Daudar Gora Book 1 Page 24

Latest Posts

6/recent/ticker-posts

Ad Space

Daudar Gora Book 1 Page 24


24_*

……….Komai daya faru tsakanin Iffah da Hadima Banou akan idon Daneen Ammarah ne, dan itama tayi yunÆ™urin fitowar ne ganin Banou na tono a bayan windown Mamman sai ta hango Iffah na tahowa. Kasancewar ta ganta da rigar jikinta a É—azun yasa kai tsaye ta ganeta. Da farko gabantane ya fara faÉ—uwa da tunani iri-iri, shiyyasa ta tsaya domin ganema idanunta. Sai dai kalaman Iffah da yanayin Hadima Banou É—in ya sata shiga ruÉ—anin tunani. Idan har zata auna da hankalinta matsayin babba itama Iffah taga Hadima Banou ne shiyyasa ta fito, a yanayin Banou kuma ya nuna akwai wani É“oyayyen al’amari na rashin gaskiya tattare da ita. To amma su maiyasa a tsahon shekaru basu taÉ“a ganin wannan fuskar ta Banou É—in ba? Wacece Iffah? Anya kuwa ba akwai abinda ya kamata ta sani dangane da yarinyar nan ba?……

★Iffah da al’amarin wannan masarauta ya fara ruÉ—ama tunani tana shiga É—akin dake matsayin nata yanzu ta murza key. A jikin Æ™ofar ta jingina da lumshe idanunta tana sauke numfashi. Ita kanta taga Æ™arfin halinta yau, dan zata iya rantsewa bata san a ina ta samo wannan jarumtar ba. Idanun ta buÉ—e tare da riÆ™e Æ™ugu ta karyar da kai alamar nazari. In fa har ta canka dai-dai tabbas wannan hadimar mayya ce. Dan bata manta da wani labari da Iyyani ta taÉ“a basu ba na mayya yar DanÆ™o datai zamani a kauyen jumna shekarun baya. Babu banbanci da abinda taga matar nan tayi yanzu, dan da alama kurwar wani ta laso tazo ta boye a wajen. “Bahun ubancan, eh da gaske dai ashe lamushe Æ´aÆ´an mutane ake a masarautar nan tunda ga alama harda su bayi an barbaÉ—a musu muguwar tambaya. Shi baÆ™in babban dodon nasu nacinye mutanen gari su kuma bayi nacinye junansu a cikin gida”. Tai maganar a fili cikin Æ™ankance idanu na alamar tunzuruwa…
Murmushi Daneen Ammarah dake bakin Æ™ofa tsaye ta saki, dan nutsuwar da zuciyarta ta kasa mata ya sata biyo bayan Iffah, har ta kai hannu zatai knoking sai kuma ta fasa da tunanin inhar Iffah nada wani mugun nufi a kansu to baro can zata samu wani abun take aikatawa a yanzu. Dan haka ta É—an kara kunenta kaÉ—an jikin Æ™ofar, cikin Sa’a kuwa ta jiyo mi Iffah ta faÉ—a saboda yanda tai maganar da É—an zafi sai ta fita da É—an karfi kaÉ—an. Ƙofar ta fasa bugawa ta koma É—akinta da baya. Itama dai Æ™ofar tata ta sanyama key duk da tasan babu wanda zai shigo mata. Kai tsaye wadrob É—in ta ta nufa, a cikin wani akwatin Æ™arfe karami mai Æ™yau ta fiddo waya bayan ta danna madannan sirri ya buÉ—e. Wayar ta shiga Æ™oÆ™arin kunnawa tana mai rufo windows É—in É—akin nata. Sai da tai danne-danne kusan na mintuna biyu alamar text ta tura. Kira ne ya shigo, sai a ring É—in karshe ta É—aga, batare da jiran wani gaisuwa daga wancan ba cikin bada umarni tace,
“Daga yanzu zuwa safiyar gobe idan ALLAH ya kaimu ina buÆ™atar sanin komai akan Zawjata-almilk ta uku. Idan nace komai yana nufin komai da komai”. Kitt ta yanke kiran tana wani irin murmushi tun kan ma ta samu amsar data bukaci sani. Wayar ta kashe gaba É—aya ta sake maidata inda ta dakkota……

(Wai su kowa da tasa manufar ne????)

