Daudar Gora Book 1 Page 22

Latest Posts

6/recent/ticker-posts

Ad Space

Daudar Gora Book 1 Page 22


22_*

…….Iffah ta jinjina kanta da sauke ajiyar zuciya, “Immm Mamy dama…” sai kuma tai shiru dalilin gargaÉ—in da zuciyarta ke mata tunda har yanzu fa Bama wai tasan matsayin Daneen Ammarah É—in bane a masarautar.
“Dama mi? Kinga karkiji komai kimin duk tambayar da kike buÆ™ata, insha ALLAH zan kasance mai baki amsa, idan kuma bata dace ba zan baki shawara kodan nan gaba”.
Kai Iffah ta jinjina “Dama dan ALLAH zance ne yanzu mutuwar su hadiman can shikenan ta tafi a banza baza’ai wani bincike a gano ba?”.
Kallo na kusan sakan biyar Daneen Ammarah taima Iffah da har tama É—auka tai laifi, amma sai taji taja numfashi da maida kanta kan littafin hanunta. “Mutuwarsu bazai tafi a banza ba saboda dalili mai Æ™arfi Ibnati. Dan duk wanda ya kashesu yana gudun tonuwar asirinsa ne akan cutar da ke da akai yunkurin yi. A yanzu haka Shahanshan ya saka kwamitin bincike, muna fatan kuma ta wannan hanyar za’a gano koma wanene ya saka ki a halin da kika tsinci kanki. Kuma dama kema ana jiran Æ™ara samun lafiyarki ne aji ko akwai wani abu da kika sani, ko kuma bayan su ukun can da É—ayar da aka samu nasarar ceto ranta ko akwai wasu..”
Da sauri Iffah ta dubeta. “Mamy akwai wadda bata mutu ba dama?”.
“Eh akwai amintacciyar hadimar Umm-Jasrah (haka take kiran Malikat Bushirat) mai suna Diwa. Ita an kaita asibiti kafin gubar da suka sha ta karasa katsa Æ´an hanjinta. Alhmdllh kuma an dace dan yanzu haka tana kan shan magani, tana kuma zagaye da tsatstsauran tsaro”
“ALLAH ya Æ™ara bata lafiya, sai dai kuma banajin tanada hannu a cikin al’amarin Mamy, dan da ganinta mutiniyar kirki ce”.
“Gane mutanen kirki ba’a ido yake ba Ibnati musamman a wannan masarautar da kowa kansa kawai ya sani, a mafi yawan lokuta ma ba’a gane maÆ™iyi da halayya. Akwai rikitattun abubuwa dake a matuÆ™ar cuÉ—e a wannan Daular da gani da ido bazai wadaci mai kallo ba, dan haka nakeso ki nutsu kisa hankalinki waje É—aya kafin ki koma sashenki ki koyi abubuwa da yawa na salon mulki da tsarin matsayinki na Zawjata-almilki. Saboda kunada matuÆ™ar tasiri da girma a tsarin Æ™arfin iko na masarauta da kaikawon talakawan Æ™asan ruman. Fatana kuma kece Malikat a cikin Zawjata-almilki insha ALLAHU”.
Sam Iffah bata fahimci komai ba ga kalaman Daneen Ammarah, amma sai bata sake cewa komai ba dan a ganinta tana buÆ™atar samun lokacin yin nazari na musamman a kansu kafin ta fahimcesu dallah-dallah…….

★★… ★… ★★….

