Daudar Gora Book 1 Page 37

Latest Posts

6/recent/ticker-posts

Ad Space

Daudar Gora Book 1 Page 37


37_*

 

………Duk ta inda suka gitta kwarjininta dake É“oye shekarunta kansa a bata girma irin wanda ya dace ga Zawjata-almilk da suka isa a masarautar. Hadimai kam sai zubewa suke bisa gwiwunsu sakamakon sanarwar da É—an kazagin da Iffah bata farga da shi ba sai da suka fara tafiya taji shelanta tahowarta da yake yi. A yau kam ta Æ™ara jinjinama girman wannan katafariyar masarauta mai abubuwan kallo matuÆ™a. Sai dai ga mai kallo bazai taÉ“a fahimtar hakanba a yanda take faman basarwa kai kace ita É—in tun fil’azal jinin sarauta ce. Ba wani nisa bane zuwa books room É—in, hakan ya sakasu isowa cikin Æ™anÆ™anin lokaci dan ma tafiya ce ta Æ™asaita….

Cikin Æ™ankanin lokaci labarin fitowar Zawjata-almilk ya karaÉ—e masarautar. Hadimai Æ´an leÆ™en asiri dake watse ta ko’ina sun gama kai labari ga iyayen gidansu. Da yawa mamaki ya kamasu tare da gane lallai yarinyar tazo da tsageranci. Inba tsageranci ba wace Zawjata-almilk ce ta taÉ“a fitowa bayan kaita turakar Shahan-shan da kwana É—aya kacal. Wasu kuma kai tsaye fassara wannan fita suke da gatsali, acewarsu Iffah nason tabbatar musu tafi Æ™arfin iyawarsu, Æ™arfin ikon su kuma ba komai bane dan ta gagaresu.

★Malikat Bushirat kanta isowar wannan labari a kunenta sai da tai wani tsamm na nuna mamaki, sai dai bata ce uffan ba kasancewarta mace mai tsananin jin kai da izza. Tana son Iffah, kuma Æ™arfin halin yarinyar na kawatar da ita. Sai dai hakan ba yana nufin zata dama damawarta ne a yanda taso ba ko Æ™etare tsarin zama a masarautar musamman ga Zawjata-almilk irinta da Æ™a’ida komai sai da umarnin Malikat zatayi sa. (Kamar dai ita dake mahaifiya ga Tajwar Eshaan. A Æ™a’ida dole komi Iffah zatayi sai ta nema izinin mahaifiyarsa kafin ta aiwatar). Jin al’amarin ya cigaba da caccakar zuciyarta ta sallami duk hadimanta. Kamar Æ™iftawar ido suka É“ace kuwa. Rai a É“ace ta É—aga waya tai kiran Jasrah da ita bama tasan wainar da ake toyawa a masarautar ba kasancewar a É—an tsakanin nan tana fama da laulayin ciki ne sama-sama.
Duk da a halin rashin jin daÉ—i da take ciki bazata iya Æ™in amsa kiran Æ´ar uwar tata da takema kallon uwa a yanzu ba. Haka ta kimtsa cikin dauriya ta nufi sashen Malikat Bushirat É—in. A tsaye ta sameta cikin yanayin É“acin rai da ya kasa É“oyuwa a kan fuskarta. Sai duk taji itama nata ran a jagule…
“Akia kina lafiya kuwa? Miya É“ata miki rai haka har fuskarki ta kasa É“oye wa?”.
Malikat Bushirat ta zuÆ™a kakkaurar iska ta fesar tana mai kallon Æ´ar uwar tata. Cikin É—acin murya tace, “Yarinyar nan ce”.
“Yarinya kuma? Wace yarinya kenan?”.
Kamar bazata tanka ba, tai taku É—aya zuwa uku batare data dubi Jasrah ba tace, “Zawjata-almilk. Da alama tana buÆ™atar sai an saita mata zama da tuna mata nan daular ruman ce ba getto eria É—in data rayu ba. Komai muna yinsa da Æ™a’ida bisa umarnin na gaba”.
“Kiyi haÆ™uri Akia. Amma na kasa fahimtar miya kawo wannan maganar, wace kuma Zawjata-almilk ce a cikin yaran? Dan nasan dai kinfi kowa so da Æ™aunar wadda ke tare da shi a halin yanzu”.
“Ina sonta bashi zai bata lasisin shimfiÉ—a abinda ta gadama na a saman nawa Æ™arfin ikon ba. Yanzu labari ya iso gareni ta fito daga sashen Saiful-malik zuwa books room tare da hadimai”.
“Tofa, ita kuma da wannan tazo? Mu muna murnar samunta matsayin wadda zata share kukanmu amma zata fara da haka?. To amma fa Akia wani hanzari ba gudu ba. Shin baki ganin salon yarinyar a wani mahangar nasara ce a garemu. Na farko dai babu wanda yasan ta fito ne batare da umarninki ba. Na biyu koba komai ta sake jaddada isar da saÆ™onmu akan maÆ™iya. Na uku salonta tamkar barazana ce ga duk wani shu’umi dake rayuwa a wannan masarautar. Inaga bai kamata ki damu ba, dan a wani É“angaren ma kamar mune masu laifi, karki manta Mammah ta mikata sashen Abni batare da bin Æ™a’idojin da ake kai Zawjata-almilk turakarsa ba. Sannan inada tabbacin ba’a sanar da ita komai game da tsarin komai ba fa, sai aikin da muka faÉ—a mata zatayi a garemu”.
A hankali Malikat Bushirat ta saki wata nannauyar ajiyar zuciya. Cikin kwantar da murya ta ce, “Hakane kumafa Jasrah, kin tunatar da ni abinda ya É“acemin har idona ya rufe. Sai yanzu na fahimci lallai wannan fitar tata ma da alama tanada manufa akan umarnin aikinmu. Duk Mamma ce da wannan kwamacalar da muka kasa fahimtar manufarta a kai, nayi niyyar zuwa sashen nata ma naji dalili baÆ™in nan na É—azun suka cinyemin lokaci. Amma munyi magana da Ammarah zuwa anjima zanje ko cikin É“adda kama ne”.
“Hakan yayi, dan koni ina son sanin yaya akai hakan ta kasance. Duk da dai Alhamdullah yarinyar ta kuÉ“uta. Amma mun kwana a fargaba ai dan ko barci jiya banajin waninmu yayi wlhy. Hatta da Abu Harith kwana yay tunani”.
Murmushi Malikat Bushirat tayi, dan har cikin ranta tana Æ™aunar Æ™anin mijin nata kuma mijin Æ™anwarta, tare da yaba Æ™oÆ™arin sa akan kulawa da kaunar da yake nunawa ga gudan jinin nata tilo da har wasu ke jin zafinsa a gidan bisa hakan…..

