Daudar Gora Book 1 Page 36

Latest Posts

6/recent/ticker-posts

Ad Space

Daudar Gora Book 1 Page 36


36_*

……..Isowar labarin tashin nakiya a jihar Hubab ya matuÆ™ar tada hankalin duk wani mai faÉ—a a ji a daular ruman. Dan abune da bai taÉ“a faruwa ba a kasar ta ruman. Amma abin mamaki ga Tajwar Eshaan ba hakan bane, dan babu wani alamar damuwa ko nuna kaÉ—uwa da lamarin. Kallo É—aya yayma akwatin talabijin ma ya É—auke kai kamar ba’a Æ™asar da yake mulka matsayin shugan kowa da kowa al’amarin ya faru ba. A karan farko wani abu da tun shigowar Iffah masarauta bataji akansa ba ya tsikari zuciyarta sakamakon ganin halin da ya nuna akan wannan al’amari da duk wanda ya kwana ya tashi a Æ™asar ta ruman bazai ce bai shiga ruÉ—ani ba. Duk da ance ba’ai asarar rai ko É—aya ba taji kamar ta tashi ta shaÆ™ure wuyan Shahan-shan É—in ta huta da ganin wannan azzalumin shugaba da kansa kawai ya sani sai ahalinsa.
“Mi hakan ke nufi?”.
Ta faÉ—a tana faman kai kawo a ruÉ—e itama duk da a labarin an sanar da ba’a samu asarar rai ko É—aya ba sai dai dukiya. Abu mafi caja Æ™waÆ™walwa ga kowa ma ba ita kaÉ—ai ba shine jin wai wanda ya dasa bomb É—in ya tsere Bayan wasu sun tabbatar da sunga fuskarsa da shigarsa motar, musamman ma wasu samari huÉ—u da suka tanbatar da tare suke da wannan mota tun daga Æ™auyen Lufana da alama mutumin daga can ya fito. Tabbas sai tayi ajalin wannan mutumin a zuciyarta zataji salama. Dan a ganinta idan yau ya tashi kowa bai rasa ransa ba na gobe kuma fa? A wannan gaÉ“ar ta fara zargin anya wannan sarkin bada wata manufa dama ya dawo ya karÉ“a mulkin mahaifinsa ba? Dan alamu sun fara nuna uban nasa ma shine ya kasheshi.
“Lokaci yayi da zan fara aikina gadan-gadan”.
Ta faÉ—a a zahiri cikin tabbatarma kanta da yanayin É—aukar alwashi….

(Muma kam muna bayanki Iffah, dan muna son sanin mike zuciyar wannan bahagon sarki haka mai wahalar fahimta).

