Daudar Gora Book 1 Page 27

Latest Posts

6/recent/ticker-posts

Ad Space

Daudar Gora Book 1 Page 27


27_*

 

…….“Assalamu alaikum”.
Ya faɗa a daƙile saboda rashin sanin wanene. A maimakon amsa masa sallamarsa aka ambaci sunansa tamkar a lokacin ake raɗa masa shi.
“Barrister Abdallah Ibn Adam Aas! Kar kayi taurin kai, dan zaka iya rasa kanka dama waÉ—an da kake yunÆ™urin taimakawar. Ni umarni nake baka ba shawara ba kamar shi, domin hatta iyalanka ba zasu tsira ba daga tarko na”..
ÆŠan zabura Barrister yay tamkar wanda cinnaka ya ciza. Daga can aka cigaba da magana cike da isa. “Suna hanyar zuwa gareka, ya rage naka tun yanzu ka raba gari da su, ka kuma gargaÉ—i surikinka. Na barka lafiya”. Yana kokarin yin magana Æ™itt aka yanke kiran. Ciro wayar yay da sauri daga kunensa, ganin ta yanke yay Æ™oÆ™arin kiran number…
Mutumin dake tare da shi ya miÆ™e yana dariya. “Barrister shawara karma ka wahal da kanka dan basake samunsa zakai ba har abada in har a wannan layin ne. Na barka lafiya”.
Da Æ™yar Barrister ya kwato numfashinsa gab da mutumin zai fice. Cikin jarumtarsa ya dakatar da shi a É—an tsawace. “Ni kurari ko gizago basa firgitani ai. Dawowa ka É—auka trash bag É—inka zai fi maka alkairi fiye daka barta anan ta zamewa rayuwarka BAYA DA ƘURA. wannan shawara ce”.
Har cikin rai maganganun Barrister sun sokesa. Amma kasancewar sa ɗan hannu a iya bariki sai ya saki murmushi. Batare da yace komai ba yay salute ɗin Barrister dake masa kallon ƙasƙanci yay ficewarsa.
Baya Kaka da Abu Zainab dake yunÆ™urin shigowa office É—in suka ja dan kaÉ—an ya rage suyi gware. Suna masa sallama bai ko amsa su ba yay musu kallon Æ™asa da sama yay wucewarsa. Basu damu ba, dan daga ganinsa kaga babban mutum. Barrister da aka bari da juyawar kai ya amsa musu sallama cike da son danne É“acin ran dake a fuskarsa. Sun gaisa da mutuntawa kamar yanda suka saba. Fuskar Kaka da É—an murmushi ya ce, “Ashe kuma an dace da sanin inda suke?”.
Murmushin Æ™arfin hali Barrister yayi da jinjina kansa, ya jawo wani file dake gefensa. “Nima banyi tunanin abin zai zo mana da sauÆ™i haka ba Baba. Amma Alhamdullah addu’a bata faÉ—uwa Æ™asa banza. Inaga muyi azamar zuwa ma kar’a samu wani tazgaro kuma kasan halin Æ™asar tamu”.
Daga Kaka har Abu Zainab sunyi na’am da hakan. Duk suka miÆ™e babu É“ata lokaci suka fice kowa da abinda ke masa kai kawo a cikin rai musamman Kaka da Barrister…..

*_MASARAUTA. (MALIKAT BUSHIRAT_*

Cikin zumuÉ—in son jin yaya haÉ—uwar Shahan-shan da Zawjata-almilk ta kasance a jiya Malikat Bushirat tai shirin ziyartar sashen Malikat Haseena a yau. A Æ´an rakkiyarta har da Jasrah dake son sake duba jikin Iffah. Tuni Æ´an leÆ™en asirin cikin hadimai sun kwasa zuwa sassan iyayen gijinsu kuwa. Dan wannan ya zama kamar al’ada a masarautar kowane É—an leÆ™en asiri kan kai wa uwargijiyarsa ko uban gidansa duk wani motsin wani babba a daular. Ta wannan hanyar ne a mafi yawan lokuta abubuwa ke yaÉ—uwa kunnen duk wani mai faÉ—a aji na gidan musamman abinda ya kasance na sirri.
Malikat Bushirat ta samu tarba ta girmamawa ga surukar tasu a fadarta. Tuni hadimai sun cika gabansu da kayan motsa baki. Kasancewar ganawar ta shafi wani yanki na É“oyayyen sirrinsu duk wani hadimi aka sallamesa. Katafaren falon ya kasance daga Malikat Haseena sai Malikat Bushirat da Jasrah sai Daneen Ammarah. Tattaunawar ta jasu tsahon lokaci kafin Malikat Haseena ta aika amintacciyar hadimarta Banou kiran Iffah….

