Daudar Gora Book 1 Page 20

Latest Posts

6/recent/ticker-posts

Ad Space

Daudar Gora Book 1 Page 20


20_*

 

……..Abu Moosa dake sonyin magana ya dafe Æ™irjinsa da numfashi ke kokawar kufcewa, tari ne ya suÉ“uce masa sai ga jini. Hankalin Babiy da Ummu ya tashi, amma Hanash ko’a jikinsa. Da Æ™yar tarin ya lafa, Babiy dake riÆ™e da shi yace, “Kayi haÆ™uri muje asibiti, aman jini fa kake yi”. Murmushi yay mai ciwo da kaÉ—a ma Babiy kansa da Æ™yar. “Abu Hanash zuwa asibiti bazai canja komai ba, dan gubar da aka shayar da ni bata da makari a ko’ina sai a wajensu.”
“Ya ALLAH! Guba kuma?” “Wannan shine hukuncin daya dace da masu irin halina ai karka damu, kai dai kawai ka saurareni zan gaya maka ta hanyar da zaka kuÉ“utar da yarinyarka, ina fatan hakan ya zamar min aikin alkairin dazan samu sassauci a kabarina”. Babiy zai yi magana ya dakatar da shi. “Ka saurareni kawa Ab…..” ya kasa Æ™arasawa saboda sabon tarin daya sake sarÆ™esa. Sosai Babiy ya rikice ya shiga Æ™wala kiran Hanash duk da yana a kusa da shi. Hanash dake jin tamkar yasa wuÆ™a ya Æ™arasa numfashin wanan shegen tsoho ya amsa da Æ™yar.
“Kaga kamashi maza muje asibiti”. “K…k…karku wahal da kan.. Ku. ka saurareni kawai”.
Abu Moosa ya tari numfashinsu da Æ™yar yana dafe Æ™ircinsa da tari ke yunÆ™urowa. Babiy ya buÉ—e baki zai yi magana cikin taresa shima sai kawai sukaga yarab alamar rai yayi halinsa. Salati suka É—auka a tare, wanda yay dai-dai da shigowar jami’an tsaro dake na Æ´an sanda a Æ™asar, bayansu wata mata ce ke rusar kuka… “Ranka ya daÉ—e dama na faÉ—a muku, na faÉ—a muku mutumin nan baya Æ™aunar mijina, yanzu kun gani da idonku gashi nan ya kashe mini shi, dama kullum yana faÉ—a min neman rayuwarsa yake yi, ashe dai shine É—in zai zama ajalinsa…..” ta zube Æ™asa tana cigaba da kuka harda kururuwa…….

