Daudar Gora Book 1 Page 28

Latest Posts

6/recent/ticker-posts

Ad Space

Daudar Gora Book 1 Page 28


28_*

……..Na farko ji a ranta UBANGIJI ya amsa mata addu’ar ta akan burin data shigo da shi Daular ruman. Na biyu minene dalilin waÉ—an nan mutane na buÉ—e mata cikinsu?. Na Æ™arshe da yafi kowanne razani da ban mamaki a Æ™waÆ™walwarta dama suma sun san shike aikata kisan kenan? Amma suka zaÉ“i yin shiru saboda ba Æ´aÆ´ansu ake halakawa ba kokuwa suma tsoronsa sukeji? A É—an Æ™aramin tunaninta tanaga zasu iya yin amfani da Æ™wanji wajen sanin mi Shahan-shan É—in ke aikatawa musamman Malikat Haseena da Malikat Bushirat. Amma miyasa suka zaÉ“i yin amfani da ita? Kodai sun gama gane manufarta ne a kansa…..?
“Ibnati!”.
Daneen Ammarah ta katseta daga nisan da tai a tunani ta hanyar kiran sunanta da taÉ“ata. Firgigit kuwa ta kawo ajiyar zuciya. “Karki kasance a dogon nazari, manufarmu ta sakaki a wannan sabgar tana da nasaba ne da dalilai biyu. Na farko juriyarki ta bamu Æ™warin gwiwar kallonki a jaruma. Na biyu jinki wata abu mai muhimmanci da muke fatan nasara ta dalilinta kodan tsallake tarkon masu aikata wannan É“arna da kika tsallake a harin farko da muke jin shine lagon da aka dinga É—anawa a farko wajen salwantar da rayukan da suka gabata….”
“Mamy nima zata yuwu bana tsallake bane dan nafi Æ™arfinsu, maybe na tsallake ne saboda tsayawarku da fatanku akan ganin na tsallake É—in. Amma tabbas zan iya sadaukarwa, zan kuma iya bin umarninku badan inajin Æ™arfina ya kai ba sai dan kun isa ku bani umarni”.
Su dukansu kalamanta sunyi wani tasiri na musamman a zukatansu tare da ƙawatata a cikin idanunsu. A wani gefen sunyi amanna irinta ɗansu ya dace ya samu tun farko, dan ƙarfin gwiwarta sunyi dai-dai da Zawjata-almilk da akafi buƙata ga kowane Shahan-shan. Sannan Malikat da sukema kansu fata.
“ALLAH yay miki albarka”.
Suka faɗa kusan a tare su duka huɗun. A kan laɓɓanta ta amsa da amin.
Sun cigaba da tattaunawar da gaba É—aya ta saka Iffah cikin Æ™agara, Æ™agara mai nasaba da shiga ruÉ—anin wani furici daga Daneen Ammarah. Wai jiya Shahan-shan ne wanda ya ziyarcesu a wannan falon, tana buÆ™atar samun filin tunani dan zuciyarta da Æ™waÆ™walwarta fa gaba É—aya sun kulle, ruÉ—ani ya gama mamaye duk wani hangenta da dama bai wuce iya tsayin Æ™afafunta da shekarunta ba….

★★….

