Daudar Gora Book 1 Page 42

Latest Posts

6/recent/ticker-posts

Ad Space

Daudar Gora Book 1 Page 42


42_*

………Kasancewar Barrister Akeem ba baÆ™o bane na shigowa gidan masu hidima a gidan suka dinga gaidashi. Amsa musu Barrister Abdallah ya dingayi da fara’a da kuma muryar Barrister Akeem data zama yana kwaikwaya a yanzu kamar yanda aka horar da shi. Ya iso katafaren falon da yaji komai na more rayuwar duniya, ga kamshi na tashi irin wanda aka san duk wani jinin Æ™asar ruman da shi. Cikin girmamawa ya kai zaune fuskarsa da murmushi ya shiga gaida babban mutum É—in dake zaune a falon cikin shigar kayan Æ™asar na alfarma.
Da Æ´ar sakin fuska mutumin ya amsa masa da faÉ—in, “Barrister sai yau ake ganinka? Bayan kuma tun jiya nasa a sanar maka na dawo Æ™asar”.
“Amun afuwa ranka ya daÉ—e, an É—an samu wani tazgarone daya riÆ™eni a dalilin zaman da Boss namu ya kira, nayi zaton zamu tashi akan lokaci harna iso nan É—in sai hakan bata yiwu ba, ganin dare yayi kawai na wuce gidan dan nasan kana bukatar hutu”.
“Hakane kam. Yaya aikin naku?”.
“Alhamdullh ranka ya daÉ—e munata bubbugawa”.
Murmushi mutumin yayi, sai kuma ya ɗan gyara zamansa da zuƙar shisha ɗin hanunsa yana gyaɗa kai. Shiru ya biyo baya kasancewar ɗaya daga cikin masu masa hidima ya kawo ma Barrister shayi. Sai da ya kammala ya fice mutumin ya ajiye marikin shisha ɗin da fesar da uban hayaƙin daya tara a bakinsa.
“Barrister dama ina maka wani neman gaggawa ne akan abokinka mai shegen taurin kai Barrister Abdallah Aas”.
“Tofa oga ya Æ™ara yin wani laifi ne?”.
“Kusan haka kam, dan akwai wani case na aminina dake a rufe sai Æ™oÆ™arin ganin ya buÉ—osa yake yi. An masa gargaÉ—i kusan sau uku amma bai ji ba har sai da yajama kansa aka kauda shi kasan mutumin na ka da taurin kai”.
“Kauda shi kuma ranka ya daÉ—e?”.
Barrister ya faÉ—a cikin nuna rudanin as shine Barrister Akeem. Murmushi mutumin yayi irin nasu na manya yana É—age kafaÉ—a alamar ko’a jikinsa. “To in basu kaudashi ba mi kake so suyi Barrister?. Yana da taurin kai ne gaskiya. Nasan dai kaji zancen tashin bomb É—in can na jihar Hubab..?”
“Yes Yes ranka ya daÉ—e, ai kowa ma dake Æ™asar nan yaji wannan baÆ™on al’amari mai tada hankali tunda bai taÉ“a faruwa ba a wannan Æ™asa tamu……”
“To ga abokinka kam yaja ya faru, dan an tada wannan bomb É—inne da shi kasancewar a cikin motarsa aka sakashi”.
A matuÆ™ar razane Barrister ya furta “What! Ranka ya daÉ—e abokin nawa?”.
“Kaga kwantar min da hankalinka wannan ba wani abu bane. Sakamakonsa ya amsa a hannunsa. Kaga ko anan gaba masu shirin taurin kai irin nasa sai su kiyaye. Ba wannan ne abin damuwa bisa maÆ™asudin kiranka nan ba. Muna son ne ka maye gurbinsa a wancan case É—in ne domin kwaso mana dukkan wasu bayanai da ya haÉ—a. Mun zaÉ“oka ne saboda kamaninku É—aya, har yanzu kuma babu wanda yasan da shi bomb É—in ya tashi. Kafin masu bincike su gama gano motarsa ce wadda bomb É—in ya tashi a ciki muke bukatar ka kamla komai”.
“Amma ranka ya daÉ—e……”
Hannu ya É—aga masa da sauri. “Karkace komai Barrister, nasan zafin rasashi kakeji, ina maka ta’aziyyar hakan. Sai dai ka sani, wanda ya É“atar da shi kaima zai iya É“addaka kai da duk a halinka wannan yafi shan shayi sauÆ™i a garesa. Dan haka ka kula. Akwai saÆ™o na kafin alkalami a motar ka mu yini lafiya”.
Hakan da yay na nufin ya sallamesa. Barrister Abdallah ya miƙe jiki a sanyaye. Gaba ɗaya tunaninsa ya rabu da zuciya da kwakwalwarsa. A yanzu kam ya gagara fahimtar komai gaskiya. Shin idan har waɗan nan ɗin sune mugaye a garesa, waɗan da kuma su yake bibiya a case ɗin su Babiy to sukuma waɗan da suka sakashi wannan aikin fa? Kenan fa kuɓutar da shi sukai a waccan ranar ko mi abinda sukai ɗin ke nufi? Ya ALLAH mike shirin faruwa da ni ni Abdallah?.
Ya tambayi kansa batare da yasan ina zai kama ba har ya Æ™araso jikin motarsa ya shiga. Da Æ™yar ya iya tuÆ™in zuwa waje, yana hawa titi É—an nesa da gidan aka dakatar da shi akan cewar yay parking ta cikin bluetooth É—in kunnensa. Hakan ba karamin taimako bane a garesa, dan a yanda yake jinsa tabbas zai iya kife kansa a titin ma gaba É—aya……..

