Daudar Gora Book 1 Page 35

Latest Posts

6/recent/ticker-posts

Ad Space

Daudar Gora Book 1 Page 35


35_*

……..Hadiman sashin gaba É—aya kamshin turaren da sukaji ya sakasu tunanin Tajwar Eshaan da bai jima da shigowa ba daga fada ne ya sake fitowa. Sai kuma sukaga saÉ“anin haka lokacin da Iffah ke Æ™arasowa cikin katafaren falon mai É—auke da duk wani nau’in kayan more rayuwa irin na wanda suka isa. A kujerar da ko ba’a faÉ—aba tsarin zubinta ya isa tabbatar ma mai kallo Shahan-shan ne kawai ke zamanta ta kai zaune da bismillah a bakinta. Ƙafa É—aya kan É—aya ta harÉ—e fiye da salon sarauniyar Ingila tana kallonsu. Cikin rawar harshe dajin kwarjininta ya cike falon tsaf suka shiga zubewa suna gaisheta. Yatsu biyu ta É—aga musu cike da Æ™asaita batare data amsa ba dan haka kawai yanayin da ta tashi da shi taji bata buÆ™atar magana. Basu iya sun motsa ba har ta gama zuÆ™ar iska da fesarwa tamkar mai lissafin kaÉ—awarta sannan ta dubesu, sai kuma ta maida ga tarin abincin da aka shirya yanzu akan wata lallausar darduma saÉ“anin na É—azun akan teburin cin abinci. Akan farin tambulan na gilashi mai É—auke da madara fara Æ™al-Æ™al ta sauke idanun nata (mafarkina ya zama gaskiya kenan ko saÉ“aninsa) zuciyarta ta ayyana har lokacin idanunta tsaye akan tambulan É—in..
Hadiman da basu fahimci ma’anar kallon da takema kayan abincinba cike da girmamawa a gareta É—aya ke faÉ—in, “Ya Zawjata-almilk abincine daga saken mai babban É—aki, an shiryashi ne matsayin liyafa gareki ke da shugaba”. A hankali Iffah ta janye idanunta daga wajen ta maida kan hadimar na tsahon wasu sakkani, acan Æ™asan zuciyarta kuwa nanata sunan Malikat Haseenat take tamkar mai bitar karatun hadda. Batare da tace komai ba kuma sai ta kaÉ—a kanta. Shiru ya sake biyo baya kafin Iffah ta katseshi da duban hadiman da har yanzu dai ke tsaye da alama zaman jiransu sukeyi kenan, dan ta fahimci idan zaici abinci haka suke zagayesa. Kanta ta kauda da faÉ—in,
“Maleek fa?”.
Kai tsaye duk suka fahimci wa take nufi, tunda dai duk sun san minene ma’anar kalmar Malik É—in. Cikin tsantsan da kai É—aya daga ciki ta amsa mata da “Yanzu ya shigo daga fada”. Bata amsa ba, sai É—an jimm da tai na tunani akan ambatar fada da hadimar tayi, amma a zahiri ta basar abinta.

