Daudar Gora Book 1 Page 21

Latest Posts

6/recent/ticker-posts

Ad Space

Daudar Gora Book 1 Page 21


*_21_*

________________________

_Innalillahi wa-inna ilaihirraji’un. A madadin É—aukacin É—alibai na G.G.A.S.S D/Z. Muna miÆ™a saÆ™on ta’aziyyar ga Æ´an uwanmu da iyayenmu da yayyenmu na rasa Uwa abin alfaharin duk wani É—a na gari da mukai *Hajiya Ai’sha Ahmad Tukur* tsohuwar principal É—inmu. Ya rabbi ka gafarta mata, ka yafe mata kurakuranta. Ka bama iyalanta da mu haÆ™urin rashinta. Mu data bama tarbiyya a wani bigire na rayuwa, ALLAH yasa muyi koyi da Æ™yawawan halayenta managarta. Dan ita É—in abin alfaharinmu ce da bazamu taÉ“a iya mantawa ba, zamu tunata, zamu cigaba da tunawa da ita, zakuma mu tunatar dana bayanmu kyawawan halayenta da alkairinta. (ALLAH ya gafarta mata.)_

________________________

………..“Ina kan Æ™oÆ™arin yin hakan yawaitar kiranyanki ya katse ni, amma tabbas wanda ya aikata yana a cikin wannan daula ne, yana kuma da babban shirin daya kamata mu sani tun a yanzu. Ina kuma ji a jikina babban yaÆ™ine da kema ya shafeki, kuma za’a cigaba da amfani da yarinyar ne wajen tabbatar da shi in har tana cikin masarautar nan”.
“Shiyyasa tun farko nace a kawar da ita Uwa, dan babu wani amfani da wannan yarinyar zatamin face cigaba da É—agamin hankali, gashi kuma har tana neman zama tafinta a al’amurana dake gab da kammala bayan gumurzun yaÆ™in da naci na tsahon shekaru a baya kafin zuwa lokacin tattara ganima”.
“Abinda kike Æ™oÆ™arin yi shine mafi girman kuskure da zai rusa dukkan nasarorinki Ta-kurya. Domin yunÆ™urin kashe wannan Æ´ar shilar da kike tamkar kashe rayuwarki ne baki É—aya. Tun farko na faÉ—a miki kasheta kai tsaye bashine mafitar ba, ba kuma shine Æ™arshen daÆ™ile yunÆ™urinta ba ita a karan kanta. Hasalima a yanzu rayuwarta mukafi buÆ™ata, zamu jefata ne matsayin dutse É—aya dazai wargaza tsuntsaye biyu. An wargaza mana shirin mu na farko a kanta, dan haka zamu tafi na biyu. YaÆ™inki a yanzu shine kiyi duk yanda zaki ta baro wancan sashen daga nan zuwa cikar kwanaki bakwai. Zakiyi yanka na baÆ™ar babbar dabba a daren goma sha uku, zakuma ki dawo da rigar data sanya. Kiyi duk wani Æ™oÆ™arin da zai hana kusancinta da Ajlaan a turaka. Dan maganar kaita turakarsa ta rushe kuma zamu sake sabon salo ne domin kama tsuntsu mai wayo…….”
“An gama Uwa mai share kukan masu kuka. Sai dai dawo da rigar nan zai zama abu mai wahala kasancewar tana a hanun Mamma (Malikat Haseena) ne a yanzu haka”.
“Wannan umarni ne Ta-Æ™urya”.
“Zanyi iya Æ™oÆ™arina Uwa. Sai kuma maganar mutuwar Hadiman can, Shahanshan da kansa ya saka kwamitin bincike masu tsauri da basu taÉ“a Æ™etare nasarar cika umarnin da’aka basu ba. Kinga akwai matsala kenan tunda waÉ—an can sun laÉ“e ne a jikin aikinmu suka zartar da nasu, sannan suka kashe hadiman tamkar yanda muka shirya kafin mu mu aiwatar da hakan”.
Wata irin mahaukaciyar dariya mai amsa kuwwa Uwa ta shiga Æ™yalkyalawa, sai da ta É—auka tsahon lokaci tanayi kafin ta tsagaita ta tsuke fuska tamkar ba itace tayin ba. Har ta Æ™urya ta fidda ran samun amsa sai kuma Uwa ta sake Æ™yalkyalewa da dariya tana ambaton “Ajlan! Ajlan!! Ajlan!!!” ta Æ™ara kwashewa da dariya tana mai disashewa a idanun Ta-kurya da zuciyarta ta kasa fassara ma’ana ko dalilin dariyar ta uwa…

Ko miye naku tunanin a wannan gaɓar kuma masu karatu???.