Ana idar da sallar asuba drivern daya kawo su Kaka jiya dan hanashi komawa yay saboda dare ya É—auka Iyyani da Ummu suka wuce. Kaka da Abu Zainab kuma sukai shirin fara neman inda zasu samo Babiy da Hanash.
Dai-dai suna shiga mota kaka ya dubi Abu Zainab da É—an murmushin Æ™arfin hali a fuskarsa, “To Zakariyya kai ne É—an gari, yanzu ta ina zamu fara kenan?”.
Numfashi Abu Zainab ya furzar, tare da yin É—an jimm alamar tunani, “E to Baba banace ba dai, dan al’amari nada wuya, saboda bamu da tabbacin waÉ—an nan jami’ai daga wane station suke. Amma ni yanzu a nawa shawaran ina ganin kamar mu nema gidan shi marigayi É—in, tunda matarsa ita ta kawo jami’an tasan daga ina suke”.
“Hakane, wannan ma shawara ce mai kyau, sai dai inda gizo ke saÆ™ar kai koka san ina gidan Dawood É—in yake? Dan ni dai rabona da shi ma kusan shekara biyar kenan tun suna tare da Muhammad Zayyan”.
“Ito baba banace ba, dan kusan nima hakan dai take, amma bayan tashinsa daga anguwarmu nasan inda ya koma, sai dai bani da tabbacin ko har yanzu acan É—in yake zaune tunda ba wani huÉ—É—a muke ba gaskiya, dama dalilin Abu Hanash É—inne ake gaisawa sai kuma idan wani zama na anguwa ya haÉ—a kafin ya tashi kenan. Amma yanzu dai bara mu tafi can É—in kawai rana ma nayi”.

Cikin Æ™anÆ™anin lokaci suka iso anguwar, kasancewar ma ta cika ba kamar da ba da kyar suka iya samo gidan. Duk da jikinsu ya É—anyi sanyi ganin Æ™ofar gidan babu alamar anyi wani abu daya shafi mutuwa Abu Zainab yay sallama har sau uku. Ana huÉ—un wani mutum ya fito. Cikin binsu da kallon rashin sani ya basu hannu suka gaisa. Abu Zainab da shima dai jikinsa yay sanyi ya ce, “Kayi haÆ™uri nasan baka sammu ba. Muma dai munzo nan É—inne neman wani bawan ALLAH daya zauna anan shekara kusan huÉ—u haka baya. Sunansa Dawood, amma ana masa alkunya da Abu Moosa. Matarsa É—aya bashi kuma da yaro ko É—aya”.
“ALLAH sarki, gaskiya ban sanshi ba, dan nima dai ban wuce shekara biyu da tarewa anan É—in ba. Na kuma sayi gidanne a hanun wani mutum Ibrahim Askari”.
Abu Zainab zai sake magana Kaka ya girgiza masa kai alamar kar yace komai. Godiya sukai masa da sallama suka wuce.

“Baba ban san miyasa ka dakatar dani ba. Dama zan tambayesa ne ko zai faÉ—a mana inda zamu samu shi Ibrahim Askari É—inne”.
Numfashi Kaka yaja ya fesar, “Dalilin da yasa na dakatar da kai kenan. Kasan shi al’amari irin wannan yana buÆ™atar kasan dawa zakai maganar abu na gaba. Inaji a jikina waÉ—anda suka haddasa tushen wannan matsalar dole suma zasu kasance suna bin bayanmu domin toshe duk wata hanyar da zamu iya bi. Dalili kuwa shine ina kallon lauje ne cikin naÉ—i akan al’amarin”.
“Eh gaskiya hakane kuma Baba. To amma in har hakane mizai hana mu nema lauya, sai nake ganin cikin sauÆ™i shi zai iya binciko mana inda suke ma, kuma koma minene sai yazo cikin sauÆ™i tunda ana magana ne akan abinda ya shafi shari’a ko kuwa?”.
“Itama wannan babbar shawara ce a mahangar hankali Zakariyya, sai dai shi lauyan ne matsala musanma irin mu wanda muke bukata. Mai gaskiya da amana”.
“In dai dan wannan ne babu damuwa insha ALLAHU, akwai yayan matata data rasu, kwararren lauyane kuma mai nagarta da nasan zakaso aikinsa kuma zai taimakemu kasancewarsa babba. A yanzu dai nasan bazamu samesa a gidansa ba. Bara kawai muje ofishinsa”…

★★….. ★… ★★…..

