Daudar Gora Book 1 Page 19

Latest Posts

6/recent/ticker-posts

Ad Space

Daudar Gora Book 1 Page 19


19_*

……….Shigar Malikat Bushirat sashen Tajwar da yanayin data fito ya sake zama wasu Æ™ananun maganganu a masarautar, musamman ga masu ikon faÉ—a aji. Dan ta ko’ina suna da masu leÆ™en asiri a cikin hadimai da masu tsaron gidan kamar yanda itama Malikat É—in ke dasu a kowanne sashe. Ga hadimai dai babu damar yin faÉ—a da kuwwa sai Æ´ar Æ™us-Æ™us, Æ™us-Æ™us É—in ma sai ka samu wanda kafi yarda da shi kuÉ—an zanta gudun karka faÉ—a tarko.

★★……

Tun barowarta sashen Tajwar ta kasa zaune ta kasa tsaye. Abubuwane birjik ke faman mata kaikawo a zuciya. A karo na farko kenan da zuciyarta ta fara rawa akan al’amarin dake faruwa tun daga randa aka É—ora tilon É—anta karagar mulkin kujerar Shahan-shan. Anya kuwa ba’akwai lauje cikin naÉ—i ba a wannan al’amarin?. Sannan ba zaton wuta a maÆ™era sukema komai ba alhalin yana a masaÆ™a?. Ta rumtse idanunta da sukai matuÆ™ar ja da Æ™arfi, saboda zuciyarta ke hasaso abun, amma Æ™irjinta ne keci da wutar Æ™unar dangantashi da abinda tafi so fiye da komai a duniya. Sai dai ya zatai, hakan kamar dole ne a gareta kodan rashin samun wani bakin zare har yanzu….
Kalmar bakin zare data faÉ—o a tunaninta ce ta sata buÉ—e idanu da sauri, sai kuma ta jawo É—aya daga cikin wayoyinta da dan tsumar jiki tana gyara zama. Danne-danne tai tare da kaiwa kunnemta. Daga can akai sallama tun kafin ita tayi. A taÆ™aice ta amsa da faÉ—in, “Jasrah ina buÆ™atar hadiman nan yanzun nan”.
“An gama Akia”.
Jasrah ta amsa mata da girmamawa. Mikewa tai itama ta hau shirin fita fadarta. Sai dai komai tana yinsa ne a tsanake amma yanayinta tattare da matsananciyar damuwa. Fitowarta dai-dai da shigowar Ghazi, ya zube ƙasa yana mai miƙa gaisuwa a gareta. Hannu kawai ta daga masa bayan ta kai zaune. Jasrah ma dake zaman jiran fitowar tata tai mata sannu da fitowa. Kai ta jinjina mata da maida hankalinta ga Ghazi dake gurfane kansa a risine. Itama Jasrah hankalinta ta maida kansa.
“Ghazi ya naganka kai É—aya?”.
“Ranki ya daÉ—e an samu matsala ne”.
“Matsala kuma? Kamar ya kenan?”.
ÆŠan jimm yay na jimamin faÉ—ar abinda ke bakinsa. Sanin Malikat Bushirat bata buÆ™atar kawane-kwane a magana ya sashi girgiza kansa idanunsa na canja kala zuwa ja sosai. “Ranki ya daÉ—e gawar uku daga cikinsu kawai muka samu, tare da hadiman dake tsaron inda aka killace sun su duka biyun. Diwa da ta rage ma bana zaton zata kai labari, kuma da alama yanzu-yanzu aka aikata ta hanyar madarar da aka basu matsayin abincin rana.
Ba Æ™aramar zabura Jasrah tai ba, yayinda Malikat ta rumtse idanu da sauri Æ™irjinta yay wata irin harbawa da Æ™arfi tamkar zai buÉ—e dan firgici. Amma a zahiri miskilancinta da Æ™asaitar mulki bazai taÉ“a haska maka komai ba daga yanayin nata…..

★Kamar yanda labarin mutuwar hadiman nan ya isa kunnen Malikat Bushirat haka ya karaÉ—e kunen kowa a masarautar. Yayinda likitoci suka rufu akan Diwa da itama gab take da rasa tata rayuwar. Wasu kuma sun duÆ™ufa ne akan binciken madarar da suka sha ta Æ™arshe duk da kowa ya san daga cikinta ne akama zuba musu ko minene…….