★★★

A babban zauren majalisan manyan masu faÉ—a aji na daular ruman kuwa na can yana neman hargitsewa dangane da faruwar wannan al’amari. Kowa faÉ—ar albarkacin bakinsa yake a duk yanda zuciyarsa ta ayyana masa musamman masu sukar mulkin Tajwar Eshaan a fakaice. Duk wannan kace nace da akeyi Tajwar Eshaan É—in na zaune cikinsu amma uffan bai tofa ba har suka ci suka tsire. Sai da suka lafa dan kansu da kuma maganar Miran Arshaan cikin É“acin rai a garesu sannan Tajwar Eshaan É—in ya buÉ—e idanunsa dake a lumshe ya gama Æ™are musu kallo É—aya bayan É—aya..
Akan Miran Arshaan dake cigaba da faÉ—a rai É“ace kan kausasan maganganu nasu ga É—an É—an uwansa kuma sarkinsu a yau basu dace ba ya sauke idanunsa. Cikin muryarsa mai zurfi da Æ™asaita ya fara magana a gadarance kuma a fisge…
“Barsu Aami. Waninsu bazai canja komai ba, kamar yanda bazai tirsasa Eshaan yin komai ba. Abinda kawai nake son ku sani, Eshaan Ibn Haysam Abdul-majeed guguwace data gama turniÆ™eku, kuma babu ruwan kogin da zai iya shayar da ita ruwan da zata lafa. Ku daina bama kanku wahala Æ™asar ruman da jama’ar cikinta a rubuce suke tsakkiyar tafin hannuna. Idan na murza kwafsanku kawai duniya zata gani a cikin guguwata, idan na matsa, jininku ne zai dinga É—iga a Æ™arÆ™ashin sawun Æ™afata na ringa bi ina takawa matsayin kwalta, ya rage naku ku zauna a inda na baku zaÉ“i ko ku zaÉ“o mummunan Æ™addararku da kanku tun lokacin É“acewarku a doron Æ™asa baiyi ba”.
Yana gama faɗa ya miƙe cike da takun Izza da kasaita ya bar falon. Da kallo duk suka bishi ran wasunsu na ƙuna, zukatansu kam tamkar zasu kifo ƙasa dan firgici. Cikin dauriya da nuna jarumta wani ƙyamusashen dattijo da tsufansa ya fara bayyana a cikinsu yay ƙwafa rai ɓace da kausasa murya.
“Lallai wannan yaron ya cika ya tumbatsa kuwa. Wai kenan haka zamu cigaba da zama yaro Æ™arami na tafka kuskure da mulkin zalunci yana kuma takamu a yanda ya gadama. Akaf tarihin mulkin daular ruman ba’a taÉ“a tsageran yaro kamar wannan ba, amma ubansa ya É—aura shi matsayin Shahan-shan bayan babu mai makamancin shekarunsa daya taÉ“a zama a wannan matsayin. lokaci yayi da zamuyi bore wajen tsigesa kafin ya gama halaka Æ™asar baki É—aya tunda naga shi ran É—an adam ba’a bakin komai yake garesa ba. wama ya sani ko shine yasa a dasa nakiyar kamar yanda ya kashe ubansa da Æ´aÆ´an mutane da aka aura masa. Koda yake minene ma na tantama tunda ga amsa ya bamu da bakinsa cewar Æ™asar da Æ´an Æ™asar duk a tafin hannunsa muke”.
A zahiri dai kowa yay tsitt yana sauraren dattijon, amma a zukatan wasunsu farin cikine fal da zantukan wannan tsoho ga Tajwar Eshaan É—in da mafi yawansu shakkarsa ta gama zagaye tunaninsu duk da kuwa kusan duk sun haifesa dan babu wani sa’ansa, dan har yanzu tun Æ´an majalissar mulkin mahaifinsa ne bai canja ba. Dattijon na rufe baki Miran Jasim ya miÆ™e rai a É“ace shima. Dattijon ya watsama wani mummunan kallo da faÉ—in, “A lallai ka cika dattijon banza dan bazan kalleka matsayin Aami É—inmu ba yau kam. Mun godema ALLAH daya fara nuna mana ku a zahiri, ai bamu san É—an É—an uwanmu ya kai muku har haka a zuciya ba sai yanzu. To ku sani duk ma mai irin wannan tunanin ya makaro, Eshaan kuma a gareku sai gani sai hange sai hararar nesa, dan badai mutum ba ku rubuta ku aje”. Ya kare maganar yana É—an Æ™yaftama Miran Arshaan daya saki baki tsabar al’ajabin É—an uwan nasa da kasa fahimtar inda ya dosa. Cikin sauri ya kaÉ—an kansa da amshe zancen a fusace shima yana miÆ™ewa. “Aam ai ban san haka kakeba wlhy sai a yau, ashe zaka zama na farko a jerin wanda zasu soki jinin Haysam Akhi kuma É—an uwanka mahaifinmu dan Æ™asa ta rufe idanunsu? To bazamu ce da ku komaiba a yanzu, amma kusani duk wanda yake da wannan Æ™udirin a ransa jininmu fansa ne ga kare Eshaan tako wace fuska. Mun barku lafiya”.
WaÉ—an nan zantuka na Miran Jasim da Miran Arshaan sun matuÆ™ar saka ruÉ—ani a zukatan duk wanda ke a wannan zauren taron. A take wasu suka shiga barranta kansu ga wannan magana ta dattijon Aamin sun ganin waÉ—anda ma ya dace suyi hanÆ™oro da kwarema Tajwar Eshaan É—in baya saboda kwaÉ—ayin kujerar da yake kai tunda suma sunada hakki a kanta na tare da shi su kuma a wa. Anan fa rikici ya kaure aka tashi baram-baram….

