Daudar Gora Book 1 Page 2

Latest Posts

6/recent/ticker-posts

Ad Space

Daudar Gora Book 1 Page 2


_2_*

………..Cikin Æ™arfin hali Babiy ya zabura hanyar soro domin dubawa duk da halin ciwo da yake ciki. Baya yaja da sauri saboda cin karo da suka kusayi da tawagar jama’ar Daular Ruman dake Æ™oÆ™arin shigowa suma. Kansa ya rissinar alamar girmamawa a garesu. Hanash da Ummu ma a kusan tare suka zabura. Cike da girmamawa mai haÉ—e da matsanancin tsoro Babiy ya zube bisa gwuyawunsa. Hakan da su Ummu sukaga yayi ya sasu zubewar suma tare da risinar da kawunansu, jikkunansu na matuÆ™ar tsuma dan abune da ba’a taÉ“a gani kojin labarin faruwarsa a tarihin Æ™asar Ruman ba. Babban mutum dake jagorantar tawagar ya tsaida idanunsa akan Babiy. “Ya kai wannan talaka dake a Æ™arÆ™ashin mulkin daular ruman, munzo da babbar magana ne gareka bisa umarnin daular ruman”.
Ƙasa Babiy ya Æ™arayi da kansa, tare da haÉ—e hannayensa waje guda. “Ina mai matuÆ™ar farin cikin ganinku tare dani, ni mai biyayyane ga kowanne umarninku”.
Duk da maganar Babiy ta musu daɗi babu alamar hakan a fuskokinsu. Ya miƙe cikin rawar jiki zuwa ɗakin Ummu. Mintuna kaɗan ya dawo da babbar tabarma sabuwa ƙal data saya domin auren Arfa zai shimfiɗa a gabansu. Dakatar da shi Shugaban tawagar tasu yayi cikin ɗaga hannu.
*_“Munzo nan ne domin isar da saÆ™o ba zama ba ya kai wannan talaka dake a Æ™arÆ™ashin daular ruman. Umarni a gareka daga daular ruman, taga iri a gidanka kuma tana buÆ™ata. Muna mai tayaka farin cikin zama É—aya daga cikin surukan tarihin daular ruman”_*.
A matuƙar firgice Babiy da iyalansa duka suka ɗago cikin zabura da matasanancin rikicewa. Sai dai basu da ikon koda motsa bakunansu balle neman ƙarin bayani. Kasancewar ba amsa dama suke buƙata ba mutumin ya janye idanunsa daga Babiy ya maida kansu Arfa da suka ƙanƙame hannayen junansu.
“Wacece babba a cikinku?!”.
Kalamai huÉ—u masu Æ™arfin razani da neman fasa zukatan mai saurare da har abada bazasu bar amsa sauti cikin zuciya da É“argonsu ba suka fita daga bakin É—aya daga firÉ—a-firÉ—an samudawan dake zagaye da mutumin. Babu wanda ya iya motsawa a cikinsu, dan kuwa sake dulmiya suke a cikin duhuwa…..
Saukar sautin wata zabgegiyar bulala mai adon jikin zakanya a jikinta ya sakasu zallo baki ɗaya. Babiy ya zube a ƙasa saboda azaba na raɗaɗin shigar wannan bahaguwar bulala a jikinsa, ganin basamuden mutumin dake riƙe da bulalar ya sake ɗagawa zai zuba masa Arfa ta miƙe tana mai fashewa da kuka jikinta na karkarwa tace..
“Nice!”.
Cikin daka tsawa basamuden hadimin yaba Fariha da Iffah umarnin suma su É—ago. ÆŠagowa sukai jikkunansu na karkarwa ga hawayen tausayin mahaifinsu ya wanke musu fuskoki. Idanu ya zuba musu kusan na sakan goma, kafin ya janye ya maida ga shugaban tawagar tasu…. “Zancenta nakan gaskiya ALLAH ya Æ™ara maka lafiya”. ya faÉ—a cikin girmamawa ga shugaban tawagar tasu. Shugaban ya gyaÉ—a kansa shima idanunsa akan Arfa “Mahaifinta da É—an uwanta zasu zama waliyyanta”.
Ya faÉ—a cike da cika umarni yana mai nufar hanyar fita batare da wani Æ™arin bayani ba……

