da sarai take jin maganar Malikat dan ba barci take ba azaba ce kawai ke ratsata tai murmushin Æ™arfin hali a zuciyarta, a karan farko taji Æ™aunar matar a ranta da sake ganin kima da girmanta…….

★★_______★★

“Sun jiÆ™a mana aiki! Sun É“ata mana shiri! Ya Æ™wace mana damarmu wadda sake samun samuwarta a garemu cikin sauÆ™i haka zata iya zame mana mai wahala!!”.
Kakkausar muryar Uwa mai matuÆ™ar rashin daÉ—in saurare ta fara karaÉ—e É—akin cikin amon sauti mai tashi sama. A firgice ta miÆ™e a zabure tare da zube gwuyawunta Æ™asa jikinta na tsuma dan dama zaune take ido biyu tana jiran tsammani. “A gafarce ni uwa ba laifina bane, ni kaina ina cikin damuwar tangarÉ—ar da aka samu”.
“Bana buÆ™atar jin komai daga gareki TaÆ™urya. Domin sakacinki ne ya jawo hakan. Nasha faÉ—a miki ki san suwa zaki bama aikin da ke bazaki iya yinsa kai tsaye ba. Su kuma waÉ—an can sakarkarun barinsu sukai wayewar gari tamkar rasa sauran damar data rage miki ne….”
ÆŠan zabura tayi da nufin cewa wani abu, sai dai tamkar walÆ™iya Uwa ta É“ace a É—akin. Hakan na nufin ranta a É“ace yake. Itama kanta ta dafe nata ran na suya da Æ™ara girmamar baÆ™in cikinta. Miyasa kowa bai bata matsala ba sai wannan Æ´ar shilar yarinyar da bata wuce sauron gidanta ba da feshi É—aya take kawar da shi. Zuciyarta ta fara raya mata Uwa kodai tsoron yarinyar nan takeyi, yo inba tsoro ba taya zata dinga wani gewaye-gewaye bayan bai wuce da Æ™yaftawar ido kawai ta shafe babin rayuwarta ba. Dama mutum na gagarar aljani ne banda ta fara maidata susu……

WASHE GARI..

Duk wanda ya kwana ya tashi a masarauta a yau ya tashi ne da tashin hankalin da yafi na jiya sakamakon mawuyacin yanayin da Iffah ta wayi gari. Dole tun gabatowar sallar asuba aka maidata cikin clinic É—in dake a masarautar saboda É“allewar jini ta kowane sashe na jikinta. Da farko aman jini ta fara, sai kuma ta hancinta, sai gashi ta ido da kunne harda ma ramin cibiyarta. Hankalin Jasrah da Malikat dake tare da ita ya kai matuÆ™ar Æ™ololuwar tashi. Duk da kowa yasan ciwo ne bana asibiti ba haka likitoci suka rufu a kanta domin Æ™oÆ™arin ganin sun tsaida jinin amma abu na neman gagara. Har kusan goma na safe a gogon Æ™asar babu wani cigaba, jikin Iffah ma ya fara saki alamar jininta yayi Æ™asa matuÆ™a….

★★…

“Bari-Hamshira! Inaga ya kamata a bama masu maganin dake waje dama suma suzo su gwada sa’arsu tunda ba’a dace dana cikin masarauta ba.”
Malikat da damuwar duniya ta tattaro a kanta yau ko fadarta bata iya fitaba tana cikin É—akin barcinta har zuwa yanzu ta É—ago idanunta dake jajur ta sauke akan Æ™anwarta ta uku mai suna Zaimah, cikin nuna sallamawa ta jinjina kanta. “Wannan ma shawara ce mai Æ™yau Akia, ruÉ—ewa tasa sam wannan tunanin bai zomin ba. A sanar da Ghazi su faÉ—ama Baba Yaro. Sai dai komai ya kasance cikin sirri da amana dan kar maÆ™iyanmu suyi amfani da wannan damar wajen ruguza É—an sauran Æ™warin gwiwar mu akan wannan yarinya”.
Kai Zaimah ta jinjina mata, sai kuma ta miÆ™e da hanzari domin isar da umarnin…..

