Daudar Gora Book 1 Page 3

Latest Posts

6/recent/ticker-posts

Ad Space

Daudar Gora Book 1 Page 3


_3_*

_____________

_*MAAB LUXURY HOME!!* Sabuwar duniyar hamshakan mata da Æ´aÆ´an gata._

_*GIDAN* ƙawa da ƙawata gidajen da suka cika gida._

_*SABUWAR DUNIYAR* Amare da uwargidan data amsa sunanta Æ´ar gaban goshi._

_*MAAB LUXURY HOME* wata duniya ce ta ƙawa da ƙawata gidajenmu da kayan ƙyale-kyale na burgewa da ɗaukar hankalin duk wani mai kallo_.

_*SUNYI FICE* Fice irin na É—aya a cikin tsara, sune na farkon fari, a farin da za’a kira fari a kowace irin duniya._

_*A GAREMU* ba sitturu na alfarma da kawa ne kawai ke tabbatar da mu hamshakai ba. Sai mun haÉ—a da Æ™awata gidajenmu da kayan MAAB LUXURY HOME zamu kasance cikakkun Æ´an gata ababen kallo da nunawa sa’a koda a cikin dubun da sukafi dubu._

_*MAAB LUXURY HOME* sun takaita mana dukkan wahalar nema ko order a kasashen ketare ta hanyar wadatamu da galla-gallan kayayyakin adon gidajenmu_

_*MAAB LUXURY HOME.* Duniyar kayan Kitchen da decoration din gida na keta raini._

_*INA UWARGIDA INA AMARYA!!?* Ku ziyarci shagon mu dake No 22 Ahmadu Bello Way, Kano state. Ko kuyi order daga shafin mu na Instagram @maabluxuryhome. Ko Facebook @maabluxuryhome. Ko Ku nememu a lambar waya *08034631010*._

*_Mai azama shi za’a kira dana farkon fari. Bara nai sauri nawa suzo hannuna kafin a kwashe⛹‍♀️⛹‍♀️⛹‍♀️._*

______________

………A wannan gaÉ“ar haukane kawai ya rage wannan ahali suyi, dan duk dauriyar Babiy ya kasa danne raÉ—aÉ—i da zafin da yakeji. Itako Iffah kalaman dake fita a bakinta kausasa sun saka kowa ke É—aukar tama zare kawai. Daga Æ™arshe maganin barci aka É—ura mata. Bata tashi farkawa ba sai a Æ™auyen da kakanninsu ke rayuwa. Wato iyayen Ummu. Rayuwa a Æ™auyen Jumna a gareta tamkar mai gushewar hankali ya zame mata. Domin bata gane komai sai sambatu da kalamun É—aura É—ammarar É—aukar fansa ga duk ahalin Daular Ruman. Ba Æ™aramin dagewa da jajircewa kakannisu da su Babiy sukai ba a kanta wajen ganin ta samu lafiya ta dawo hayyacinta. A cikin watanni takwas ta rasa yayunta guda biyu, wannan babban tarihine da bazai gogu a zuciya da ruhinta ba har karshen rayuwarta. Bayan jiyyar watanni kusan uku ta dawo hayyacinta. Sai dai ta daina fira’a da kowa, an daina ganin dariyarta ko farin cikinta. Babu abinda ke’a ranta sai buri da Æ™udirin É—aukar fansa. Tama kanta alÆ™awarin ita da hannunta zata kashe *_Tajwar Eshaan ibn Haysam Abdull-majeed_*. Bayan nan idan itama an kasheta burinta ya cika na kawar da azzalumin sarki mai mulki irin na fir’auna a Æ™asarta a cikin al’ummarta….

*_(Babbar magana. Tayaya wannan buri naki zai cika Iffah? Sarki mai cikakken iko irin Tajwar Eshaan, mai amsa sunan Shahan-shan da ko fuskarsa babu wanda ya iya sani a cikin kasar Ruman har yanzun. Anya kuwa….? To mudaije zuwa wai mahaukaci ya sai kura)_*

 

