Daudar Gora Book 1 Page 4

Latest Posts

6/recent/ticker-posts

Ad Space

Daudar Gora Book 1 Page 4


_3_*

_____________

_*MAAB LUXURY HOME!!* Sabuwar duniyar hamshakan mata da Æ´aÆ´an gata._

_*GIDAN* ƙawa da ƙawata gidajen da suka cika gida._

_*SABUWAR DUNIYAR* Amare da uwargidan data amsa sunanta Æ´ar gaban goshi._

_*MAAB LUXURY HOME* wata duniya ce ta ƙawa da ƙawata gidajenmu da kayan ƙyale-kyale na burgewa da ɗaukar hankalin duk wani mai kallo_.

_*SUNYI FICE* Fice irin na É—aya a cikin tsara, sune na farkon fari, a farin da za’a kira fari a kowace irin duniya._

_*A GAREMU* ba sitturu na alfarma da kawa ne kawai ke tabbatar da mu hamshakai ba. Sai mun haÉ—a da Æ™awata gidajenmu da kayan MAAB LUXURY HOME zamu kasance cikakkun Æ´an gata ababen kallo da nunawa sa’a koda a cikin dubun da sukafi dubu._

_*MAAB LUXURY HOME* sun takaita mana dukkan wahalar nema ko order a kasashen ketare ta hanyar wadatamu da galla-gallan kayayyakin adon gidajenmu_

_*MAAB LUXURY HOME.* Duniyar kayan Kitchen da decoration din gida na keta raini._

_*INA UWARGIDA INA AMARYA!!?* Ku ziyarci shagon mu dake No 22 Ahmadu Bello Way, Kano state. Ko kuyi order daga shafin mu na Instagram @maabluxuryhome. Ko Facebook @maabluxuryhome. Ko Ku nememu a lambar waya *08034631010*._

*_Mai azama shi za’a kira dana farkon fari. Bara nai sauri nawa suzo hannuna kafin a kwashe⛹‍♀️⛹‍♀️⛹‍♀️._*

______________

………A wannan gaÉ“ar haukane kawai ya rage wannan ahali suyi, dan duk dauriyar Babiy ya kasa danne raÉ—aÉ—i da zafin da yakeji. Itako Iffah kalaman dake fita a bakinta kausasa sun saka kowa ke É—aukar tama zare kawai. Daga Æ™arshe maganin barci aka É—ura mata. Bata tashi farkawa ba sai a Æ™auyen da kakanninsu ke rayuwa. Wato iyayen Ummu. Rayuwa a Æ™auyen Jumna a gareta tamkar mai gushewar hankali ya zame mata. Domin bata gane komai sai sambatu da kalamun É—aura É—ammarar É—aukar fansa ga duk ahalin Daular Ruman. Ba Æ™aramin dagewa da jajircewa kakannisu da su Babiy sukai ba a kanta wajen ganin ta samu lafiya ta dawo hayyacinta. A cikin watanni takwas ta rasa yayunta guda biyu, wannan babban tarihine da bazai gogu a zuciya da ruhinta ba har karshen rayuwarta. Bayan jiyyar watanni kusan uku ta dawo hayyacinta. Sai dai ta daina fira’a da kowa, an daina ganin dariyarta ko farin cikinta. Babu abinda ke’a ranta sai buri da Æ™udirin É—aukar fansa. Tama kanta alÆ™awarin ita da hannunta zata kashe *_Tajwar Eshaan ibn Haysam Abdull-majeed_*. Bayan nan idan itama an kasheta burinta ya cika na kawar da azzalumin sarki mai mulki irin na fir’auna a Æ™asarta a cikin al’ummarta….

*_(Babbar magana. Tayaya wannan buri naki zai cika Iffah? Sarki mai cikakken iko irin Tajwar Eshaan, mai amsa sunan Shahan-shan da ko fuskarsa babu wanda ya iya sani a cikin kasar Ruman har yanzun. Anya kuwa….? To mudaije zuwa wai mahaukaci ya sai kura)_*

 