★★….

Katafaren ɗakin daya kasance mai cika ido ga Iffah tsarinsa ya matuƙar ƙawatar da ita. Ta samu jagorancin shiga lungu da saƙo na cikinsa bisa taimakon masu kula da ɗakin. Inda a zagayen nasu suke nuna mata abubuwan tarihi na tun farkon ƙarnin kafa Daular ruman ɗin da suka shuɗe cike da girmamawa a gareta. Tafiya kam mabuɗin ilimice haƙƙun dan Iffah ta ilmantu da abinda yafi wanda ta sani ƙalilan a baya dangane da tarihin daular ta ruman da akan tsakura musu a darasin makarantu.
Shugaban masu kula da sashen ya matuÆ™ar nuna jin daÉ—insa da bata shawarwari kan tsarin zama mai nazarin tarihi data ambata dan abune daba kasafai ake ganinsa ga matan cikin masarautar ba. Akwai wadda ma bata taÉ“a taka Æ™afarta cikin É—akin litattafan ba. Amma ita gata Æ™aramar yarinya da rayuwarta ke kamar akan É—ar-É—ar abinda ta fara nuna sha’awa na farko akansa kenan. Shine ya fara zaÉ“a mata books daya ga ya dace ta fara dubawa, hakan yasa ta basar da waÉ—anda ta shigo nema kai tsaye, dan a ganinta bin shawarar tasa zaifi bata fiye da abinda take buÆ™ata É—in. Shugaban da shekaru sunyi matuÆ™ar ja a garesa yaji daÉ—in amsar shawarar tasa da tayi, dan yasan duk da zai iya haifarta matsayinta ya bata ikon yin duk yanda taso a sama da shi…

