Daudar Gora Book 1 Page 31

Latest Posts

6/recent/ticker-posts

Ad Space

Daudar Gora Book 1 Page 31


31_*

…….Takun da baifi uku ba Kaka ya juyo ya bisa da kallo, kamar a bazata saurayin ya tsinkayi muryarsa na faÉ—in, “Jumna zanje”.
Yi yay tamkar bai jisa ba. Hakan yasa Kaka sake É—aga murya amma ya cigaba da sharesa shima. Yana Æ™oÆ™arin shiga motarsa Kaka daya biyosa a baya yace, “Haba É—an nan baka jini bane?”.
“Sarai na jika Baba. Na fahimci ba tafiyar zakai ba, ba kuma hurimina bane tilastaka”.
A karan farko kaka ya saki murmushi. “ALLAH sarki, to ayima tsoho haÆ™uri É—ana”.
“Baba kamin laifin komai ba ALLAH, ai aikina ne. Dama naji kana sanarma wancan ne ni kuma hanyatace shiyyasa ma naje gareka. Zanje Æ™auyen Yamanu ne dama”.
“A Alhamdullah, lallai hanyarmu É—aya Bara na É—akko kayana.”

Mutum biyu kawai saurayin ya Æ™ara É—auka bayan kaka suka É—auki hanya. Hakan baisa kaka ya ji wani zargi game da shi ba. Sai ma hira da suka dingayi kai kace sun san juna. Bayan sauke mutum biyun daya É—akko har Æ™ofar gida ya kai Kaka. Yaji matuÆ™ar jin daÉ—in wannan karamci dan haka yay masa tayin shiga ciki yasha ruwa. Saurayin ya É—an nuna tirjewa amma Kaka ya janye ra’ayinsa a dole ya bisa suka shiga, sai dai dama a ransa hakan yake fata.
Ummu na zaune a tsakar gida ita da Iyyani, ta rame matuƙa tayi duhu irin na wanda ya shiga damuwa. Tamkar an sare gwiyawun Kaka ya ƙarasa shiga idanunsa akan Ummu data tsurama bayansa ido. Iyyani ma jiki a sanyaye ta miƙe dan tasan komai tunda kullum sai sunyi waya da Kaka. Itace tai ƙarfin halin masa sannu da zuwa. Ya amsa a sanyaye yana waiga bayansa.
“Yaro shigo mana”.
Kaka ya faɗa domin samawa Ummu nutsuwa. Da sallama saurayin ya shiga. Ummu tai ƙasa da kanta a hankali.

Bayan sun gama zama a tabarmar da Iyyani ta shimfiÉ—a musu saurayin ya fara gaishe da Ummu. Bata amsa ba, hakan ya sakashi shan jinin jikinsa yay shiru a sanyaye. Iyyani data sake kawo musu ruwa ce ta amsa masa da “Bata magana yaro”.
“ALLAH sarki” ya faÉ—a cikin sauke ajiyar zuciya ita ya gaisheta. Da kulawa ta amsa masa dukkan hankalinta a kan Kaka dake kallon Ummu tamkar ya samu television. Ummu da hawaye suka cikama ido ta miÆ™e a hankali, É—aki ta shige duk suka bita da kallo. Kaka baice komai ba hakama Iyyani data zarce kitchen sai gata da kwanon abinci…….