★★★

“Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un” bakinta ke ambata cikin firgici da rawar jiki sakamakon farkawar da tayi daga mummunan mafarkin daya risketa a cikin barcinta. Ta dafe kanta dake wata irin sarawa na ciwo tamkar ana mata luguden taÉ“aren daka a tsakkiyarsa, gaba É—aya jikinta ya jiÆ™e da zufa tamkar tayi wanka. Kusan watanni biyar kafin mutuwar Æ´an uwanta da fara canjawar salon mafarkainta saÉ“anin na baya, abu mafi tsoratarwa kuma kusan mafarki É—aya ne ke maimaita kansa a kowane barcinta idan ta kwanta. Sai dai mafi tashin hankalin a yau yayi kamanceceniya da na wasu dare da tarihi bazai taÉ“a mantawa da shi ba a cikin rayuwarsu ita da ahalinta.
“Nina Arfa! Nina Fariha!”.
Ta ambata a zahiri zuciyata na Æ™ara Æ™arfin gudu, yayinda hawaye suka shiga rige-rigen sauka a kumatunta. Tabbas irin wannan mafarkin tayi a daren da suka rasa Arfa, hakama daren mutuwar fariha. Yau kuma gashi ta maimaitashi akan kanta. Itama kenan zasu rasata?. Kai ta shiga girgizawa wani kuka masu Æ™arfi na sake tahomata, hannu tasa ta toshe bakinta gudun kar sautinsa ya kai ga kunnen kakanninta. Sai dai aikin gama ya gama. Dan kuwa muryar kakanta takeji jikin Æ™ofar É—akin nata a hankali yana ambatar sunanta. Da sauri ta shiga goge hawayen, kafin ta tashi daga shimfiÉ—ar barcin nata wadda karan gado ne da katifar rimi. Mayafi ta É—auka ta yanama jikinta, ta Æ™arasa ga Æ™ofar ta buÉ—e…
“Kina lafiya kuwa É—iyar nan?”.
Ya faɗa cikin kafeta da idanu. Kanta dake rissine ta jinjina masa, cikin son danne kukan dake yunƙuromata ta bashi amsa.
“Ina lafiya Kaka”.
Jin shiru bai sake cewa komai ba ta É—ago ta dubesa a karon farko. Shima dai kallon nata yakeyi tamkar mai nazari. Sake maida idonta tai Æ™asa, hawayen da take faman riÆ™ewa suka É“alle mata da gudu. Bata san ta ambaci “Kaka nima zasu kashe muku ni ko?. Inaji a jikina nima zaku iya rasani nan kusa tamkar yanda muka rasa su Nina Arfa”. Rawar da jikinta ta fara ta sata zubewa a gabansa kuka na Æ™wace mata. Kusan minti biyu baice da ita komai ba, ita kuma ta kasa tsaida kukan.. Jin saukar hanunsa saman kafaÉ—arta ya sata haÉ—iye kukan, ya É—agota tsaye yana É—an murmushi dake sake bayyana tsufansa. Gefen mayafin jikinta ya kama ya shiga goge mata hawayen. “Fareedatu! Ki kwantar da hankalinki, insha ALLAHU babu abinda zai faru da ke, mafarki ai ba gaskiya bane ba. Suma su Arfa kwanansu ne ya Æ™are, koba komai kuma sun rasu a gidan aurensu. Wannan kawai ya ishemu farin ciki”.
Kanta ta jinjina masa tana sauke ajiyar zuciya a jajjere. Ya cigaba da shafa kanta a hankali har zuwa wani É—an lokaci. “Kije kiyi addu’a ki kwanta abinki da safe zamuyi magana”.
A hankali tace, “Kaka ina son zuwa naga su Ummu gobe to dan ALLAH”.
Da sauri ya girgizamata kansa. “A’a bazai yuwu ba Iffah, iyayenki sun kawoki nan ne domin kuÉ“utar dake, taya kike tunanin zan barki komawa cikin daular Ruman?. Tun ina Æ™anÆ™anin yaro nake bauta wa masarautar Ruman, bayan mutuwar mahaifina na cigaba da bautar saÆ™a kayan doki a garesu kamar yanda mahaifina ya barmin gado, a haka na haifi Æ™anin mahaifiyarku shima ya mayeni, gashi har girma ya riskesa shima yana bauta musu. Mun rasa É—an uwan mahaifiyarku a yaÆ™in kare daular Ruman, mun rasa Arfa, da Fariha. Ke É—aya da kika rage mana da yayanki wajen mahaifiyarku kuma sai muyi wasa da rayuwarki? Bazai yuwuba jeki kwanta…”
Batare daya sake bata damar yin magana ba ya juya ya koma bayan ya jamata murfin kofar. Da kallo kawai ta bisa hawaye na silalo mata. Duk yanda taso komawa barcin bayan tafiyarsa hakan ya gagara, zuciyarta ta kasa fita da ga Æ™angin fargaba, da gaske tanajin matuÆ™ar tsoro bayan rasa Fariha da Arfa da sukai watanni Æ™alilan da suka shuÉ—e itama su rasata, tanaji zuciyar ahalinta bazata iya É—auka ba idan itama suka rasatan. Wasu zafafan hawaye suka sake silalo mata masu raÉ—aÉ—i da saka Æ™una a Æ™irji……