★Kasancewar saÆ™on haÉ—a liyafar cin abincin na Malikat Haseenat da tai akan iya shi da wadda ake kira matar tasa ya riskesa tunma kafin Iffah, dan kusan shine ma yay sanadin barowarsa fada duk da Aaminsa Miran Jasim (Aami. Kawunsa)ya buÆ™aci zaman tattaunawa da shi. Badan son ransa ba ya kimtsa ya fito cikin shiga mai sauÆ™i ta zaman gida. Kamshinsa da takun sawayensa dake tabbatar da girman ikonsa tuni ya iso a kunne da hancin Iffah dama hadiman dake zagaye da ita. Tuni hadiman duk sun zube bisa gwiwunsu kawuna a Æ™asa dan kallon shugaban nasu kai tsaye haramunne garesu bisa al’adar masarautar, idanma hakan ta faru gaban Ghazi zaka iya fuskantar tsatstsauran hukunci a dalilin hakan. Akanta dake harÉ—e kan kujerar da bayan shi babu wani mahaluki daya iya kwatanta zama kanta ya fara sauke Æ™asaittun idanunsa. Dai-dai itama ta É—ago nata sakamakon jin takun sawayensa da zubewar hadiman. Cikin ido suka kalla juna, hakan yay matuÆ™ar tsikarar zuciyar Iffah da abinda take faman hasashe da neman tabbaci a kwanakin nan ya tabbata É—in yau a idanunta. Dan tabbas shigar jikinsa ta yanzu ta sake tabbatar mata da waccan fuskar… Shine ya fara janye nasa kausasan idanun batare data iya tsinto komai a cikinsu ba. Kamewa da gagara fassara abinda ke kan fuskarsa kuma ya taka rawar gani wajen É“oye ainahinsa. Sai ma kallonsa da ya maida kan Æ™aton agogon dake kafe a falon cike da basarwa kai kace bai ganta bane. Ita madai basar da shi É—in tayi kamar ma bata san da fitowar tasa ba, sai zuciyarta dake faman kai kawo a Æ™irjinta cikin sauri-sauri. So take ta gaskata shi É—inne kota Æ™aryata amma zuciyarta taÆ™i bata haÉ—in kan karkata akan ko É—aya a cikinsu. Sai ma neman jefata a ruÉ—ani takeyi……

*_BARRISTER_*

Duk yanda Barrister yaso sanin suwaye su? Mi kuma yay musu basu saurareshi ba suka turasa cikin jibgegiyar baƙar motarsu, yayinda ɗaya daga cikinsu kuma ya shiga motar Barrister ɗin ya fiddo komai na ciki a cikin wata ƙatuwar jakka suka bar wajen.. Suna ɗan matsawa a wajen wani abu mai masifar ƙara ya ziyarci kunnuwan kowa. A take aka fara gudun ceton rai dan duk wanda yasan bomb yasan shine a yanzun ma.
“Innalillahi wa inna’illaihirraji’un”. Barrister ya faÉ—a idonsa nabin motarsa da tai sama ta shiga dawowa pieces Æ™asa alamar dai bomb É—in daga cikinta ya tashi. Duk da ya firgita da mutanen yay jarumtar dubansu fuska a dake. “Ku su waye? Miyasa kuka aikata min haka?”.
Babu wanda ya tanka masa a cikinsu, kamarma basu jisa ba sukayi. Hakan sai ya Æ™ara tada hankalin Barrister, dan ya fahimci ya shiga hannun mugayen mutanen nan kenan. YunÆ™urowa yayi da nufin Æ™ara magana suka jefa masa handkherciff a fuska, daga haka bai sake sanin inda yake ba sai buÉ—e idanu yay ya gansa a wani É—aki da bai san inane ba…

Gaba É—aya jihar Hubab da Æ™asar Ruman a rikice ake akan tashin wannan bomb, dan abune da bai taÉ“a faruwa da su ba. Jami’an tsaro sun iso akan lokaci, sai dai Alhamdullah ba’a samu asarar rai ko É—aya ba daga mutanen gari, amma ana tunanin harda drivern motar al’amarin ya rutsa saboda babu wanda ya lura da sanda mutanen nan suka Æ™wamushe Barrister É—in kasancewar komai sun yisa ne cikin Æ™warewa…
Jami’an tsaro da Æ´an jarida tuni sun iso wajen akan lokaci, hakama jama’ar gari masu jarumta sun zagaye wajen domin ganema idanunsu. Babu gawar direban motar a duk iya bincike da jami’an tsaro sukayi, dan basu ga wani alamar sassan jikin mutum ba ko É—an yatsa, hakan sai ya É—aure musu kai dan mutanen da abun ya faru a idonsu sun tabbatar sunga lokacin da mai motar ya ajiye ta a wajen ya shiga masallaci, koda aka fito kuma mutane da yawa sun tabbatar sunga lokacin daya nufi motar wasu ma sunce har ya shiga. Wannan zance ya sake É—aukar hankalin jama’a kowa yana faÉ—ar albarkacin bakinsa akan al’amarin…