★★… ★★★ ….★

Tamkar raÆ™umi da akala haka Iffah ke tafiya bisa jagorancin Malikat Haseenat. Kasancewar dare ne babu yawaitar hadimai masu hidima. Sai dai masu tsaro tako ina kai kace zasu iya kare ran wanda suke tsaye a dalilinsa daga ziyartar mutuwa. Tsirarun hadiman da suka samu nata zubewa kwasar gaisuwa, Malikat Haseenat ce kawai ke iya jinsu da ganinsu. Iffah dake ta faman sauke ajiyar zuciya da al’ajabin dukiyar dake narke a wannan gini ji take komai ya Æ™wace mata. Ta kasa fasalta komai ta kasa auna komai a ma’aunin rinjayen aikin zuciya dana Æ™waÆ™walwa….
“Bismillah”.
Malikat Haseenat ta katse mata ɗimuwar da take ciki ta hanyar nuna mata ɗaya daga cikin kujerun katafaren falon mai cike da abubuwan da bazasu lissafu ba. Da gaske Iffah bazata ma iya tantance yanda akai ƙafarta tazo nan ɗin ba.
Komai Malikat Haseenat batace ba, dan ta gama karance É—imuwar dake jagorantar fitar numfashin Iffah. Amintattun Hadiman dake a falon na uku suka zube gaban Malikat Haseenat kawunansu a Æ™asa. Hannu kawai ta iya É—aga musu. Babu buÆ™atar sai ta faÉ—a abinda tazo dan shi, shugaban hadiman dake a wannan falon ya miÆ™e zuwa ga landline domin isar da saÆ™on zuwanta…
“Tsahon rai da lafiya su tabbata ga Uwa a garemu, shugaban na tsumayen isarku a falon sama”.
Shiru malikat Haseenat batace komai ba. Yayinda Iffah da zuciyarta ke luguden ke saurarensu cikin juyewar tunaninta da har yanzu bai dawo dai-dai ba. Kusan mintuna uku Malikat Haseenat taima Iffah nuni data miÆ™e, ita kuma ta birka wheelchair É—inta suka shiga lifter. Mintuna biyu ne kacal suka iso da su katafaren falon da yafi kowane falo Æ™awatuwa a kaf daular ma da sashen kawai ba. Iffah tai Æ™oÆ™arin danne harbawar Æ™irjinta sakamakon tozali da wanda ke zaune a falon cikin zama na Æ™asaita da izzar masu mulki. Tafiya take tamkar hawainiya saboda tsabar kasala da sanyin gaÉ“É“ai. Zuwa yanzu wannan fuskar bata aljani take fassarata ba, neman Æ™arin bayani take a kanta a dalilin ganinta a waje biyu da basu da alaÆ™a da juna a zahirin rayuwa…
Tajwar Eshaan da ke kishingiÉ—e bisa Æ™ayataccen kujera mai kama da wani madaidaicin gado gabansa butar shayi ce da Æ™aramin kofin da alamu suka nuna yasha ko zai sha, idanunsa ya janye daga kan television da yake kallo ya É—an waigo garesu. Akan Iffah dake tafiya tamkar hawainiya ya fara saukewa, fuskarta a sakaye take, hanunta dake riÆ™e da rigar jikinta ne ta Æ™asa kawai a bayyane. Janye wa yay ya maida ga Malikat Haseenat. Ta É—an hararesa da salon kulawa da nuna damuwa. Idanun ya janye a sannu daga kanta itama yana sakin kasaitaccen murmushi….
Harya gama gaisawa da kakar tasa a yanda yake kishingiÉ—e batare da ya motsa ba Iffah na tsaye Æ™yam tamkar an dasata. Malikat Haseenat ta maida kallonta gareta tare da ambatar sunanta. A dake Iffah ta amsa dan tayi alÆ™awari ma kanta bazata taÉ“a barin rauninta sake bayyana ga kowa ba a yanzun. Kafinma Malikat ta sake cewa wani abu tai Æ™asa a hankali, cikin rashin Æ™warin jiki ta zube Æ™asan lallausan carpet É—in da ko jikin zomo bazai nuna masa laushi ba. Ƙamshi ko ba’a magana dan ko’anan ake shukashi iyaka kenan.
“Amincin ALLAH ya tabbata a gareka”.
Ta faÉ—a badan har zuciyarta abinda take son faÉ—ar kenan ba. Sai dai kwarjininsa daya mamaye falon da duk girmansa take jinta a matse yaÆ™i bata damar fitar jin zafinsa dake a Æ™asan zuciyarta a zahiri. Kamar a waccan ranar yau ma bai amsa ba, babu ma alamar yajita tattare da shi. Daga cikin hular alkyabbar jikinta ta cije lips É—inta da masifar Æ™arfi tamkar zata hudasu da haÆ™ori…..
“Ai ma Zawjata-almilk rakkiya É—akin da Tajwar zaiyi barci a yau”.
Furucin Malikat Haseenat ga hadiman dake rakuÉ“e gefe zube a Æ™asa kawunansu rissine tun shugowarsu ya nema sarÆ™e numfashin Iffah da Tajwar Eshaan a lokaci guda. Babu wanda Malikat Haseenat ta kalla a cikinsu sai É—aya daga cikin Hadiman ce da suke girki ta miÆ™e da rawar jiki zuwa inda Iffah take. Dole ta mike dan a furucin Malikat Haseenat babu wasa ko É—aukar turjiya ga kowannensu….
Shiru falon babu wanda ya sake ƙwaƙwƙwaran motsi har hadimar data raka Iffah iyakar ƙofar ɗakin ta dawo Malikat Haseenat ta sallamesu. Da ga shi sai ita suka rage, dan haka ya kafeta da idanunsa. Kai Malikat Haseenat ta ɗauke gefe tamkar bata gansa ba ko fahimtar kallon.
“Anan zata zauna, sai ka zaÉ“i inda kake buÆ™atar ta kasance har tsahon sati É—aya, dan zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu masu mata hidima zasu kasance tare da ita. Na damÆ™a amanarta a hannunka, ina kuma fatan ta kasance Æ™arÆ™ashin kariyar UBANGIJI. Fatan alkairi da shiga sabuwar rayuwa, tare da tayaka murnar sabon aure. Na barku cikin amincin ALLAH”.
Da alama gushewar numfashi da rikicin wannan tsohuwa ya gama daskarar da jinin Shahan-shan. Dan harta fice a falon ko gashin idonsa bai Æ™yafta ba, kai kace wani butun butumine aka dasa a wajen domin tarihi…….

