Daudar Gora Book 1 Page 43

Latest Posts

6/recent/ticker-posts

Ad Space

Daudar Gora Book 1 Page 43


43_*

……….Yau kwanaki huÉ—u kenan da rashin ganin Sayyid Khairul-Bashar, kwana shidda kuma cur da kai Iffah sashen Tajwar Eshaan Ibn Haysam Abdul-majeed. Sosai masarautar a harmutse take, yayinda Æ™ananun magana da rikice-rikice ke neman tashi a dalilin fitar zantukan da Sayeed Khairul-Bashar É—in yayi kan Tajwar Eshaan a daren da za’a rasashi. Nan fa kowa ya shiga yima al’amarin fashin baÆ™i da ga É“angaren masu faÉ—a ajin gidan, wanda kai tsaye kusan mafi yawansu sun karkata zarginsu ne da kalaman da Tajwar Eshaan yayi shi kuma..

Duk abinda ke faruwa sarai yana isa kunensa, sai dai abin mamaki yayi biris kamar yanda ya saba. Yayinda shirun nasa ke Æ™ara wutar al’amarin matuÆ™a a tsakanin ahalin gidan baki É—aya. Rashin daÉ—in maganganun da ke neman kawo bore ga mulkin Shahan-shan É—in kai tsaye ne ya tada hankalin Malikat Bushirat matuÆ™a ta nema ganawa da É—an nata, dan tun ana yi iya su ahali har abu ya zagaye masarauta yana neman fara fita waje.
Bayan mintinan da basu gaza talatin ba amsa daga Tajwar Eshaan ta dawo ga Malikat Bushirat cewar baya buƙatar ganawa da kowa. Ranta ya matuƙar ɓaci da wannan amsa, dan take ta kori dukkan hadimanta ta shiga Safa da marwa. Tasan kota kirashi bazai ɗaga ba, kuma tunda yace bai buƙatar ganawa da kowan ta san halinsa har zuciya baya bukatar hakan. A kaikawon nata Iffah ta faɗo mata a rai, babu ɓata lokaci a karo na biyu ta bukaci ganinta duk da kuwa sune sukai mata katanga da sake baro sashen Tajwar Eshaan tun a waccan fitar acewarsu har sai ta cika kwanakin bakwai ciff.
Iffah na zaune a Æ´ar barandar da takan sha iska da nazarin littattafan data maida hankali saÆ™on na Malikat Bushirat ya risketa, ta É—anji mamaki, amma sai ta shanye a ranta kawai, dan tun washe garin kwananta na biyu Malikat Haseenat ta kirata a waya da kanta ta sanar mata karta sake cewa zata baro sashen Tajwar É—in har sai kwanakin bakwai sun cika. HaÆ™uri ta bada bisa kuskurenta, daga ranar kuma ta haÆ™ura duk da a takure take matuÆ™a da zaman, ganin ranta zaita É“aci ma a banza sai ta maida hankalinta ga nazarin littattafan nan data É—ibo a books room, ko shi Tajwar Eshaan É—in ma sai ta Æ™ulla wasan É“uya da shi, dan tun faruwar tashin bomb É—in nan ta riÆ™esa a rai, sai kuma maganar É“atan Sayeed Khairul-Bashar da a yanzu aketa dangantashi da shi ya Æ™ara tabbatar mata da shi mutumin banza ne….
Cikin ƙanƙanin lokaci ta kimtsa, ta saka kamshin data maida nata ta ƙarfi da yaji. Tana fitowa daga sashen ta samu hadimanta na jiranta. Gaisuwarsu ta amsa a yau kam da kulawa, kafin ta shiga motar da zasuje sashen Malikat Bushirat ɗin a ciki duk da bawani uban nisa bane, amma akwai tazara gaskiya. Sojan daya buɗe mata yay salute ɗinta kafin ya maida ƙofar ya rufe, da sauri suma hadiman suka shiga ɗayar motar bayanta.
A tafiyar da bata gaza mintuna biyar zuwa bakwai ba suka iso, anan ɗin ma dai buɗe mata akai, yayinda hadimai ke faman zubewa ƙasa bisa gwiyawunsu. Hannu kawai Iffah ke ɗaga musu da sakewa. Tausayinsu da sake jin zafin wannan mulkin iko na kasarsu a ranta. Tun a falo na farko tabar hadimanta, inda amintacciyar hadimar Malikat Bushirat ta karasa mata iso har inda take.
“Barka da yamma Mah-mah”.
Iffah ta faɗa cikin girmamawa ga Malikat Bushirat dake hakimce fuska babu walwala. Hannu kawai ta ɗaga mata, daga haka falon yayi shiru. Sai da ta gama shan kamshinta kafin ta tashi zaune da ƙyau idonta akan Iffah da ta rissinar da kai .
“Ibnati kin san miyasa na kiraki?”.
“A’a Mah-mah”.
Iffah ta amsata da sauri. Cikin É—acin murya Malikat Bushirat ta cigaba da faÉ—in, “Akan mijinki ne, nasan duk abinda ke faruwa a Masarautar nan kin sani kema”.
“Hakane Mah-mah, amma sai nake ganin kamar ba haka bane, kawai dai wasu ne ke son É“ata masa suna”.
Har cikin rai kamalan Iffah sun saka Malikat Bushirat jin sanyi a rai, sai zuciyarta na rawa dan zuwa yanzu al’amarin É—an nata da gaske tsoro yake bata. Yayinda ita ko Iffah ta faÉ—i hakanne da manufar wayon da ALLAH ya bata domin son fahimtar abinda take son sani.
Malikat Bushirat ta katse mata tunani da faÉ—in, “Hakan zai iya zama gaskiya, sai dai bazamu saki jiki ba dan da gaske al’amarin mijinki na bani tsoro. A yanzu haka na bukaci ganinsa amma shi yace bai buÆ™atar ganin kowa”.
Da mamaki Iffah ta É—an É—ago ta dubeta, a ranta kam jinjina rashin mutuncin sa take, a tunaninta ai ko kowa bai tsiraba mahaifiyarsa ta tsira. “Mah-mah kuma shi É—inne ya faÉ—a?”.
A karan farko Malikat Bushirat tai murmushin takaici. “Kar kiji ko tantama akan hakan Ibnati. Dan duk yanda kike tunaninsa ya wuce nan É—in. A yanzu dai tunda ya nuna bai buÆ™atar ganin kowan bazai gani É—in ba. Shiyyasa na kiraki nan dan kimin wani taimako na haÉ—ani da shi ta waya”.
Yawu Iffah ta haÉ—iye muÆ™ut, dan itama dai a karan kanta kwanaki huÉ—u kenan bata sanyashi a ido ba. Tayaya kuma zata haÉ—asu a waya. To wanda ma ya nuna kai tsaye bazai haÉ—u da ita matsayin mahaifiyarsa ba ita kuma Æ´ar karere taya zatai hakan?. Amma bara ta amsa mata kawai, dan koba komai itama tana buÆ™atar jin gaskiyar lamarin ai…….