★★★

“Iffah! Iffah!!…..”
Sautin Æ™wala kiran sunanta daga muryar kakarsu da suke kira Iyyani ya sakata fitowa daga banÉ—aki data zagaya domin yin fitsari. Turus ta tsaya tare da haÉ—iye maganar da zatayi tana mai kallon É—an-uwanta Hanash dake zaune gefen kakar tasu a Æ™arÆ™ashin bishiyar É—oruwa da take a tsakar gidan. Murmushin da yakemata ta maida masa, kafin ta ajiye butar hannunta ta Æ™arasa garesa. Dab da shi ta zauna tana mai É—an rungumesa ta gefe da faÉ—in, “Ina kewarku Akhi”.
Murmushinsa ya sake faÉ—aÉ—a yana mai kallon fuskarta. Ya kai hannu ya shafi yalwataccen gashin kanta da mayafin ya zame mai tsaho da santsi. “Muma muna kewarki Little angel. Gidan duk ya sake zama mana babu daÉ—i”.
Yanda maganar tasa ta ƙare cikin rauni itama sai idonta ya cika da ƙwalla. Amma sai ta dannesu da murmushin mai ɗaci tana kaɗa kanta kawai.
“Tashi ki bashi ruwa mana, k haka ake tarbar baÆ™o a garinku”.
Baki ta É—an tura gaba da kallon Iyyani mai maganar, tayi hakane danta katse raunin data hanga a fuskokinsu. Ta miÆ™e tana bata amsa cike da shagwaÉ“a. “Iyyani laifinkine fa, ban taÉ“a ganin matar da bata tattalin mai gida ba irinki, dole Yayana ya miki kishiya”.
DaÆ™uwa tamata cikin gatsina fuska. “Ungo naki nan Fareedah, yo bandama lalacewa mizanyi da wannan faratun mai kama da jar tsada tuzurin banza”.
Hanash ya tsuke fuska yana kallon Iyyani. Murmushi Iffah tayi tun kafin ya faÉ—i abinda ke bakinsa. Dan dama inhar suka haÉ—u da Iyyani sai ta hasalashi take jin daÉ—i shi da Arfa akan Æ™inyin aure, duk da bawani shekarune da shi ba, dan ashirin da shida ne kawai, Arfa nada ashirin da uku, Fariha nada ashirin da É—aya. Iffah nada goma sha takwas….
Iffah ta dire masa abinci da ruwa ta sake kaiwa zaune kusa da shi sannan ta dubesa. “Akhi yasu Babiy suke?”.
Ya nisa a hankali bayan ya dire moÉ—ar ruwan daya sha. “Duka lafiya suke. Suna gaisheki ke da su kaka. Duk da suma dai nan da kwana kusa zamu ma dawo nan É—in muma. Yanzu haka nazo duba can tsohon gidanmu ne dan asan gyaran da za’ai masa”.
Sosai ta kafesa da ido ita da Iyyani. Kafin cikin Æ™arfin hali Iffah tai magana. “Amma Yaya su Babiy basa ganin rayuwa zata mana wahala anan sakamakon bamu sababa sam. Sannan ayyukansu dake acan miye makomarsu? Da karatunmu muma?. Abinda ya faru ya riga ya faru, tunda hannayenmu bazasu iya maidosu ba, mi zaisa zukatanmu bazasu cigaba da haÆ™uri ba. Barowarmu cikin Daular ruman tamkar munji tsorone, ko sake sakin rayuwarmu a hanun waÉ—anda kansu kawai suka sani…….”
“Tsoro halak ne Iffah. Bama muba mafi yawan masu yara mata sunata barin daular ruman a yanzu domin tseratar da Æ´aÆ´ansu daga auren jeka nayika. Karatun Æ´ammata yana neman tsayawa cak, kowace na tsoron fitowa ta zama nama a hanun hadiman daular ruman. a yanda lissafin yake a yanzu an rasa mata goma sha huÉ—u fa, a tunaninki kafin Æ™arewar wannan shekarar ba’a rasa fin hakaba duk da bawai ya cigaba da auren bane.”
Wasu hawayene masu É—aci da Æ™una suka silalo ma Iffah, tai saurin saka gefen mayafinta ta share tana murmushin takaici. “Niko a ganina gudu bashine mafita ba, muryoyinmu ya kama mu É—aga wa duniya kowa yasan halin da muke ciki, idan har a Æ™asar Ruman babu wani sama da nasa mulkin ai a sauran Æ™asashen duniya akwai wanda suka fisa…”
“Humm Iffah ke yarinya ce har yanzu.”
“Sosai kuwa Hanash. Shiyyasa bata gane komai sai abinda yanzu take zuwa da shi”.
“Humm Iyyani kenan”.
