Daudar Gora Book 1 Page 29

Latest Posts

6/recent/ticker-posts

Ad Space

Daudar Gora Book 1 Page 29


29_*

………Barrister na Æ™oÆ™arin shiga layin gidan Abu Moosa wata baÆ™ar mota na ficewa. Babu wanda ya damu da ganinta a cikinsu, suka Æ™arasa kutsa kai har Æ™ofar gidansa. Ganin gidan rufe daga nesa baisa sun kawo wani abu a ransu ba duk suka fita. Abu Zainab ne ya Æ™arasa har jikin Æ™ofar. Kansa tsaye ya kai hannu ya fara knoking, amma har tsahon mintuna biyu babu alamar motsin mutum.
Juyowa yay ya É—an kalli su Kaka dake kallonsa. Cikin sarewa ya girgiza musu kai. “Banajin fa akwai mutum a gidan nan, dan babu wani motsi”.
“Kara dai bugawa”.
Cewar Barrister cikin bashi ƙwarin gwiwa. Kai Abu Zainab ya kaɗa ya cigaba da bugawa, maimakon a buɗe nan sai ƙofar makwaftansu ce ta buɗe. Wani matashin saurayi ya fito. Abu Zainab ya maida hankalinsa garesa suka gaisa. Kafinma ya tambaya saurayin ya bashi amsa.
“Ai banajin akwai kowa gidan nan. Saboda yanzu babu jimawa matar gidan aka É—auke a mota harda Æ™aton akwati”.
Da mamaki Abu Zainab ya ce, “Kana nufin yanzun?”.
“Eh, dan banajin sunma rufa minti goma. Ta kuma yima mahaifiyata sallama akan zata koma garinsu ne. Harma mukayi mamakin hakan ganin duka rasuwar mijinta bai wuce kwanaki goma sha biyar ba”.
Godiya Abu Zainab yay masa jiki a saÉ“ule ya koma gasu Kaka. “Waifa kunji babu jimawa tabar anguwar nan. A yanda tacema makwaftansu ma ta koma garinsu ne”.
“Garinsu kuma?”.
“Haka dai yace. Nifa na fara tsorata da lamarin nan, dan tabbas akwai abinda ke É“oye da bamu sanshi ba”.
Tsakanin Kaka da Barrister babu wanda ya iya cewa komai….

*_MASARAUTA (JASRAH)_*

“Wai ni naga sai faman moso kike, kinma kasa bani labarin yanda kukai da Akia akan zancenmu na jiya. Kuma naga wucewarku ke da ita É—azun zuwa sashin Mamma (Malikat Haseena)”.
Cike da zolaya ta É—an hararesa. “Ko kuma dai Æ´an leÆ™en asirinku sun sanar maka ba”.
“LeÆ™en asiri kuma? Haba sai kace dai ku. Kudai matan masarautar nan ne dai da baÆ™wa iya rayuwa sai dai Æ´an leÆ™en asiri. Amma mu maza miya haÉ—amu da wani leÆ™en asiri kamar marasa aikin yi”.
Ta É—an dara kaÉ—an da taÉ“e baki. “Muma É—in ba kowa ne yake hakan ba kamar yanda kuke zargi. Niko waya dameni a daular nan dahar zan damu da saka wani bibiyarsa. Ko lamarin Zaki addu’a ce tamu a garesa kawai”.
“To ALLAH yasa hakan. Yaya zaman naku ya kasance?”.
“Zama an samu nasara. Dan inama Akia bayani a take ta amince, ta kumace muje sashen Mamma itama muji ta bakinta. Alhamdullah sai aka dace itama zancen ya Æ™ayatar da ita. Na taÆ™aice maka zance a yanzu haka ma mun zauna da ita yarinyar. Insha ALLAHU zuwa gobe ma zata koma sashenta. Sai dai abu É—aya ne fa Mamma bata amince da shi ba”.
“Minene shi?”.
“Sake kai wata Zawjata-almilk turakarsa. Acewarta za’a Æ™ara jinkirtawa aga abinda yarinyar zata samo. Sannan za’a sakema duka Zawjata-almilk É—in sabon horo akan kasancewar su Zawjata-almilk a wannan karon”.
(Wata sabuwa kenan, wannan tsinanniyar tsohuwar ko) ya ambata a zuciyarsa. A fili kam fuskarsa ya kawata da sabon murmushi da faÉ—in, “Woow wannan tsarin yayi, shiyyasa Mamma ke daÉ—a birgeni. Hakan ma wani mataki ne da zai taimakemu matuÆ™a. ALLAH kuma yasa mu dace”.
“Amin dai Abu Harith. Dan gaskiya a wannan gaÉ“ar ina tsoron a ce abinda ya faru ya sake maimaita kansa. Saboda zuwa yanzu hankalin manyan Æ™asashen duniya ya fara dawowa kan Æ™asar ruman. Dan ma ana shakkarmu ne da tuni wani zancen ake ba wannan É—in ba. ALLAH dai ka bayyana gaskiya ka kuma wanke wanda ake neman disashewa saboda son zuciya”.
“Amin Meera. Amma ko yanzu É—in ma akwai abinda baku sani ba. Shahan-shan na É“oyewa ne kawai dan karya tashi hankalin kowa. A wata mai kamawa shugabannin manyan Æ™asashe bakwai na africa zasu kawo ziyara Æ™asar ruman. Bisa jagorancin shugaban Æ™asar Nijeriya, bama raba É—ayan biyu akan wannan al’amarin ne kuma”.
“Ya Arrahaman”.
Jasrah ta faÉ—a a tsorace.
“Ki kwantar da hankalinki, dan ALLAH kuma kar kowa yasan wannan, dan na sanar miki ne kema saboda na yarda da ke”.
Badan hankalin nata ya kwanta ba ta jin jina masa kanta kawai. Cigaba da kwantar mata da hankali yay cikin kwantar da murya har barci É“arawo ya kwashe ta. Sai da ya tabbatar barcinta yayi nisa sannan ya zare jikinsa cikin sanÉ—a ya fice zuwa É—ayan É—akin dake jikin wanda suke kwance da waya a hannunsa……