*_ƘAUYEN JUMNA_*

Tafiya saurayin yake tamkar zai tashi sama dan gaggawa, wani lokacin har tuntuɓe yakanci sai dai kafin ya kai ƙasa yay azamar taro kansa ta hanyar dafe duk abinda ke kusa da shi. Wurjanjan ya isa ƙofar gidan Dattijon da kowa yafi sani da suna Abu Huzaifah ya kwaɗa sallama da iya ƙarfin muryarsa har sau huɗu babu ko jiran a amsa masa.
Dattijo Abu Huzaifah Da mukafi sani da Kaka ya dakata da ga É—inkin kwalliyar doki daya duÆ™ufa yi ya dago suka kalla juna da Iyyani dake shara a tsakar gidan. “Kamarfa sallama naji Abu Jamaima a Æ™ofar gidan nan”
KafaÉ—a yaÉ—an rausayar gefe da ajiye zungureriyar allurar da yake É—inkin da ita. Kafin ya ce wani abu aka Æ™ara zungura sallamar a jajjere tamkar yaÆ™i. Kansa ya Æ™ara jijjigawa ya miÆ™e dajan tsaki. “Kai wasu dai mutanen sam basu da lissafi, irin wannan ai saka É—auka tashin hankali ne”. Kaka ya faÉ—a cikin mita yana gyara takalmansa. Iyyani da takaici ya Æ™ulle itama ta bisa da kallo harya fice a soron gidan…
“Ayyub! dama kai ne kake Æ™waÉ—a irin wannan sallama haka? Lafiya dai ko?”.
“Da sauÆ™i dai Baba, amma amin afuwa bani da wani zaÉ“i bayan hakan. SaÆ™one daga Baba yaro”. Ya Æ™are maganar da miÆ™ama Kaka takardar hanunsa. Kaka ya amsa takardar yana É—an juyata, sai kuma ya nuna hanyar shiga da faÉ—in, “Kaga shigo daga ciki”.
A tare suka shiga cikin gidan, Kaka ya buÉ—e takarda yana dubawa, yayinda Iyyani ta kawoma baÆ™o dake gaisheta ruwa. Kaka ya É—an murmusa bayan gama karanta takarda tare da girgiza kansa. “Ayyub naga saÆ™o, sai dai kuma inaga basai naje da kaina ba. Zan baka saÆ™o ka kai masa nima. Ita kuma ALLAH ya bata lafiya yasa ya zama kaffara a gareta”.
ÆŠan jimm Ayyub yayi, sai dai kafin yace wani abu Kaka ya miÆ™e. ÆŠakinsa ya shiga, kusan mintuna ashirin sai gashi ya fito da wata jakkar fata. “Kayi maza ka kai masa wannan. Kace kuma ina gaishesa”.
Cike da girmamawa Ayyub ya amsa da faÉ—in “Angama Baba. A huta lafiya”. Kai kawai Kaka ya jinjina masa yana murmushi. Sai da ya rakasa har Æ™ofar gida sannan ya dawo. Iyyani da duk ta shiga damuwa ko zama baiyiba ta jeho masa tambaya, dan tasan ma’anar wannan murmushin nasa bana farin ciki bane, yakan yisane a lokacin da wani abu ke masa Æ™una a zuciya.
“Itama sun taÉ“ata ko?”.
Bai bata amsa ba sai da ya zauna. Ya jawo allurarsa zai cigaba da É—inkinsa. “Dama ai bazasu barta haka ba saboda wasu dalilai”.
“Dalilai kuma? Nami to?”.
“Kinga sarkin tambaya bani zaren cen dana manta kan bunu”.
Iyyani tasan tambayarce baya son amsa mata, dan haka taja bakinta tai shiru bayan ta kawo masa zaren. Sai dai sam zuciyarta babu nutsuwa……

★★.MASARAUTA.★★

Bayan sallar azhar Ayyub ya iso masarauta. Zuwa yanzun har an fara raɗe raɗin mutuwar Iffah, duk da kuwa ya tadda masu maganin da suka isa suka tumbatsa da matuƙar yawa an tarasu kowa nata gwada ƙoƙarinsa da baiwar da ALLAH ya basa.
Baba Yayaroya furzar da nannauyan numfashi bayan ya amshi saÆ™on kaka a hanun Ayyub “Dama nasan da wuya Dattijo ya zo”.
“Amma duk da haka ka aika masa Baba?”.
“Ya cancanci a aika masan”.
“To amma miyasa yaÆ™i zuwa? Bayan kuma alamu sun nuna kai tsaye ma yasan abinda ke faruwa anan É—in”.
Baba ya tsurama É—an nasa ido na wasu sakanni, sai kuma ya girgiza kansa. “Ba lallai sani irin wanda kake tunani yayi ba. Dan nidai nasan baida wata alaÆ™a da abinda ke faruwa anan. Sai dai ya sani ta dalilin baiwar da ALLAH ya masa duk da shi yana gudunta ne”.
“Amma Baba….”
“Kaga Ayyub wannan ba lokacin tambayoyi bane. Bara naje muga ko za’a dace anan.”
Da kallo Ayyub yabi mahaifin nasa. Sai dai Æ™asan ransa fal tambayoyine da yasan samun amsarsu zaiyi wuya a lokacin da yake buÆ™ata. Yasan mahaifinsa gawurtaccen masanin magani ne irin na gargajiya dama na gusar da junnu. Shahararsa tasa Daular Ruman É—aukarsa da bashi matsayin (Mai magani a gonar yaro) amma ya rasa minene dalilinsa na bama wancan dattijon girma mai tsanani duk da shi kowa bai sanshi ba sai da sunan mai É—inka kayan doki…..

