Daudar Gora Book 1 Page 32

Latest Posts

6/recent/ticker-posts

Ad Space

Daudar Gora Book 1 Page 32


32_*

……..Ni’imtaccen Æ™amshin dake tashi a katafaren É—akin ta zuÆ™a ta fesar da cigaba da bin komai daki-daki. ÆŠaki kam ya cika a kirasa É—aki ga masu arziÆ™in dake É—aukar duniya gidan zama. Sai dai ta gama ayyanawa a ranta babu wani Æ™yale-Æ™yale da zatai sakacin da zai ruÉ—eta har ya dakatar mata da Æ™udirinta data fara taka tsanin nasararsa a yau insha ALLAH. Ta saki kasaitaccen murmushi da ware hannayenta iskar na’urar ac ta busota tare da Æ™amshi, idanunta ta lumshe ta buÉ—e tare da tsuke fuska. Cikin wani kakkausan sauti daya bambanta da nata na baya ta furta.
“Yanzu ne za’a fara wasan na gaskiya. Dodon matsafa MATAN ƘWARAI bisa kanka!!”…

( Iffahn mu irin wannan alwashi haka kinfa fara bani tsoro).

★★…

Tun wucewar Malikat Haseenat ya bar falon shima. Tsaye yake jikin windown Æ™aramin falonsa na hutawa da babu mai shigarsa sai shi É—aya tak da amintacen hadiminsa mai gyarasa. Dan a doka ma hatta matarsa bata da hurumin shiga wannan falon a tsari da Æ™a’idar masarautar. Hasken daya Æ™awata cikin masarautar ya bashi damar iya ganin abubuwan dake kusa daga inda yake, sai dai kuma a zahiri idanun nasa ne kawai ke kallon zuciyarsa sam ba’a nan take ba. Ya kwashe tsahon lokaci a wajen kafin ya warware hannayensa dake goye a bayansa ya furzar da numfashi. Ƙofar É—akin barci Æ™waya É—aya dake a falon ya nufa. Shima tsaf yake tamkar anan yake zaman din-din-din. A maimakon kwanciya anan É—in ma zaune yakai cikin kujerar dake ajiye a gefe domin hutawa kawai. Tun agogon É—akin na juya sakanni da mintuna har ya koma awanni yana zaune idanunsa lumshe, ya kwantar da bayansa a makarin kujerar dake É—an juyawa a hankali. A kallon fuska baka isa gane yanayinsa ba balle ka samu damar masa fassara. Bugawar agogon É—akin mai nuni da cikar Æ™arfe biyu dai-dai ta sakashi buÉ—e idanunsa da Æ™arancin hasken É—akin ya hana damar iya tantance launinsu a yanzu. Agogon ya tsurama ido tamkar mai lissafa daÆ™iÆ™un da suka cigaba da motsawa…..

A É“angaren Iffah wannan lokaci na dai-dai da kai goshinta Æ™asa domin yima UBANGIJI suduja a karo na babu adadi. Tun bayan kammala lissafe-lissafenta da Æ™idaye-Æ™idaye ta zanzare rigar jikinta, Æ™aramin akwatinta ta buÉ—e babu alamar damuwa tattare da ita ta sauya kayanta zuwa abaya. Daga haka ta nufi bayi bakinta Æ™unshe da tarin addu’oin da taketa yi tun shigowarta É—akin. A karan farko data buÉ—e fanfo da nufin yin alwala saÉ“anin zubar ruwa sai taci karo da jan abu tamkar jini. Tabbas taji firgici, amma sai tai yaÆ™i da rauninta wajen cigaba da addu’a da son daidaita harbawar da zuciyarta keyi da sauri-sauri. Tamkar almara kalar jan ya É“ace a idanunta ainahin ruwa ya maye gurbinsa. Numfashi taja ta fesar zuciyarta na tabbatar mata ta Æ™ara dakewa. Tsaf ta É—aura alwalarta kuwa ta miÆ™e, tana Æ™oÆ™arin gyara É—an kwalinta taji tamkar an gitta ta bayanta. Anan É—inma dai zuciyarta ta tsinke, amma sai ta cigaba da ambaton sunan ALLAH ta basar. Bata damu da nan wanin abin salla ba, dan tsaftar dardumar da aka Æ™awata É—akin da ita ya gamsar da ita. Mayafinta ta naÉ—a tai nagartacciyar tsayuwar salla domin fuskantar UBANGIJIN talikai mai jin kukan wanda ma basu fara kukan ba, mai bada kariya ga wanda ya yarda babu abin dogaro sama da shi…
Taja tsahon lokaci a sujidar tana mai zubda hawaye da Æ™askantar da kai ga mai gani a duk inda ka É“uya. Bayan ta sallame tai zaman karatun Alkur’ani a cikin wayarta dan batajin zata samu Alkur’ani a wannan É—akin da Æ™yaleÆ™yalen cikinsa ya tabbatar mata zamowa fadar aljanu ba komai bane. Sai da ta gama karance baÆ™ara har zuwa inda suka tsaya a makaranta sannan tai addu’a mai tsawo itama. Sosai taji wata iriyar nutsuwa na ratsa dukkan jikinta, ta sauke ajiyar zuciya da miÆ™ewa. Hankalinta kwance ta haye katafaren lafiyayyen gadon da Shahan-shan ne kawai ya taÉ“a hawansa a tarihi. Nanma zama tai tai addu’ar barci ya shafe jikinta ta gyara lausasan filos É—in da aka Æ™awata adon gadon da su ta kwanta tana sauke ajiyar zuciya. Barci mai daÉ—i ya fara fisgar idanunta a sannu-sannu sai gata tana sauke numfashi…….