*_ZAWJATA-ALMILKI_*

Yayinda ake tsaka da jimamin rasa hadiman da sukai sanadin shigar Iffah a mawuyacin halin da take ciki, ita kuma waraka ALLAH ya saukar a gareta bayan duƙufar Baba yaro akanta da maganin da aka amso a wajen Kaka. Tun a mata hayaƙin farko jinin dake fita a jikinta ya tsaya. Hakan ya basu hope ɗin cigaba da bin dokokin da kaka ya kafa na maganin daki-daki har ALLAH yasa aka dace ta kawo wani nannauyan numfashi da ambaton sunan ALLAH.
“Ruwa!”.
Shine abinda ta ambata na biyu. Cikin sauri Daneen Ammarah Æ™anwa ta biyu ga marigayi Tajwar Haysam da ayanzu ke tare da ita ta zabura da kanta ta É—auka É—aya daga cikin bottle water dake a É—akin ta É“alle murfin ta kafa mata a baki. Cikin mawuyacin hali Iffah take zuÆ™ar ruwar, sai dai kasancewar shine abinda tafi buÆ™ata a Æ™anÆ™anin lokaci ta shanye sa tas. Yumma da itama dai uwa ce gasu Daneen Ammarah É—in, sannan matsayin Kaka ga Tajwar Eshaan dan Æ™anwace ga Malikat Haseena ta sake É“alle wani ta zuba a hanunta ta shafa a goshin Iffah dake jiÆ™e sharkaf da gumi. Ajiyar zuciya ta sake ja a hankali tare da buÉ—e idanunta da sukai mata matuÆ™ar nauyi. KaÉ—an ta buÉ—e ta maida ta rufe. Alhmdllh suka shiga ambata da mata sannu, yayinda Daneen Ammarah cike da zumuÉ—i tai kiran Malikat Bushirat. Ita ta fara sanar mawa kafin mahaifiyarsu Malikat Haseena duk da tana cikin halin ciwon Æ™afa da bata iya ko miÆ™ewa sai da taimakon wheelchair dama ga tsufa…..
Cikin abinda baifi mintuna goma ba ɗakin da Iffah ke kwance ya cika da wasu a manyan masarauta. A fuska dai suna nuna farin cikin farkawar tata ne, amma a ƙasan zuciya mafi yawansu kowa da irin tasa manufar. Malikat Bushirat kuwa harda hawayen farin cikinta, farkawar yarinyar da a kallon farko ta gama shiga ranta ya goge mata sauran damuwar abinda ya faru game da kashe Hadiman da aka aika suka aikata sherin daya jawo komai. A take Malikat Bushirat ta bada ƙyauta mai tsoka ga Baba yaro. Hakama wasu a cikin manyan sun masa ƙyautar. Daneen Ammara ce ta biyu, itama kuma ta bada mai tsoka daya bama kowa mamaki.
Ana Æ™oÆ™ari daukar Iffah zuwa sashen Malikat Bushirat kamar yanda ta buÆ™ata sai ga saÆ™o da ga Malikat Haseena cewar akai Zawjata-almilki sashenta. Take fuskokin mutane da yawa ya canja a wajen, saÉ“anin ta Malikat Bushirat data nuna tsantsar farin ciki da jin Æ™aunar surukar tata. Dan dama zuciyarta cike take da fargabar sake kasancewar Iffah babu tsaro. Duk da sashenta ma bazai iya zama kanwar lasa ba ga wani mahaluki a zahiri, sai dai yaÆ™in sunÆ™uru. To amma idan ta danganta da abinda zuciyarta ke rawa a kai komawar Iffah sashenta kamar an gudu ba’a tsira bane. Sashen Malikat Haseena kuwa sunyi imanin ko ifiritu da kansa zaiji tsoron gittawa kai tsaye balle wani shiryayye dake a masarautar….
Rashin Æ™arfin jiki da rashin dai-daiton tunani yasa Iffah ba fahimtar komai take ba, hasalima tun yunÆ™urin farko bata sake gwada buÉ—e idanunta ba suna a lumshe. Sai dai tana jin komai dake gudana har É—aukarta da akai akan keken asibitin zuwa waje. A mota a ka sakata Daneen Ammarah tare da ita. Sai Malikat Bushirat da tabi bayansu a tata motar da ake tuÆ™ata. Ganin haka sauran Æ´an son ganin Æ™waf suma duk suka bisu can dan babu mai fatar yin laifi ga Malikat Haseena…….