★… ★.★.★ ★…

*_GIDAN BABIY_*

Sun dawo har yanzu da ɗan sauran mutane maƙwafta da aketa ɗan ƙus-ƙus akan lamarin. Cikin ƙanƙanin lokaci aka baibaye motar, waɗanda suka shige gidaje suka fara fitowa. A yanayin da aka fidda Ummu mafi yawansu sunma ɗauka dai bata da rai, dan kuwa da gaske babu alamar rai tare da itan. Kuka da salatin da mafi yawan mutane suka ɗauka na tunanin ta mutun ne yasa Abu Zainab saurin dakatar da su.
“Dan ALLAH kowa ya kwantar da hankalinsa. Umm-Arfa ba mutuwa tai ba”.
Badan hankalin su ya kwantaba sukai shiru, sai dai dama kukan na wasu na munafurci ne dai. Matane suka kamata aka shiga da ita, a tabarmar da suka samu tsakar gida suka shimfiÉ—eta. Cikin sa’a Abu Zainab yaci karo da wayar Babiy dake yashe a Æ™asa. Da alama sanda jami’an nan zasu fita da shine ta faÉ—i. Jikinsa har tsuma yake a duba contact É—in wayar, cikin sa’a ya samo number da akai saving da Baba. Baya raba É—ayan biyu mai sunan nada babban matsayin baban a wajen Babiy É—in, dan haka ya danna masa kira kai tsaye, sai dai harta tsinke ba’a É—aga ba. Sake kiran yay yana addu’ar dacewa sai ko gashi an É—aga…

★A lokacin da kiran Abu Zainab ya riski su kaka ta hanyar wayar Babiy ba’a Æ™aramin tashin hankali suka tsinci kansu ba shi da Iyyani. Duk da kasancewar yamma tayi kuma yasan a yau dole ne sai ya dangana da daular ruman dole ya bazama neman wani yaro mai mota a Æ™auyen nasu dake jigila a ko yaushe, cikin sa’a ya samesa ya dawo kenan ma ko gida bai shiga ba. Amma saboda mutuncinsa da ake gani yana masa bayani babu musu ya amsa masa suka É—auka hanya harda Iyyani daketa faman sharar hawayen da suka kasa tsaya mata. Ana sallar isha’i suka iso cikin daular ruman. Basu sami mutane ba a gidan kamar É—azun, sai Umm Yazeed da matar Abu Zainab dake dai tare da ita har yanzun. Zuwa yanzu Ummu ta farfaÉ—o, sai dai taÆ™i magana da kowa sai hawaye da taketa faman zirarwa ta gefen ido, ga numfashinta baya fita normal kamar na kowa, tana fitar da shine da fisgosa a wahale sannan a fiffisge. Kuka Iyyani ta sake fashe da shi da rungume Ummu a jikinta tana kiran sunanta. Kaka kam tsaye yay kawai zuciyarsa na harbawa da Æ™una. Suna a haka Abu Zainab ya dawo, dama sallar isha’i yaje. Cikin girmamawa ya gaida kaka, shima ya amsa masa da kulawa da godiya. Ya É—an murmusa kansa a risine. “Ai ba komai baba yiwa kai ne. Sannan mun zama É—aya ai mu da Abu Hanash. Ko mu irin haka ta faru da mu zai tsaya tsayin dakane a kan komai. RuÉ—anin halin da Umm Arfa ke ciki yasa su bamu bibiyesu musan miya faru ba har yanzu gaskiya. Dan munata yawo a asibitoci amma sunÆ™i amsarta, ga jikin nata kuma yana buÆ™atar a duba mata shi, shiyyasa yanzu dana idar da sallar magrib naje na samo É—an uwana dake aikin asibiti gashi muna tare, sai dai ba wani babban likita bane dai….”
Kai kawai Kaka ya jinjina masa da faÉ—in, “ALLAH ya saka muku da alkairi, haka ake fatan zaman makwaftaka, domin ita makwaftaka tanada Æ™arfin da zata iya fin Æ´an uwantaka muhimmanci ma a wani É“angaren. Yanzu gashi abu ya samesu, kafin mu muzo kun basu É—auki, da bakwa zaman lafiya kuma hakan bazai yuwuba. Dan haka duk wani mutum na Æ™warai daya san kansa ya dace ya rayu da maÆ™wafcinsa lafiya da Æ™aunar juna”. “Hakane Baba, ALLAH ya saka da alkairi. Bara na shigo da shi”. Murmushi Kaka yayi da jinjina masa kai. Koda suka shigo tare da É—an uwan nasa shima ya gaida Kaka da girmamawa, hakama Iyyani da har yanzu ke faman sharar hawaye tana tofama Ummu addu’a. Damar duba Ummun Kaka ya bashi dan haka ya shiga aikinsa. Ya tabbatar musu jinin Ummu ya hau matuÆ™a, amma zai mata allurar barci ta samu nutsuwa dan barinta a ido biyu akwai haÉ—ari komai zai iya faruwa. Sai da suka maida Ummu É—aki sannan ya saka mata ruwa da allurai aciki, cikin sa’a kuwa babu jimawa barci yay awan gaba da ita. Sosai Kaka yay musu godiya da sanya albarka, dan ko sisi É—an uwan nasa bai amsaba ma…….