Iffah ta faÉ—a a yanayin jin raÉ—aÉ—i a maÆ™oshinta. Su duka kallonta sukai, sai dai ta É—auke kanta gefe tamkar bata gansu ba. Daga haka babu wanda ya sake cewa komai har tsahon wani lokaci. Iyyani ce ta canja hirar da wani abu daban har Hanash ya kammala. Tare da shi suka fita wajen duba tsohon gidan da kakaninsu da suka haifi Babiy ne suka rayu a ciki, dan sudai tunda suka taso a cikin birinin daular ruman suka san kansu duk da a É—an gefen gari suke acan É—in ma. Sai dai su shigo cikin Æ™auyen Jumna a matsayin duba kakannin nasu. zuwa yanzu su duk sun rasu, shiyyasa gidan ya kasance babu kowa. Duk ma ya rusa ya fita hayyacinsa dan ginine na jar laka tamkar yanda duka gidajen Æ™auyen suke. Sun É—an jima acan suka dawo, sun iske kaka ya dawo shima daga fitar da yay tun ta safe gona É—ebo sassaÆ™e-sassaÆ™en magunguna. Ƙara zaman tattaunawa sukayi iya su uku, ita dai Iffah bata cewa komai. Daga Æ™arshe ma tashi tai ta shige É—akin kwananta. Bata sake fitowa ba sai da kaka ya neme ta. SassaÆ™e-SassaÆ™en magungunan daya É—ibo É—azun ne a gabansa, kowanne ya É—auresa daban-daban. Ya turamata babban robar da suke ciki… “Zaki fara amfani da su Iffah, bana son kiyi wasa dan ALLAH. WaÉ—annan kuma hayaÆ™ine, a kowacce duhun magriba ki tabbatar kinyi turarensu, wannan kuma a ruwan wanka ne, da kin idar da sallar asuba ki zubasu cikin ruwa kaÉ—an ki cire kayanki ki tabbatar duk jikinki ya samu”.
“Tofa kaka wannan É—in kuma duk na miye?”. Iffah ta tambaya cikin nuna mamaki.
Idanu ya tsiramata na kusan mintuna uku tamkar mai nazari, sai kuma ya É—auke kansa da wani yanayi mai wahalar fassara. “Faruwar Æ™addararmu bashi ke nuna baza’a sake jarabtarmu ba. Idan jiya ta shuÉ—e da É—aci zata iya yuwuwa yau É—inmu da dariya zata kasance, sai dai sanin mike a gobenmu al’amarine mai girman gaske, damin gaibunmu ce ita ALLAH ne kaÉ—ai masanin mi zaizo.”
Kallon juna sukai ita da Hanash, Iffah ta É—an É—age kafaÉ—a cikin yanayin ban fahinta ba, shima sai ya kaÉ—amata idanu alamar shima hakan take. Atare suka maida dubansu ga kaka. Amma sai ya kauda kansa alamar baya buÆ™atar kowacce irin tambaya daga garesu. Iffah ta jinjina kai kawai alamar ko’oho. Sai kuma ta miÆ™e tana mai faÉ—in, “Ni dama fa na yanke shawarar zanbi Akhi mu koma. Tunda dai naji sauÆ™i gara naje na koma makaranta anata wuceni a darasi”.
Ba karamin waro idanu Hanash yay ba, zaiyi magana kaka ya dakatar da shi ta hanyar yin murmushi da kaÉ—a kansa. “Ita rayuwa rubutacciya ce tunkan halitta, an rubutatane da alÆ™alamin da ba’a goge rubutunsa, babu wani hannu daya isa gogeta koda da Æ™arfin iko. Dole ne sai anyi hakan, ko muna so ko bama so mashin nan sai ya isa inda aka aikashi. Domin ita *KIBIYAR AJALI! SULKE BAYA TARETA SAI TA GITTA*”.
A rikice Hanash ya tari numfashinsa. “Kaka bana gane dunÆ™ulallun zantukan nan naka, ka fito fili dan ALLAH ka sanar mana mi kake son faÉ—a…”
“Hanash! Lokacin faÉ—ar baiyiba ai, nima kurman baÆ™in kawai na gani, fassarar sai UBANGIJI”.
Sosai Hanash ya sake tsare fuskar kaka da idanu, kamar yanda itama Iffah tai tsai tana kallon nasa. Su dukansu sun jima da sanin kaka mutum ne hatsabibi, dan kuwa mahaifinsa gawurtaccen masanine da azamaninsa akan kallesa tamkar matsafi ko wani mai gani har hanji, sai dai kasancewar bai ajiye buzu ya zauna akan iya wannan al’amarin ba yasa ake shakkar faÉ—a, yana bada taimako na magani akan abubuwa daban-daban musamman harkar aljanu komai Æ™arfinsu da shaiÉ—ancinsu. Sannan yana sana’arsa ta saÆ™a kayan kwalliyar doki. Kaka ya gaji abubuwa da dama a garesa, sai dai shi ya watsar da harkar bada maganin dan shima dai a karan kansa yana ta’allaÆ™a sanin mahaifin nasa da bokancin, duk da dai bai fito fili ya bayyana hakan ba kuwa, amma rashin maida hankali akan abinda ya shafi hakan zaisa ka zargi ko haka É—inne. Akwai kayan aiki na mahaifinsa da yawa a killace a wani waje da shi kaÉ—ai ya sani, kuma tun bayan mutuwarsa shi ya tattare su ya killace su…………✍