★★…….

Har lokacin kwanciya barci Iffah bata samu wata makamar riƙewa na tunkarar Tajwar Eshaan ba. Hasalima bata da tabbacin a inda zata samesa. Tambayar hadimai kuma tamkar gazawace a gareta matsayinta na Zawjata-almilk. Kusan ƙarfe ɗayan dare tana tsaka da kai kawonta da faman jan tsaki saƙo ya shigo wayarta. Kamar zata share sai kuma ta ɗauka dan koba komai kullum a cikin tsumayen ji daga su Babiy take. Mamaki ya sata buɗe saƙon da hanzari ganin Malikat Bushirat.
_Ina alfahari da kasancewar ki tare da gudan jinina Ibnati. ALLAH yay miki albarka, yanda kika zama sanadin yaye damuwata kema ALLAH ya yaye miki taki yanzu na gama waya da shi_.
“What!!”.
Iffah ta faÉ—a cikin É—an zabura tana sakin wayar akan carpet. To mi hakan ke nufi? Ita da batama gansa ba taya har yay kiran mahaifiyar tasa da har ta gamsu itace sanadi. “Anya mutumin nan kuwa ba ifiritin aljani bane?”. Ta faÉ—a a zahiri tana waige-waige a É—akin da tunanin ko dai akwai camara, to inma camara É—in ce itada sukai magana a sashen Malikat Bushirat ma ta ina camara É—in zatai tasiri kenan…

Har waye war gari babu nutsuwata tattare da Iffah akan wannan al’amarin, dan ko barcin kirki batayi ba sam. Sai dai tuna a’a yau zata bar sashen ya saka mata É—an jin sassauci ka É—an a zuciyarta. Tana ko idar da sallar asubahi ta taattara kayanta waje guda tsaf tana jiran gari ya Æ™ara haske ta kama gabanta duk da kuwa wata zuciyar na bata shawarar take akan zuwa Tajwar Eshaan wai ko zata fahimci wata gaskiya saÉ“anin wadda zuciyarta ke tabbatar mata. Amma dai ta dake dan tana buÆ™atar damar keÉ“ance kanta ko zata samu nutsuwa.
A bisa al’adar masarautar kamar yanda ake kai Zawjata-almilk turakar Shahan-shan haka ake zuwa a É—akkota cikin tattali da giramamawa tare da manyan Æ™yaututtuka a randa ta cika kwanaki bakwai cif. Kowa ya É—auka tunda an kai Iffah ba bisa Æ™a’ida ba baza’ai wannan al’ada ba gareta musamman yanda tama karya doka a kwana É—aya ta fito. Ga kuma a yanda masarautar take harmutse kwana biyun nan. Amma sai Malikat Haseena ta bama kowa mamaki ta hanyar haÉ—a komai na al’ada da akeyi, tare da mukulllin zabgegiyar mota Æ™irar zamani da masu hidima har guda goma, da tarin turarurruka na musamman, Daneen Ammarah da tsaffin dake da hurumin gudanar da al’adar a masarautar suka yima sashen Tajwar Eshaan tsinke cikin busar sarewa mai tabbatar da isar da saÆ™on manufar al’amarin.