★★…. ★★…..

Babu kowa a É—akin sai wani irin Æ™amshi mai matuÆ™ar saka jiki kasala da sanyin ac. Iffah ta lumshe manyan idanunta tana ambaton sunan ALLAH da sake buÉ—esu. (Kai kai kai duniya fa na inda take) ta ayyana a zuciya tana dire tray É—in hannunta saman wani É—an table dake gaban Æ™yaÆ™yÆ™yawar kukera ta hutawa. (Dama ce fa wannan) ta zabura dalilin wancan furucin da zuciyarta ta ayyana. “Tabbas dama ce kam”. Ta maimaita a fili tana É—an waige-waige a nutse cikin hikima kuma É—an gudun kar ya zam akwai camara a É—akin kamar yanda aka bazasu ta waje ko’ina a sashen. Adai iya dubanta babu kamar sauran É—akunan data kwana, dan haka ta cire takalmanta cikin sanÉ—a ta nufi Æ™ofar toilet da zuciyarta ke raya mata yana ciki. Tabbas yana cikin kuwa dan jin motsin ruwa. Ta daga hannayenta sama alamar Alhamdullah sannan ta baro wajen. Da ma’ajiyar turarrukan sa ta fara, sai da ta gama É—agasu É—aya bayan É—aya ta shinshina. Sam babu alamar irin wancan, cikin damuwa ta maida ta rufe badan zuciyarta ta wankesa da zargiba har yanzu. Dan ta gama haƙƙaÆ™ewa aljanun tsafinsa ya tura suka É—akkota a daren na jiya dan ya cika burinsa. Amma ALLAH ya hanashi sa’a shiyyasama taga É—akin kaca-kaca kamar anyi dambe a cikinsa. Da alama sun gusar mata da hankaline shiyyasama bataji sanda aka É—akkotan daga can É—in ba.
Harta juya zata fita zuciyarta ta sake nata shawarar ta ɗan sake duddubawa ko zataga wani shaida da suke buƙata akansa. Cikin yanayin dai ɗan tsoro-tsoro na mara gaskiyar dake gudun a kamasa take ɗan buɗe-buɗen ta, sai dai abin mamaki idan ka cire turarrukan data gama dubawa, da wasu tarin books a cikin wata ƙyakykywan show glass, babu wani abu a ɗakin bayan kayan gado da na ƙawata adon ɗakin kuma. Sai kuma kayan barci kala-kala a cikin wani dogon gilashi shima alamar matsayin wadrub, sai dai kasancewar zallar gilashi komai ana gani fes dan duk rataye suke a jikin hanger ma.
Iffah da gaba É—aya kanta ya kulle na mamakin ina kayan da yake sakawa? Da takalma? Su agogo dama duk wani nau’in kayan da yake ado dasu fa?. Dan acan ma sauran É—akunan da ta kwana iya irin abinda ke anan É—in kawai ta gani. Lallai dole akwai abinda yake buÆ™atar tayi nazari a kansa kenan? (Minene to?) Zuciyarta ta ayyana mata tare da katse tunaninta sakamakon jin wani masifaffen kamshin shower gel da tsumammun turarrukan wanka Æ´an asali da bata taÉ“a shaÆ™ar irinsu ba.
A É—an firgice ta juyo, sai kuma ta sake juyawa da sauri tana mai rumtse idanunta da faÉ—in, “Wayyo ni Iffah” ta nufi Æ™ofar fita da matuÆ™ar sassarfa tamkar zata kifa dan hatta da tsumar jikinta a bayyane take..