*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*

*DAUDAR GORA Billyn abdul*

*KI KULANI hafsat xoxo*

*A RUBUCE TAKE Huguma*

*RUMBUN K’AYA Hafsat rano*

*IDON NERA Mamuh ghee*

_LITTAFI DAYA: 400_
_LITTAFI BIYU: 600_
_LITTAFI UKU: 800_
_LITTAFI HUDU :1000_
_LITTAFI BIYAR: 1200_

_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_

_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_

_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_

_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_

_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_

_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_

ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN

MARYAM SANI
ACCESS BANK
0022419171

SAI A TURA SHAIDAR BIYAN

09033181070

IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA

09166221261

*ƳAN ƘASAR NIGER. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*

+22799643131

Books biyar 1250CFA
Books hudu 1050CFA
Books uku 850CFA
Books biyu 650CFA
Bookk daya 450CFA

KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.

MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.

 

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*

✨ÆŠ ✨
( )

 

*_4_*

_______________

_*MAAB LUXURY HOME!!* Sabuwar duniyar hamshakan mata da Æ´aÆ´an gata._

_*GIDAN* ƙawa da ƙawata gidajen da suka cika gida._

_*SABUWAR DUNIYAR* Amare da uwargidan data amsa sunanta Æ´ar gaban goshi._

_*MAAB LUXURY HOME* wata duniya ce ta ƙawa da ƙawata gidajenmu da kayan ƙyale-kyale na burgewa da ɗaukar hankalin duk wani mai kallo_.

_*SUNYI FICE* Fice irin na É—aya a cikin tsara, sune na farkon fari, a farin da za’a kira fari a kowace irin duniya._

_*A GAREMU* ba sitturu na alfarma da kawa ne kawai ke tabbatar da mu hamshakai ba. Sai mun haÉ—a da Æ™awata gidajenmu da kayan MAAB LUXURY HOME zamu kasance cikakkun Æ´an gata ababen kallo da nunawa sa’a koda a cikin dubun da sukafi dubu._

_*MAAB LUXURY HOME* sun takaita mana dukkan wahalar nema ko order a kasashen ketare ta hanyar wadatamu da galla-gallan kayayyakin adon gidajenmu_

_*MAAB LUXURY HOME.* Duniyar kayan Kitchen da decoration din gida na keta raini._

_*INA UWARGIDA INA AMARYA!!?* Ku ziyarci shagon mu dake No 22 Ahmadu Bello Way, Kano state. Ko kuyi order daga shafin mu na Instagram @maabluxuryhome. Ko Facebook @maabluxuryhome. Ko Ku nememu a lambar waya *08034631010*._

*_Mai azama shi za’a kira dana farkon fari. Bara nai sauri nawa suzo hannuna kafin a kwashe⛹‍♀️⛹‍♀️⛹‍♀️._*

________________

………Iffah tayi mamaki da kaka ya bari salin alin tabi Hanash washe gari, duk da Iyyani taso borewa ita. Amma wasu lafuza daga cuÉ—aÉ—É—un kalamansa ya sata yin shiru ta bisu da addu’a. Kaka yayma Iffah gargaÉ—i matuÆ™a akan abubuwan daya bata, ya kuma tabbatar mata ko guda É—aya taÆ™iyi zaiji hakan a jikinsa.
A hankali ta murza awarwarayen hannunta da shine ya sakamata, ta sake lumshe idanunta da sakin ajiyar zuciya. Haka kawai takejin awarwarayen da girma da kuma banbanci da irin wanda take sakawa a baya domin kwalliya, ko miye dalili oho.

Daga Ummu har Babiy a tsorace suke kallon Iffah da Hanash da suka shigo. Hanash ya girgiza musu kansa cikin sauri yana faÉ—in, “Wlhy ba laifina bane Babiy. Itace ta bore akan saita biyoni, kaka kuma ya bata goyon baya. Dan a cewarsa _(Babu wani nisa dake bada tazarar gujema Æ™addara. A wani ajin jarabawar data biyoka ma gara kai ka tunkareta. Dan ba kowane kogo bane ke zama kogo ga ma’abocin gudun ceton rai)._ Babiy na kasa fassarawa, akoda yaushe cirkuÉ—aÉ—É—un kalamai daga bakin Kaka masu tsaurine da wahalar fahimta. Dan ALLAH idan kun sani ku fassara mana”.
Maimakon amsa daga Babiy baya sukaga yayi tamkar zai faÉ—i, sai dai cikin sa’a ya dafe gini tare da dafe kansa alamar hajijiya. Ummu ma Æ™asa takai zaune jikinta na rawa, hakan sai ya Æ™ara firgitasu. Da sauri duk sukai kansu suna mai tambayarsu suna lafiya kuwa?. Da kai kawai suka amsa musu, Babiy harda Æ™oÆ™arin Æ™aÆ™aro murmushi. Cikin son kwantar musu da hankali yake kallonsu. “Kunga karku sakama zukatanku wata damuwa, ba maganar Baba bace ba, kawai dai bana jin daÉ—ine kwana biyun nan dama”.
Jimm sukai alamar tunani, sai dai kuma babu damar yin musu ko ƙin aminta da cewar tasa. Hanash ya taimaka masa suka koma cikin runfa, Iffah kuma tana riƙe da Ummu..