Hankali tashe su Babiy ke kallon wannan mata da jami’an tsaron, ba shigowarce ta tada hankalinsu ba da farko, dan tunaninsu ya basu duk wanda ya bama Abu Moosa guba shine yasa suka biyo sa. Furicin wannan mata da kai tsaye Babiy ya gane matar Abu Moosa ce ya firgitar dasu. Cikin Æ™arfin hali Babiy yace, “YallaÉ“ai taya daga taimako kuma zan zama mai kisa? Abu Moosa abokina ne tun Æ™uruciya kowa ya sani, ban kashesa a da da muke tare ba sai yanzu da a Æ™alla nama kai shekara biyar kenan ban sakashi a idona ba sai yanzu dana gansa ayam cikin gidana babu zato…..”
“……Shiyyasa akaga gawarsa a cikin gidanka yanzu daka samu damar ganin nasa ko?”. Jami’in ya tari numfashin Babiy da sauri yana wani makirin murmushin Æ™eta…
“Allahumma ajirni fi musibati wa’akhlifni khairin minha” Babiy ya faÉ—a a zahiri gumi na karyo masa. Duban jami’in yay zaiyi magana matar ta taresa tana cigaba da kukanta mai cike da bori…. “Ƙarya yake wlhy yallaÉ“ai, shekaran jiya jiyan nan sai da yaje har gidanmu ya faffaÉ—a masa magana mara daÉ—i da tabbatar masa shine ajalinsa, idan ya Æ™aryata ai munada shaidar hakan”.
Hanash da zuciyarsa tazo ta tokare maÆ™oshi a hasale yayo kan matar, wata shegiyar shaÆ™a yakai mata saiga idanunta tamkar zasu fito waje. “K! baÆ™ar matsiyaciya, dan kawai anga gawar mutum a waje sai ya tabbatar masu wajen suka kashe shi!!”. Idanuta ta rumtse da Æ™arfi jikinta na É“ari, ta fara kakarin azaba dan da gaske ta shaÆ™u. Tuni jami’an tsaron duk sukai kansu da Æ™oÆ™arin É“anÉ“are hanun Hanash a wuyanta amma sun kasa. Ummu kuka ta sanya, yayinda Babiy keta kiran sunan Hanash da faÉ—in ya saketa amma sam babu alamar yana ma jinsa. Da Æ™yar aka iya É“anÉ“are Hanash, ta zube gefe tana sauke nunfashi da Æ™yar hanunta riÆ™e da wuyanta. Sai da suka bata ruwan da suka fita suka É—akko a mota da sauri tasha ta samu dai-daiton numfashi.
Cike da gadara ogan tawagar ya bama yaransa umarnin kama Babiy da Hanash. Sosai Ummu ke kuka da roÆ™onsu amma babu wanda ya saurareta, har Æ™ofar gidansu daya cika da mutane tun isowar jami’an tsaron ta biyosu amma kamarma basu san tanayi ba. Haka aka saka Babiy da Hanash a mota, sai gawar Abu Moosa a Ambulance da sukazo da ita (Alamar akwai dai lauje cikin naÉ—i kenan. Inba hakaba miye na zuwa da Ambulance É—in?).
Matan anguwar ne suka rufu kan Ummu data yanke jiki ta faɗi bayan wucewar motocin. Amma koda suka zuba mata ruwa bata farfaɗo ba. Hankalinsu ne ya sake tashi, makwafcinsu ya bada umarnin a sakata a motarsa a kaita asibiti. Da taimakon matan aka sakata a mota, matarsa da wata mata dake anguwar itama mijinta ya rasu suka shiga. Sai lokacinne mutane suka samu bakin magana. Wasu na nuna tausayawa ga wannan ahali, wasu na jin farin ciki badan sun taɓa musu komaiba, sai dan kawai dalilin hassada na rashin dalili.
A asibiti kam har an amshesu za’a fara dubata sai sukaga Doctor É—in ya dakata sakamakon kiran wayarsa da akayi. Kansa ya girgiza musu ya nufi barin É—akin yana sanar musu yanada uziri. Hankali tashe makwafcin nan nasu da ake kira Abu Zainab ya shiga roÆ™onsa amma bai sauraresu ba. Sun fara neman taikon Nurses suma sai zuÆ™ewa suke saboda gargaÉ—in da Doctor yay musu. Al’amarin kamar wasa anÆ™i taÉ“a Ummu, dole suka É—auketa suka bar asibitin zuwa wani, sai dai acan É—in ma har an amshesu aka koresu. Basu gajiyaba suna kuka suka nufi privet ko acan za’a dace tunda aikin kuÉ—ine. Anan sun amsheta, amma sun sara musu maÆ™udan kuÉ—aÉ—e kafin su taÉ“ata, acewarsu dokarsu kenan. Matar nan da mijinta ya rasu ta fashe da kuka tana girgiza kai. “Suma basa son su amshemu ne kawai, shiyyasa suke mana kora da hali. Inba kora da hali ba ai banajin Abu Hanash ya mallaki koda kwatar waÉ—an nan kuÉ—aÉ—en da suka ambata inba dai kaddararsa zai saida ba”.
“Hakane Umm Yazeed maganarki nakan gaskiya, kuma tabbas na fara ji a jikina akwai lauje cikin naÉ—i a wannan lamarin, da alama hanasu amsarmu akeyi”. Abu Zainab ya faÉ—a ransa a É“ace.
Matar Abu Zainab dake share hawayen itama ta ce, “Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un. Wannan wace irin masiface haka? Mi bayin ALLAH nan suka tarema wani da zafi haka?”.
“Sanin gaibu sai ALLAH, inaga inada mafita É—aya, mu É—auketa mu maidata gida sai a sanar da Æ´an uwansu ko? Tunda mudai munyi iya Æ™oÆ™arin mu…”
“Da hakan kukai tun farko da baku wahal da kanku ba”. Wata murya ta faÉ—a a bayansu. Da sauri suka juya su duka, sai dai bayan mutumin kawai suka iya gani. Da gudu Abu Zainab ya bisa, amma kafin yaÆ™arasa garesan harya shige mota sai Æ™ura ya bulesa da shi…….