★★★

“Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un” bakinta ke ambata cikin firgici da rawar jiki sakamakon farkawar da tayi daga mummunan mafarkin daya risketa a cikin barcinta. Ta dafe kanta dake wata irin sarawa na ciwo tamkar ana mata luguden taÉ“aren daka a tsakkiyarsa, gaba É—aya jikinta ya jiÆ™e da zufa tamkar tayi wanka. Kusan watanni biyar kafin mutuwar Æ´an uwanta da fara canjawar salon mafarkainta saÉ“anin na baya, abu mafi tsoratarwa kuma kusan mafarki É—aya ne ke maimaita kansa a kowane barcinta idan ta kwanta. Sai dai mafi tashin hankalin a yau yayi kamanceceniya da na wasu dare da tarihi bazai taÉ“a mantawa da shi ba a cikin rayuwarsu ita da ahalinta.
“Nina Arfa! Nina Fariha!”.
Ta ambata a zahiri zuciyata na Æ™ara Æ™arfin gudu, yayinda hawaye suka shiga rige-rigen sauka a kumatunta. Tabbas irin wannan mafarkin tayi a daren da suka rasa Arfa, hakama daren mutuwar fariha. Yau kuma gashi ta maimaitashi akan kanta. Itama kenan zasu rasata?. Kai ta shiga girgizawa wani kuka masu Æ™arfi na sake tahomata, hannu tasa ta toshe bakinta gudun kar sautinsa ya kai ga kunnen kakanninta. Sai dai aikin gama ya gama. Dan kuwa muryar kakanta takeji jikin Æ™ofar É—akin nata a hankali yana ambatar sunanta. Da sauri ta shiga goge hawayen, kafin ta tashi daga shimfiÉ—ar barcin nata wadda karan gado ne da katifar rimi. Mayafi ta É—auka ta yanama jikinta, ta Æ™arasa ga Æ™ofar ta buÉ—e…
“Kina lafiya kuwa É—iyar nan?”.
Ya faɗa cikin kafeta da idanu. Kanta dake rissine ta jinjina masa, cikin son danne kukan dake yunƙuromata ta bashi amsa.
“Ina lafiya Kaka”.
Jin shiru bai sake cewa komai ba ta É—ago ta dubesa a karon farko. Shima dai kallon nata yakeyi tamkar mai nazari. Sake maida idonta tai Æ™asa, hawayen da take faman riÆ™ewa suka É“alle mata da gudu. Bata san ta ambaci “Kaka nima zasu kashe muku ni ko?. Inaji a jikina nima zaku iya rasani nan kusa tamkar yanda muka rasa su Nina Arfa”. Rawar da jikinta ta fara ta sata zubewa a gabansa kuka na Æ™wace mata. Kusan minti biyu baice da ita komai ba, ita kuma ta kasa tsaida kukan.. Jin saukar hanunsa saman kafaÉ—arta ya sata haÉ—iye kukan, ya É—agota tsaye yana É—an murmushi dake sake bayyana tsufansa. Gefen mayafin jikinta ya kama ya shiga goge mata hawayen. “Fareedatu! Ki kwantar da hankalinki, insha ALLAHU babu abinda zai faru da ke, mafarki ai ba gaskiya bane ba. Suma su Arfa kwanansu ne ya Æ™are, koba komai kuma sun rasu a gidan aurensu. Wannan kawai ya ishemu farin ciki”.
Kanta ta jinjina masa tana sauke ajiyar zuciya a jajjere. Ya cigaba da shafa kanta a hankali har zuwa wani É—an lokaci. “Kije kiyi addu’a ki kwanta abinki da safe zamuyi magana”.
A hankali tace, “Kaka ina son zuwa naga su Ummu gobe to dan ALLAH”.
Da sauri ya girgizamata kansa. “A’a bazai yuwu ba Iffah, iyayenki sun kawoki nan ne domin kuÉ“utar dake, taya kike tunanin zan barki komawa cikin daular Ruman?. Tun ina Æ™anÆ™anin yaro nake bauta wa masarautar Ruman, bayan mutuwar mahaifina na cigaba da bautar saÆ™a kayan doki a garesu kamar yanda mahaifina ya barmin gado, a haka na haifi Æ™anin mahaifiyarku shima ya mayeni, gashi har girma ya riskesa shima yana bauta musu. Mun rasa É—an uwan mahaifiyarku a yaÆ™in kare daular Ruman, mun rasa Arfa, da Fariha. Ke É—aya da kika rage mana da yayanki wajen mahaifiyarku kuma sai muyi wasa da rayuwarki? Bazai yuwuba jeki kwanta…”
Batare daya sake bata damar yin magana ba ya juya ya koma bayan ya jamata murfin kofar. Da kallo kawai ta bisa hawaye na silalo mata. Duk yanda taso komawa barcin bayan tafiyarsa hakan ya gagara, zuciyarta ta kasa fita da ga Æ™angin fargaba, da gaske tanajin matuÆ™ar tsoro bayan rasa Fariha da Arfa da sukai watanni Æ™alilan da suka shuÉ—e itama su rasata, tanaji zuciyar ahalinta bazata iya É—auka ba idan itama suka rasatan. Wasu zafafan hawaye suka sake silalo mata masu raÉ—aÉ—i da saka Æ™una a Æ™irji……