★★★

Washe gari batare da sun sani ba Babiy yay sammakon yin tafiya zuwa Æ™auyen Jumna. Ya samu tarba daga surukan nasa ko ta girmamawa….

Ƙyaƙyƙyawan tsohon da Tattarowar fatarsa ta tsufa bai hana bayyanar ƙyawun cikar halittarsa ba ya sake kallon dattijon gabansa a karo na babu adadadi. Murmushi ya saki a karon farko, cikin karyar da kai da ƙanƙan da idanu ya kai hannu bisa kafaɗar dattijon. Numfashi yaja kakkaura da juyowa alamar dawowa hayyaci. Ya maida kansa ƙasa ya sunkiyar saboda girmamawa ta surukuta dake a tsakaninsu na tsahon shekaru.
“Humm Muhammadu Zayyanu!”.
Tsohon ya kira sunan tamkar mai sake bita a ranar da aka raÉ—a ga mai shi. ÆŠago idanu ya sakeyi a karo na biyu sai kuma ya risinar tare da amsawa da “Na’am Baba”.
“Tun isowarka magana nake gani shimfiÉ—e a fuskarka amma bakinka ya kasa furtawa, ko wani abu ya sami Hanash da Æ´ar uwarsa ne a hanyarsu ta komawa gida jiya?”.
“A’a baba ko É—aya, lafiya lau sukaje cikin Æ™oshin lafiya kuma, sai dai…..”
Sai kuma yay shiru ya kasa Æ™arasawa. Kaka dake kallonsa yay É—an murmushi, “Sai dai baku so komawar Iffah ba ko?”.
“Hakane baba. Domin kuwa babu abinda ya canja a daular Ruman, muna jin tsoron rasata itama kamar Æ´an uwanta, duk da bamu da tabbacin zasu sake waiwayrnmu, sai dai kalamanka sun sakamu a ruÉ—ani har muka kasa rumtse idanu a daren jiya domin yin barc……”
“Hana ido barci bashi ke nufin damar iya sauya abinda bakai ka rubuta ba. Muhammadu Zayyanu! Da ace Æ™addararmu a hannayenmu take da kaf mutane bazasu zana zaman duniya ba a littafinsu musamman idan sun san koda daÉ—in busawar iskar dake cikin aljanna ce. Karka damu kanka da sanin sirrin cikin dutsen da ko’a kallo abin firgitarwa ne. Mumini yakan kasance mai azumtar yini daga UBANGIJI, ya kuma sallaci duhun dare daga UBANGIJI domin yaye damuwa ko samuwar nutsuwa a duniyarsa. Gaibu daga ALLAH take, zahirin da yaso mu sani kawai yake iya nuna mana ta isharar rayuwa ko canjawar tunanin zuciyo
yi”.
Nannauyan numfashi yaja ya fesar tare da jinjina kai, bawai kwanciyar hankalin da yazo nema ya samu ba, sai dai rashin zaÉ“i ko bakin zaren kamawa ya sashi fahimtar tsohon na masa nuni da shiru ne kawai a zubama sarautar ALLAH ido dan shine kawai gagara misali…..