*_MALIKAT BUSHIRAT_*

Zaune take hakimce kamar ko yaushe cikin kwalliya mai matukar É—aukar idanu. Ga wani sihirtaccen Æ™amshi mai ratsa zuciyar duk wani mai shaÆ™a na tashi. Shi kansa falon kamshinsa na musamman ne. Gefenta na dama Jasrah ce itama cikin kwalliyar, zuwanta kenan sashen sakamakon aiken data samu daga Æ´ar uwar tata. (Itama dai Jasrah anan cikin masarautar take aure, tana kuma auren Æ™anin marigayi Tajwar Haysam ne da suke uba É—aya. Dan kamar yanda Tajwar Haysam suke su huÉ—u a É—akinsu suna kuma da Æ´an uba har su kusan tara, sai dai mata sunfi yawa a ciki. Su tarannan kuma Æ´aÆ´an mata uku ne. Mijin Jasrah shine babba a cikin Æ´aÆ´an amaryar Tajwar Haysam da ake kira Ameera Aasfah a masarautar. Mace ce mai kirki da sanin ya kamata, jininsu kuma yay matuÆ™ar haÉ—uwa da Malikat Haseena. Dan idan ka gansu bazaka taÉ“a É—auka kishiyoyi bane a sanda tana raye. Yaranta biyune ita kacal, Miran Arshaan shine babba, shine kuma É—a na takwas a wajen Tajwar Abdul-majeed, a maza kuma na uku, shine mijin Jasrah a yanzu, sai Æ™anwarsa Daneen Fu’ada, a yanzu haka tana aure itama. Ƙaunar dake tsakanin Malikat Haseena da Ameera Aasfah yasa shaÆ™uwa sosai a tsakanin Æ´aÆ´ansu, hakan yasa Tajwar Haysam ke kallon Miran Arshaan tamkar Æ™aninsa Miran Nayyar daya rasa, shine ma da kansa ya aura masa Jasrah. Wannan kenan, ALLAH yasa kun gane).
“Akia kince nazo amma kin kasa cewa komai? Wani abun ya sake faruwa ne?”.
Numfashi Malikat Bushirat ta sauke a hankali tana kallon Æ´ar uwar tata da takema kallo tamkar first born É—in ta. Kamar bazatai magana ba sai kuma ta nisa cike da kasaita. “Komai bai sake faruwa ba, sai dai ina gudun sake faruwar. Sanin kanki ne Jasrah ba lallai kosu waye su haÆ™ura ba dan yarinyar nan ta kuÉ“uta a yanzun, sannan ma bayan ita akwai sauran yaran biyu da har yanzu fargaba ta hanamu kaisu turakar Saifulmalik. Kin san kuma rashin kai su zuwa nan da É—an lokaci sai kinji an fara kace-nace”.
“Hakane Akia. Amma ke mikike son cewa?”.
“Zancen dai É—aya ne shine inajin tsoro, na biyu kuma da gaske yarinyar nan ta shiga raina fiye da duk matan da aka kawo gidan nan matsayin Zawjata-almilk”.
“Wlhy nima har cikin rai yarinyar ta shiga raina. Gata da tarbiyya daga ganinta, sannan itace mafi Æ™anÆ™anta a duk matan na Son”.
“Wannan yana É—aya daga cikin abinda ya sake jan hankalina a kanta Jasrah, shiyyasa yanzu da wani tunani yazo min nace bara nai shawara da ke. Shin kina ganin naima Mamma (Malikat Haseena) magana gobe idan ALLAH ya kaimu da Saifulmalik zaije gaisheta a kusanta shi da yarinyar nan suga juna? Sai nake ganin hakan zai canja wani babban al’amari da masu mana yankan baya ke Æ™ullawa. Tunda kinga dai duk matansa sai an kaisu turaka yake da damar ganinsu kamar yanda kowa yasan dokar kenan ga duk Zawjata-almilk tun Æ™arnin baya”.
“Eh gaskiya kuma wannan tunani ne mai Æ™yau Akia inhar Mamma zata amince É—in. Dan Kinga muma a karan kammu wata hanya ce da zamu fuskanci wani abu akan shi kansa..”
“Wannan gaskiya ne. Dan da gaske Jasrah a yanzu har shi kansa zuciyata rawa take ga al’amarinsa, dan abinda ke faruwa dole ne kowa ya zama abin zargi har mu kammu, ke nama takaice miki zance ni kaina yanzu ban yarda da kaina ba”.
Murmushi Jasrah tai har haÆ™oranta na bayyana. Tace, “Kai Akia kinada abin dariya wlhy wani lokacin. To inke baki yarda da kanki ba mu kuma dawa zamu yarda kenan?. Kawai dai inaji a jikina koma minene ya kusa zuwa Æ™arshe ta silar yarinyar nan tunda har ALLAH ya fara nuna musu iyakarsu suka gaza cin nasara a harin farko da suka kai mata. Yanzu dai bamu da lokaci, ki tattauna da Mamma É—in kawai. Hukuncin data yanke sai mu karÉ“a kawai”.
Malikat Bushirat ta jinjina kai kaunar Æ´ar uwar tata na sake ratsata. Koba komai idan ta tattauna da ita takanji sanyi a ranta…….