Tofa wannan fa shine an tsokalo tsuliyar dodo. Dan kuma masu rajin faÉ—a aji tuni sun sake buÉ—e shafin caccakar Tajwar Eshaan Ibn Haysam Abdul-majeed da kakar tasa Malikat Haseena kan basu damu da É“atan Sayeed Khairul-Bashar ba. Ko kuma ma dai sun san komai É—in da gaske. Wannan al’ada ta sake saka jikin Iffah mutuwa da shiga É—unbin mamaki na gaske, har aka maidata sashinta babu alamar tana cikin cikakken tunaninta ma. Bin dai kowa take da ido tamkar gunkiyar da aka Æ™irÆ™ira domin tarihi…

★Ashe duk wan can Æ™arami ne a abin mamaki da Malikat Haseena ta tanada a yau É—in. Dan Æ™arfe tara na dare da kanta kamar yanda tayi akan Iffah ta sake jagorantar rakiyar É—aya cikin biyun Zawjata-almilk dake gidan tun kafin zuwan Iffah. Duk da bata haÉ—u da Tajwar Eshaan ba yau bata dawo da ita ba kuma dan acewarta zai ma gaji ne itama ya kulata idan ya gama zaman kulle kansa a É—akin kamar yanda zukatansu ke basu sakamakon sanin hakan al’adarsa ce a duk sanda ransa ke É“ace.
A wannan gaÉ“ar kam kowa ya saki jiki waccan matsalar ta shuÉ—e tunda ga Iffah tai kwanakinta lafiya ta fito. Maimakon shiga fargabar rasata itama sai kowa ya É“ige da Æ™ananun magana akan rashin dacewar hakan. Yau É—in ma dai malikat Haseenat tayi kunnen uwar shegu da su, yayinda Malikat Bushirat da Daneen Ammarah suka shiga halin mamaki da hukuncin na Malikat Haseenat a karo na biyu saÉ“anin dukkan shirye-shiryen su. A wannan karon kam sun yanke Æ™uirin tun kararta suji ba’asi, sai dai sun barma safiya komai….

★★

Surutai akan É—imuwar da aka wayi gari da shi a masarautar ne ya farkar da Iffah dake fashin salla É—an barcin daya figeta, dama da Æ™yar ta yisa sakamakon kwana da tai neman Sir Fawzan da Sir Ajmaal a waya amma bata samesu a online ba hakama a kira. Sai abinda ta karanta da yay matuÆ™ar tada hankalinta a É—aya daga cikin littafan da take nazarta akan Tajwar Eshaan. “Tabbas babu lafiya” ta faÉ—a a zahiri tana miÆ™ewa zumbur. Har ta nufi Æ™ofa ta dawo da sauri, toilet ta shiga a gurguje ta watsa ruwa ta fito. Sama-sama ta kimtsa jikinta ta fito. Hadiman ta da alamun sanyin jiki ya bayyana a agaresu suka dinga zubewa gaisheta. Maimakon amsa ta jefa musu tambayar da ruÉ—ani ya bayyana kansa a cikin idanunsu da jikkunansu lokaci É—aya.
“Mike faruwa a masarautar nan? Da alama babu lafiya?”.
Duk sun rikice babu alamar wani zai amsa mata. Sai kaÉ—uwa suke kamar masu jin sanyi. Halin da take ciki ya assasa mata jin zafin hakan ta daka musu tsawa. Sake firgicewa sukai, sai dai wajibi ne a gare su bin umarninta, dan haka cikin Æ™arfin hali wadda ke matsayin amintatta a gareta ta sanar mata cewar an wayi gari da rashin Zawjata-almilk ne ta farko da jiya ta kwana turakar Shahan-shan sai Sayeed Khairul-Bashar shima da aka samu gawarsa a wani É—aki cikin masarautar. Iffah da bata san da hakan ba ta Æ™ame Æ™am alamar sumar tsaye ta wucin gadi ce ta risketa. Sai kuma hajijiya ta fara juya mata falon da hadiman, a hankali duhu ya dinga lulluÉ“e idanunta data kafa musu tabbacin bata cikin hayyacinta……….✍️

*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*

*DAUDAR GORA Billyn abdul*

*KI KULANI hafsat xoxo*

*A RUBUCE TAKE Huguma*

*RUMBUN K’AYA Hafsat rano*

*IDON NERA Mamuh ghee*

_LITTAFI DAYA: 400_
_LITTAFI BIYU: 600_
_LITTAFI UKU: 800_
_LITTAFI HUDU :1000_
_LITTAFI BIYAR: 1200_

_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_

_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_

_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_

_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_

_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_

_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_

ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN

MARYAM SANI
ACCESS BANK
0022419171

SAI A TURA SHAIDAR BIYAN

09033181070

IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA

09166221261

*ƳAN ƘASAR NIGER. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*

+227 96 09 67 63

Books biyar 1250CFA
Books hudu 1050CFA
Books uku 850CFA
Books biyu 650CFA
Bookk daya 450CFA

KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.

MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.

 

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*

✨ÆŠ ✨
( )

 

 

Post a Comment

0 Comments