Daudar Gora Book 1 Page 39

Latest Posts

6/recent/ticker-posts

Ad Space

Daudar Gora Book 1 Page 39


39_*

……..A É“angaren Iffah kam bayan sallamar Hadimanta data Æ™udiri nutsuwa wajen fahimtarsu a tsanake itama ciki ta shige. Kamar yanda ta saba sai da ta gudanar da duk wani al’adan rayuwarta kafin barci. Ta haye sabon katafaren gadon nata bakinta da addu’a. Manya-manyan littafan dake jere a bideside drawer É—inta data kwaso a books room ta kalla cikin nazari har idonta ya sauka kan wanda ya kamata ta fara dubawa. Sai da taja lalausan bargon dake a saman gadon ta É—an rufe kafafunta zuwa cinya ta gyara zamanta da Æ™yau ta buÉ—e littafin da bismillah. A nutse kuma daki-daki ta fara nazartar littafin da Æ™oÆ™arin dinga fahimtarsa yanda ya kamata da irin fahimtar dai-dai nata tunanin.
Taja wani tsahon lokaci a nazartar littafin barci gwanin iya sata ya cigaba da rinjayar idanunta. Haka badan taso ba ta kife book É—in a gefen ta zame ta kwanta tana hamma. Da Æ™yar ta kammala haÉ—a addu’ar barci……

★★….. ★…..

“Uwa komai ya rikicemun wlhy, narasa ina zan kama. Ki taimakeni kar yaÆ™in dana sha a baya ya zama wahalar banza akan cikar burina”.
Ta-kurya ce mai maganar cikin tsananin tashin hankali da susucewa game da rashin mutuwar Iffah kamar na sauran matan baya”.
Uwa dake hakimce duk tana saurarenta ta nisa tana mai girgiza kanta da sake tsuke mummunar fuskarta. “Ƴar shilar nan bata isa ja dani ba Ta-kurya, kin Sanni kin san aikina kin kuma san mizan iyayi. Ya kamata ki nutsu tsaf akan bayanin danai miki tun a baya. Tabbas mutuwarta zata iya zame mana mai wahala a lokacin da muke buÆ™ata, shiyyasa naji takaicin suÉ“ucewar waccan damar da muka samu a farko. Gashi kema sakacinki yasa har zuwa yanzu kin gagara kawo mana rigar dake sashen mai Babban É—aki ko zamu iya kamo bakin wancan zaren dan zuwa yanzu na fahimci akwai masu irin manufarmu akan yarinyar kamar yanda na sanar miki. An kuma mana karan tsaye na kaita sashen Ajlaan ta hanyar Æ™in bin dokokin kaita turakarsa, kin san kuma mu munbi matakanne wajen É—ana tarko akan waÉ—an ca har mukai na sara, sun shammacemu sun kaita ne, sai dai abinda basu sani ba hakan bazai taba tseratar da itaba a tarkonmu na gaba da kuma mutuwarta”
“Uwa ba sakaci bane, a yanzu haka hadimar dana saka wannan aikin tana gab da kammala min shi. Ni yanzu tashin hankalina shine cikar lokacin kalmashe bakin zaren burina na biyu dake Æ™ara nisa. Har yanzu da buÆ™atar cikamakon aikin fa kafin na tsallaka na uku da shine cikar gaba É—ayan nasarata akan wannan yaÆ™in. Uwa ya kamata kiyi wani abu. Idan ita wannan yarinyar mutuwar tata bazai yuwu ba ta wannan silar inaga mu ajiye batunta gefe a haÉ—e wannan bakin zaren”.
“Kema kinzo da magana mai Æ™yau kam ta Æ™urya. Kuma inaganin ya kamata cikin Zawjata-almilk biyu da suka rage É—aya zata zama cikamakin ayyukanmu na biyu. Kinga sai mu haÉ—a aikinmu na uku dana Æ´ar shilar sudan can, amma duk da haka a kwana bakwai da zatai bazamu daina gwada sa’ar mu ba dai”.
“Haka shine dai-dai uwa mai share kukan masu kuka. Madubin rayuwar duk wani mai buÆ™atar kallon Æ™arshen Æ™yawun nasararsa.”
“Nasara takice Ta-kurya tunda har kina tare damu. Sai dai maganar yarinyar can dole ki haÉ—a da kirsa a yanzu kamar yanda kika saba wajen nasarar haÉ—a dukkan auren Ajlaan ta hanyar mai Babban É—aki a yanda kika so. Ki kusanta kanki da yarinyar itama sosai”.
“Indai wannan ne angama Uwa”.
“Na barki lafiya”.
Uwa ta faÉ—a tana mai É“acema ganinta a sannu-sannu harta daina ganinta. Ajiyar zuciya mai nauyi ta sauke ranta duk babu daÉ—i. Dan zuciyarta kam ta fara ayyana mata Æ™arfin ikon uwa ya fara sanyi. Dole ne ta nema sabon mai taimakonta duk da bazata taÉ“a mantawa da gudunmawar da uwa ta bata ba harta kawo wannan matsayin a wannan daula ta ruman da ayanzu take kamar mai juyata ta Æ™arÆ™ashin Æ™asa da zahiri a yanda take so. Amma ga karamar yarinya da bata wuce kiyashin da take murjewa a Æ™asan tsinin takalminta batare data sani ba tana neman zamewa rayuwarta wata Æ™adangaren bakin tulu a gabar cikar babban burinta na Æ™arshe……