Kamar yanda Iffan ta nema alfarma a wajen Daneen Ammarah akan É—akko mata akwatinta da aka kawo ta gidan dashi ya iso gareta. Taji matuÆ™ar sanyi a ranta da farin ciki. Hadimar data kawo na fita ta buÉ—e akwatin ta shiga dubawa. Alhamdullah komai yana nan yanda yake, hatta takardar da malam Fawzan ya bata É—innan itama tana a inda ta É“oye ta. Tana idar da sallar azhar littafin data sako a kayan nata kawai ta É—auka da biro ta fara rubutu. Anutse take rubuta komai daya faru daki-daki tun daga barowarta gida har zuwa shigowarta cikin masarautar, abinda ya faru da ita dama wanda ke kan faruwa bayan warkewarta. Da zarar taji motsi koda ma Daneen Ammarah ne sai ta boye, a haka ta kwashe kaf yinin har zuwa dare tana abu É—aya. Da daddare bayan kammala shirin barci maimakon kwanciya zaman karatun Alkur’ani tayi, koda Daneen Ammarah ta shigo ta sameta a hakan bata katseta ba. Tasa Hadimar dake biye da ita ajiye mata madarar da suka shigo da ita. Daga haka ta fice taja mata Æ™ofar da nufin ta dawo zuwa anjima, dan yanzu tana son zuwa ta duba Malikat Haseena ne da yai batajin daÉ—i.
Iffah na ganin ta fice ta sauke ajiyar zuciya, addu’a tai ta rufe Alkur’anin ta mike, kofar taje ta sanyama key bayan ta leÆ™a babu kowa a corridor É—in. Ta É—an jingina da Æ™ofar tana mai ambaton “Alhamdullah” da sakin É“oyayyen murmushi. Cikin sassarfa tabar jikin Æ™ofar zuwa ga akwatinta, ta buÉ—e tare da É—akko wayar Arfa da takardar da Malam Fawzan ya bata. Number da aka rubuta ta kwashe a wayar, ta haye tsakkiyar gadon ta kwanta tare da jan lallausan bargon ta shige ciki har kanta sannan tai dailing number. Gaba É—aya a kage take da zumuÉ—in a É—auka. Dan haka take bin sautin shigar kiran da zuciyarta. Sai dai harta yanke ba’a É—aga É—in ba. Kira ta sake yi, nan ma dai shiru, bata gajiya ba ta cigaba da kira har fin sau goma kafin a É—aga a karo kusan na goma sha biyar. Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke tamkar wadda aka tsamo daga cikin Æ™anÆ™ara. Sai kuma tai saurin faÉ—in, “Assalamu alaikum”.
“Wa’ake nema?”.
Aka faÉ—a daga can maimakon amsa sallamar tata. Da lafiya lafiya ne sai tayi mitar Æ™in amsa sallamar, amma sai tai saurin faÉ—in, “Sir Ajmaal”.
“Wa’ake nema?”.
Aka sake maimaita mata tambayar.
Zuciyarta ta É—an fara zabura amma sai ta danne ta sake maimaitawa itama.
“Sir Ajmaal”.
“Wa’ake nema?”.
Still aka sake faÉ—a kamar dai ba’ama jita ba.
Wayar ta janye a kunenta ta tashi zaune ta É—auka takardar, number dai dake a jikice dai-dai batai mistake ba. Sake maida wayar tai kunne aranta tana faÉ—in (bara naga Æ™arshen ku dai) ta sake amsawa da “Sir Ajmaal”.
“Kin saÉ“a lamba”.
Aka bata amsa da yanke wayar lokaci guda batare da anjira cewar ta ba……

★★….. ★… ★★…..