★★★

“Iffah! Iffah!!…..”
Sautin Æ™wala kiran sunanta daga muryar kakarsu da suke kira Iyyani ya sakata fitowa daga banÉ—aki data zagaya domin yin fitsari. Turus ta tsaya tare da haÉ—iye maganar da zatayi tana mai kallon É—an-uwanta Hanash dake zaune gefen kakar tasu a Æ™arÆ™ashin bishiyar É—oruwa da take a tsakar gidan. Murmushin da yakemata ta maida masa, kafin ta ajiye butar hannunta ta Æ™arasa garesa. Dab da shi ta zauna tana mai É—an rungumesa ta gefe da faÉ—in, “Ina kewarku Akhi”.
Murmushinsa ya sake faÉ—aÉ—a yana mai kallon fuskarta. Ya kai hannu ya shafi yalwataccen gashin kanta da mayafin ya zame mai tsaho da santsi. “Muma muna kewarki Little angel. Gidan duk ya sake zama mana babu daÉ—i”.
Yanda maganar tasa ta ƙare cikin rauni itama sai idonta ya cika da ƙwalla. Amma sai ta dannesu da murmushin mai ɗaci tana kaɗa kanta kawai.
“Tashi ki bashi ruwa mana, k haka ake tarbar baÆ™o a garinku”.
Baki ta É—an tura gaba da kallon Iyyani mai maganar, tayi hakane danta katse raunin data hanga a fuskokinsu. Ta miÆ™e tana bata amsa cike da shagwaÉ“a. “Iyyani laifinkine fa, ban taÉ“a ganin matar da bata tattalin mai gida ba irinki, dole Yayana ya miki kishiya”.
DaÆ™uwa tamata cikin gatsina fuska. “Ungo naki nan Fareedah, yo bandama lalacewa mizanyi da wannan faratun mai kama da jar tsada tuzurin banza”.
Hanash ya tsuke fuska yana kallon Iyyani. Murmushi Iffah tayi tun kafin ya faÉ—i abinda ke bakinsa. Dan dama inhar suka haÉ—u da Iyyani sai ta hasalashi take jin daÉ—i shi da Arfa akan Æ™inyin aure, duk da bawani shekarune da shi ba, dan ashirin da shida ne kawai, Arfa nada ashirin da uku, Fariha nada ashirin da É—aya. Iffah nada goma sha takwas….
Iffah ta dire masa abinci da ruwa ta sake kaiwa zaune kusa da shi sannan ta dubesa. “Akhi yasu Babiy suke?”.
Ya nisa a hankali bayan ya dire moÉ—ar ruwan daya sha. “Duka lafiya suke. Suna gaisheki ke da su kaka. Duk da suma dai nan da kwana kusa zamu ma dawo nan É—in muma. Yanzu haka nazo duba can tsohon gidanmu ne dan asan gyaran da za’ai masa”.
Sosai ta kafesa da ido ita da Iyyani. Kafin cikin Æ™arfin hali Iffah tai magana. “Amma Yaya su Babiy basa ganin rayuwa zata mana wahala anan sakamakon bamu sababa sam. Sannan ayyukansu dake acan miye makomarsu? Da karatunmu muma?. Abinda ya faru ya riga ya faru, tunda hannayenmu bazasu iya maidosu ba, mi zaisa zukatanmu bazasu cigaba da haÆ™uri ba. Barowarmu cikin Daular ruman tamkar munji tsorone, ko sake sakin rayuwarmu a hanun waÉ—anda kansu kawai suka sani…….”
“Tsoro halak ne Iffah. Bama muba mafi yawan masu yara mata sunata barin daular ruman a yanzu domin tseratar da Æ´aÆ´ansu daga auren jeka nayika. Karatun Æ´ammata yana neman tsayawa cak, kowace na tsoron fitowa ta zama nama a hanun hadiman daular ruman. a yanda lissafin yake a yanzu an rasa mata goma sha huÉ—u fa, a tunaninki kafin Æ™arewar wannan shekarar ba’a rasa fin hakaba duk da bawai ya cigaba da auren bane.”
Wasu hawayene masu É—aci da Æ™una suka silalo ma Iffah, tai saurin saka gefen mayafinta ta share tana murmushin takaici. “Niko a ganina gudu bashine mafita ba, muryoyinmu ya kama mu É—aga wa duniya kowa yasan halin da muke ciki, idan har a Æ™asar Ruman babu wani sama da nasa mulkin ai a sauran Æ™asashen duniya akwai wanda suka fisa…”
“Humm Iffah ke yarinya ce har yanzu.”
“Sosai kuwa Hanash. Shiyyasa bata gane komai sai abinda yanzu take zuwa da shi”.
“Humm Iyyani kenan”.