A hankali ta maida Æ™ofar ta rufe tare da jingina a jikinta ta lumshe ido da sauke numfashi tamkar mai kokawar jawosa. Shin murna zatayi a wannan gaÉ“ar ko kuwa shiga ruÉ—ani?. Idan ance Shahan-shan ne a jiya ta yarda, shi kuma wanda tai gamo da shi a mabanbanta wajeje kafin shigowarta masarauta wanene shi?. Wannan tambaya tafi kowace tambaya girma da girgiza zuciyarta a duk abubuwan dake cin ranta. “Kai nifa nama ruÉ—e wlhy”.
Ta faÉ—a a zahiri tana zamewa cikin sarewa ta zube Æ™asa. Ta jima a wajen cikin halin shiru da ambaton hasbinallahu wa ni’imal wakil ko zata samu dai-daiton komawa cikin hankali dan da gaske komai na halittarta mai motsi ya raunana da rauni mafi ban tsoro da shiga ruÉ—ani. Tsahon lokaci ta kwashe a wajen tana kokawa da raunin zuciyarta da rashin Æ™arfin gudanar jini. Fahimtar wancan tunanin na buÆ™atar lokaci ya sata turesa ta maida hankali akan tattaunawarsu da su Malikat. Tabbas wannan shine babban Æ™udirinta dayin Æ™undunbalar juriya na tunkarar rayuwar da bata da tabbacin tsallakewa. Duk da tasan anfi Æ™arfinta, dama duk wani mai Æ™arfi da take kallon Æ™arfinta ta zaÉ“i fuskantar mutum mafi girman iko da tsaro domin É—aukar fansa. A kwanakin da suka gabata na kasancewarta cikin wannan daula ta fara fidda ran samun cikar burinta saboda dalilai masu yawa. Ciki harda rashin samun koda Æ™anÆ™anuwar Æ™ofar sanin minene ma daular ruman É—in ta Æ™unsa balle Shahan-shan da kansa. Sai gashi a yau cikin sauÆ™i an buÆ™aci kaita inda zuciyarta ta fara raya mata zuwansa ba Æ™aramin tsalle bane da ba’a da tabbacin fita idan an shiga, aka kuma sanar mata wani yanki na sirrin daular ruman mai girman gaske da ko na ciki basu san da shi ba Æ™ila. “Anya babu wani abu a ran mutanen nan saÉ“anin abinda suka faÉ—a?” bakinta ya furta a zahiri cikin sake dulmiya a ruÉ—ani. (Koda akwaisa yardar ki dasu ce zata baki ilimin sanin hakan) zuciyarta ta faÉ—a cikin Æ™arfafata da ture raunin dake neman rinjayarta….
Knoking Æ™ofar daya wanzu a dai-dai lokacin ya sata jan numfashi a sauÆ™aÆ™e. Da Æ™yar ta iya miÆ™ewa daga zaman daÉ“aron da tayi ta buÉ—e. Daneen Ammarah ta sakar mata murmushi. Cikin yaÆ™e ta mayar mata da murtani da matsawa ta bata hanya. Rissinawa hadimar da suke tare tai ta gaisheta, hannu kawai ta É—aga mata alamar amsawa tana bin ledar hanunta da kallo……

★★…. ★…. ★★…..

Kamar yanda aka sanar da Barrister kai tsaye station É—in da akace su Babiy suke suka nufa. Kasancewarsa babba kuma sananne basusha wahalar ganin ogan station É—in ba kai tsaye. Sunyi gaisuwa irin tasu ta manyan ma’aikata, su kai kuma gaisuwar girmama juna da su Kaka.
Barrister ya gabatar da kansa, ya kuma gabatar da abinda suke tafe da shi harda hoton su Babiy domin sauÆ™aÆ™awa. Jami’in yay shiru yana kallon hotunan kamar mai hasashe, sai kuma ya É—ago ya kalla Barrister “Gaskiya banajin akwai waÉ—an nan mutanen a wannan station É—in Barrister”.
Barrister daya fahimci matsala ce ke neman shigowa yay É—an murmushi da muskuta zamansa. “YallaÉ“ai adai sake dubawa, zata iya yuwuwa ko akwaisu É—in baka da labarin hakan. Amma tabbas suna a wannan station É—in. A matsayina na Barrister ba nazo nan dan a bani belinsu bane ba, duk da nasan basu da hannu a abinda ake zarginsu. Nazo ne dan na gana da su, sannan a miÆ™asu kotu saboda nasan dai ita matar data saka aka kawosu nan burinta a kwatar mata hakkin mijinta”.
“Iya gaskiyata nake faÉ—a maka Barrister babu waÉ—an nan mutanen a wannan station É—in. Amma mizai hana ku sami ita matar na tabbata tunda tare da ita akaje tasan wane station ne”.
Barrister yay shiru yana kallonsa cike da nazari. Hakama Kaka da Abu Zainab. Kusan minti biyu shiru babu wanda ya motsa, kafin Barrister ya miÆ™e yana É—an murmushi ya bashi hannu. Suma su Abu Zainab miÆ™ewar sukai…

Da kallo ya bisu har suka gama ficewa, ya kai hannu kan wayarsa dake saman desk É—in sa yana wani murmushi. A bugu biyu aka É—auka wayar daya kira. Sallama kawai yay da faÉ—in, “Kamar yanda kai hasashe ranka ya daÉ—e yanzu suka bar office É—ina”.
Shiru yana sauraren mi’ake faÉ—a daga can, sai kuma yay murmushi da amsawa da “Angama ranka ya daÉ—e”. Daga haka ya ajiye wayar yana wata Æ´ar iskar dariya…