★★

“Nikam na kasa fahimtar dalilin ka nayin hakan”.
Miran Arshaan ya faÉ—a bayan fitowarsu daga zauren tattaunawar. Wani shegen murmushi Miran Jasim ya saki cike da basarwa. Sai da sukai nisa da sashen Tajwar Eshaan gaba É—aya sannan yay wata Æ´ar dariya batare daya kalla Miran Arshaan É—in ba. ShimfiÉ—a kenan daga cikin plan b, harinmu na gaba shine Æ™ulla alaÆ™a da yarinyar nan, dan na san yanzu abinda zatai yinÆ™urin farawa shine bincike akan wanene shi”.
“Wai ya akai duk kake sanin hakan?”. Miran Arshaan ya tambaya cikin mamaki. Dariya Miran Jasim yayi sosai da faÉ—in, “Arshaan Akhi har yanzu kai É—in yaro ne. Waya gaya maka mai nema yana zaman jiran tsammani. Tashi yake da Æ™wanji da zuciya wajen samowa ai. Karka damu da inda na sani, kai dai kawai ka tabbatar littatafan nan da mukai magana kwanaki an kaisu books room an ajiye a daren yau, dan bana raba É—ayan biyu zuwa gobe zata iya bukatarsu”.
Cikin halin ko’in kula Miran Arshaan ya É—age kafaÉ—u da tabe baki, sai dai acan Æ™asan ransa dariya yake dan shima akwai nasa shirin akan hakan tun randa sukai maganar……

★★

Duk da fuskarsa mai tsananin É“oye sirrin zuciyace a yau É“acin ransa sai da ya bayyana. Huci kawai yake faman furzarwa a kai-akai. Dan daga É—akin meeting É—in nasu da ba’a samu damar tattauna abinda ya dace ba kai tsaye sama yay can Æ™arshen rufin ginin sashen nasa da aka gyara domin hutawa kawai. Ko gaisuwar hadiman dake tsare da Æ™ofar shiga wajen baiyi ba. Ya jima yana faman kai kawo hannayensa zube cikin aljihun farin wandonsa. Bakajin komai tattare da shi sai shaÆ™a da furzar da numfashi. Sai da ya É—an samu nutsuwar da yake bukata ya zaro waya dake cikin aljihunsa. Kira yay, bugu É—aya kuwa aka É—aga, batare daya amsa gaisuwar da ake masa ba a kausashe ya furta. “A sakaya min shi, inda babu wani mahaluki da zai taÉ“a hasashe a kansa”. Yana gama faÉ—a ya yanke kiran cikin sake tsuke fuska da zuÆ™a ya fesar…..

(Anya kuwa….?? bakina kanen kafa ta dai).

★★

A É“angaren Iffah tana tsaka da kai kawonta da Æ™ullawa da warwarewa itama wani tunani ya sata tsayawa cak. MiÆ™ewa tai cikin gamsuwa, sai kuma ta koma ta zauna bisa wani tunanin da yazo a bayan wanda ya sata mikewar. A kallo É—aya zaka fahimci tana cikin yanayin da duk wani É—an Æ™asar zaka iya ganin ya shiga sakamakon wannan baÆ™on al’amari daya shigo musu. Da farko bai lura da ita ba saboda idonsa rufe yake da É“acin rai har lokacin, sai da ya kai zaune yay Æ™oÆ™arin lumshe ido sai kuma ya buÉ—esu a kanta dai-dai itama ta kallesan mamakin yanayinsa na yanzun kuma fes a fuskarta. Ita ta fara janye nata shima sai ya furzar da huci mai zafi yana maida nasa ya lumshe kamar yanda yayi a farko.
Falon ya É—auka shiru babu alamar wani zai tanka sai karar na’urorin ac dana tv da har yanzu ake cigaba da nuna al’amarin da yanda hankulan jama’a ke tashe. Kiran sallar la’asar ne ya katse zaman shirun nasu. Iffah ta fara yunÆ™urawa ta tashi batare da ta ko sake kallonsa ba dan da gaske har cikin rai haushinsa takeji yau. Da kallon Æ™asan ido ya bita harta É“acema ganinsa. Ya É—an sauke É“oyayyar ajiyar zuciya da maida idanunsa ya rufe. Sai da Iffah tai kusan mintuna huÉ—u da barin wajen sannan ya mike shima har yanzu da alamar É“acin rai tattare da shi….

★★★….