(????)

*_MASARAUTA_*

Babban É—aki na musamman aka warema Iffah a sashen Malikat Haseena. Tare da amintattun hadimai biyar da zasu dinga mata hidima. Sai Ghazi biyar suma da zasu dinga bata tsaro duk da dama sashen zagaye yake da masu tsaron, amma an ware biyar É—inne na musamman domin kula da duk wani motsin shiga da fitar mutane da zai shafi Iffah. Hakan ya sake saka Malikat Bushirat a farin ciki matuÆ™a. Yayinda sabanin haka ya bayyana a fuskokin munafukai, sai dai wasu sunyi jarumtar dannewa baÆ™in cikin nacin zukatansu tamkar wutar daji. Malikat Haseena data zartar da hukuncin batama nuna tasan sunai ba. Ita kuwa Daneen Ammarah damar nutsuwar nazartarsu ta samu É—aya bayan É—aya dalilin wani É“oyayyen al’amari dake ajiye a zuciyarta tsahon shekaru.

Daneen Ammarah ta kasance É—aya daga cikin Æ´aÆ´an Malikat Haseena da Tajwar Abdul-majeed Ibn Aliy. Su huÉ—u suka haifa. Tajwar Haysam shine babba, (sarkin daya shuÉ—e kuma mahaifin sarkin yanzun). Sai Daneen Waheeda tana auren wani babban sarki a yankin larabawa. Sai Daneen Ammarah, itama tayi aure sai dai auren bai jimaba sakamakon wani É“oyayyen al’amari dake tattare da ita, wannan ne sanadin dawowarta gida take zaune kusan shekara goma sha tara kenan bata kuma sake wani auren ba. Ƴar uwarta da mahaifiyarsu Malikat Haseena da marigayi Tajwar Haysam da mahaifinsu daya bar duniya da tabon damuwar Æ™addarar É—iyar tasa ne kawai sukasan wannan sirrin, al’amarin ya sameta tun tana Æ™arama dan bata wuce shekara 14 ba, shiyyasa ta jima batayi aure ba, bayan ta samu tai auren kuma bata jimaba suka rabu da mijin dan auren baifi wata takwas ba ma. Manyan masarauta sunta Æ™ananan magana akan hakan da fassara al’amarin na Daneen Ammarah ta siga daban-daban amma su Malikat Haseena sukai biris dasu. Sai auta Miran Nayyar nada shekara bakwai ALLAH yay masa rasuwa.

Bazamuce Iffah tayi garau ba kam a wannan yini. Dan har yanzu ko idanunta bata iya É—agawa ta kalla kowa. Sai dai daidaituwar fitar numfashinta ya saka nutsuwa a zuciyar kowa. Koba komai dai an samu sassauci ai. Daneen Ammarah itace da kanta ta gogema Iffah jiki ta canja mata kaya, itace kuma da kanta tai zaman bata abinci daya kasance mai ruwa-ruwa. Daga haka aka Æ™ara bata magungunan da duk suka dace da gyara mata kwanciya a lafiyayyen gadon da yaji shimfiÉ—u na alfarma. Wani irin barcine mai daÉ—i yay awon gaba da ita, cikin Æ™anÆ™anin lokaci ta fara sauke numfashi. Daneen Ammarah dake kallonta cike da tausayawa da jin wani É“oyayyen al’amari akan yarinyar ta sauke numfashi ahankali da mata addu’ar samun lafiya da fatan ya zama kaffara a gareta…….

★★…. ★…. ★★…..