*_ZAWJATA-ALMILK_*

Dukan matakin shawarar da Sir Fawzan ya bata shi tabi, dan tunda sukai bankwana da Daneen Ammarah tai shirin barci ta sakama Æ™ofarta key. Ta fara da buÉ—e Watsap, sannan ta lalubo number Ajmaal. Cikin sa’a kuwa yana online, wani farin ciki ne ya ratsata. Taja kakkauran numfashi da godema ALLAH.
_Assalamu alaikum_
Ta fara turawa da fatan samun amsa zuciyarta na harbawa da sauri-sauri. Tsahon mintuna kusan goma babu alamar zama a buɗe saƙon. Sake tura sallamar tayi a karo na biyu. Ta dasama wayar ido kamar mai irgan fitan numfashinta. Kamar a mafarki taga an buɗe, tai kasare tana jiran taga an amsa sai dai shiru har kusan wasu mintuna goman. A yanzu kam zuciyarta ta sosu, dan duk yanda take buƙatar abu ga mutum ta tsani a wulakantata. Ta cije lips da ƙarfi tana danne fushin dake son mata tasiri.
_Wa’alaikissalam_.
Aka amsa mata a bazata. Nannauyar iska ta furzar, itama ta buɗe saƙon ta share. Da ƙyar ta iya danne zuciyarta mintuna bakwai suka cika.
_Sunana Fareedah bint Zayyan_.
Tsahon mintuna kusan goma yanzu ma sannan aka buÉ—e.
_Na sani_.
Tai shiru tana kallon amsar, sai kuma taja tsaki na takaici. A fili ta furta, “Aikin banza. Ka sani shine baka san aikinka ba mtsoww!!”.
Sharewa tai, ta rubuta masa.
_Kwanaki na kira, amma akaimun tarbar da har yau ina mamakinta. Shin dama manyan ƴan jarida haka suke da wulaƙanta bukatar marasa ƙarfi?_
Tsahon minti ashirin da buÉ—e saÆ™on babu alamar za’a amsata. Hakan yay mata ciwo matuÆ™a. Sir Fawzan ta kira, bugu biyu kuwa ya É—aga. A É—an rikice yace, “Iffah baki ganin akwai matsala yawan kiran nan? Masarauta fa ba irin ko’ina bane sunada hanyoyin tsaro É“oyayyu ciki harda cctv”.
“Hakane Sir, amma nima dole ce ta sakani kiran. Anya kuwa wannan abokin naka da gaske É—an jaridar ne? Sam baya É—aukar al’amarina da muhimmanci, duk É—an jarida na kwarai zaka samesa da zumuÉ—i akan labari, musamman ma irin nawa daya kasance babba”.
“Miya faru? Bai amsa saÆ™onki ba ne?”.
“Ya amsa. Amma yanamun yanga. Harna fara jin gundira a huÉ—É—a da shi”.
“Karki saurin karaya, amma nayi mamaki dan masan Ajmaal ba mutum bane mai irin wannan siffar wlhy. Inaga dai akwai aikin da yake yi a wannan gaÉ“ar shiyyasa. Kin san su abubuwan nasu da yawa. Kin san kuwa yanda ya Æ™agu akan son jinki, dan É—azun na fara Æ™yara masa abinda ke ranki kaÉ—an”.