*_GIDAN BABIY_*

Tun bayan barin Iffah gidan É—an sauran kakkaÉ“in farin ciki da Æ™warin gwiwar da su Fareeha suka barsu da shi ya ida kakkaÉ“ewa. Ummu bata da aiki sai kuka. A kwana uku kawai duk ta rame saboda ko abinci bata ci yanda ya kamata. Hanash kam ba’a magana dan makamancin irin ciwon Iffah na damuwa ne ke neman bugarsa (Depression). Shi kansa Babiy dake dauriya duk ya zuÆ™e a tsaye wani lokaci har yi yake kamar zai faÉ—i. Komai ya tsaya musu cak, kunnuwansu ne kawai a buÉ—e na jiran kiran jana’izar tilon Æ´arsu mace data rage. Dan gushewar kwana uku bai sa sun saka ran ta tsallake ba. Suna tsaka da wannan zaman jigum-jigum akai sallama da Babiy Æ™ofar gida. Kamar bazai fita ba sai kuma ya miÆ™e cikin Æ™arfin hali ya zura takalma ya fita. ÆŠan turus yayi idanunsa kafe akan wanda yay sallamar da shi… Abu Moosa da shima ke kallonsa ya iso gabansa da Æ™yar yana tangaÉ—i. RiÆ™esa Babiy yay da sauri da faÉ—in, “Subahanallahi Abu Moosa!”.
Bai iya ya amsa masa ba saboda halin da yake ciki. RiÆ™esa da Æ™yau Babiy yay suka shiga ciki yana jera masa sannu. Zai zaunar da shi a soro ya girgiza masa kai cike da Æ™arfin hali. “Kamin alfarma mu shiga ciki”. Ya faÉ—a da Æ™yar tamkar numfashinsa zai rabu da gangar jikinsa. Cikin sauri Babiy ya cigaba da riÆ™esa suka shiga cikin gidan, shigowarsu yasa Ummu miÆ™ewa da sauri ta É—akko tabarma ta shimfiÉ—a a Æ™asan bishiyar dake tsakar gidan…
“Ku bani ruwa dan ALLAH”.
Abu Moosa Ya sake faÉ—a da Æ™yar yana fisgar numfashi. Ruwan Ummu ta kawo masa, dai-dai da fitowar Hanash daga É—aki saboda jin maganganu na tashi a gidan nasu. Da Æ™yar ya iya maÆ™warwa uku saboda numfashinsa fisga yake. Babiy ya ajiye ruwan da sake tallafosa jikinsa. “Abu Moosa mike faruwa ne haka? Daga ina kake?”.
Da Æ™yar ya iya É—aga idanunsa dake zubar da hawaye ya kalla Babiy. Sai kuma ya girgiza kan yana jan numfashi da shashsheka. “Abu Hanash ka gafarceni dan ALLAH, nasan wannan yana cikin numfashin bankwana da nakeyi”.
“Babu abinda kamun nikam, dan ALLAH kuma ka daina faÉ—ar wannan magana bara mu kaika asibiti”. RiÆ™o hanun Babiy dake yunÆ™urin tashi yay yana girgiza masa kai da Æ™yar. “Babu buÆ™atar hakan, domin ban cancanci kwatankwacin wannan adalcin daga gareka ba, kayi haÆ™uri ka zauna ka saurari abinda zan faÉ—a maka da yafi kaini asibiti muhimmanci, nasan kuma insha ALLAHU zai maka amfani da kuÉ“utar da yarinyarka dama sauran yaran da zasu iya biyo baya a makamancin halin data tsinci kanta”. Numfashin dake neman kufce masa yaja da Æ™yar kafin ya cigaba da faÉ—in, “Abu Hanash ka gafarce ni nine nai sanadin shigar Æ´aÆ´anka wannan halin, dan nine nai shunensu ga masarauta”. Da ga Babiy har Ummu da Hanash wani irin zabura sukai mai bugawa da bugun Æ™irji. Ya cigaba da faÉ—in, “Nayi hakane dan son zuciya da shegen son abin duniya. Sai hassadarka data daÉ—e a zuciyata saboda sana’armu ta kasance iri É—aya, ada tare ake amsar zumar mu a masarauta amma daga baya aka koma amsar taka kawai saboda gaskiyarka da rashin algus. Maimakon na gyara nima na zama mutumin kirki kamarka sai na kasa hakan, shaiÉ—an ya dinga tunzurani akan kayi sammu ne shiyyasa. Tun daga wancan lokaci naketa Æ™ulla hanyoyin ganin bayanka a matsayin É—aukar fansa, sai dai duk wadda na Æ™ulla sai ALLAH ya kuÉ“utar da kai, hakan ya cigaba da Æ™aramin tsanarka, dan haka na cigaba da kutsa kaina cikin masarauta dan kawai naga na É“ataka an wulaÆ™antaka, nan ma banci nasara ba dai. Kwatsam sai aka samu canji gwamnati, ni kuma nai amfani da wannan dama wajen sake cusa kaina cikin tsakkiyar masarauta harna samu nasarar amsuwa, nasan komai game da mutuwar Zawjata-almilki, dan ina gaba-gaba a hadiman da ke aiki ga masu aikatawar”. Yaja numfashinsa da ke fisga da Æ™yar. “Lokacin da aka sakamu aikin binciken yara mata guda biyu masu hankali dan a aurama Tajwar naji a raina lokacin nasarata a kanka ya yi, dan haka na bada sunanka da adireshin gidanka. An É—auka tsahon kwanaki ana bibiyar yaranka da kai kanka kafin azo gareka. Ko bayan mutuwar ta farko ni na Æ™ara Æ™ulla aka sake dawowa ta biyu dan burina kawai naga na durÆ™usar da kai Æ™asa. Ka gafarceni Abu Hanash dan nayi nasara, sai dai ramin muguntar dana gina daga Æ™arshe ni na afka ciki……”
Babiy da hawaye suka gama wanke masa fuska ya share yana duban Abu Moosa “Kenan kai ne ka Æ™ulla na uku ma?”.
“Wlhy a’a bani da alaÆ™a da wannan, hasalima ban san Æ´ar wajenka bace sai ranar da aka kawo kuÉ—in aure”.
“Waye ya kashe min Æ´aÆ´a? Kai kuma miya faru da kai?”…….✍