Iffah ta faÉ—a a yanayin jin raÉ—aÉ—i a maÆ™oshinta. Su duka kallonta sukai, sai dai ta É—auke kanta gefe tamkar bata gansu ba. Daga haka babu wanda ya sake cewa komai har tsahon wani lokaci. Iyyani ce ta canja hirar da wani abu daban har Hanash ya kammala. Tare da shi suka fita wajen duba tsohon gidan da kakaninsu da suka haifi Babiy ne suka rayu a ciki, dan sudai tunda suka taso a cikin birinin daular ruman suka san kansu duk da a É—an gefen gari suke acan É—in ma. Sai dai su shigo cikin Æ™auyen Jumna a matsayin duba kakannin nasu. zuwa yanzu su duk sun rasu, shiyyasa gidan ya kasance babu kowa. Duk ma ya rusa ya fita hayyacinsa dan ginine na jar laka tamkar yanda duka gidajen Æ™auyen suke. Sun É—an jima acan suka dawo, sun iske kaka ya dawo shima daga fitar da yay tun ta safe gona É—ebo sassaÆ™e-sassaÆ™en magunguna. Ƙara zaman tattaunawa sukayi iya su uku, ita dai Iffah bata cewa komai. Daga Æ™arshe ma tashi tai ta shige É—akin kwananta. Bata sake fitowa ba sai da kaka ya neme ta. SassaÆ™e-SassaÆ™en magungunan daya É—ibo É—azun ne a gabansa, kowanne ya É—auresa daban-daban. Ya turamata babban robar da suke ciki… “Zaki fara amfani da su Iffah, bana son kiyi wasa dan ALLAH. WaÉ—annan kuma hayaÆ™ine, a kowacce duhun magriba ki tabbatar kinyi turarensu, wannan kuma a ruwan wanka ne, da kin idar da sallar asuba ki zubasu cikin ruwa kaÉ—an ki cire kayanki ki tabbatar duk jikinki ya samu”.
“Tofa kaka wannan É—in kuma duk na miye?”. Iffah ta tambaya cikin nuna mamaki.
Idanu ya tsiramata na kusan mintuna uku tamkar mai nazari, sai kuma ya É—auke kansa da wani yanayi mai wahalar fassara. “Faruwar Æ™addararmu bashi ke nuna baza’a sake jarabtarmu ba. Idan jiya ta shuÉ—e da É—aci zata iya yuwuwa yau É—inmu da dariya zata kasance, sai dai sanin mike a gobenmu al’amarine mai girman gaske, damin gaibunmu ce ita ALLAH ne kaÉ—ai masanin mi zaizo.”
Kallon juna sukai ita da Hanash, Iffah ta É—an É—age kafaÉ—a cikin yanayin ban fahinta ba, shima sai ya kaÉ—amata idanu alamar shima hakan take. Atare suka maida dubansu ga kaka. Amma sai ya kauda kansa alamar baya buÆ™atar kowacce irin tambaya daga garesu. Iffah ta jinjina kai kawai alamar ko’oho. Sai kuma ta miÆ™e tana mai faÉ—in, “Ni dama fa na yanke shawarar zanbi Akhi mu koma. Tunda dai naji sauÆ™i gara naje na koma makaranta anata wuceni a darasi”.
Ba karamin waro idanu Hanash yay ba, zaiyi magana kaka ya dakatar da shi ta hanyar yin murmushi da kaÉ—a kansa. “Ita rayuwa rubutacciya ce tunkan halitta, an rubutatane da alÆ™alamin da ba’a goge rubutunsa, babu wani hannu daya isa gogeta koda da Æ™arfin iko. Dole ne sai anyi hakan, ko muna so ko bama so mashin nan sai ya isa inda aka aikashi. Domin ita *KIBIYAR AJALI! SULKE BAYA TARETA SAI TA GITTA*”.
A rikice Hanash ya tari numfashinsa. “Kaka bana gane dunÆ™ulallun zantukan nan naka, ka fito fili dan ALLAH ka sanar mana mi kake son faÉ—a…”
“Hanash! Lokacin faÉ—ar baiyiba ai, nima kurman baÆ™in kawai na gani, fassarar sai UBANGIJI”.
Sosai Hanash ya sake tsare fuskar kaka da idanu, kamar yanda itama Iffah tai tsai tana kallon nasa. Su dukansu sun jima da sanin kaka mutum ne hatsabibi, dan kuwa mahaifinsa gawurtaccen masanine da azamaninsa akan kallesa tamkar matsafi ko wani mai gani har hanji, sai dai kasancewar bai ajiye buzu ya zauna akan iya wannan al’amarin ba yasa ake shakkar faÉ—a, yana bada taimako na magani akan abubuwa daban-daban musamman harkar aljanu komai Æ™arfinsu da shaiÉ—ancinsu. Sannan yana sana’arsa ta saÆ™a kayan kwalliyar doki. Kaka ya gaji abubuwa da dama a garesa, sai dai shi ya watsar da harkar bada maganin dan shima dai a karan kansa yana ta’allaÆ™a sanin mahaifin nasa da bokancin, duk da dai bai fito fili ya bayyana hakan ba kuwa, amma rashin maida hankali akan abinda ya shafi hakan zaisa ka zargi ko haka É—inne. Akwai kayan aiki na mahaifinsa da yawa a killace a wani waje da shi kaÉ—ai ya sani, kuma tun bayan mutuwarsa shi ya tattare su ya killace su…………✍