★★★….. ★★…. ★….

A É—an firgice Iffah da kiran sallar asubahi ya farkar take kallon kanta da inda take a yanzu. Cikin shiga razani mai ban tsoro ta diro a gadon daya kasance saÉ“anin inda ta kwanta a daren na jiya. Kamar wadda ake ingizawa ta fice a É—akin cikin sassarfa. Tabbas sashen Tajwar Eshaan ne dai take. “Taya haka zata kasance?”. Ta faÉ—a cikin bugun zuciya. Sai kuma ta fara tunanin kodai mafarki take yine. Hannu takai ta É—an mari fuskarta. Sai dai babu abinda ya canja daga wanda idonta ke gane mata a yanzu. Dan lallai da gaske a sashen Shahan-shan É—in dai take.
“Ya ALLAH mike faruwa da ni ne haka wai. Taya zan kwanta a sashen da ba wannan ba na kuma buÉ—e ido na gannni? Jiya an É—aukeni daga Æ™asa an maida saman gado na share, amma shine yau kuma za’a É—akkoni daga wani sashe zuwa wani daban. Anya ba matsafan gidan nan ke son min wasa da hankali na ba?”.
Wannan tunani na karshe ya sata saurin kama rigarta ta shinshina. Tabbas irin dai Æ™amshin turaren jiya ne da karfinsa harya danne nata. “Ya Arrahaman” ta sake faÉ—a tana mai juyawa ta shiga kallon É—akin da sauri. A kan tarin kayan turarruka da idonta ya sauka a kai ta nufa, ta buÉ—e gilashin da suke ciki kamar dai nacan É—akin ta fara shinshinasu É—aya bayan É—aya. Sai dai abin mamaki babu wanda Æ™amshinsa yay kama da wanda takeji a jikinta. (Dole ne ma na gano, kuma ta wannan Æ™amshin insha ALLAH). Ta ayyana a zuciyarta cike da alwashin hakan. Alwala taje ta dauro jin makara na neman riskarta. Bayan ta idarne kuma ta sake nutsuwa wajen Æ™arema É—akin kallo yanda ya kamata. sai yanzu ma ta gane ba inda ta kwana a jiya bane wani ne daban. Sai dai shima wannan É—in ya matuÆ™ar haÉ—uwa fiye ma da wancan É—in. SaÉ“anin wancan da tsarin komai na cikinsa ke fari anan kuwa komai blue ne, ga wani Æ™amshi na fitina na tashi kamar dai wancan. Abu mafi ban mamaki nan É—in dai duk da ya nuna ana tsaftaceshi a hargitse yake kamar anyi dambe a cikinsa. Ita kanta dama a shigarsa toilet har mamakin yanda taga kanta a birkice tai, dan tasan dai tsaf ta kwanta kuma bata buge-buge a barcin. Son yin salla a kan lokaci ya sakata bata maida hankali ba sai yanzu data idar ta samu nutsuwa. Tayi tunanin gyara É—akin da fita binciken turaren nan na jikinta da alama ya tabbatar mata mai shi ke son wasa da tunaninta, sai dai wata zuciyarta ta bata shawarar ajiye waÉ—an nan batun ta sake kwanciya irin ta jiya tai likimo kozata samu bakin zaren ta hanyar shigowar wanda take zargin kamar jiya. Ta gamsu da hakan tako kwanta, sai dai tsahon kusan awa É—aya babu wani wanda ya zo É—akin, babu ma alamar wani É—in zai zo harta tashi akan dole ta kimtsa É—akin ta shiga wanka. Kayan data samu a lokacin gyaran É—akin ta sanya babu ko É—ar a ranta. Tayi Æ™yau sosai, ta kuma sake baza turarurrukansa a jikinta kamar jiya sannan ta fice a sannan kusan Æ™arfe bakwai da rabi…