★Sam Iffah dake cikin wani yanayi na tsananin faÉ—uwar gaba da sanyin gaÉ“É“ai sakamakon mummunan mafarkin da tai akan su Babiy a barcin zuhur daya figeta bata san mi ake ba saboda bata fita ko’inaba yau iyakarta É—akinta. Yanzu hakama da aka idar da sallar la’asar tana tsumayen Daneen Ammarah ne kamar yanda ta saba, dan duk yinin yau ma basu haÉ—u ba tun bayan idar da sallar asuba dai data fita ta gaishesu kamar yanda ta saba ita da Malikat Haseena. Hadimai dai sun kawo abinci tare da saÆ™on gaisuwa daga Daneen Ammarah É—in É—azun da rana akan cewar tana nan tafe. Malikat Haseenah ma kullum da kanta takan zo ta duba ta, kasancewarta tsohuwa mai dattako da iya zama da mutane tuni ta shige zuciyar Iffah itama, dan duk da bata da sakewa da yawan fara’a har dan jan Iffah take da hira. Sallayar datai sallar ta linke har yanzu jikinta a sanyaye ga damuwa fal ranta akan iyayenta, acan Æ™asan zuciyarta takeji akwai wani mummunan abu dake sake tunkarota koma ya riga ya iso garetan ta hanyar iyayenta batare data sani ba. Yanayin É—an zafi da ake ya sata yaye mayafin abayan data naÉ—e kanta da shi ta ajiye, É—aurarren dogon baÆ™in gashinta dake reto a tsakkiya ya bayyana. Abincin da aka shirya mata tun É—azun da bata ci ba ta nufa, ta bubbuÉ—e taga komai, batama jin cin komai har yanzun, dan haka ta tsiyayyi madara kawai da shanta tamkar al’adar Æ´an Æ™asar ne. Tana buÆ™atar fara canja kayanta zuwa marasa nauyi, dan haka ta ajiye kofin madarar a bedside drawer. Toilet ta fara shiga ta fito sannan ta shirya cikin wata yar yololuwar rigar mara nauyi mai zubin shimi. Iyakar rigar gwiwar ta ne, gata kalar fari da adon jajayen firanni. Ta matuÆ™ar haskata da fidda Æ™uruciyarta tamkar Æ´ar budurwar balarabiya. Turarrukan da Daneen Ammarah ta tule mata ta zaÉ“a kusan kala uku ta fesama jikinta. Cikin nutsatstsen takunta ta dawo saman gadon tana mai kallon fatar hanunta dake jajir saboda saÉ“ar da tayi. “ALLAH dai ya isana wlhy” ta faÉ—a cike da halin tsiwarta tana jan bargo ta rufa iya cinyoyinta bayan ta jingina jikinta da fuskar gadon. Littafin da take rubuce-rubucenta na duk abinda ya faru ta É—auka ta buÉ—e ko zata ji sassaucin tunane-tunen da zuciyarta ke mata marasa daÉ—i akan iyayenta, dan sam mafarkin nan yaÆ™i barin ranta koda na sakan É—aya… A zahiri rubutun tai shirin fawara, dan yanda ta tsurama littafin ido da riÆ™e biron da nutsuwa matuÆ™a zai saka ka hasashen haka. Sai dai sam ko kalma biyu ta kasa rubutawa tamkar ma an mata wankin Æ™waÆ™walwa komai ya gudu, hasalima nisan da tai a tunani yasa bibbiyu take ganin rubutun baya da tayi….
Knoking Æ™ofar da akai ya sata jan numfashi ta fesar, sai kuma taja mayafin dake gefenta ta yane jikinta har saman kanta tare da amsawa da “Yes! Kowaye ya shigo”.
A É—arare hadima banou ta shigo, tsananin tsoron Iffah shimfiÉ—e akan fuskarta ya kasa boyuwa. Daga bakin Æ™ofar ta zube muryarta na É—an rawa kamar yanda jikinta ke tsuma. “Amincin ALLAH da lafiya su tabbata ga Zawjata-almilk”.
Harara Iffah dake kallonta ta zabga mata. “Ina tare da masu lashe kurwar mutane irinku lafiyar zata tabbata a gareni? mtsoww!! Malama faÉ—i abinda ya kawoki bana son gulma”.
Ƙasa Banou ta sakeyi da kanta muryarta na rawa, dan harga ALLAH tana shakkar wannan yarinya da ko magana gatsau take yinta babu alamar shakku tattare da ita. “Uhm uhm dama Malikat ce take buÆ™atar ganinki”.
Hannu kawai Iffah ta É—aga mata, dan har cikin rai ta tsani matar nan matuka. Sai da ta miÆ™e zata buÉ—e Æ™ofa sannan tai magana a gadarance. “Ki jirani a Æ™ofa, saura kuma kafin na fito ki lashe mun hadimai azzalumar bamza”.
Da rawar jiki data harshe Banou tace, “Hakan bazata faru ba ranki ya daÉ—e”.
“Uhm munafuka kamar gaske”.
Iffah ta faÉ—a tana sauka a gadon cikin mita……