*_ZAWJATA-ALMILKI_*

Zuwa yanzu numfashin Iffah ma yana fitane da taimakon na’urori, yayinda jinin dake fita a jikinta har yanzu yake fita ta kunenta. Na ido da hanci da baki ne kawai likitoci suka samu nasarar tsaidawa. Baba yaro shine shugaba na masu maganin, dan haka ake basa damar shiga kai maganin da duk aka bayar dan ai mata amma da taimakon Jasrah kai tsaye. Yanzu É—inma dai hakance ta kasance. Bayan neman iso aka bashi iznin shiga inda Iffah take, sai dai babu mai iya ganinta kasancewar zagaye take da glass…..

*_SHAHAN-SHAN_*

Bani kaÉ—ai ba, nasan duk masu karatu tambayarsu zata rinjayane akan wai shin duk abin nan dake faruwa ina _Shahan-shan_ yake ne a matsayinsa na shugaba ga Æ™asar ruman baki É—aya bama daular ruman ba?. To amsar itace yana nan a cikin masarautar, sai dai kuma tun a yammacin jiya bayan dawowa daga sallar juma’a babu wanda ya sakejin motsinsa. Duk da dama fitarsa a zahiri ta zuwa massallaci ce kawai. Yana kuma da Æ™ofar dake kaisa har massallaci daga sashensa batare daya fito wani ya gansa kai tsaye a masarautar ba. Shiyyasa har zuwa yanzu wanda suka san fuskarsa ko’a cikin masarautar ma Æ™alilanne musamman a cikin hadimai. Duk abinda ke faruwa a masarautar kuma kowa nada yaÆ™inin ya sani, sai dai ba’an miyasa ya zaÉ“i yin shiru ba.
Kamar jiya yau ma labari yajema Malikat Bushirat akan Shahan-shan bai fito sallaba har ta asubahi. A yanzu kam hankalinta ya tashi ba kamar a jiya ba data É—auka dan yana fushi da auren da yaso bijiremawa ne. A take ta bada umarnin shirya mata zama da shi. Dan ita a karan kanta na uwa garesa bata da hurumin ganinsa a duk sanda taso ko kai tsaye bisa doka da al’adar masarauta da Æ™arfin iko na Shahan-shan. Sai zuwa É—aya tak na kowanne wata da yakanyi kawai na zahiri. Amma duk da haka Tajwar Eshaan kan saci jiki wani lokacin ya kawo mata ziyarar tsakkiyar dare cikin É“adda kama batare da wani ya taÉ“a fahimtaba har yanzu a cikin masarautar.
Shiri ta farayi duk da batada tabbacin samun damar ganin nasa a yanzu, sai dai sanin duk Æ´an majalissar fada na’a masarautar yau yasa bata fidda tsammani ba. Cikin sa’a kuwa cikin abinda baifi mintuna ashirin ba Ghazi ya zo ya isar mata da sakon Æ™arÉ“uwar buÆ™atarta. Dan dama suma Æ´an majalisar fadan nada buÆ™atar samun wanda zai duba shi, hakan kuma bamai yuwuwa bane dan ita dake amsa suna mahaifiyarsa da Malikat Haseena (Kakarsa) da matansa ne kawai ke da wannan hurumin saboda an tabbatar tun jiya baiko zo falo na uku ba. Sannan duk abincin da mai dafa masa ya shirya tun daga kan na daren jiya har safiyar yau da rana haka yake zuwa ya kwashesa ba’a taÉ“a ba.
Cikin shiri na alfarma da rakkiyar tawagar hadimai maza da mata Malikat Bushirat ta doshi sashen Tajwar Eshaan ibn Haysam Abdull-majeed………✍

*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*

*DAUDAR GORA Billyn abdul*

*KI KULANI hafsat xoxo*

*A RUBUCE TAKE Huguma*

*RUMBUN K’AYA Hafsat rano*

*IDON NERA Mamuh ghee*

_LITTAFI DAYA: 400_
_LITTAFI BIYU: 600_
_LITTAFI UKU: 800_
_LITTAFI HUDU :1000_
_LITTAFI BIYAR: 1200_

_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_

_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_

_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_

_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_

_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_

_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_

ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN

MARYAM SANI
ACCESS BANK
0022419171

SAI A TURA SHAIDAR BIYAN

09033181070

IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA

09166221261

*ƳAN ƘASAR NIGER. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*

+227 90165991

Books biyar 1250CFA
Books hudu 1050CFA
Books uku 850CFA
Books biyu 650CFA
Bookk daya 450CFA

KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.

MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.

 

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*

✨ÆŠ ✨
( )

 

 

Post a Comment

0 Comments