Da Æ™yar yau ma ta iya gano É—akin data kwana a shekaran jiya, cikin Sa’a kuma ta samesa a buÉ—e. Shiga tai da sallama duk da bata zaton samun kowa a ciki. Tsaf yake kamar batai bidiri cikinsa ba jiya, an canja zanin gadon ga kamshi na tashi mai daÉ—i da sanyin ac. A yanda hadiman suka nuna sun É—an yi shock da ganinta ya É—an sakata a mamaki, amma sai ta dake babu alamar hakan gareta ta nufi É—aya daga cikin kujerun falon tai zaman Æ™asaita da ita kanta bata farga da yinsa. Hadiman da duk ganinta ya sakasu a firgici suka iso gabanta suka zube domin miÆ™a gaisuwa. Rayukansu kam cike da mamaki dan kowa dai yasan a jiya ba sashen ta kwana ba, tun fitar yamma da tai bata sake dawowa ba har suka rufe waje suka kwanta. Tun bayan idar da salla asuba kuma suka fito balle suce koda safen nan ta dawo.
A fisge ta amsa gaisuwarsu tana mai sauke manyan fararen idanunta akan Æ™yaÆ™yÆ™ywan tray É—in dake ajiye a table É—in gaban kujerar data zauna a jiya wadda koda ba’a faÉ—a mata matsayin kujerar ba tasan ta zaman Shahan-shan ce. ÆŠan juyiwa tai ta dubi hadiman da har sun fara miÆ™ewa. Ta jeho musu tambaya da faÉ—in,
“Wannan fa?”.
Cikin sauri mai sanye da kayan kuku ta amsa da “Shayi na farko da Shugaba ke sha bayan gama motsa jiki”…
“Kayan haÉ—in sa?”.
Ta tambaya a takaice. Nanma da tsumar jiki ta lissafa mata. Iffah ta yamutsa fuska da sake harÉ—e Æ™afafu. “A canja minsu da tatattun kayan itatuwa da ganyen koren shayi”.
Cikin tsoro duk suka dubeta, ta sake tsuke fuska da musu alamar gargaɗi da hannunta. Kamar ƙyaftawar ido kukun ta ɓace a wajen. Cikin abinda bai fi mintuna goma sha biyu ba aka dawo da wani sabon haɗin shayin. Miƙewa Iffah tai da nuna hanya alamar ta kaita inda yake. Anan ma ba karamin tsoro bane ya bayyana a idanun hadimar har ma da sauran ƴan uwanta, amma tsayayyun idanunta masu ƙarfi fiye da girman shekarunta ya hana hadimar iya furtawa a baki. Kai tsaye hanyar dake acan gefe ta nufa, sai dai suna zuwa ta dubi Iffah a mariraice sai kuma ta duƙar da kai.
“Tsahon rai da amincin UBANGIJI su zama kariya ga Zawjata-almilk, wlhy bani da hurumin tsallake wannan iyakar”.
(Kinyi mai wuyar) cewar Iffah a zuciya. A zahiri kam hannu ta miÆ™a ta amshi tray É—in batare da tace uffan ba. Cikin rawar jiki hadimar ta buÉ—e mata Æ™ofar gilashin dake a wajen, Iffah ta É—an tsirama steps na bene daya bayyana alamar shi zatabi kusan na sakan ashirin kafin ta maida ga hadimar da kanta ke duÆ™e, “Zaki iya komawa bakin aikinki”.
Kamar dama umarnin take jira, cike da sassarfa tabar wajen ƙwaƙwalwarta fal mamakin wannan baiwa har zufa na taruwa a goshinta.