★★…. ★…. ★★…..

“Wai nikam É—azu ina Æ™oÆ™arin shiga fada naga kamar motarki ta gitta, kinje wani waje ne?”.
Shayin da take Æ™oÆ™arin zuba masa ta karasa tare da miÆ™a masa. Sai da ya amsa ta koma ta zauna tana mai É—an É—age kafaÉ—unta. “Kaima kasan fita ta bata wuce wajen Akia ai Abu Harith, wlhy itace fa tai min kiran gaggawa shine ka ganni na fitan. Amma lafiya kuwa har irin wannan lokacin kuna a fada?”.
“Uhm to lafiya lau za’ace, anyi baÆ™in bazata ne kawai ga Shahan-shan ya rigada ya shige kuma. Dole mu mukai zaman tarbarsu. Amma kiran gaggawa wata matsalar ne ta sake faruwa? Ko jikin Zawjata-almilk É—inne dai?”.
“No akan dai wadda ake cikine. Jikinta kuma Alhamdullah, idan ma ka ganta yanzu bazakace wani abu ya faru ba. Kawai dai Akia ce ke ganin ya kamata idan Shahan-shan yaje gaida Mamma gobe idan ALLAH ya kaimu Zawjata-almilk ta ziyarcesa ko hakan zai kawo wani sauyi kan abinda har yanzu muka kasa sanin kansa”.
“Amma baÆ™wa ganin hakan wani ganganci ne? Sannan dokace fa Shahan-shan baya ganin matansa sai a turaka”.
“Eh muma mun duba wannan É—in, dan haka ma bamu wani yanke shawara ba akace sai an sanarma Mamma. Amma kai ya kake gani akan hakan. Abu Harith wlhy Akia na bani tausayi matuÆ™a, a yanzu har takai da kanta itama zarginsa take shi yake É“arnar nan”.
“Ya ALLAH wannan wace irin magana ce haka? Miyasa zatai irin wannan tunanin akan É—anta. Bana jin Eshaan zai taÉ“a aikata makamancin hakan. Kawai dai akwai abinda yake ba daidai ba”.
“Sosai kuwa. Amma insha ALLAHU ta sanadin yarinyar nan kowa sai yaci Æ™aniyarsa. Dan haka kawai nakeji a jikina ita É—in haske ce a wannan daula. Tunda har gashi ta karya tarihin farko na azzalumai”.
“Haka muke fata, dan muma an tattauna akan hakan sosai jiya da yau a fada. Kusanma issue É—in da ake kai kenan kawai yanzu a majalissa. Sai na kisan hadiman can”.
“To ALLAH ya dafa mana mu da ku, ya kaimu ranar da zamu ga iyakar wannan al’amari”.
“Amin my meera”.
Yay maganar da wani salon kashe ido mai cike da soyayya da kaunarta. Murmushi tayi itama tana miÆ™ewa, “Bara na kimtsa kafin ka kammala ko”.
Kai ya gyaÉ—a mata idanunsa narke a kanta.. Tana juya baya ya bita da wani irin matsiyacin kallo mai ma’anoni da yawan gaske yana tsuke fuska da jan tsaki……

Jasrah kamar yanda Æ´ar uwarki ta faÉ—a miki kowa ba abin yarda bane yanzu.