Har aka tafi da Hanash da Babiy babu abinda su Fariha suka fahimta, balle ma Iffah da kallon kowa kawai take. Kukan Ummu ne ya dawo da su hankalinsu, gaba É—ayansu sukai kanta. Ummu dake kuka kamar ranta zai fita ta haÉ—asu su duka ukun ta rungume jikinta na wani irin rawa……

★★_______★★

Tafiyarsu da kamar awanni uku Babiy da Hanash suka dawo gida da doki É—aya da tarin kayayyaki, sai rakuma guda uku. Fuskokinsu cike suke da firgici mai tsayawa a zukatan masu kallo. Ba abinda sukazo da shi bane a gabansu Ummu, burinsu susan mike faruwa? Kawai. Basu samu amsa ba daga garesu har bayan shuÉ—ewar wasu awanni, kafin Babiy ya basu amsa cikin dakewa….
“Na bada aurenta ga *_Shahan-shan_*, bamu baro ba sai da aka É—aura musu aure, wannan raÆ™uman da dokin sadakinta ne”. Ya Æ™are maganar idonsa akan Arfa.
Tamkar saukar aradu mai tarnatsa haka furucin ya isa cikin kunnuwansu, Ummu tai baya zata faÉ—i Babiy ya riÆ™ota, kansa yake girgiza mata alamar kartace komai, suma yaran ya juyo garesu yay musu nuni da shiru ya jata suka shige É—aki. Umarnin mahaifinsu shine mafi girman biyayyarsu garesa matsayinsu na waÉ—anda ke rayuwa a Æ™arÆ™ashinsa, badan sun so ba suka zaÉ“i shiru, sai dai shirun nasu bai hanasu haÉ—e kai a É—aki suyi kuka ba su ukun. Kuka irin wanda za’a kira kuka a duk idaniyar da zubar hawaye ke kwaranya na rashin lissafin Æ™ididdiga. Mintuna sun shuÉ—e, hakama awannin da suka Æ™arasa kalmashe wannan yinin. Bayan sallar magrib saiga motoci da tawagar hadimai tare da wasu hamshaÆ™an mata huÉ—u wai sunzo É—aukar Amarya Arfa. Kuka suke tamkar ransu zai fita, haka sunaji suna gani suda iyayensu aka shirya Arfa cikin shiga ta alfarma aka wuce da ita Daular Ruman.
Dare ya riski zukatansu cike da damuwa, yayinda sai É“arawo mafi iya satane ya samu nasarar sama musu nutsuwar wucin gadi wato barci. Sun wayi gari kunnuwansu a buÉ—e na jiran jin labarin mutuwar Æ´ar uwarsu, sai dai babu wani alamar hakan har sake shuÉ—ewar kwanakin zuwan ranar bikin al’ada.
Babu fashi aka gudanar da bikin al’ada na Æ™arshen kowace shekara. Sai dai su a zuri’arsu babu wanda ya leÆ™a koda Æ™ofar gida. Anyi an gama, kamar kowace shekara an samu rashin rayuka a wasanni daban-daban, da kuma haÉ—arin mota dana mashina suma a tituna daban-daban saboda cinkoson jama’a dalilin garin shine babban birni da Daular Ruman ke ciki. Bikin al’adar Æ™asar ruman kuma yana É—aya daga cikin biki mai tsananin Æ™ayatarwa da mutane daban-daban suke halarta daga sassan duniya ta ko ina. Shahan-shan ya fito zagaye tamkar kowace shekara cikin shiga ta alfarma, bashi a karan kansa ba hatta keken dokinsa ma abin kallo ne, sai dai a wannan karon ma babu wanda zaice ga kamanin Tajwar Eshaan ibn Haysam Abdull-majeed É—in.