Isowar wasu samari wajen kusan dai-dai da tashin bomb É—in, kallon juna sukai da sakin dariya a tare suna tafawa. Sai da sukai mai isarsu drivern dake jan motar ya É—auka waya. Nuni yay musu da suyi shiru. Take motar tai tsit kuwa. Ya É—an rissina cike da girmamawa tamkar yana a gabansa ne yana kwasar gaisuwa, bai damu da a yanda aka amsa masa a daÆ™ile ba ya cigaba da faÉ—in, “An rufe babinsa ranka ya daÉ—e”. Murmushi yayi alamar an amsasa da magana mai daÉ—i daga can. Sai kuma ya sauke wayar da juyawa yana kallon Æ´an uwansa ya kashe musu ido. Dariya suka shiga kwasa a yanzun ma, bayan sanyi wadda suka gamsu sun wadata sannan suka fita suma suma shige cikin taron mutanen dake wajen dan jin mi’ake tattaunawa…..

★★★….. MASARAUTA ★…..

Sai da ya kai zaune a inda aka shirya tarin abincin da kusan minti biyu sannan ta motsa itama dalilin maganar da Hadimai sukai mata. Bata musa ba ta miÆ™e zuwa inda yaken cikin takunta na nutsuwa da wasu ke É—auka yanga ko makamancin hakan. Zama tai irin nasa na Æ™asaita sai dai da alama ita kanta bata fahimci tayi hakan ba ma. Tsaurin idonta ya sakashi dubanta ta gefen ido batare da alamar hakan ta bayyana a yanayinsa ba. Tuni hadiman suka Æ™araso domin shirya abincin garesu. Iffah batai yunÆ™urin hanasu ba, dan a ganinta dole ta nutsu ta fara fahimtar yanda ake masa komai kafin ta karÉ“a wannan tsarin shima. Ta É—an bi madarar da hadimar ta É—auka, har yanzu zuciyarta na mata wasiwasi akan madarar batare data san dalili ba…
“Bar nan”.
Ta faÉ—a dai-dai Hadimar na yunÆ™urin zuba madarar a Æ™aramin cup na glass daya gama haÉ—uwa. Cikin mamaki hadimar ta sake risinar da kai domin girmamawa ga Iffah tana faÉ—in, “Ya Zawjata-almilk madara na É—aya daga cikin abinda shugaba yafi buÆ™atar amfani da shi a irin wannan lokacin”.
Kai tsaye babu ko É—ar tattare da Iffah tace, “Na yau dai bazai sha ba. A É—aukesa anan”.
Tsoro ne ya bayyana sosai a fuskar hadimar, gashi bata da damar ko satar kallon sashin da Tajwar ɗin yake balle ta fahimci karatun tasa fuskar. A ɗan ɗar-ɗar na rashin madafa ta ajiye tambulan ɗin a gefe ta ƙarasa aikinta. Duk da abinda ake yi a gaban Tajwar Eshaan ne, yanaji kuma yana gani. amma tsabar miskilanci da ƙarfin iko irin na masu ƙasa a hannu bai ko motsa ba balle bada wata alama akan abinda Iffah tayi ya bashi mamaki, ko ya ɗimautashi, koya birgesa, koya bashi haushi. Ko ɗaya babu mai iya tsinta a yanayinsa. Iffah ma dai bata yarda ta dubesa ba balle ta tsinta komai a tattare da shi ɗin. Sai ma wani kallon da taima hadiman ya tabbatar musu bata bukatarsu a wajen. Dan haka tuni suka ɓace tamkar ƙyaftawar ido.
Ya ɗan ja wasu mintuna zaune batare da ya taɓa komai ba, Iffah ta ɗan laɓe baki, acan ƙasan maƙoshi ta furta
“Ranka ya daÉ—e barka da wannan lokaci”.
A hankali ya É—ago ya zuba mata idanunsa, a mamakinsa bashi take kalloba ma. Kuma ya tabbatar itace tai maganar ba wani ba dai. Sake tsukewar fuskarsa mai cike da gizago da motsa hanunsa dake kan spoon ya tilasta Iffah É—an É—agowa garesa. Sai kuma ta tsaya cak tare da É—ago birkitattun idanunta da Æ™yau. Cikin nasa dake kallonta suka shige tamkar ya tsara hakan da gayya. MuÆ™ut ta haÉ—iye yawu da Æ™oÆ™arin kame rauninta dake neman bayyana a fili ta kauda kai gefe.. Shima nasan ya janye a Æ™asaitance ya fara cakulal abincin kamar mai cin magani batare da ya amsa mata gaisuwar tata ba. Hakan da yay ya sosa zuciyar Iffah, dan haka ta kumbura fuska lips É—inta suka shiga motsawa alamar akwai magana a bakinta sai dai babu damar faÉ—a…