★★…. ★★…..

Kamar yanda Malikat Bushirat suka tattauna da Jasrah batai Æ™asa a gwiwa ba tana idar da sallar asuba ta fita daga sashenta cikin badda kama zuwa sashen Malikat Haseena. Kasancewar ta sanarma Daneen Ammarah tare suka nufi É—akin Malikat Haseena É—in. Itama tasan da zuwan Malikat Bushirat É—in. Dan haka basu É“ata lokaci ba suka fara tattaunawa dan ta samu ta koma kafin gari yay haske. Da farko dai malikat Haseena ta kakkawo musu dokokin masarautar masu tsari dangane da haÉ—a Shahan-shan da Zawjata-almilk kai tsaye ba’a turakarsa ba. Sai dai bayanin da sukai mata da nusar da ita abinda suke son tabbatarwa yasa itama ta amince. Sai dai da sharaÉ—in komi ya biyo bayan hakan laifinsu zata gani. Cike da yaÆ™inin fatan karma wani abu ya faru suka amince. Dan haka tai musu sallama ta koma. Daneen Ammarah da tunaninta nada banbanci da na Malikat Bushirat akan wannan haÉ—uwa tai murmushi a ranta tana mai addu’ar samun nasara. Domin wannan yaÆ™i kamar natane ita kaÉ—ai sakamakon itace kawai tasan É“oyayyen sirrin daba kowa ya sani ba sai UBANGIJIN talikai. Fatanta shine komai yazam yana gangarowane ga faÉ—an karshe akan maÆ™iya koda ita zata rasa rayuwartane a yayin gumurzun…

(Daneen Ammarah kin fara bani tsoro fa).

*_SHAHAN-SHAN_*

Yau É—in ce dai ta kasance rana da yake zuwa gaishe da kakarsa Malikat Haseenah. Irin wannan rana kuma tana zuwane sau É—aya a kowanne wata. Sai dai idan ita ke buÆ™atar ganinsa ta samesa a sashensa. Amma a kowane wata yanada ranaku biyu na ziyartar kakar tasa da mahaifiyarsa. Malikat Haseena yake fara dubawa a farkon wata, Malikat Bushirat a tsakkiyar wata. Duk da fitace ta dare da ba lallai kowa ya gansa ba ya kasance cikin shiri mai É“oye ainahinsa, ga wani Æ™amshi na isassun da suka isa na tashi tattare da shi. Takunsa da Æ™arfin izzarsa ya isa tabbatar maka eh lallai Shahan-shan ne da kansa. Ƙasaita jinin jikinsa ce, kamewa da isa adonsa ce, kwarjini da nutsuwa halittarsa ce….
Duk da farkon dare ne dan kwata-kwata Æ™arfe takwas ne, amma masarautar tayi tsit kowa ya nutsu a inda ya dace saboda sanin wannan rana ce da Shahan-shan ke fitowa zuwa sashen Malikat Bushirat. Babu wani Hadimi dake kai kawo sai Ghazi da masu tsaro da suka tsare ko’ina fiye da kullum. Hakama sauran jama’a in ba babba mai faÉ—a aji ba babu wanda keda hurumin wani kaikawo a irin wannan daren dake zuwa a wannan rana saboda fitowar Shahan-shan………..✍️

*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*

*DAUDAR GORA Billyn abdul*

*KI KULANI hafsat xoxo*

*A RUBUCE TAKE Huguma*

*RUMBUN K’AYA Hafsat rano*

*IDON NERA Mamuh ghee*

_LITTAFI DAYA: 400_
_LITTAFI BIYU: 600_
_LITTAFI UKU: 800_
_LITTAFI HUDU :1000_
_LITTAFI BIYAR: 1200_

_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_

_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_

_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_

_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_

_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_

_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_

ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN

MARYAM SANI
ACCESS BANK
0022419171

SAI A TURA SHAIDAR BIYAN

09033181070

IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA

09166221261

*ƳAN ƘASAR NIGER. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*

+227 90165991

Books biyar 1250CFA
Books hudu 1050CFA
Books uku 850CFA
Books biyu 650CFA
Bookk daya 450CFA

KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.

MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.

 

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*

✨ÆŠ ✨
( )

 

Post a Comment

0 Comments