★ A haka lokaci ya Æ™ara turawar da kwanaki suka zama watanni kusan uku. Shuru na waÉ—annan watanni bai sama musu wata nutsuwa ba, dan a kallon farko da mai gani zaima gidansu zai san akwai matsala tattare dasu. Komai ya sauya, sauyawa irin wadda Æ™addara ta shigo cikin tarihinsu. Babu mai walwala a cikinsu, komai na Æ™arfin hali sukeyi, abinci ya gagara ciyuwa yanda ya kamata a koda yaushe garesu, sai cin Æ´aÆ´an itatuwa, tunkan a sanar musu alamominsu sun tabbatar da zaman makokinsu. A haka duhun wani dare na cika watanni uku da kwana uku da auren Arfa ya sake riskarsu, suka sake zama Æ™arÆ™ashin mulkin mallakar É“arawo mafi iya sata koda shiri ko babu wato (barci). Daren da yazo ma Iffah da wasu irin munanan mafarkai masu firgici daban tsoron.
Har rige-rigen fitowa suke daga ɗakunan barcinsu sakamakon fitar sautin razananniyar ƙarar data karaɗe gidan mai ban tashin hankali. Su duka huɗun suka rufu a kanta kowa na ambaton sunanta da kai hannu jikinta. Duk da sanyi da akeyi jike take sharkaf da zufa ga illahirin jikin nata daya ɗauka zafi. Ummu ta rungumeta tana mai sakin hawayen da ke kwance a cikin idanunta. Ta riga ta farka dan haka itama ta ƙanƙame Ummun tana fashewa da nata kukan.
Ba yau ne karan farko da Iffah ke shiga irin wannan tsoron ba sakamakon firgici a mafarki, sai dai na kwanakin nan yafi razanarwa da saka ruɗani a zukatansu. Babiy ya kai hannu ya shafa yalwataccen gashin kanta, murya a raunane yake ambatar sunanta.. Kanta ta ɗago a hankali fuskata sharɓan da hawaye, ta dubi mahaifin nasu da Yayansu Hanash da Fariha, sassanyar ajiyar zuciya ta sauke tare da haɗiye sauran kukan tana tashi zaune daga jikin Ummu ta share hawayen dake jiƙe da fuskarta. Matsawa tai jikin mahaifinsu tana mai kamo hanunsa.
“Babiy inajin tsoro, matuÆ™ar tsoro a wannan mafarkin fiye dana kullum. Babiy itama Nina Arfa kashemana ita zasuyi kamar sauran matan daya aura?, itama zamu rasata na gani a mafarki na…”
Da sauri Hanash da dukkan rauninsa ya bayyana a fuskarsa ya shiga girgiza mata kansa cikin aro jarumta. “Mafarki ba gaskiya bane Iffah, ki kwantar da hankalinki Arfa na cikin Æ™oshin lafiya tamkar mu insha ALLAHU…”
“Amma Akh Hanash nawa yasha zama gaskiya, a daren da Nina Arfa zata bar gidan nan irin wannan mafarkin nayi a kanta, yau ma shine na maimaita da ita babu banbanci a cikinsa na rantse maka”.
Har Æ™asan zukata zancen nata ya dake su, ganin bayyanar rauni a fuskokinsu ya saka Babiy yin murmushin Æ™arfin hali yana shafa kanta. “ShaiÉ—anu zasu iya dawo miki da makamancin sa ai Ibnati, dan haka ki kwantar da hankalinki Arfa na lafiya a gidan aurenta”.