Shiko da komai ya faru dominsa babu alamar hakan ya damesa. Dan ko kallon inda take baiba tunda ya fito. Babu ma alamar yasan da ita a É—akin tattare da shi. Amma abin mamaki sai gashi ya zauna a kujerar da table É—in ke tare da ita, wanda kuma anan ne Iffah ta ajiye shayin nasa. banbancin É—anÉ—ano da wanda ya saba sha kamar É—azun ya sakashi yin tsamm da tsurama shiyin ido tamkar a cikinsa yake neman amsar sanin yaya hakan wai ke faruwa?. A zahiri ko babu wani abu a fuskarsa sai ma glowing da take irin na mai lafiyayyar fatar data jiÆ™u da hutu da jin daÉ—i. Yatsunsa biyu ya É—an kai saman goshinsa ya murza kusan tsahon sakanni arba’in, kafin kuma ya janye yana mai ajiye kofin ya miÆ™e batare da ya sha ba. Ta can wajen gilashin da kayan barcinsa suke ya taka, hannunsa ya daura akan gilashin sai gashi gaba É—ayan drawer É—in ta zuge a hankali Æ™ofa ta bayyana. Takawa yay ya shige, ta maida kanta ta zuge……..

(an wani rufe dan kar na gani, to Iffahn mu zata gano mana ai ehe).

★★…..

Da gaske dai É“atan Sayeed Khairul-Bashar ya tabbata a cikin masarauta. Dan Iya duk wani bincike babu wata alama ta yana a cikin gidan. Iyalansa sai kuka suke duk sun hargitsa masarautar. (Kamar yanda kukaji a baya Sayeed Khairul-Bashar Aami ne a wajen su Tajwar Haysam, Miran Arshaan, Miran Jasim da dai sauransu. Kaka kenan a wajen Tajwar Eshaan shi kuma. Sayeed Khairul-Bashar da Tajwar Abdul-majeed kakan Tajwar Eshaan Æ´an uba ne suma. Kamar yanda a yanzu Tajwar Eshaan ke shan gwagwarmaya a hannun su Miran Jasim haka mahaifinsa Tajwar Haysam yasha wannan wahalar a hannun Aamin nasu irin su Sayeed Khairul-Bashar. Sai dai ko kusa basu ci galaba ba dan Tajwar Haysam ma dai kaifi É—aya ne kuma tsayayyen mutum kamar yanda kuke ganin Tajwar Eshaan a yanzun. Wannan rashin nasarar tasu akan Tajwar Abdul-majeed da É—ansa Tajwar Haysam ce ta dawo kan Tajwar Eshaan a yanzu, sai dai kuma da alama bazai taÉ“a ya raga musu ba. A gefe kuma su Miran Jasim na amfani da wannan damar wajen dama garinsu akan Tajwar Eshaan… ALLAH ya sa kun gane ni dai ba ruwana)

Duk bidirin da ake Tajwar Eshaan bai sani ba, dan yau ya fita fada ne a makare. Koda ya isa fada kuma aka kawo zancen da farko bai É—auka abin na gaske bane, dan haka cikin halin ko’in kula irin nasa ya nuna musu maybe yayi fitar da kowa baya buÆ™atar ya sani ne. A bashi lokaci a gani. A cikin wasu Æ´an majalissar tasa wasu sun gamsu da wannan jawabi, harma aka fiddashi waje dan hankulan mutane su kwanta. Sai dai a wani gefen kuma jawabin Shahan-shan É—in tamkar samun wani makamine na dukansa da shi ga maÆ™iyansa na É“oye dana zahiri, sai dai sun danne a yanzu basuce komai ba suna jiran lokaci……..

★★….. BARRISTER ★★…..