(Tsohuwar nan kuwa na lafiya? Zata kai mana Iffah har ƙuryar Dodon Mayu).

★★… ★★….

Duk da dare ne gaba É—aya masarautar ta É—auki É—umi bisa wannan bahagon hukunci na Malikat Haseenat. Basu da al’amarin yazoma a bazata ba, hatta Malikat Bushirat da Daneen Ammarah da Jasrah da akai zaman da su komai ya musu cak. Abinda suka sani kawai komawar Iffah sashenta, bawai kaita turakar Shahan-shan ba. Miyasa Malikat Haseenat ta canja lissafin a kan kansu suma?. Wannan itace tambayar daketa musu kaikawo su duka.

“Ni kam dai a wannan gaÉ“ar na kasa gane komai wlhy Akia. Shin minene dalilin Mamma nayin haka? Miyasa lissafin ya canja daga yanda muka tsara gaba É—aya?”.
Kamar malikat Bushirat bazata tanka har ta kai ta kawo kusan sau uku kafin ta dubi Jasrah mai maganar. “Kaina ya kulle Jasrah”. Ta faÉ—a a takaice da kaiwa zaune bakin gadon ta dafe kanta.
“Ya ALLAH! Wlhy zuciyata ta fara kai ni ga hasashen wani abu daban?”. Jasrah ta sake faÉ—a tana dafe nata kan itama.

A É“angaren Daneen Ammarah ma dai a rikicen take. Sai dai ita nata lissafin yasha banban da nasu Malikat Haseenat. Daga É—akin taro bedroom É—in Malikat Haseenat ta wuce zaman jiranta. A zaman da bai wuce mintuna arba’in ba kuwa sai gata. Kallo É—aya taimata ta É—auke kai. Hadimar dake biye da ita ta ajiye madarar hanunta da zubewa Æ™asa tana gaida Daneen Ammarah. Hannu kawai ta É—aga mata….
“Na matuÆ™ar gajiya, kwanciya kawai nafi buÆ™ata”. Malikat Haseenat ta faÉ—a tana wulla kekenta hanyar bathroom É—inta batare data sake kallon Daneen Ammarah ba. Da kallo ta bita cikin shakku da shan jinin jiki. Dan duk da a dunÆ™ule tai magana tana nufin bata bukatarta a É—akin kenan. Jiki a sanyaye ta miÆ™e ta fice zuciyarta na faman tsalle-tsalle…

Duk yanda taso kwanciya ta kasa hakan, fargaba da tausayin Iffah ne ke matukar É—awainiya da ita. Har cikin zuciya bata son rasa yarinyar dan ta matuÆ™ar shiga ranta. Soyayya take mata irin ta Æ´a da uwa. Ita kanta har takanyi mamakin yanda takejin Iffah a rai matuÆ™a, amma tasan wannan Æ™aunar daga ALLAH ne kawai. Wayar dake a hannunta ta Æ™ara rumtsewa, ta gwada kiran Iffah ya kai sau huÉ—u kenan amma tana fasawa, so take taji lafiyarta ko zata samu Æ´ar nutsuwa, amma wata zuciya na gargaÉ—arta da kalmar rashin dacewa….

★★…..