★★…. ★…. ★★…..

An wayi gari da samun canji sosai a yanayin Iffah, dan zuwa yau kam Alhmdllh. Sai dai jikinta dake wani irin saÉ“a saikace wata macijiya. Sai kuma rauni data tsinci kanta a ciki sakamakon mummunan mafarkin datai akan su Babiy daya haddasa mata matsanancin faÉ—uwar gaba da akai-akai. Gata dai iya gata tana gani wajen tsohuwa Malikat Haseena duk da bata da lafiyar Æ™afa sai a wheelchair take komai. Hakama Daneen Ammarah tsaye take kan Iffah, yanda take kula da ita yasa Iffah jin Æ™aunarta batare data san dalili ba, ganinta take tamkar Ummu. Yanda ake tsaye kanta da gata da kulawa yasa ko damar yin Æ™waÆ™waran tunani bata da shi, dan da tayi shiru Daneen Ammarah zata nuna damuwa taita jera mata tambayar mike damunta? Ko tamanin wani abu ne a jikinta har yanzu?. Dole take sassauta damuwarta, sai dai tayi matuÆ™ar dagewa wajen ambaton UBANGIJI kamar yanda Babiy da Ummu suka dinga jaddada mata a nasiharsu ta Æ™arshe gareta. Labarin mutuwar hadiman da suka kai mata rigar nan ta saka yazo kunenta itama, sai dai jin sanadin mutuwar tasu ya tsaya mata a rai matuÆ™a, harma ta rasa yaya zata fassara al’amarin…
Bayan idar da sallar isha’i tana zaune tayi tagumi gaba É—aya hankalinta ya tattara ga tunanin iyayenta da mummunan mafarkin daren jiya a kansu Daneen Ammarah ta shigo hadimai uku biye da ita. A bakin gadon takai zaune tare da kai hannu ta janye tagumin da Iffah tai. Nannauyan nunfashi ta sauke da É—an É—agowa ta kalla Daneen Ammarah É—in, sai kuma ta maida kanta ta risinar da mata sannu da zuwa. Daneen Ammarah dake kallonta cikin damuwa taja numfashi ta fesar batare data amsa ba. Dai-dai nan Hadiman da suke tare suka zube gaban Iffah bayan sun ajiye kayan hanunsu. Gaisheta suke da tsantsar girmamawar da ko iya É—aga kawunansu basayi su dubi sashen da take. Sam Iffah batajin daÉ—in yanda suke matan saboda bata sababa, a ranta gani take kamar Æ™asÆ™ancine. Hannu Daneen Ammarah ta kaÉ—a musu alamar suje, zumut suka miÆ™e tamkar Æ™yaftawar ido suka fice. Iffah ta bisu da kallo cike da jin raÉ—aÉ—i a zuciyarta.
“Ibnati!”.
“Na’am Mamy!”.
Iffah ta amsa cike da girmamawa ga Daneen Ammarah. Sosai sunan da Iffah ke kiranta da shi ke raunanata da sake jin ƙaunar yarinyar, dan a bakin mutum ɗaya tak take jinsa kafin ita. Taja numfashi da haɗiye hawayen da suka cika mata ido ta maye gurbinsu da murmushi.
“Ibnati bana son cigaba da ganin damuwar nan a fuskarki, ki kwantar da hankalinki insha ALLAHU babu abinda zai sake samunki. Wanda ma ya sameki ki É—auka kaddararkice kinji, amma inaji a jikina insha ALLAH kece mabuÉ—in nasararmu, ke ce hasken da zata haska mana duhun da muke a ciki a Daular nan kinji”.
Kai Iffah ta jinjina a hankali, haka kawai take jin matuÆ™ar nutsuwar kasancewa da wannan baiwar ALLAH, sam batajin irin zafi da tsanar da takema duk wani mai alaÆ™a da masarauta a kanta. Kallonta take tamkar wata katanga ta wani babban al’amari dake tunkarota. “Mamy bana tare da damuwa in har kina a kusa dani, duk abinda ya sameni kuma dama ALLAH ya Æ™addara sai ya sameni koda banzo nan ba. Ina tunanin su Ummu ne da jin tsananin kewarsu saboda mummunan mafarkin danai akansu jiya, ina tsoron kar wani abu ya samesu ne suma?”.
Cike da jin tausayita Daneen Ammarah ta shafa kanta, “Duk É—a na gari dolene ya kasance cikin kewa a lokacin da yay nesa da ahalinsa, da ace inada dama da a yau sai na kaiki kinga su Ummunki. Amma dokar masarauta ce Zawjata-almilki tana fitane kawai bisa Æ™waÆ™waran dalili, zuwa gidansu kuwa tana yinsa ne sau biyu tak a shekara, É—aya a sirrance, É—aya a bayyane tare da rakkiyar hadimai. Shiko mafarki ai na gaskiya bane Ibnati, MANZANNI ne kawai idan suka yisa yake gaskiya a garesu, amma mu namu yakanzo da wasu sigogi ciki harda sheÉ—anu”.