Abu Zainab daya kasa fahimtar komai saÉ“anin Kaka da Barrister dake hangen wani abu dalilin kashedi da akai musu kafin zuwansu nan dama ya katse shirun da motar ta É—auka ta hanyar nisawa. “Anya kuwa wannan jami’in akwai gaskiya a maganarsa Barrister. Kagafa yanda yake Æ™yaf-Æ™yaf da idanu kamar tsohon É—an jari hujja. Nifa wannan al’amari ya fara bani tsoro wlhy”.
Barrister da zuciyarsa ke kai kawo ya fesar da huci, “Kana tunanin yaÆ™i faÉ—a mana gaskiya ne Zakariyya?”.
“Fuskarsa ta nuna hakan ai Barrister, ko kuwa Kaka?”.
Kaka da shima dai yake aune-aunensa a rai ya girgiza kansa. “Zata iya yuwuwa gaskiyar ya faÉ—a, sai dai kumin wani taimako É—aya dazai warware mana gaskiyar tasa ko saÉ“aninta, bayan nan zan sanar muku abinda ya faru kafin zuwanmu nan”.
Barrister da shima abinda ke’a ransa kenan ya É—an juyo ya kalla kaka ta madubi, “Muna jinka Baba”.
“Muyi gaggawar isa gidan Dawood”.
“Shawara mai Æ™yau Baba”.
Barrister ya faÉ—a yana juya motar hanyar da zata kaisa gidan Abu Moosa.

★★… ★★… ★★…

“Mamy kuma duka wayar da lap-top É—inne nawa?”.
Iffah ta faÉ—a da mamaki. Murmushi Daneen Ammarah tayi, “Ibnati wannan ai ba komai bane ba, sannan ko baki faÉ—a ba kina buÆ™atar su tare da ke kodan ki dinga jin motsin gida. Na biyu kuma wannan aikin da zaki fara kowa yasan mai haÉ—ari ne, dolene ki kasance da waya a duk inda kike a masarautar nan. Da zarar Kinga abinda zuciyarki bata kwanta da shi ba a cikin mu huÉ—un zaki iya kiran kowa ki sanar masa. Lap-top kuwa ni naga ya dace na kawo miki ita domin É—ebe kewa. Amma kiyi taka tsantsan ki kuma kula sosai, dan samun waÉ—an nan na nufin zaki iya mu’amula da kowa musamman a yanar gizo batare da kin samu tabbacin wanene É—in ba”.
“Haka ne Mamy, insha ALLAH zan kiyaye. Nagode sosai ALLAH ya saka da alkairi”.
“Karki damu kin cancanta ne ai”.