Kasancewar Abu Zainab suruki ga barrister cikin sauÆ™i suka samu ganinsa ta hanyar kiran waya. Har office yasa masinjansa daya fita yay musu iso ya shiga da su. Ganin lafiyayyen office É—in nasa dama hukumar tasu ya sake tabbatar ma da Kaka babbane gaskiya. Sun gaisa cikin nuna sanayya shi da Abu Zainab. Ya kuma gaida Kaka da girmamawa kasancewar tsoho dama zai iya haifarsa. Basu saurari lemo da aka kawo musu ba Abu Zainab ya shiga masa bayani dalla-dalla. Sai da ya gama tsaf Barrister Abdallah dake rubuta wa ya ajiye biron yana jinjina kansa. Kaka ya fuskanta cikin son Æ™arin bayani….
“Baba kaima kasan shi Dawood É—in kenan?”.
“Tabbas na sanshi yaro. Hasalima ga gidan mahaifin shi Muhammad Zayyanu gana mahaifin Dawood. Sannan ta É“angaren mahaifiyata ma munada alaÆ™ar jini da mahaifin nasa. Shine kuma yay sanadin zuwan Muhammad Zayyanu garin nan, shi kuma Muhammad Zayyanu ya koya masa noman zuma daya gada ga mahaifinsa”.
“Eh lallai sanayya ce babba kam. Sai dai kuma inaga ya kamata nasan miya rabasu? Dan yanzu hujjojin hanunmu sune zasu taimaka mana wajen kubutar da su saboda wannan case ne babba kuma da alama shiryayye”
“To nidai kai tsaye banace ga abinda ya zama sanadin rabuwar kawunan nasu ba. Dan shi Muhammad Zayyanu mutum ne mai zurfin ciki da rashin kwaramniya. Amma dai lokacin da naga bana ganinsu tare na tambayesa ko akwai matsala? Shi da abokin nasa. Sai ya sanar min shi dai a saninsa bai masa komai ba ya janye daga jikinsa, ya kuma bisa ya bisa babu adadi danya faÉ—a masa amma yaÆ™i, daga karshe ma ya tattare kayansa da iyalinsa sukabar anguwar, bai kuma sake ganinsa ba har watanni sunja a lokacin. Na bashi shawarar ya Æ™ara nemansa dai, da muka sake haÉ—uwa na tambayesa sai yace ai yama bincika yabar gari. Iyakar abinda na sani kenan gaskiya”.
“Shi kuma Dawood É—in baka sake ganinsa ba kaima?”.
“Eh to gaskiya ban sake ganinsa ba. Dan ko’a rasuwar mahaifinsa sai wai-wai mukaji yazo yay gaisuwa ya tafi kawai. Daga nan kuma dai bamu sake jin É—uriyar tasa ba dan dama mahaifiyarsa bata raye tuni”.
Barrister dake faman kaÉ—a kai ya sake ajiye bironsa. “Uhhm yanzu to inaga mataki na biyu shine musan wane station suke. Ko kuma inda ita matar tasa take”.
Cikin damuwa Abu Zainab yace, “Munje inda muke tunanin samun nata bamu sameta ba. Sai dai an ambata mana sunan wanda ya saida gidan ga wanda ke ciki yanzu”.
“Miye sunan”.
“Ibrahim Askari”.
“Badamuwa kuje abunku, insha ALLAHU daga nan zuwa gobe za’a nema mana Ibrahim Askari É—in. Suma kuma zan É—an bincika ta hanyar jami’an dana sani a mabanbanta station na garin nan”.
Sosai kaka ya dinga ma barrister godiya. Hakama Abu Zainab. Shi dai faÉ—a musu yake karsu damu. Aje a cigaba da addu’a komai zai zama labari insha ALLAHU……

★★….. ★★…. ★★…..

Iffah kamar zatai kuka ta Æ™ara dailing number amma sai ma aka sanar mata switch up. Wani irin zafi da lugude Æ™irjinta ya shiga yi, ta shiga neman number Malam Fawzan cikin rawar jiki tunda dai shine ya bata number……….✍️

*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*

*DAUDAR GORA Billyn abdul*

*KI KULANI hafsat xoxo*

*A RUBUCE TAKE Huguma*

*RUMBUN K’AYA Hafsat rano*

*IDON NERA Mamuh ghee*

_LITTAFI DAYA: 400_
_LITTAFI BIYU: 600_
_LITTAFI UKU: 800_
_LITTAFI HUDU :1000_
_LITTAFI BIYAR: 1200_

_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_

_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_

_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_

_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_

_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_

_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_

ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN

MARYAM SANI
ACCESS BANK
0022419171

SAI A TURA SHAIDAR BIYAN

09033181070

IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA

09166221261

*ƳAN ƘASAR NIGER. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*

+227 90165991

Books biyar 1250CFA
Books hudu 1050CFA
Books uku 850CFA
Books biyu 650CFA
Bookk daya 450CFA

KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.

MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANE LOKACI.

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*

✨ÆŠ ✨
( )

 

Post a Comment

0 Comments