A hankali hawaye suka silalo a kumatun Iffah, bawai lokacin ziyarar bane yay mata nisa, rashin tabbacin kaiwa lokacin ziyararne ya sata zubar hawaye. Ita dake zaman jiran Æ™addarar mutuwarta taya zatai tunanin zuwan waÉ—an can damarmaki guda biyu na ganin su Babiy, maganar mafarki kam ta san gaskiya Mamyn ta faÉ—a, itama kuma ba tana dangantashi da zama tabbaci bane, kawai tana matuÆ™ar jin tsoron faruwar wani abu ne a dalilin mafarkanta na baya…. Ganin hawayen Iffah ya matuÆ™ar tada hankalin Daneen Ammarah, a rikice ta shiga tambayarta kamar yanda ta saba in har ta ganta a makamancin damuwar nan. Hannu Iffah tasa ta share hawayen nata da Æ™irÆ™iro murmushi.
“Mamy ki kwantar da hankalinki hawayen sunzo ne kawai da kansu babu dalili”.
“Haba Ibnati, dama ana kuka babu dalili ne? Ko baki faÉ—aba nasan kinada dalilan yin kuka, amma idan kika zama mai haÆ™uri da juriya wataran ke zakiyi dariya a gaban waÉ—anda suka cancanta suyi kuka.” (ALLAH ya tabbatar da wannan ranar) Iffah ta faÉ—a a zuciyarta, a zahiri kam sai ta goge hawayen tana murmushi. Hakan yasa Daneen Ammarah yin murmushin itama, kafin kuma ta mike tsaye da kama Iffah suka koma kan dardumar da aka shirya abinci acan gefe na É—akin, dan É—akine Æ™aton gaske mai dauke da komai na jin daÉ—in duniya. Tare sukaci abincin, Daneen Ammarah har tana bama Iffah wani lokacin a baki, jitake inama Iffah É—iyartace, dan da’ace tana gidan aurenta har yanzu É—iyarta ta fari zata iya kasancewa dai-dai da shekarun Iffah ne. Kulawar Daneen Ammarah ta sake saka sassauci a zuciyar Iffah harta É—an saki jikinta. Bayan sun kammala ta sakata shiga bayi tai wankan maganin da take amfani da shi, data fitoma da kanta tai mata hayaÆ™in turare. Iffah ta hau gado ta zauna, Daneen Ammarah a gefenta da littafin tarihin annabawa acewarta zata dinga karantama Iffah har sai taga tayi barci domin É—ebe mata kewa.
“Yauwa Ibnati kin shirya dai ko?”.
Fuskar Iffah da É—an murmushi tace, “Eh Mamy na”
“Masha ALLAHU ashe dai Habibty na tare dani”.
Hannu Iffah tasa ta rufe fuska tana murmushi, itama dai Daneen Ammarah murmushin take. Ta fara buÉ—e littafin. Iffah dake kallonta tai dauriyar finciko É—aya daga É—unmbin tabayoyin dake cin ranta ganin zata fara karatun…
“Mamy dan ALLAH na tambayeki wani abu?”.
“Oh Ibnati tambayeni mana kanki ma tsaye kuwa.”
Iffah ta jinjina kanta da sauke ajiyar zuciya……….✍️

*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*

*DAUDAR GORA Billyn abdul*

*KI KULANI hafsat xoxo*

*A RUBUCE TAKE Huguma*

*RUMBUN K’AYA Hafsat rano*

*IDON NERA Mamuh ghee*

_LITTAFI DAYA: 400_
_LITTAFI BIYU: 600_
_LITTAFI UKU: 800_
_LITTAFI HUDU :1000_
_LITTAFI BIYAR: 1200_

_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_

_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_

_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_

_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_

_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_

_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_

ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN

MARYAM SANI
ACCESS BANK
0022419171

SAI A TURA SHAIDAR BIYAN

09033181070

IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA

09166221261

*ƳAN ƘASAR NIGER. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*

+227 90165991

Books biyar 1250CFA
Books hudu 1050CFA
Books uku 850CFA
Books biyu 650CFA
Bookk daya 450CFA

KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.

MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.

 

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*

✨ÆŠ ✨
( )

 

Post a Comment

0 Comments