Bazata cigaba dayin jayayya da su ba, amma tana cikin matsanancin damuwa tamkar yanda take hango tasu akan fuskokinsu. Maimakon komawarsu barci sai duk suka miÆ™e zuwa tsakar gida, alwala suka É—auro, suka koma can runfar dake matsayin falon iyayensu suka fara salla da miÆ™a kukansu ga UBANGIJIN talikai da fatan hana tabbatuwar abinda zukatansu ke cikin tsananin fargaba. Haka suka kasance har sallar asubahi gaban mahaliccinmu, bayan idar da sallar asubahi maimakon kwanciya sai suka riski kansu a zaman jugum-jigum na jiran tsammani. Har fitowar rana babu wani yunÆ™uri daga É—ayansu. Sai ko ga isowar abinda suke fargabar ya riskesu ya iso garesun. Shigar bugun gidan a cikin kunnuwansu ta sakasu miÆ™ewa a zabure gaba É—aya kuma a lokaci É—aya, kowanne cikin rawar jiki da fidda tsammani. Babiy ne yay jarumtar Æ™arasawa ga soro cikin jan Æ™afa. Tunda yay tozali da hadiman masarauta zuciyarsa tai wata irin masifar wulÆ™itawa…..
“Kun kasheta itama ko?!”.
Da shi da hadiman suka riski muryarta a cikin kunnensu a bazata. Sam babu tsoro ko shakka irin wadda akema duk wani mai alaÆ™a da masarauta a Æ™asar cikin idanunta a yau. Sun soye sunyi jazur irin na tashin hankali. A harzuÆ™e cikin hadiman É—aya ya daka mata tsawa da faÉ—in, “Hattara É—iyar talakawa, bakin rijiya ba wajen wasan yaro bane”.
“Idan yaron ya kasance rago ba!!”.
Ta bashi amsa itama a tsawace. ShimfiÉ—eÉ—iyar bulalar hanunsa ya É—aga zai zuba mata Babiy ya kare cikin rawar jiki yana mai zubewa Æ™asa a kan gwiyawunsa. Sosai a zaba ta ratsashi, ya rimtse idanu cikin aro dakiya da jarumtar dole, “A gafarceta ita É—in yarinyace masu nasara”. Ya faÉ—a cikin rawar murya saboda azabar tasirin shigar bulalar.
Ƙasa Iffah takai durƙushe gaban Babiy tana mai fashewa da kuka, kafin ta ɗago ta dubesu zatayi magana Babiy yasa hannu ya rufe mata baki jikinsa na tsuma. Jikin nata itama tsumar yakeyi, sai dai ita bana tsoro bane na tsananin baƙin ciki ne da bushewar zuciya. So take ta amayar da abinda ke bakinta an hanata. Batare da hadiman sun sake bi takantaba suma suka isar da saƙon dake tafe da su.
“Kasancewarka mai biyayya da bin umarnin masarauta a karo na biyu an sake baka damar halartar jana’izar É—iyarka kai da zuri’ar ka. Mun barka lafiya”.
Innalillahi wa-inna’ilaihirraji’un. Babiy ya shiga ambata, kusan a tare Ummu da Fariha suka saki razananniyar Æ™ara wadda ta jawo hankalin maÆ™wafta da mutanen dake tsaitsaye a Æ™ofar gida tun wucewar hadiman masarauta. Dan sun san dai labarin gizo bazai wuce na Æ™oÆ™i ba……..