★Tunda suka shigo ko sau É—aya Iffah bata iya É—aga kai ta kalla ko É—aya a cikinsu ba. SaÉ“anin su da duk suka zuba mata ido cike da jin Æ™aunarta a rayukansu. Cike da nutsuwarta ta karasa garesu, maimakon kujera da duk suke zaune sai ta kai Æ™asan lallausan dardumar…
“Haba Ibnati tashi ki hau sama mana”.
Jasrah tai yunÆ™urin dakatar da ita. Kai Iffah ta girgiza da É—an murmushi a fuskarta, “A’a nanma ya isa”. Cike da sha’awa da jin daÉ—i duk suke dubanta. Ta juya ta gaishe da Malikat Haseena, da fara’a da kulawa ta amsa mata tana mai sanya mata albarka. Cikin jin daÉ—i ta juya gasu Malikat Bushirat ta gaidasu suma. Suma da kulawar suka amsa mata, dan duk Æ™asaita da jin kan Malikat Bushirat sai ta tsinci kanta da murmushi da sauÆ™aÆ™awa akan yarinyar saboda kwarjini da tai mata. Shiru na wasu Æ´an sakkani ya biyo baya, kafin Daneen Ammarah ta katse shirun ta hanyar kiran sunan Iffah.
Ta amsa mata da girmamawa sai dai bata iya ta É—ago kanta ba. Daneen Ammarah ta sake kiran sunanta da faÉ—in, “Kinga É—ago ki kallemu”. Da Æ™yar ta iya dauriyar bin umarninta. Dan duk rashin jin Iffah tana da wani hali na girmama duk mai nuna mata Æ™auna koda bai cancanta ga sauran mutane ba. “Ibnati nasan nan zuwa yanzu duk kin sammu ko?”.
“Eh Mamy”.
“Amma baki san matsayinmu ba?”.
Nanma tace “Eh Mamy”.
“To Alhamdullah yau duk zaki sani. Ina son ki bani dukkan hankalinki nan ki kuma saurare ni yanda ya kamata”.
Ta jin jina mata kai.
“Kamar yanda nasan kikaji Mamma a garemu mahaifiya ce, itace ta haifi Hama (Suruki) É—in ki, da ni dama wasu biyu da zaki sani anan gaba sai dai É—aya ya rasu”.
“ALLAH ya gafarta masa”.
Ta faÉ—a cike da rauni. A tare suka amsa mata da Amin. Daneen Ammarah ta ciga da faÉ—in, “Wannan da kike jin ana kira Malikat Bushirat itace Hamah (Suruka) É—inki data haifi Shahan-shan na yanzu kuma mijinki da yazo nan jiya……”
A razane Iffan ta waro idanu Æ™irjinta na wani irin harbawa kamar zai wantsalo. Cikin subutar baki ta ce, “Shahan-shan! Na jiy…..” sai kuma tai shiru ta haÉ—iye sauran maganar saboda tuna a inda take…
“Kin sanshi ne kafin jiya?”.
Malikat Haseena dake nazartarta ta jeho mata tambayar a bazata. Da sauri Iffah da zufa ta jiÆ™ema dukkan jiki, ta girgiza kanta. Kasancewar ta gwanar wayo tai saurin faÉ—in, “Mamma ina mamaki ne dai, ban zaci ganin Shahan-shan É—in nada sauÆ™i kamar haka ba”.
Kusan a tare suka saki murmushi saboda hango tsantsar Æ™uruciya a maganar tata. Sai dai malikat Haseena tsaf ta gama karantar Iffah waskewa tai. Amma kasancewar ta tsohuwa mai dattako sai ta dake itama ta shiga jerin Æ´an murmushin.. Daneen Ammarah ta cigaba da faÉ—in, “Wannan Æ™anwa ce ga Malikat Bushirat, Khaalah (Aunt) ga mijinki. Na baki ne a dunÆ™ule iyamu da muke anan saboda muhimmancin abinda zakiji a yanzu”.
Kai Iffah ta jinjina mata da alamun gamsuwa. Jasrah ta cigaba daga inda Daneen Ammarah ta tsaya.