Ta É—anji sassauci daga haushinsa. Taja ajiyar zuciya a fili da faÉ—in, “Shike nan bara na koma”.
Sallama yay mata ya yanke wayar.
_Am sorry na haÉ—a wani aikin ne da saurarenki. Yanzu ina jinki_.
Da wannan saƙon taci karo bayan yanke wayar. Sanyi ta ƙaraji a ranta. Cikin ɗan karsashi ta maida amsa.
_Ayya kayi jaƙuri na maka gurguwar fahimta._
_Babu damuwa_
Aka amsa mata cikin Æ´an sakanni. Cike da karfin gwiwa ta rubuta.
_Nasan abokinka ya fara maka bayani akan nemanka da nake ido rufe._
_Hakane. A yanzu haka ma munyi dashi zai bani wani yankin rubutunki dake hanunsa._
_Alhamdullahi. A yanzuma akwai cigaban wancan rubutun a hannuna nima. Sai dai ban san ta hanyar da zai zo garesa ba ko gareka_.
_Wannan mai sauƙine ai. Zaki iya turamin shi tanan_
_Wai! Amma typing É—in zaimun wahala gaskiya_.
_Karki damu ki É—auki hoto_
Cike da zumuɗi ta miƙe. Gado ta ɗaga ta ɗakko notebook ɗinta, a take ta ɗauka hoton duka rubutun ta tura masa.
_Gashi, insha ALLAHU duk bayan kwanaki uku zaka iya ganin saƙona_
_Masha ALLAH hakan yayi, sai dai a maimakon kwana uku mizai hana muyi mako-mako. Dan wani abun da zai zo yana buƙatar bin diddigi da faɗaɗa bincike mu tanan a garemu._
_Yanda kace haka za’ayi. Ni dai fatana ka kasance É—an jarida mai gaskiya da riÆ™on amanar kimar Æ™asarsa. ALLAH shine shaidata na baku dukkan yarda kai da Sir Fawzan. Idan akasin nasarata ya biyo bayan yunÆ™urina ku zan zarga. Duk kuma yarinyar data samu kanta a irin halin da Æ´an uwana da ni muka kasance kuma zaku amsa sunan azzalumai ne kamar yanda Shahan-shan É—in ke amsawa a yanzu. Ku kuma dinga tunawa da mala’iku tare da ku masu rubutawa daga ayyukanku na zahiri da baÉ—ini. ALLAH ya cigaba da tsare Æ™asar ruman. Idan kanada wata tambaya zaka iya tura min text message na Barka lafiya_.
Bata jira amsa daga garesa ba ta fita gaba É—aya. Watsap É—in ta goge ta kashe wayar gaba É—ayama tana sakin ajiyar zuciya a jajjere. Sai takejin wani kaso na damuwarta da nauyin zuciyarta ya ragu kaÉ—an. A wani gefe kuma kamannin mutumin can da wanda ta gani a jiya matsayin Shahan-shan ne ke ta faman mata kaikawo babu alamar zai barta ta huta……