Ikon ALLAH, wannan duniya ina zaki kaimu, baka damu da kowa ba amma kana barcine da rashin barcin wasu, kana ci ne da rashin cin abincin wasu. Kana numfashi ne da burin ƙaruwar na wasu. Kana farin ciki da gushewar farin cikin wasu. Kana shiga tarkon wahala da dariyar bakunan wasu. Ya ALLAHU ka ɗoramu akan maƙiyammu, ka hanemu yin hassada da zaluntar wani koda ace shi ɗin ya zaluncemu. ALLAH sarki Babiy namu

*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*

*DAUDAR GORA Billyn abdul*

*KI KULANI hafsat xoxo*

*A RUBUCE TAKE Huguma*

*RUMBUN K’AYA Hafsat rano*

*IDON NERA Mamuh ghee*

_LITTAFI DAYA: 400_
_LITTAFI BIYU: 600_
_LITTAFI UKU: 800_
_LITTAFI HUDU :1000_
_LITTAFI BIYAR: 1200_

_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_

_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_

_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_

_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_

_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_

_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_

ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN

MARYAM SANI
ACCESS BANK
0022419171

SAI A TURA SHAIDAR BIYAN

09033181070

IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA

09166221261

*ƳAN ƘASAR NIGER. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*

+227 90165991

Books biyar 1250CFA
Books hudu 1050CFA
Books uku 850CFA
Books biyu 650CFA
Bookk daya 450CFA

KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.

MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*

✨ÆŠ ✨
( )

Post a Comment

0 Comments