★Ba karamin sake jinjinama al’amarin wannan masarauta Iffah tai ba, dan tana É—aura kafarta a step na farko na’ura ta fara shelanta kasancewarta a wajen. Abu mafi bata mamakin kalmar sunan da na’urar ta ambaceta da shi. Kafin ta sami damar wani waige-waige lifter data kwasota ta direta a wata Æ™ofar da hadimai biyu ke tsaye hannunsu riÆ™e da manyan bindugu. Tayi mamakin ganin yanda suka rissinar da kawuna sunka fara gaisheta. (Shin sun yarda da zancen na’urar ne? Kokuwa sun santa a matsayin Zawjata-almilk É—in ne dama?).
Da wannan tambayar da babu mai bata amsa ta cigaba da takawa a hankali kasancewar sun buÉ—e mata Æ™ofar wajen. Iska mai daÉ—i dake busawa ta sanyin safiya ta fara cin karo, ta zuÆ™a a hankali tana mai lumshe idanunta. Sai kuma ta buÉ—esu a sannu, a lokaci É—aya bugawar zuciya da tsinkewar jini suka nema sarÆ™e numfashinta, neman daburcewa take sakamakon abinda tai tozali da shi. Babu shiri ta maida idanunta ta rumtse tana mai ambaton sunan ALLAH akan wannan mummunan gani da tai. To mummunan gani mana, dan tunda take a rayuwarta bata taÉ“a tozali da namiji a irin wannan yanayin da idonta ya gane mata ba.. Ji take kawai ta zura da gudu ta koma, sai dai hadiman dake bayanta fa? Wane irin kallo zasu mata bayan na’ura ta gama fallasata a garesu. Tabbas nuna gazawarta na nufin faÉ—uwarta, faÉ—uwarta a matakin farko kuwa na nufin rushewar gaba É—aya nasararta.
Da karfi taja numfashi mai kauri ta haÉ—iye, kamar zatai kuka ta sake buÉ—e idanun a hankali, sai dai koda wasa bata yarda ta kalla gaban nata ba…..

Shigar ƙamshin turarensa da bayan shi babu wani mai irinsa da sautin takun takalman ƙafarta ya sashi juya sharɓeɓen takobin dake a hanunsa cike da gwanancewa ya karci ƙasa ya gocema Aamin nasa da suke wasan tare ya juyashi zuwa hannunsa na haggu saɓanin na dama sai gashi akan wuyan Iffah da numfashinta yay wata irin mummunan fisga.
“Who are yo…..?”.
Yay yunÆ™urin faÉ—a cikin alamun bayyanar fushi mai haÉ—i da isa da Æ™asaita, sai dai kalmar ta gagara Æ™arasa fita a harshen nasa dalilin tozali da abinda bashi yay tsammanin gani ba. Tar-tar fuskokinsu suka bayyana akan takobin mai matuÆ™ar Æ™yalli da sheÆ™i da kai tsaye za’a iya kiranta faÉ—ama jini na wuce……..✍️

*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*

*DAUDAR GORA Billyn abdul*

*KI KULANI hafsat xoxo*

*A RUBUCE TAKE Huguma*

*RUMBUN K’AYA Hafsat rano*

*IDON NERA Mamuh ghee*

_LITTAFI DAYA: 400_
_LITTAFI BIYU: 600_
_LITTAFI UKU: 800_
_LITTAFI HUDU :1000_
_LITTAFI BIYAR: 1200_

_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_

_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_

_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_

_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_

_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_

_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_

ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN

MARYAM SANI
ACCESS BANK
0022419171

SAI A TURA SHAIDAR BIYAN

09033181070

IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA

09166221261

*ƳAN ƘASAR NIGER. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*

+227 96 09 67 63

Books biyar 1250CFA
Books hudu 1050CFA
Books uku 850CFA
Books biyu 650CFA
Bookk daya 450CFA

KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.

MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.

 

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*

✨ÆŠ ✨
( )

 

 

Post a Comment

0 Comments