A cikin farin cikin daya goge duk wani damuwarta a wannan yini ta fito hadimanta na take mata baya É—auke da É—irka-É—irkan littafan da ta É—ebo. A yanzu É—in ma dai tako ina hadimai faman zubewa suke domin girmamawa a gareta harta isa sashenta data basu umarnin su kaita saÉ“anin sashen Shahan-shan daya kamata ace ta koma tunda a Æ™a’ida sati guda zatayi kamar yanda Malikat Haseena ta sanar da Tajwar Eshaan. Iffah kam da ba zama akai aka faÉ—a mata komai na Æ™a’idojin ba haka kawai taji bata bukatar komawa zaman takura da zuciyarta ta ayyana mata rashin amfaninsa. Shi dai wanda aka kaita dominsa ko kallo bata ishesa ba, hasalima baya kallonta da suffar da suka miÆ™ata garesan kai tsaye. Yo dole ta faÉ—i haka, tunda wane mijin Æ™warai ne zai jefama matarsa kalmar tambaya ta ita (wacece?) Bayan da saninsa aka kai sadakinsa domin aurota. Bazata iya É—aukar waÉ—an nan abubuwan ba, dan bama abinda ya kawota nan É—in ba kenan tun fil’azal. A ganinta kuma ba sai dole an kaita garesa an Æ™askantar da ita ba, zatabi hanyoyin daya dace na haÉ—uwa da shi har lokacin da zata cika É“oyayyen burinta….
Da wannan tunanin suka ƙarasa sabon sashen nata. Tabbas ta jinjinama ƙoƙarin su, dan ko makaho ya laluba yasan wannan sashen yayma wanda aka kaita fintinkau a komai duk da shima wancan ɗin dai ba baya bane a tsaruwar. Ta ɗan sauke numfashi da kaiwa zaune bisa ɗaya daga cikin lumbutsa-lumbutsan kujerun da aka shirya falon da su bakinta ɗauke da bismillah. Suma dai hadiman nata bayan sun ajiye litattafan a saman Centre table a gabanta suka zube. Taja tsahon mintuna goma tana mai nazarinsu kafin ta ɗan sauke numfashi da miƙewa.
“Ina buÆ™atar zama da duk wanda zai kasance da Ni a wannan sashen zuwa anjima”.
Cike da girmamawa duk suka amsa mata kawunansu a Æ™asa. Ta Æ™ara jan numfashi ta fesar batare data farga da salon izzar da yay kutse ga al’amarin ta na yanzu ba ta kai dubanta ga agogon falon. “Muna da sauran lokaci yanzu da zai ishemu zagaya sashen kafin na shige salla”.
Anan ma sun amsa mata É—inne da girmamawa. Batare da ta sake cewa komai ba tai gaba duk suka miÆ™e suna take mata baya. A yanzu ma dai wadda ta jagorancesu zuwa books room ce ke mata bayanin sashen da tsarinsa yanda ya kamata. Cike da gamsuwa batare data furta komai ba koda so É—aya take gyaÉ—a mata kai. Sashen ya Æ™unsa abubuwa masu yawa da zaman lissafinsa zai zama É“ata lokaci da cinye mana page, bayan sun kammala zaga ko’ina Iffah ta shiga bedroom É—in da zuciyarta tafi aminta da shi matsayin master bedroom É—in ta.
Mamaki ya kamata lokacin da taci karo da guntuwar takarda a saman duvet É—in saman gadon. _Ibnati wannan É—akin ki tabbar ya kasance É—akin sirrinki, shiyyasa nasa a shirya miji duk wani abu na buÆ™atar ki._ takardar ta É—an juya tana mai jan numfashi da fesarwa. Sai kuma ta saki murmushi dan ta fahimci saÆ™on na Daneen Ammarah ne. Wayarta ta É—auka a É—an gaggauce ta aika mata saÆ™o. Sannan ta nufi bayi gabatar da al’wala…….

*_★★SHAHAN-SHAN★★_*

Tun bayan faruwar komai daya shige É—aya daga cikin É—akunan barcinsa bai sake fitowa ba sai yanzu a cikin shirin zuwa Masallaci. Sau É—aya ya É—agama hadiman dake zube Æ™asa a dalilin fitowarsa hannu ya fice. Da kallon Æ™asan ido duk suka bisa, kowa da abinda zuciyarsa ke ayyana masa game da shi…

Bayan idar da sallar isha’i bai samu damar shigowa ba yay zaman ganawa da Aamin sa su biyu da suka buÆ™aci hakan. (Miran Jasim da Miran Arshaan). Miran Arshaan shi yafi jansa a jiki tun fil’azal, sannan kuma kamar yafi kusanci garesa ta bangarorin biyu kasancewarsa miji ga Khaalti (Aunt) É—insa da yake kallo tamkar yaya. Shima dai Miran Jasim É—in bai taÉ“a nuna masa wani abu mara kyau ba a zahirin rayuwa, a komai ma da zai taso yakan bada Æ™arfinsa wajen karesu ne ga kowa koda a fada ne. WaÉ—annan hallayya tasu ya sashi É—aukar yarda ya basu har yakan iya tattauna wasu abubuwa da suka shafi mulkinsa, sai dai abinda duk ya shafesa a karan kansa duk yanda zasu so sani baya taÉ“a basu fuskar hakan dan ko’a zahiri kowa na masa kallon mutum mai wuyar sha’ani, bahagon mai bauÉ—aÉ—É—en hali da zurfin ciki ne.
Bayan ficewar hadimin daya gama hidimar zuba shayi a gaban kowannensu ya fice Miran Jasim ya fara katse shirun dan yasan in zasu kwashe awa É—aya a wajen Tajwar Eshaan bazai sake tofa komai ba bayan gaisuwar da yay musu. “Abni nasan zakai mamakin wannan zaman namu, sai dai a dubi da abinda ya faru É—azun ba abin mamaki bane. Abinda ya faru É—azun ya matuÆ™ar Kona mana zuciya, dan bazamu taÉ“a so a aibantaka ba muna ji muna gani kodan amanar da Haysam Akhi ya barmana taka. Akwai wasu abubuwan da yawa daya kamata dama mu tattauna da kai kafin wannan É—in, amma a yanzu kamar wannan É—in ne importent”.
“Hakane Jasim Akhi”. Miran Arshaan ya karÉ“e fuskarsa na nuna tsantsar damuwa. Ya cigaba da faÉ—in, Abni lokaci yayi da nake ganin ya dace wasu a cikin iyayen nan namu dake zaman fadanci ya kamata su huta Æ´aÆ´ayensu su karÉ“esu. Duba da kai matashi ne, a koda yaushe ra’ayinka da hangenka zai cigaba da zama banbanci ne da nasun. Koda yake su a gare sun ma ba haka bane, dan haka mahaifinka yasha gwagwarmaya matuÆ™a da su a yayin nasa mulkin. Amma kai mi kake gani akan hakan?”.
Shiru babu alamar Tajwar Eshaan zai tanka, sai ma cigaba da kurÉ“ar shayinsa yake cike da Æ™asaita idanunsa akan television dake aiki a falon……….✍️