*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*

*DAUDAR GORA Billyn abdul*

*KI KULANI hafsat xoxo*

*A RUBUCE TAKE Huguma*

*RUMBUN K’AYA Hafsat rano*

*IDON NERA Mamuh ghee*

_LITTAFI DAYA: 400_
_LITTAFI BIYU: 600_
_LITTAFI UKU: 800_
_LITTAFI HUDU :1000_
_LITTAFI BIYAR: 1200_

_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_

_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_

_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_

_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_

_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_

_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_

ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN

MARYAM SANI
ACCESS BANK
0022419171

SAI A TURA SHAIDAR BIYAN

09033181070

IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA

09166221261

*ƳAN ƘASAR NIGER. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*

+22799643131

Books biyar 1250CFA
Books hudu 1050CFA
Books uku 850CFA
Books biyu 650CFA
Bookk daya 450CFA

KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.

MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.

 

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*

✨ÆŠ ✨
( )

 

*_4_*

_______________

_*MAAB LUXURY HOME!!* Sabuwar duniyar hamshakan mata da Æ´aÆ´an gata._

_*GIDAN* ƙawa da ƙawata gidajen da suka cika gida._

_*SABUWAR DUNIYAR* Amare da uwargidan data amsa sunanta Æ´ar gaban goshi._

_*MAAB LUXURY HOME* wata duniya ce ta ƙawa da ƙawata gidajenmu da kayan ƙyale-kyale na burgewa da ɗaukar hankalin duk wani mai kallo_.

_*SUNYI FICE* Fice irin na É—aya a cikin tsara, sune na farkon fari, a farin da za’a kira fari a kowace irin duniya._

_*A GAREMU* ba sitturu na alfarma da kawa ne kawai ke tabbatar da mu hamshakai ba. Sai mun haÉ—a da Æ™awata gidajenmu da kayan MAAB LUXURY HOME zamu kasance cikakkun Æ´an gata ababen kallo da nunawa sa’a koda a cikin dubun da sukafi dubu._

_*MAAB LUXURY HOME* sun takaita mana dukkan wahalar nema ko order a kasashen ketare ta hanyar wadatamu da galla-gallan kayayyakin adon gidajenmu_

_*MAAB LUXURY HOME.* Duniyar kayan Kitchen da decoration din gida na keta raini._

_*INA UWARGIDA INA AMARYA!!?* Ku ziyarci shagon mu dake No 22 Ahmadu Bello Way, Kano state. Ko kuyi order daga shafin mu na Instagram @maabluxuryhome. Ko Facebook @maabluxuryhome. Ko Ku nememu a lambar waya *08034631010*._

*_Mai azama shi za’a kira dana farkon fari. Bara nai sauri nawa suzo hannuna kafin a kwashe⛹‍♀️⛹‍♀️⛹‍♀️._*

________________

Post a Comment

0 Comments