RuÉ—anin da Barrister yake ciki ya wuce duk yanda mai hasashe zaiyi tunani. Gashi tunda suka maidashi gidan suka sake kullesa a É—akin babu wanda ya waiwayesa har duhun magriba ya kawo, bayan idar da sallar isha’i ne aka kawo masa abinci. Dan haka ya fuskanci mai kawo abincin da alamar yar yanzu zuciyarsa ta kasa tsayawa waje É—aya.
“Dan ALLAH ina son magana da ogan ku Akhi. Ina da abubuwan tattaunawa da shi masu yawan gaske da muhimmanci”.
Kamar bazai tanka masa ba sai kuma ya amsa shi da faÉ—in, “Boss baya nan, ganinsa kuma abune bamai sauÆ™i ba dan bana jin ma yana Æ™asar. Karka damu idan yana buÆ™atar magana da kai zai zo da kansa basai ka nema hakan ba”. Daga haka yay ficewarsa. Jiki a sanyaye Barrister ya bisa da kallo harya maida Æ™ofar zai rufe yay saurin faÉ—in, “Na roÆ™eka kota wayane ka haÉ—amu, da gaske maganar da zanyi da shi nada matuÆ™ar muhimmanci, da kuma buÆ™atar yinta da gaggawa”.
Jimm saurayin yay yana kallon Barrister É—in daga inda yake, sai kuma ya É—an rausayar da kansa da faÉ—in, “Okay duk yanda mukai zan dawo”.
“Nagode sosai”.

Baifi mintuna biyar da fita ba sai gashi, har lokacin Barrister na zaune a inda ya barsa. Ya miÆ™a masa wayar hannunsa. Cikin jin daÉ—i Barrister ya amsa. Shi ya fara sallama da gaisuwa batare da la’akari daya girmi boss É—in nasu ba. Amsa masa akai daga can a taÆ™aice, nan ma bai nuna ya damu ba cikin tashin hankali ya fara maganar dake cimasa rai..
“Alhmdullah na cika umarninku, sai dai sakamakon dana samo ya matuÆ™ar rikita tunani na. Dan wannan case É—in case É—in da nake yine, kuma a dalilinsa naje Æ™auyen Lufana. Yanzu kuma sun bani aiki akan kaina, Ina cikin ruÉ—ani sosai, dan na gagara fahimtar manufarku ku da su, shiyyasa gaba É—aya ruÉ—ani ya kasa barina na fahimci abinda ya dace na fahimta….”
“Karka damu kanka da son sai ka fahimta Barrister. Kai dai kai musu aikin da suka buÆ™ata, basu bayanai akan naka da case É—in kawai”.
“Idan nai haka zan saka rayuwar bayin ALLAH ne a haÉ—ari, wlhy mutanen na mutanen kirki ne komai an shiryashi garesu ne bisa wata manufa. Ina matuÆ™ar jin tausayinsu, an rabasu da Æ´aÆ´ansu har uku, an kuma biyo ta wata hanyar rusasu da shine nake son ma san dalili, yanzu kuma ace nine da hannuna zan miÆ™asu, idan nai hakan bazan taÉ“a yafema kaina ba”.
“Baka da wani zaÉ“i bayan hakan Barrister. Idan kuma ka shirya rasa iyalanka ne fine”. Kitt aka yanke wayar. Barrister dake jin hajijiya na É—an kwasarsa ya dafe bango da sauri yana mai ambaton sunan ALLAH domin neman É—auki………✍️

*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*

*DAUDAR GORA Billyn abdul*

*KI KULANI hafsat xoxo*

*A RUBUCE TAKE Huguma*

*RUMBUN K’AYA Hafsat rano*

*IDON NERA Mamuh ghee*

_LITTAFI DAYA: 400_
_LITTAFI BIYU: 600_
_LITTAFI UKU: 800_
_LITTAFI HUDU :1000_
_LITTAFI BIYAR: 1200_

_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_

_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_

_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_

_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_

_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_

_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_

ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN

MARYAM SANI
ACCESS BANK
0022419171

SAI A TURA SHAIDAR BIYAN

09033181070

IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA

09166221261

*ƳAN ƘASAR NIGER. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*

+227 96 09 67 63

Books biyar 1250CFA
Books hudu 1050CFA
Books uku 850CFA
Books biyu 650CFA
Bookk daya 450CFA

KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.

MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.

 

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*

✨ÆŠ ✨
( )

 

 

Post a Comment

0 Comments