*_WASA FARI GIRKI_*

Dole ne zuri’ar mal. Zayyan su ambaci rasuwar Arfa da kalmar WASA FARIN GIRKI a jerin zaren Æ™addarar da ta kutso a rayuwarsu mai É—auke da almakashin da ya datse farin cikinsu. Sun rasata tamkar labarin hikayoyin marubuta ko wasan kwaikwayo na film. Ta tafi tafiyar da bazasu sake ganita ba, tafiyar da babu wanda aka bawa damar yin cikkakkiyar sallama da ita a cikinsu hatta mahaifansu. Ta shuÉ—e a Æ™addararsu tamkar yanda ruwan damuna kan tafi da duk wani yayin dakan tare masa hanya a lokacin wucewa. Komai ya faru tamkar ba’aiba. Babu mai iya koda tari balle bin ba’asi. Iyakarsu kukan idanu dana zuci wanda muryarsu kan tsayane kawai iya filin gidansu ko katanga basu isa bari ta haura ba. A yau ma dai Babiy da Hanash ne sukaje domin jana’izarta. Suko aka barsu da amsar gaisuwa a cikin gida wadda mutanensu talakawa na zuwa musu itane a É—arare…….

Kwanaki sun cikagaba da shuÉ—awa tamkar ba’ai komai ba, yayinda É—ayar matar Tajwar da aka aura masa tare da Arfa itama dai ta mutu bayan wasu watanni. Bayan su Arfa ba’a sake jin Tajwar yayi wani aure ba, sai dai mutane na raÉ—eraÉ—in a duk randa aka kaisu domin ziyartar turakarsa babu fashi gawarsuce take fitowa. Hakan yasa kowa ke danganta mutuwar matan da tsafi yakeyi dasu.
Wata huÉ—u da sati É—aya cif tarihi ya sake maimaita kansa, dan kuwa Fariha ta sake faÉ—owa a jerin matan da aka É—aurama Tajwar Eshaan ibn Haysam Abdul-majeed aure da su. Batare da wani shawara ba a safiyar alhamis suna zaune kira ya riski Babiy daga masarauta, babu wanda bai shiga tsoro da firgici ba a cikinsu, sai dai babu wanda ya isa hana hakan a duk faÉ—in ruman. Sunaji suna gani babiy yay shiri ya amsa kiran. Tafiyarsa da awanin da basu gaza biyar ba sai ga hadiman masarauta sunzo sunma Fariha É—aukar amarya itama babu wani bayani daga garesu. Ranar dai kam Iffah bata gazaba kojin tsoro wajen gwada musu hauka, dan bata bari an fita da Fariha ba har sai da basamuden nan ya zabga mata bulalar dorinar hanunsa data sakata zubewa, bata tashi dawowa hayyacinta ba sai bayan wucewarsu da kusan awa guda. Zuwa lokacin har Babiy ya dawo. Kamar dai Arfa itama Fariha an É—aura mata aure da sarkin da kowa yake masa inkiya da fir’aunan wannan Æ™arnin. Sai dai a É“oye wannan suna ke fita a bakunan talakawan gari irinsu Iffah. Sakamakon bulalar da aka zabga ma Iffah bayanta yay mugun fashewa har akan mazaunanta, ga wani raÉ—aÉ—i mai azaba na ratsata har ta kasa riÆ™ewa sai da ta saki Æ™ara. Babiy da Ummu suka rufu a kanta, hawaye suke suna jeramata sannu, Hanash na gefe zaune idanunsa jajur alamar tsananin É“acin ran da babu Æ™arfin É—aukar mataki……
Tayi jiyya ta kwanaki uku, wajen ya warke, daga haka kwanaki suka cigaba da tafiya, inda a cikar watanni biyu itama Fariha mutuwarta ta riskesu tamkar ba’ayita ba. Sun sake rasa Fariha a dalilin auren Tajwar Eshaan ibn Haysam Abdul-majeed……..✍

*_Hummmm!!_*

 

*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*

*DAUDAR GORA Billyn abdul*

*KI KULANI hafsat xoxo*

*A RUBUCE TAKE Huguma*

*RUMBUN K’AYA Hafsat rano*

*IDON NERA Mamuh ghee*

_LITTAFI DAYA: 400_
_LITTAFI BIYU: 600_
_LITTAFI UKU: 800_
_LITTAFI HUDU :1000_
_LITTAFI BIYAR: 1200_

_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_

_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_

_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_

_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_

_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_

_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_

ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN

MARYAM SANI
ACCESS BANK
0022419171

SAI A TURA SHAIDAR BIYAN

09033181070

IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA

09166221261

*ƳAN ƘASAR NIGER. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*

+22799643131

Books biyar 1250CFA
Books hudu 1050CFA
Books uku 850CFA
Books biyu 650CFA
Bookk daya 450CFA

KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.

MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.

 

*_ALLAH ka gafarta ma iyayenmu_*

✨ÆŠ ✨
( )

 

Post a Comment

0 Comments