★★…… ★★….. ★★…….

Bayan wucewar saurayin da Kaka ya shimfiɗama sha tara na arziƙi gidan yay shiru. Kamar yanda bai cema Iyyani komai ba itama batace ba, tsahon wasu mintuna sannan ya miƙe ya shiga ɗakinsa. Tashi Iyyani tai ta bisa, dan ta fahimci maganarce baya buƙatar ayi sam..
A É—akin ma baice mata komai ba har tsahon wani lokaci, ganin haka ta katse shirun da faÉ—in, “A haÉ—a maka ruwan wanka?”.
Batare da ya bar abinda yake ba ya jinjina mata kai. Fita tai jiki a sanyaye, babu jimawa ta koma ta sanar masa an haÉ—a. “ALLAH yay miki albarka”. Ya faÉ—a kamar yanda ya saba. Ta É—an ji sanyi a ranta, dan haka ta amsa da “Amin tare da kai” cikin sauke ajiyar zuciya….

“Ai bakaci wani abincin kirki ba”.
Iyyani ta faÉ—a idonta akan kwanikan gaban Kaka da ya gama cin abincin data kawo masa bayan fitowarsa wanka. Kai ya jinjina mata da sakin murmushi a karan farko tun bayan shigowarsa gidan. “Alhamdulillahi wanda naci ya wadatar dani”. Kai kawai ta jinjina masa jikinta na Æ™ara sanyaya. Duk wanda zai sam mijinta a bayanta yake, ta san murmushin sa ba yana nufin farin ciki bane na tsantsar damuwa ce…..
“Yaya jikinta?”.
Ya katse tunaninta da abinda taketa zumuÉ—in san ji a bakinsa. “Alhamdulillahi da sauÆ™i”.
“ALLAH ya Æ™ara afuwa. Bara na ganta”.

Ummu na zaune shiru ta tsurama waje ɗaya idanu suka shiga. Har suka kai zaune gefenta babu alamar tana san da zuwan nasu. Kaka ya kafa mata idanu na wasu sakanni sai kuma ya kauda kai. Taɓata Iyyani tayi, ta kawo nannauyan numfashi da ɗan zabura na ganinsu a ɗakin dan da gaske bata san da shigowar tasu ba. Kaka ta kalla idanunta na cikowa da ƙwalla, sai kuma ta duƙar da kai ta fara gaishesa. A hankali ya nisa kafin ya amsa a taƙaice kamar yanda tai gaisuwar.
“Jumaimah!”.
Ya kira ainahin sunanta.
“Na’am Baba”.
Ta amsa akan laɓɓanta.
“Damuwa ko Æ™untata kai bata sauya Æ™addarar bawa. Juriya da tsantsar jarumta baya hana Æ™addarar zuwa. HaÆ™ilo ko nuna Æ™arfin iko baya ture ta a lokacin da aka so. Rauni ko rashin tawwakali bazai dawo maka da abinda dama can ba naka bane ba. HaÆ™uri shike samar da komai koda kuwa a zahiri yafi Æ™arfin Æ™arfinka”.
“Hakane Baba”.
Ta faÉ—a cikin rawar murya.
Murmushi ya saki da matsawa kusa da ita sosai. ÆŠa a gaban iyayensa baya girma koda ace yayi furfura a saman kai. Kaka ya riÆ™o hanun Ummu cikin nasa, É—ayan kuma ya shafa kanta. “ALLAH yayi miki albarka. Yasa Æ™addarar su ta zama kaffara a garemu baki É—aya.”
“Baba mun rasa su suma ko?”.
Ummu dake dubansa idanu cike da Æ™walla ta faÉ—a. Murmushin ya sake sakar mata. Sai kuma ya girgiza kansa da kwanto da kanta bisa kafaÉ—arsa. “Bamu rasa su ba, ba kuma mu fidda rai da samunsu ba”.
A hankali hawayen da suka kasa fita a idonta tsahon kwanaki suka fara sauka a kafaÉ—arsa…….