_________________

★Kwanaki biyu kenan da dawowar Iffah gida, inda dawowar tata ta zame mata tamkar wani famin ciwo a jikinta. Dan a kullum takanyi hawaye sama da sau babu adadi akan rashin Æ´an uwanta guda biyu. Komai ta kalla nasu yakan dawo mata da jiyansune mai cike da farin ciki da babu tunanin yankewa. Duk halin da take a ciki Ummu da Babiy na hankalce da ita, tausayi take basu matuÆ™a, wani lokacin Ummu har hawaye takan share itama.
Yau ma tamkar kullum tun bayan dawowarta tai shirin makaranta ta fice badan hankalin su Ummu ya kwanta ba. Kawai dai dan ta dagene akan komawar. Sun bartane ko komawar zaisa ta sake samun nutsuwa da farin cikin da ko’a fuskarta yanzu baka hangosa. Sanye take cikin skirt golden yellow da t-shirt fara da suka kasance Uniform É—insu, sai hijjab fari Æ™arami shima ta É—ora niÆ™ab ta yanda Æ™wayar idanunta kawai ake iya gani. Bayanta goye da school bag. A nutse take tafiya kanta a Æ™asa tamkar bata son taka Æ™asar har ta iso bakin titi, tsayuwar da batafi ta mintuna uku ba ta samu abin hawa kamar sauran É—alibai daketa É“illowa a kowane kusurwa. Makarantarsu babbar makarantace mai É—auke da É—alibai masu hazaÆ™a, domin kuwa an tattarosu ne daga mabanbanta makarantu aka kawo nan saboda hazaÆ™arsu. Kowa bata kulaba ta shige aji tai zamanta, saÉ“anin da da kowa yasan Iffah mai tsiwa da surutu, gata ba’a kadata a himma. KauÉ—inta yasa mafi yawan malamai saninta ga kuma Æ™oÆ™ari. Amma tunda ta dawo yanzu ta canjama kowa, magana ma saita zo har a tashi batai da wani ba. Kamar yanda malaman sukai mata uziri haka É—aliban ma sukai mata, dan kowa yasan tana cikin yanayin da uzirin kawai tafi buÆ™ata.
Duk wanda ya shigo yakan miÆ™a mata hannu su gaisa, itama babu musu take miÆ™awa tare da amsa sallamar da sukai mata. A haka har duk É—aliban ajin suka kammala shigowa malamin farko ya shigo musu. Da farko ta nutsu wajen fara fahimtar darasin da yake musu, a hankali kuma tunaninta ya fara janyewa zuwa ga abinda taketa faman shiryawa da zuciyarta a kwanakin nan har malamin ya kammala ya fita babu abinda ta É—auka. Haka na bayansa suka cigaba da shigowa basu darasi daban-daban, wani hankalinta na kai wani harya fita babu abinda zatace ta saurara. Ana tashi tana a É—alibai sahun farko da suka fara fitowa, jitai kawai tana sha’awar yin tattaki da Æ™afafunta yau, dan haka bata tsaya neman abun hawa ba ta miÆ™o titi da Æ™afa ta fara tafiya kamar wasu tsirarun É—alibai irinta da gidajensu ke kusa da makarantar. Tafiya tayi mai nisa sosai batare da nuna alamun gajiyawa ba, harta kusa isowa roundabout É—in daya raba hanyar gidansu da ainahin titin hanyar masarauta daular ruman. Daga roundabout É—in ana iya hango Æ™aton tambarin Æ™osashen zaki da akayisa da gold na tambarin Masarauta. Iffah taja wani kakkauran tsaki da É—auke kanta zuciyarta na mata zafi. Harta kusa tsallakawa ta hango wata tsohuwa dake riÆ™e da wani yaro da Uniform a jikinsa da alama titin take so su tsallaka amma sunata inda-inda. Karan farko murmushi ya suÉ“uce mata ganin yanda yaron ke jan hanun tsohuwar sai sun tafi kamar zasu tsallaka saita fisgo yaron su dawo baya tana masifa. Sallama tai musu, tsohuwar ta amsa mata. Ta gaisheta da girmamawa tare da faÉ—in, “Ammi kuna so ku tsalla ne?”.
Amsawa tsohuwar tai da “Eh Ibnati ”.
Iffah ta sake murmusawa daga cikin niÆ™ab É—inta, kafin takai hannu ta riÆ™o na tsohuwar dake riÆ™e da yaron ita kuma. Suna gab da kaiwa tsakkiya yaron ya fisge hanunsa ya koma baya da gudu yana faÉ—in yabar abunsa a baya. Tsohuwar zata fisge itama tana masifa da kiran yaron ya dawo Iffah ta riÆ™eta gam suka karasa tsallakawa. “Ammi yi haÆ™uri barsa naje zan sake tsallako miki da shi. Rufe bakin Iffah yay dai-dai da taka wani bahagon birkin daya bada sautin Æ™uuuuuu!!!. Sai sautin fitar Æ™ara mai razanarwa ta biyo bayansa.
Wani irin zabura Iffah tai na juyowa dan ƙarar har tsakkiyar kanta ta jita. Ai batama san sanda ta yaye niƙab ɗin fuskarta ba da waro manyan ƙyawawan idanunta waje gaba ɗaya ba tana mai ambaton sunan ALLAH ganin yaron nan tsaye cak a tsakkiyar titi hancin wata mota gab da shi allamar kaɗan ya hana ayi ɗanyen aiki. Kusan a tare suka isa kansa ita da tsohuwar data fashe da kuka da ƙwala kiran sunan yaron a matuƙar firgice.
Iffah da jikinta ke ɓari ta riƙo yaron jikinta tana duddubashi da sauke ajiyar zuciya a jajjere, ganin babu ko ƙwarzane a jikin nasa. Saurin sakin yaron tai ga tsohuwar tasha gaban motar ranta a ɓace ganin mai motar ko fitowa baiyiba ya ɗan leƙone kawai, ganin baima yaron komaiba ya maida kansa yanama ƙoƙarin barin wajen. A fusace ta buɗe murfin, ba saurayin daya kasance drivern motar ba hatta wanda ke gefensa hankalinsa akan lap-top dake saman cinyarsa sai da ya ɗago suka zuba mata idanu. Gaba ɗayansu ta haɗa ta dallama harara da manyan idanunta masu matuƙar haske tamkar madara.
“Kai malam baka san darajar mutane bane?….” ZazzaÆ™ar muryarta mai taushi da nutsuwa a cikinta ta daki kunnuwansu cikin faÉ—a babu ko É—igon tsoro a tare da ita. Batare data damu da yanda suka zuba mata ido ba ta murguÉ—a musu bakinta da sake dalla musu harara ta cigaba da masifarta, “Ka kusan bige yaro amma tsabar kanka ba’a daidai yake ba shine koka fito kaga yaya yake ma saboda ku masu kuÉ—in nan É—aukar talaka kuke baida banbanci da titin da kuke gurza tayoyin banzayen motocinku da kuka saya da kuÉ—inmu”.
“Kai!”.
Drivern ya faÉ—a da maÉ—aukakin mamaki Iffah.
Harara ta sake dalla masa da zira hannunta ta zare key É—in motar daya riga ya kashe tun É“uÉ—e musu murfin da tayi.
“K! K! Dalla bani key kajimun fitsararriyar yarinya kinga mun taÉ“ashi ne?”.
“AnÆ™i a bakun, wlhy duk sai kun fito kun dubashi kun bama kakarsa haÆ™uri zan baku key É—in nan, inba hakaba sai dai mu kwana anan.”
Hannu saurayin ya kai da nufin warto key É—in taja baya, sai dai duk da haka saida yaÉ—an taÉ“a skirt É—inta kaÉ—an. Cikin matsanancin É“acin rai ta jinjina yatsarta a kan fuskar matashin tamkar zata tsone masa ido. “Idan hanunka ya sake gigin taÉ“a koda hijjab É—in jikina ne sai na karyashi, Sannan koda Shahanshan ne yay wannan aikin bai isa barin wajen nan ba balle kai shashasha driver”.
“K!!”.
Na gefensa ya faÉ—a cikin matuÆ™ar waro idanu. A karan farko wanda ke hakimce zaune a sit É—in bayansu lap-top a cinyarsa da tarin takardu a gefe da gefensa ya É—ago Æ™yawawan idanunsa dake tattare da matsananciyar gajiya da Æ™osawa yana yamutsa fuska. Baya ganin yarinyar, sai dai duk abinda take faÉ—a raÉ—am a kunensa zazzaÆ™ar muryarta ke sauka. Baiko kalla yaran nasa ba ya sauke Lap-top É—in dake cinyar tasa tare da kai hannu ya buÉ—e murfin. A tare suka zabura, sai dai kafin suyi wani yunÆ™uri harya fita a motar. Dolo suka fito suma da sauri………..✍