“Ibnati dalilin miki wannan dogon sharhin a kammu shine fara aikinki matsayin Zawjata-almilk a wannan masarauta. Alhamdullah tunda kinji sauÆ™i zaki koma sashenki kamar sauran Zawjata-almilk guda biyu, sai dai zaki samu horo daga wasu amintattunmu matsayinki na Zawjata-almilk. Mun zaÉ“eki ne saboda nutsuwarki da tarbiyyarki. Basai mun zaman sharhi akan abinda ya faru ba a baya kasancewar kema Æ´ar kasa ce kin san komai na dangane da mutuwar matan Shahan-shan da suka gabata.”
Iffah ta haɗiye kududun baƙin cikin daya tokare mata maƙoshi akan famin rasa ƴan uwanta da tai da ƙyar ta jinjina kanta.
Malikat Bushirat ta amshe da cigaba da faÉ—in, “Ibnati kece zaki zama mutum ta farko a rayuwa da zan nema alfarma a gareta, hakan kuma ta faru ne saboda jinki da nake a cikin raina da kallon da duk muke miki anan matsayin wani haske da insha ALLAH zai haska mana duhun da muke ciki. Muna son ki shiga jikin Saiful-malik domin binciko mana ainahin minene matsalar, saboda dukkan waÉ—an can matan da aka rasa daga kaisu turakarsa ne ake samun matsalar. Mun miki alÆ™awarin baki dukkan kariyar da bazamu bari ki cutu ba….”
(Kariyar UBANGIJINA zata kasance tare da Ni). Iffah ta ayyana a zuciyarta.
Malikat Haseena ce ta cigaba da faÉ—in, “Zamu fara ne da matakai da hanyoyin dinga haÉ—uwarku daga nan zuwa wani lokaci, fatanmu ki zama mai saka ido a dukkan wani motsinsa, a karan kansa, da duk wasu wanda zasu mu’amulancesa har a cikin hadimai. Kiyi takan tsantsan, dan mutum ne shi mai wayo matuÆ™a, sannan mai wahalar sha’ani da fahimta. Ba’a gane mi yake nufi ko minene a ransa akan fuskarsa, kar ki yarda ki bashi wata damar da zai iya zargi a kanki. Fatanmu dai ki zama jaruma a dukkan al’amuransa dama na kowa dake a wannan masarauta, duk abinda kikaci karo da shi ba dai-dai ba kiyi maza ki sanar da É—aya daga cikinmu”.
Zantukan nasu ya saka zuciyar Iffah dinga tsalle-tsalle a kan dalilai biyu…….✍️

 

*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*

*DAUDAR GORA Billyn abdul*

*KI KULANI hafsat xoxo*

*A RUBUCE TAKE Huguma*

*RUMBUN K’AYA Hafsat rano*

*IDON NERA Mamuh ghee*

_LITTAFI DAYA: 400_
_LITTAFI BIYU: 600_
_LITTAFI UKU: 800_
_LITTAFI HUDU :1000_
_LITTAFI BIYAR: 1200_

_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_

_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_

_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_

_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_

_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_

_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_

ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN

MARYAM SANI
ACCESS BANK
0022419171

SAI A TURA SHAIDAR BIYAN

09033181070

IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA

09166221261

*ƳAN ƘASAR NIGER. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*

+227 96 09 67 63

Books biyar 1250CFA
Books hudu 1050CFA
Books uku 850CFA
Books biyu 650CFA
Bookk daya 450CFA

KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.

MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.

 

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*

✨ÆŠ ✨
( )

 

 

Post a Comment

0 Comments