“Mi wannan tsohuwar ke nufi wai shin? Ko itace abin neman mu kamar yanda barbushi ya sanar mana?”.
Miran Arshaan yaja numfashi ya fesar, kamar bazaice komai ba sai kuma ya kafe Miran Jasim da kallo yana girgiza kai. “Wlhy kaina ya kwance Jasim Akhi. Na kasa gane komai a wannan gaÉ“ar, abinda na sani kawai shine mutuwar yarinyar nan a wannan gaÉ“ar tamkar mutuwar cikar birinmu ce, dan na gama É—ora dukkan hope É—inmu a kantane. Bai kamata ta mutu a yanzu ba har sai ta Æ™arasa mana aikin da muka kwashi tsahon shekaru muna ginawa”.
“Miye mafita?”.
Cewar Miran Jasim a firgice, dan zantukan Arshaan É—in kamar sun zaburar da shi ne abinda ke gabansu. Kai tsaye Miran Arshaan yace, “Ziyartar Barbushi a wannan daren, kafin waccan sankaran matar da ban san amfaninta a tafiyarmu ba tazo ta ishemu da tsarin banza”.
“Hakan yayi mun, babu amfanin É“ata lokaci kaje kayi shiri”.
Kai Miran Arshaan ya gyaÉ—a masa, tare da mikewa ya fice. Da banzan kallo Miran Jasim ya bisa, cikin Æ™anÆ™ance idanu da wani shu’umin murmushi a fuskarsa “Ba matar can bace kawai abin banza a cikinmu, har da kai Arshaan, daka gama mun amfani zan kawar da kai, dan ni kaÉ—ai nake son mulkar daular ruman batare da É—an uba ko É—aya ba da zai zame min abokin gaba, nasan idan har na barka kaima zaka zamemin maÆ™iyi dan burinka wannan kujerar ne na sani shashasha”…

(WaÉ—an nan mutane dai to bara nayi shiru dai)

*_ZAWJATA-ALMILK_*

Duk da akwai wani É—an É“urÉ“ushin tsoro a Æ™asan zuciyar Iffah ta matuÆ™ar dakewa da addu’a ta shiga É—akin bayan ta gama Æ™arema bangon dogon corridor É—in da suka biyo kallo, ta jinjina kai cikin jin matuÆ™ar Æ™una da tausayin talakawan Æ™asan ruman baki É—aya. Tayi imanin akwai dubbunan mutane dake barci akan titi cikin yinwa da Æ™ishirwa da yawa. Amma abin mamaki yau ga bangon É—akin barcin Shahan-shan yasha ado da zinari matsayin fenti, “Taya ma imani zai zauna a zuciyar mutanen nan har su É—auka rai wani abun mai daraja?” ta faÉ—a a zahiri idanunta na cika da Æ™wallar baÆ™in ciki da Æ™ara jin tsanar Tajwar Eshaan Ibn Haysam Abdul-majeed……….✍️

(Hikenan Iffahr mu an shigo É—akin mutuwa).

Ko miye dalilin Malikat Haseenat na kai Iffah turakar Shahan-shan kai tsaye haka? Miye dalilinta na canja abinda suka tattauna da su Malikat Bushirat? Shin ko dai malikat Haseenat ce T….?.

Yaya zata kasance tsakanin Iffah da Shahan-shan ne? Ta wani ɓangaren abinda ke kashe Zawjata-almilk kuna ganin zai ƙyale rayuwar Iffah a wannan dare kuwa?.

Gadai wasu ɓoyayyun maƙiya na sake fitowa. Irinsu Miran Arshaan (mijin Jasrah kuma ƙani ga Tajwar Haysam) da Miran Jasim (shima ƙani ga Tajwar Haysam). Shin wacece wai matar nan da suketa a ambata batare da sunanta ba?.

Hhhh tabbas yanzu ne wasan zai fara. Sai ku shirya ku sake shiri dan sai a yanzu ne muka kalmashe bakin shimfiÉ—ar labarin dake cikin littafin DAUÆŠAR GORA… Wasan na asali yanzu ne filin yinsa ya kammala. Masoya sai mu antaya kawai.

*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*

*DAUDAR GORA Billyn abdul*

*KI KULANI hafsat xoxo*

*A RUBUCE TAKE Huguma*

*RUMBUN K’AYA Hafsat rano*

*IDON NERA Mamuh ghee*

_LITTAFI DAYA: 400_
_LITTAFI BIYU: 600_
_LITTAFI UKU: 800_
_LITTAFI HUDU :1000_
_LITTAFI BIYAR: 1200_

_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_

_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_

_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_

_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_

_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_

_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_

ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN

MARYAM SANI
ACCESS BANK
0022419171

SAI A TURA SHAIDAR BIYAN

09033181070

IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA

09166221261

*ƳAN ƘASAR NIGER. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*

+227 96 09 67 63

Books biyar 1250CFA
Books hudu 1050CFA
Books uku 850CFA
Books biyu 650CFA
Bookk daya 450CFA

KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.

MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.

 

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu

_

✨ÆŠ ✨
( )

 

Post a Comment

0 Comments