Duk wani nau’in kiranye ga uwa ta yisa tun lokacin da labarin abinda ya faru da yarinyar can sakamakon saka riga ya risketa, tabbas sune suka bada riga, amma abinda ya faru da yarinyar bashine ya kamata ya faru ba akan rigar, dan shirinsu sam bashi da alaÆ™a da halin da take a ciki yanzun. Hakan na nufin kenan bayansu akwai wasu masu shiri akan yarinyar kenan?. In dai har hakane kuwa to su É—in su wanene? Minene tasu manufar kuma?.
Wannan amsar take buÆ™atar ji a wajen Uwa, sai dai har zuwa duhun dare babu alamar zata ziyarce ta. Tun zuciyarta na raya mata ta jira har ta fara jin ita taje gareta mana kawai. Amma tuna zuwa ga Uwa babban al’amari ne mai wahalar yiwuwa gareta yasa ta kasa iya cigaba da tabuka komai har dare ya cigaba da tsalawa masarautar ta É—auki shiru tamkar babu wani mahaluki mai sauran numfashi. Ta cigaba da kaikawo a cikin wannan shiru, tare da Æ™ara gwada dabaru kala-kala na kiranye ga Uwa. Dai-dai lokacin da take sarewa, gaÉ“É“anta ke nuna gajiyawa mummunan sautin dariyar Uwa mara daÉ—in saurare a kunnuwa ta fara mata kaikawo tamkar tana yawo cikin iska. Ƙasa ta zube akan gwuyawunta tana mai jan nannauyan numfashi dajin sanyi a ranta. Tarwai Uwa ta bayyana a gabanta, akan kujerar baÆ™in karfenta mai adon gwal sanye cikin jajayen kaya kamar koyaushe. Mummunar fuskarta a matuÆ™ar tsuke take babu alamar itace ta gama dariyar dataita amsa kuwa a mintocin da suka shuÉ—e…..
“Barka da isowa Uwa mai share kukan masu kuka. Uwa ina cikin matuÆ™ar ruÉ—ani, dan aikinmu yasha banban da wanda ya bayyana ga Æ´ar shilar suda. Kamar yanda na riski yinin jiya a cikin ruÉ—ani, haka na kasance a duhun dare batare da na rintsa ba, na kuma sake wayar gari da Æ™ishirwar ganinki a yinin yau har zuwa iyanzu da daren ke Æ™oÆ™arin zama dare biyu da faruwar komai?. Shin kuskuren daga garemu ne? Kokuwa kece kika canja aikin ya koma hakan? Ko akwai wasu masu irin shirinmu ne a wannan daula batare da mun san dasu ba? Minene manufarsu su? Wane buri kuma suke da shirin cimmawa?. Uwa ki taimakeni nasan wannan amsoshi in ba hakaba zuciyata na gab da tarwatsewa ne”.
“Bazan gaji da tuna miki akwai Æ™alubale zagaye da cikar matakin aykinki na biyu ba, kuma wannan Æ´ar shila na tare da kaddarar Æ™alubalenne, sai dai na miki alkawarin tsayuwar daka akan hana faruwar nasarar da zatazo in har bataki bace ba. Tabbas aikin ba namu bane, kuma rigar da aka kai mata ta sanya ba tamu bace itama. Na gano hakane a daren jiya bayan mutuwar waÉ—an can hadiman da kuma samun lafiyar Æ´ar shilar.. Hakane ya sani duÆ™ufa bincike tuÆ™uru domin gano daga ina matsalar take?, wanene ya shirya aikin laÉ“ewa bayan namu? Har yaci nasarar kuÉ“utar da ita da tarkon makircin sa cikin sauÆ™i haka?……”
“Uwa kin gano kenan?”. Ta-kurya ta tari numfashinta cike da zalamar son jin amsa……..✍️

 

*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*

*DAUDAR GORA Billyn abdul*

*KI KULANI hafsat xoxo*

*A RUBUCE TAKE Huguma*

*RUMBUN K’AYA Hafsat rano*

*IDON NERA Mamuh ghee*

_LITTAFI DAYA: 400_
_LITTAFI BIYU: 600_
_LITTAFI UKU: 800_
_LITTAFI HUDU :1000_
_LITTAFI BIYAR: 1200_

_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_

_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_

_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_

_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_

_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_

_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_

ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN

MARYAM SANI
ACCESS BANK
0022419171

SAI A TURA SHAIDAR BIYAN

09033181070

IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA

09166221261

*ƳAN ƘASAR NIGER. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*

+227 90165991

Books biyar 1250CFA
Books hudu 1050CFA
Books uku 850CFA
Books biyu 650CFA
Bookk daya 450CFA

KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.

MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.

 

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*

✨ÆŠ ✨
( )

 

Post a Comment

0 Comments