★★…. ★★…. ★★…..

Mummunan mafarkin da ALLAH ya bata ikon cin galaba a cikinsa ta farka a zabure, cikin amincin UBANGIJI harshenta ya ambato addu’ar tashi daga barci kamar yanda musulinci ya É—oramu akai. Ajiyar zuciya ta sauke da saka gefen bargon data lulluÉ“a ta yarce gumin da yay ma goshinta jalab, sai kuma ta sake lumshe idanu jin sautin kiran salla da take Æ™yautata zaton a masallacin cikin masarautar ne. Hasken É—akin ta kai hannu ta Æ™ara, ta bi ko’ina na cikinsa da kallo tamkar zataga munanan halittun data gani a cikinsa a mafarki. Rashin ganin komai a zahiri ya bata Æ™arin gwiwar sakkowa a gadon ta nufi toilet. Bata damu da rashin ganin Tajwar Eshaan a É—akin ba duk da taji Malikat Haseenat ta ambata nan É—in matsayin É—akin barcinsa na daren jiya. Ƙarancin shekarunta da wautarta yasa bata É—auki tsallakewar komai ba. Abinda kawai zuciyarta ke mata kaikawo a rai shine ta tsallake daren na jiya dai koma yaya ne, ta tsallake tarihin mutuwa a daren kwana turakar dodon matsafa. Dalilin tsallakewar, ko barinta da yay da ranta ne bata sani ba, ba kuma tasan tayaya ya kamata ta sani ba. Abinda kawai take da damar yi shine buÉ—e kunne da idanuwa taga mizai biyo baya ga kowa da kowa. A yanzu É—in ma tayi zaton ganin jinin kamar jiya dai, sai dai babu alamar hakan har ta kammala uzirinta tayo alwala ta fito. Tana idar da salla wani irin nannauyan barci ya dinga fisgar idanunta. Dakewa tai cikin dauriya tai zaman yin azkar, da Æ™yar ta iya kammalawa barci yay mata baban fisga a wajen dole takai kwance tana ambaton sunan ALLAH. A hankali ta fara sauke numfashi alamar barcin nata mai nauyi ne….

★★…. ★★…..

A cikin masarauta tako ina an gama baza kunnuwan jin fito da gawar Zawjata-almilk. Hatta da Malikat Haseena bata tare da nutsuwarta gaba ɗaya. Tun ana ƙirga sakanni a bayan sallar asubahi har aka koma mintuna, mintuna suka koma awanni babu wani labari. A take aka koma ƴar ƙus-ƙus tun daga kan hadimai har manyan masu faɗa ajin masarautar.
Yayinda suma Hadiman sashen Shahan-shan suke zaune jigum-jigum na jiran tsumayen abinda kowa keda tabbacin zai kasance. bakunansu cike yake taf da abubuwan faÉ—a akan abinda suka wayi gari da shi mai matuÆ™ar rikitarwa da zai maimaita faruwa bayan ya faru ga duk wata Zawjata-almilk data kwana ta tashi a wannan sashen. Duk É—unbin yawan abin cewar iyakarsa zukatansu dan ko’a tsakaninsu bai faÉ—uwa balle gulmantawa a waje saboda tako ina camara ce zagaye da su…..