Bayan Iffah ta idar da salla kamar yanda ta tsara tai shirinta tsaf cikin wata doguwar riga mai tsananin ɗaukar idon duk wanda zai iya kallonta. Kamshin data gaje batare da umarnin mai shi ba ta baza tamkar tayi ɓarinsa a jikinta. A cikin dukkanin shirinta babu bijirema umarnin waɗan da tazo wannan matakin a dalilinsu, dan haka kai tsaye tai kiran number Daneen Ammarah. Ana ɗagawa tai sallama cikin sauƙaƙa murya mai nuna ladabi. Daga can Daneen Ammarah ta amsa cike da zumuɗi da nuna jin daɗinta da wannan kira.
“Shahrbano ce da kanta haka?”.
Murmushi Iffah tai mai bayyana haÆ™ora jin sunan da Daneen Ammarah ta kirata da shi. Ta girgiza kai tamkar tana a gabanta. “Mamy zakisa a tsire ni a tsakkiyar daular ruman fa”.
Dariya sosai maganar ta bama Daneen Ammarah. Dan haka ta dara sosai kafin ta tsagaita. “Waya isa ya tsire Ibnati kuma Shahrbano duk faÉ—in Æ™asar ruman. Babu mai wannan power É—in Ibnati, ko maÆ™iya sun san kin gagara sai kallo daga nesa, dan kowa ya tabbatar a yanzu ke É—in ce _Lady of the city_”.
Komai Iffah bata iya tace ba, sai dai Daneen Ammarah na iya jiyo sautin murmushinta harta gama kwarzantata.
“Mamy dama na kiraki ne na shaida miki ina É—an son na fito zama waje É—ayan ya isheni, daga nan sai na É—an leÆ™ama É—akin karatu kozan samo abin É—ebe kewa”.
“Hakan kam yana da Æ™yau Ibnati. Dan haka ki shirya kawai, hadimanki na sashenki za’a sanar da su su tsumayi fitowarki”.
“Nagode Mamy, ALLAH ya Æ™ara miki lafiya da tsohon rai mai amfani da albarka”.
Cikin jin daÉ—i Daneen Ammarah ta amsa da Amin tana mai saka mata albarka itama.

A yau kam Iffah ta Æ™ara tabbatar da tsantsar Æ™arfin ikon mulkin wannan daula. Dan tunda ta baro hawa na Æ™arshe hadiman sashin na Shahan-shan ke faman zubewa gabanta batare da dubi da Æ™anÆ™antar shekarunta ba, matsayinta kawai suke kalla. Duk sai taji zuciyarta babu daÉ—i ganin kusan duk shekarunsu zai iya kaiwa dai-dai dana Hanash, wasu ma sun girme masa. (Nace Iffah danma Tajwar Eshaan yayi sauyi ne da matasa kikaga hakan, da har sa’an kaka da Babiy sai kin gani kuwa). Kamar yanda Daneen Ammarah ta faÉ—a tako samu hadiman na zaman jiranta. Ta gane hakanne ta hanyar zuwa da sukai suka zube a gabanta da sanar mata matsayinsu. Batare da damuwa ba duk ta bisu da kallo, su biyar ne cif kuma duk yara Æ´ammata matasa, za’a iya samun sa’aninta dama wanda suka girme mata kamar su Fariha.
“Ina buÆ™atar zuwa books room ne akwai wani tsari akan hakan?”.
Da sauri Æ´ar babbar dake ta gabanta sosai ta girgiza kai. “Ga Zawjata-almilk babu wani dokar yin hakan ALLAH ya Æ™ara miki lafiya”.
“Okay zamu iya tafiya”.
Iffah ta amsa mata kai tsaye. Hadima É—aya ce tai gaba sosai Iffah na biye da ita cikin takunta na nutsuwa da wasu kan iya gani su fassara da abinda zuciyarsu ta basu. Bayanta Hadimai huÉ—u na biye da ita cikin taka tsantsan da nuna girma da Æ™arfin ikonta a bayyane………..✍️

*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*

*DAUDAR GORA Billyn abdul*

*KI KULANI hafsat xoxo*

*A RUBUCE TAKE Huguma*

*RUMBUN K’AYA Hafsat rano*

*IDON NERA Mamuh ghee*

_LITTAFI DAYA: 400_
_LITTAFI BIYU: 600_
_LITTAFI UKU: 800_
_LITTAFI HUDU :1000_
_LITTAFI BIYAR: 1200_

_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_

_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_

_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_

_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_

_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_

_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_

ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN

MARYAM SANI
ACCESS BANK
0022419171

SAI A TURA SHAIDAR BIYAN

09033181070

IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA

09166221261

*ƳAN ƘASAR NIGER. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*

+227 96 09 67 63

Books biyar 1250CFA
Books hudu 1050CFA
Books uku 850CFA
Books biyu 650CFA
Bookk daya 450CFA

KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.

MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.

 

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*

✨ÆŠ ✨
( )

 

 

Post a Comment

0 Comments