★Iffah ta daka tsallen murna bayan ficewar Daneen Ammarah, harda Æ´ar rawarta. Duk wani tunani da kaikawon da zuciyarta ke mata akan Shahan-shan zuwan wannan waya da lap-top ya kauda mata shi. Domin a ganinta dama biyu ce tazo mata a lokaci guda kuma zata damata ta yanda dole sai Shahan-shan ya shata. Yanzu dai abu na farko da zata fara shine malam Fawzan. Ta tura masa saÆ™o bayan nemansa da tai shi da abokinsa wayar Arfa dake hanunta ta mutu ba caji, tana buÆ™atar tasan ko yaga saÆ™on? Ya kuma iyayenta suke?.
Samun wayar da caji yasa tun a daren ta haɗata, duk da taga akwai sim card batai amfani da shi ba ta cire na Arfa ta sanya. Tamkar jira saƙon Malam Fawzan ne ya fara shigowa, jikinta har tsuma yake wajen buɗewa. Batako kai ƙarshen karantawa ba kira ya shigo. Gabanta ne ya faɗi ganin baƙuwar lamba, amma tsabar ƙarfin hali sai ta ɗaga.
“Sir!”.
Ta faÉ—a cikin gwalalo idanu da nufar Æ™ofa da sauri ta saka key. Daga can aka amsa mata da “Na’am Fareedah. Ina kika shiga haka? Tun bayan ganin saÆ™onki na kasa samunki, har zuciyata ta karaya da ko wani ya gano ki ne?”.
“Babu wanda ya gano ni Sir, akasi aka samu wayar ta mutu, na kuma rasa ta yanda zanyi cajinta dan na manta da cajan a gida”.
“Ayya. Kin ganni akoda yaushe cikin gwada wayarki nake koza’a dace. Saboda ke na samar da wannan layin na sirri. Yanzu ma gwadawa kawai nake amma banyi tunanin samunki ba sam”.
Iffah ta share hawayen da suka silalo mata tana É—an murmushi. “Nagode Sir, koda banyi nasara ba bazan taÉ“a mantawa da kai ba. Ina fatan ka bincika min su Ummu. Dan sam na kasa samun kwanciyar hankali na rashin jin su”.
ÆŠan jimm yay kamar mai tattaro abin faÉ—a, sai kuma yay É—an murmushin basarwa. “Suna lafiya dan har gida naje, sai dai ban samu shiga ba kasancewar suna tare da tsaron dakarun masarautar har yanzu. Amma nayi Æ™oÆ™ari mun haÉ—u da Hanash….”
“Amma miyasa wayoyinsu basayi?”.
Ta katsesa a Æ™agauce. Da Æ™yar ya iya tattaro abin faÉ—a a wannan gaÉ“ar ma. “Shi Babiy wayarsa ta samu matsala ne. Hanash kuwa network ne dan yace min shima yasha nemanki amma baya samunki”.
“Bani da lafiya ne, ba koyaushe kuma wayar ke kunne ba. Amma yanzu zan sake nemansa insha ALLAHU dan ina matuÆ™ar bukatar son naji muryoyinsu kozan samu nutsuwa”.
“Hakan yana da Æ™yau. ALLAH kuma ya Æ™ara lafiya. Kinyi waya da abokina kuwa?”..
“Eh nayi, amma kamar yanda na sanar maka a text message an É—aga amma ana mun wani shirmen banza. Daga Æ™arshe ma akace wai na saÉ“a lamba”.
Karan farko malam Fawzan yay Æ´ar dariya. “Taku ne kawai irin na masu iyawa. Amma a yanzu na tabbatar zai saurareki”.
Iffah ta É—an taÉ“e baki kamar tana gabansa. “Ni ALLAH harna É—auka ko ka yaudareni ne ka bani number daba itaba ma”.
“Iffah koda abin wasa kikazo da shi bazan masa riÆ™on banza ba balle wannan mai matuÆ™ar muhimmanci da ma’ana. Yanzu dai ina fatan wayar taki akwai caji?”.
“Ai bama waccan bace, sabuwa fil aka bani a kwali yau harda lap-top”.
Jimm yay na wasu Æ´an sakkani. Sai kuma ya cire wayar a kunnensa ya duba. Tuna ashema shine ya kirata ya sashi sake maidawa. “Amma baÆ™ya zargin akwai wani dalili a baki wayar? Mutanen nan fa sunada haÉ—ari sosai Iffah. Bazan É“oye miki ba inajin tsoron Æ™arfin ikonsu”.
“Nice zan baka wannan labarin Sir kasancewata a cikinsu yanzu. Sai dai kuma wanda suka bani wayar yanki ne na mutanen kirkin cikinsu. Kasan a ko ina akwai Æ™yakykyawa akwai kuma mummuna”. Tsaf ta kwashe yanda sukai ta sanar masa saboda ta matuÆ™ar yarda da shi. Shine kuma takema kallon wanda zai taimaka mata a wannan yaÆ™in kamar yanda tai fata. Ya jimanta al’amarin matuÆ™a, ta wata fuskar kuma yayi murnar ganin hanyar samun nasararsu ce tazo.
“Lallai mun samu hanya ta jifan tsuntsu biyu da dutse É—aya Iffah. Sai dai dole kiyi taka tsantsan da waÉ—an nan wayoyin. Ki buÉ—e account da duk kike É“uÆ™ata da layin da suka sanya miki, shi kuma wannan nakin watsap kawai zaki buÉ—e da shi, sai dai karki barsa akan wayar, da kuma kinyi magana da Ajmaal da shi ki goge watsap É—in ki cire layin sai zaku Æ™ara ki maida. Akoda yaushe wayarki ta kasance da security na idanunki bana wayar ba. Dan inada tabbacin suma zasu saka ido a kanki. A daren nan ki buÉ—e watsap É—in ki sake ma Ajmaal magana”.
“Nahode Sir, insha ALLAHU zan yi duk yanda kace”………✍️

*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*

*DAUDAR GORA Billyn abdul*

*KI KULANI hafsat xoxo*

*A RUBUCE TAKE Huguma*

*RUMBUN K’AYA Hafsat rano*

*IDON NERA Mamuh ghee*

_LITTAFI DAYA: 400_
_LITTAFI BIYU: 600_
_LITTAFI UKU: 800_
_LITTAFI HUDU :1000_
_LITTAFI BIYAR: 1200_

_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_

_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_

_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_

_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_

_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_

_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_

ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN

MARYAM SANI
ACCESS BANK
0022419171

SAI A TURA SHAIDAR BIYAN

09033181070

IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA

09166221261

*ƳAN ƘASAR NIGER. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*

+227 96 09 67 63

Books biyar 1250CFA
Books hudu 1050CFA
Books uku 850CFA
Books biyu 650CFA
Bookk daya 450CFA

KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.

MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu

✨ÆŠ ✨
( )

 

 

Post a Comment

0 Comments