*_★MALIKAT BUSHIRAT★_*

Ba’a safiyar yau ba, ita tun ma a daren jiya tai hanun riga da nutsuwa. Gaba É—aya a daren ko sau É—aya bata iya ta rintsa ba. A maimakon barci ma idanunta akan sashen Shahan-shan da kowa ke iya gani daga nasa sashen a cikin masarautar suka kwashe mafi yawan awannin daren na jiya. Tayi yunÆ™urin kiransa amma wayar a kashe, hakanne ya sake É—aga mata hankali da jin zafin wannan hukunci na Malikat Haseenat a karo na farko. A ganinta ganganci ne miÆ™a nagartacciyar yariya irin Iffah hannun gudan jinin nata bayan Mamma tasan minene makomar yin hakan ga rayuwar yarinyar. Duk jarumtarta a duk sanda ta tuna zuwa safiya gawar yarinyar ce zata fito takanji Æ™walla sun cika idonta. Amma takan danne ta hanasu fitowa har garin ALLAH ya kammala wayewa…
Tun idar da sallar asubahi bata iya ta motsa ba, Æ™irjinta ne ke matuÆ™ar bugawa da jiran tsammanin mummunan labari…..

*_★DANEEN AMMARAH★_*

A É“angaren Daneen Ammarah itama a kwatankwacin irin halin da Malikat Bushirat ta kwana ta tashi take ciki. Dan ita kwana tayi ma tana hawaye. Har Æ™arÆ™ashin zuciya takejin matsanancin Æ™aunar Iffah. Tana jin yarinyar a matsayin cikon wani gurbi data rasa irin na kowace uwa mai shekarunta. Sai gashi Mamma da ta fara bata tsoro a daren jiya ta rusashi da maye gurbinsa da fargaba mai matuÆ™ar tsanani da razani. Wani mutum saÉ“anin jininta bai taÉ“a mamaye zuciyarta da Æ™auna mai Æ™arfin haka ba kamar yanda yarinyar tayi mata. Sosai take jinta a rai da jinin jikinta. Itama dai tun daga sallar asuba bata sake iya kataÉ“us ba tai zaman jiran tsammani irin na duk wanda ya kwana ya tashi a cikin masarautar…….

★★… ★★…. ★★….

Harya gota É—akin cikin shiga ta blue É—in jallabiya mai tsananin Æ™yau da Æ™yalli mai É—aukar ido da nuna taushinta a zahiri dake nuna daga masallaci yake ya tsaya cak. Kamar bazai motsa ba sai kuma ya juya kansa a sannu yana kallon É—akin. Kallon kusan minti É—aya da wasu sakanni ya motsa gaÉ“É“ansa cikin takunsa na izza da kame kai ya tura kai ciki. Da farko rashin lura da ita ya sakashi yin tsamm, sai dai fuskarsa ta nuna dakewa kamar koyaushe. Ya É—aga Æ™afa da niyyar juyawa ya fita idanunsa suka sauka a kanta. Yay tsai yana kallonta na tsahon mintuna kusan huÉ—u tamkar mai rarrabe ita É—in ce ko wata? Dan a kallo É—aya zaka fahimci salla ta idar a wajen barci yay awon gaba da ita. Ya É—an furzar da numfashi da kauda kansa gefe ya sake bin É—akin da kallo kai kace baÆ™onsa ne har ya sake direwa akan fuskar Iffah dake ta barcinta numfashinta na fita a hankali………✍️

*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*

*DAUDAR GORA Billyn abdul*

*KI KULANI hafsat xoxo*

*A RUBUCE TAKE Huguma*

*RUMBUN K’AYA Hafsat rano*

*IDON NERA Mamuh ghee*

_LITTAFI DAYA: 400_
_LITTAFI BIYU: 600_
_LITTAFI UKU: 800_
_LITTAFI HUDU :1000_
_LITTAFI BIYAR: 1200_

_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_

_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_

_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_

_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_

_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_

_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_

ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN

MARYAM SANI
ACCESS BANK
0022419171

SAI A TURA SHAIDAR BIYAN

09033181070

IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA

09166221261

*ƳAN ƘASAR NIGER. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*

+227 96 09 67 63

Books biyar 1250CFA
Books hudu 1050CFA
Books uku 850CFA
Books biyu 650CFA
Bookk daya 450CFA

KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.

MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.

 

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*

✨ÆŠ ✨
( )

 

Post a Comment

0 Comments