★★…. ★….

Tun bayan tabbatar da madarar ta shiga jerin abincin liyafar da aka shiryawa Shahan-shan da Zawjata-almilk ta kasa zaune ta kasa tsaye, bukatarta kawai taji sakamakon da take buÆ™ata ga amintacciyar hadimarta akan lokaci. Sai dai kuma shiru kakeji wai malam yaci shirwa har lokacin da labarin tashin nakiya a jihar Hubab ya iso cikin masarautar. Ba wannan ne a gabanta ba, dan haka cikin jan tsaki ta kashe television É—in a harzuÆ™e. Idanunta ta sake maidawa kan agogon falon tanaji kamar tai tsalle ta ganta a sashen Tajwar Eshaan É—in ayita ta Æ™are. Dan yanzu a duniyar nan gani take bata da babban maÆ™iyya sama da yarinyar nan datai mugun shige mata hanci amma ta gagara fyatota ta huta a dalilin gargaÉ—in Uwa data kasa gane manufarsa har yanzu. Sai dai yarda da Uwa É—in ya tilasta mata bin komai É—in a sannu. Zata iya rantsuwa tunda ta san kanta bata taÉ“a cin karo da abinda ya kiÉ—ima zuciyarta ba irin saÆ™on Zawjata-almilk na raye bayan ta kwana a turakar Shahan-shan kuma. Ba ita kawai ba, hatta Uwa hakan ya kiÉ—imata da sake tabbatar da yaÆ™ine na gaske tsakaninsu da wannan yarinyar kenan. Dan haka batai wani magana mai tsaho da Ta-kurya ba bayan bata umarnin a isar da madarar data bata ga Iffah ta É“ace cikin tsanani É“acin rai daya Æ™ara birkita dukkan tunanin Ta-kurya É—in a yanzu har ta kasa zaune ta kasa tsaye sakamakon hakan……..✍️

*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*

*DAUDAR GORA Billyn abdul*

*KI KULANI hafsat xoxo*

*A RUBUCE TAKE Huguma*

*RUMBUN K’AYA Hafsat rano*

*IDON NERA Mamuh ghee*

_LITTAFI DAYA: 400_
_LITTAFI BIYU: 600_
_LITTAFI UKU: 800_
_LITTAFI HUDU :1000_
_LITTAFI BIYAR: 1200_

_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_

_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_

_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_

_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_

_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_

_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_

ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN

MARYAM SANI
ACCESS BANK
0022419171

SAI A TURA SHAIDAR BIYAN

09033181070

IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA

09166221261

*ƳAN ƘASAR NIGER. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*

+227 96 09 67 63

Books biyar 1250CFA
Books hudu 1050CFA
Books uku 850CFA
Books biyu 650CFA
Bookk daya 450CFA

KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.

MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.

 

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*

✨ÆŠ ✨
( )

 

 

Post a Comment

0 Comments