*AYYIRIRIRI AHAYYE CHAS sunan wata waƙa wai ita LUWAI*
_Ana tayi muna tayi manyan mata dai da gaske sun dage sai sun zama kalar gaban mota kalar camera tare da gudummawar Mg’s skin care Hajia ta kina ina ake ta wannan harkar arziÆ™in mata nata glowing suna faranta zuciyar mazajensu da laushi da santsin fatar su ke kina nan kina fama jiki duk kirci?_
Ah haba madam yunÆ™uro ayi tafiyar nan dake ki shiga ki wataya acikin shahararrun matan nan da ko’ina ake fatan gani dan an daÉ—e ana jin su watau *team glow by Mg’s*
Macen da ta isa itace mace karki bari ki zama cikin irin muna matan nan da suka rako mata duniya kuna tafe da mijinki yana kallon wata har miyau na zuba tsabar haÉ—uwarta da kyan fatarta
Mg’s skin care sune sirrin duk wata macen da ta isa a É—aga kai a kira da suna mace wacce ba’a jin kunyar shiga taro da ita daga nan har villah kizo/kuzo mu haÉ—e a wannan Æ™asaitacciyar tafiyar ta Mg’s skin care domin sune na gaban gaba sune suka ciri tuta indai a harkar gyaran skin ce hajiata kiyi wani fresh kiyi smooth wowkina tafe kina walwali idan fa kina amfani da *Mg’s skin care* ba kya buÆ™atar ko wanne irin mai product É—inmu katt ne duk matsalar fatarki muna da maganinta uhmm inata miki labari nace ba sister shin meye matsalarki ta gaban goshin Æ´allaÉ“ai?
Acne?, pimples? spot?, strech marks?, sunburn?.
to hutas bi’izinilLah muna da maganin matsalarki kina ganin mata a tiktok fuska luwai lumus kice dama ni ko? to in dai kina tare da *Mg’s* matsalarki tazo Æ™arshe bama cika baki gaskiya itace takenmu haka nan kuma siyen nagari mai da kuÉ—i gida *MG’s skin care gagarabadau*
Price É—inmu daidaitacce ne sannan kuma dai dai da aljihunku

*Soap price:4k*
maiso yy mgn
08062991549
07046881166
07067210195
Call 08064532391
Instagram:glow_with_mgs
Facebook: mg’s skincare

Masu bukatar cream Shima munadashi harda ma complete set nagyaranjiki
Small 12k
Medium 14k
Babba 20k

*BE PART OF THE GLOW TEAM KARKU BARI A BAKU LABARI*

*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*

*DAUDAR GORA Billyn abdul*

*KI KULANI hafsat xoxo*

*A RUBUCE TAKE Huguma*

*RUMBUN K’AYA Hafsat rano*

*IDON NERA Mamuh ghee*

_LITTAFI DAYA: 400_
_LITTAFI BIYU: 600_
_LITTAFI UKU: 800_
_LITTAFI HUDU :1000_
_LITTAFI BIYAR: 1200_

_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_

_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_

_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_

_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_

_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_

_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_

ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN

MARYAM SANI
ACCESS BANK
0022419171

SAI A TURA SHAIDAR BIYAN

09033181070

IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA

09166221261

*ƳAN ƘASAR NIGER. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*

+227 96 09 67 63

Books biyar 1250CFA
Books hudu 1050CFA
Books uku 850CFA
Books biyu 650CFA
Bookk daya 450CFA

KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.

MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.

 

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*

✨ÆŠ ✨
( )

 

Post a Comment

0 Comments