★★…. “★★” …..★

“Lafiyarki da tsahon zamani su da É—a tabbatuwa uwa mai share kukan masu kuka”.
Ta-kurya dake kai gwuyawunta ƙasa ta faɗa sakamakon zuwan Uwa gareta a bazata. Kamar ko yaushe, cikin shigarta ta jajayen kaya, ta gyara zaman ƙasaitar ta. Ƙoƙon dake hanunta ta miƙama ta ƙurya. Hannu biyu ta karɓa, ta kafa kai ta shanye abinda ke ciki.
“Tukuycin cika umarninmu na yanka babbar baÆ™ar dabba da kikai ne. Azamarki da himmarki zaisa bazaki taÉ“a nema daga garemu ba ki rasa Ta-kurya (Wa’iyazubillah ).
“Nagode uwa mai share kukan masu kuka”.
Murmushin daya sake munana fuskarta ta saki tana ƙara kalmashe ƙafafu a kujerarta.
“Karki damu ke mai nasara ce. Minene makomar ayyukan da muka barki da su?”.
“Ina kan yunÆ™urin Æ™arasawa. Na kuma samu Æ™yaÆ™yÆ™yawan labari a majiya mai Æ™arfi yarinyar zata koma sashenta. Sai dai akwai zaman sirri dasu Uwar masu gida sukai wanda babu wanda yasan misuka tattauna. Ina dai Æ™yautata zaton duk akan komawar yarinyar ne”.
“Kar tattaunawarsu ta dameki. Tabbatar da Æ´an leÆ™en asirinki cikin hadimanta shine aikinki na gaba. Dan kunada yawa masu wannan burin kema kin sani basai na sanar miki ba. Ina kuma tunatar dake rigar can dake a sashen Uwar masu gida. Da zaran ta tare ki kasance É—aya daga cikin masu janta a jiki. Yardarta gareki ne zai bamu damar amfani da ita wajen cikar burinmu”.
“Na gode da kasancewar ki haske mai haskamin duk wani surÆ™uÆ™in da zai iya zamemin duhuwa uwa”.
“Biyayyarki garemu ita ce tushen share kukanki Ta-kurya. Dan haka bazamu taÉ“a barin kiyi kuka ba maÆ™iyanki suyi dariya ba. Sai dai su suyi kuka ke ki kasance cikin dariya a kullum bisa nasararsu. Karki shagala Æ´ar shilar suda nada taurin kai, Karki zama cikin jerin mutane masu raina allura ta zame musu garma. Muna son tasha madarar nan a Æ™alla sau uku daga gareki da zaran ta tare a sashenta”. Ta Æ™are maganar da miÆ™ama ta Æ™urya Æ™oÆ™on da bata san daga ina ya fito ba. Dan ganinsa kawai tai a hannunta tamkar Æ™yaftawar idanu. Hannu biyu tasa a wajen amsa tana jera mata kirari da godiya. A hankali ta fara disashewa a idanunta tamkar baÆ™in hadarin da masha ruwa (Bakan gizo) ya shanye cikin sakanni.
Ta-Æ™urya ta sauke nannauyan ajiyar zuciya. Sai kuma ta miÆ™e da Æ™oÆ™on da Uwa ta bata. A guri na musamman da na’urar sanyi ke aiki ta ajiye madaran, murmushin jin cigaba da tabbatuwar nasararta na cigaba da Æ™awata Æ™yaÆ™ykywar fuskarta. Ji take a ranta yanzu ne fa za’a fara wasan na gaskiya. Dan dama idan aski yazo gaban goshi masu iya magana kwance yafi raÉ—aÉ—i da zafi. Ta jima bata samu irin wannan damar ga uwa ba a É—an tsakanin nan da mafi yawan lokuta sukafi ganawa cikin É“acin rai da rabuwa da É“acin ran. Amma a yau yanda uwa ta ziyarceta ya sakata jin karsashi da Æ™arin kwarin gwiwar cigaba da ruguza duk wanda ya cigaba da yunÆ™urin shiga gaban nasararta…….✍️

“Humm masu karatu, da gaske fa yanzu ne za’a fara wasan na gaskiya. Ga dai Iffah zata koma É—akinta. Komawar dake cike da burikan wasu dake zagaye da ita. Buri kuma irin wanda ke kamanceceniya da juna ta fuskar wanzuwa. Manufa kuma kowa da irin tasa. Ita kanta Iffah da nata Æ™udirin karku manta. Shin wanene zaiyi nasara ne? Yaya batun su Babiy kuma? Dan maimakon haske komai Æ™ara cuÉ—ewa yake. Kaka zaiyi wani yunkuri a alamarin kokuwa Barrister zai janye bisa gargaÉ—in da akai masa shima?. Kumuje zuwa dai dan ba’a fara komai ba sai yanzu”.

 

*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*

*DAUDAR GORA Billyn abdul*

*KI KULANI hafsat xoxo*

*A RUBUCE TAKE Huguma*

*RUMBUN K’AYA Hafsat rano*

*IDON NERA Mamuh ghee*

_LITTAFI DAYA: 400_
_LITTAFI BIYU: 600_
_LITTAFI UKU: 800_
_LITTAFI HUDU :1000_
_LITTAFI BIYAR: 1200_

_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_

_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_

_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_

_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_

_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_

_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_

ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN

MARYAM SANI
ACCESS BANK
0022419171

SAI A TURA SHAIDAR BIYAN

09033181070

IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA

09166221261

*ƳAN ƘASAR NIGER. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*

+227 96 09 67 63

Books biyar 1250CFA
Books hudu 1050CFA
Books uku 850CFA
Books biyu 650CFA
Bookk daya 450CFA

KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.

MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.

 

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*

✨ÆŠ ✨
( )

 

 

Post a Comment

0 Comments