 

*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*

*DAUDAR GORA Billyn abdul*

*KI KULANI hafsat xoxo*

*A RUBUCE TAKE Huguma*

*RUMBUN K’AYA Hafsat rano*

*IDON NERA Mamuh ghee*

_LITTAFI DAYA: 400_
_LITTAFI BIYU: 600_
_LITTAFI UKU: 800_
_LITTAFI HUDU :1000_
_LITTAFI BIYAR: 1200_

_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_

_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_

_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_

_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_

_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_

_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_

ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN

MARYAM SANI
ACCESS BANK
0022419171

SAI A TURA SHAIDAR BIYAN

09033181070

IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA

09166221261

*ƳAN ƘASAR NIGER. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*

+22799643131

Books biyar 1250CFA
Books hudu 1050CFA
Books uku 850CFA
Books biyu 650CFA
Bookk daya 450CFA

KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.

MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.

 

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*

✨ÆŠ ✨
( )

 

*_5_*

_________________

_*MAAB LUXURY HOME!!* Sabuwar duniyar hamshakan mata da Æ´aÆ´an gata._

_*GIDAN* ƙawa da ƙawata gidajen da suka cika gida._

_*SABUWAR DUNIYAR* Amare da uwargidan data amsa sunanta Æ´ar gaban goshi._

_*MAAB LUXURY HOME* wata duniya ce ta ƙawa da ƙawata gidajenmu da kayan ƙyale-kyale na burgewa da ɗaukar hankalin duk wani mai kallo_.

_*SUNYI FICE* Fice irin na É—aya a cikin tsara, sune na farkon fari, a farin da za’a kira fari a kowace irin duniya._

_*A GAREMU* ba sitturu na alfarma da kawa ne kawai ke tabbatar da mu hamshakai ba. Sai mun haÉ—a da Æ™awata gidajenmu da kayan MAAB LUXURY HOME zamu kasance cikakkun Æ´an gata ababen kallo da nunawa sa’a koda a cikin dubun da sukafi dubu._

_*MAAB LUXURY HOME* sun takaita mana dukkan wahalar nema ko order a kasashen ketare ta hanyar wadatamu da galla-gallan kayayyakin adon gidajenmu_

_*MAAB LUXURY HOME.* Duniyar kayan Kitchen da decoration din gida na keta raini._

_*INA UWARGIDA INA AMARYA!!?* Ku ziyarci shagon mu dake No 22 Ahmadu Bello Way, Kano state. Ko kuyi order daga shafin mu na Instagram @maabluxuryhome. Ko Facebook @maabluxuryhome. Ko Ku nememu a lambar waya *08034631010*._

*_Mai azama shi za’a kira dana farkon fari. Bara nai sauri nawa suzo hannuna kafin a kwashe⛹‍♀️⛹‍♀️⛹‍♀️._*

__________________

Post a Comment

0 Comments