Daudar Gora Book 1 Page 47

Latest Posts

6/recent/ticker-posts

Ad Space

Daudar Gora Book 1 Page 47


47_*

………Kamar yanda Iffah tai tunani labarin zuwanta sashen Sayeed Khairul-Bashar ta’aziyya har ya isa kunnen surukarta dama na jikin Tajwar Eshaan irinsu malikat Haseenat da su Daneen Ammarah. Dan tana fitowa kiran Daneen Ammarah ya shigo wayarta. Bata É—aga ba, aka kuma sake kira nan ma dai ta share kamar bataji ba. Sai da ta koma sashenta da kusan mintuna goma sannan tai kiran Daneen Ammarah É—in back. A bugu biyu ta É—aga, Iffah ta taÉ“e baki cikin rashin damuwa tai sallama da fara gaishe ta. Da kulawa Daneen Ammarah ta amsa. Iffah na jiran jin ta mata batun fitarta sai Daneen Ammarah ta jeho mata tambayar da bata da alaÆ™a ma da fitar.
“Ibnati na kiraki ne akan Abni, shirunsa na tadamin hankali matuÆ™a, gashi yana Æ™ara harzuÆ™a mutane Æ™asa, kinga dai yanda Æ™asar nan ke sake rikicewa. Mu dukanmu mun nemesa a waya amma bamata shiga, na fara zargin anya ma yana cikin masarautar nan?”.
Murmushin takaici Iffah tayi, amma a zahiri sai ta danne ta fara magana cikin kwantar da murya. “Wannan shine tunani na nima Mamy, sai dai ban san yanda zanyi ba ganin ku manya bakuce komai ba.”
“Shirun na dole ne Ibnati, bazaki gane babbar sarÆ™aÆ™iyar dake cikin masarautar nan ba ne. Amma tabbas akwai matsala, akwai kuma gagarumin al’amarin dake É“oye amma yana son bayyana kansa a wannan gaÉ“ar…..”
Cikin zumuÉ—i Iffah tace, “Mamy minene shi dan ALLAH?”.
“Humm Fareedah kinyi Æ™arama da yawa ba yanzu ba. Ke dai kawai abinda nake so da ke shine ki taimaka ki bincika min idan Abni yana a gidan nan…”
“To Mamy, amma dai zaiyi wuya tunda kunce idan yana cikin damuwa kulle kansa yakeyi baya kuma sauraren kowa. Sai nake ganin ni taya zai saurare ni”.
Murmushi Daneen Ammarah tayi mai sauti. “Rashin saurarenmu bashi ke nufin kema bazai saurareki ba Ibnati. Ke dai gwada sa’arki mu gani”.
Iffah dai ta jita ne kawai, amma sai bata sake musawa ba sukai sallama…..

★★…. ★…..

Miran Jasim ya sauke wayar dake a kunnensa bayan gama sauraren abokin wayar tasa, yanda fuskarsa ta canja daga farin cikin dake shimfiÉ—e a kanta kafin wayar yasa Miran Arshaan sake maida hankalinsa garesa. “Wani abu ya sake faruwa ne?”.
“Zai dai faru”.
Cewar Miran Jasim É—in a fusace yana miÆ™ewa. Miran Arshaan da maganar ta dakesa ya miÆ™e zumbur shima. “Ban gane mi kake son cewa ba Jasim Akh?”.
Kamar bazai tanka masa ba sai kuma yaja kakkauran tsaki. “Harun Al-rashid ne dai akan waccan maganar banzar ta ranar, duk yabi ya tashi hankalinsa yana cigaba da damuna nima, tun abin bai tasiri a raina ba har ya fara, wai Barrister da suka bama aikin can kan É—an iskan can ne ke cigaba da musu bayani dai kan Barrister Abdallah bai mutu ba dai da gaske.”
“Wai suna nufin shi ya tabbatar da hakan kenan?”.
“Abinda ke cazamun kai kenan, na rasa wane shirme ne kuma hakan? Taya wanda bomb ya tashi da shi ace bai mutu ba?”.
“To amma fa kuma maganarsu fa abin a duba ce Jasim Akh. Dan koni naji shakku a randa bomb É—in nan ya tashi amma jami’an tsaro suka tabbatar babu wani alamar an rasa rai……”
“Amma shine kai shiru?!”.
Miran Jasim ya katsesa a zafafe. “Mi kake so nayi bayan wanda nayi to? ina son ka tuna tun a ranar na kawo maka wannan zancen amma ka nuna min cewar zata iya yuwuwa Æ™arfin tashin nakiyar ya cillashi wani waje ne shiyyasa basu gansa ba. A kuma shekaran jiya da suka kawo maganar na kuma Æ™oÆ™arin maka nuni ka kalli zancensu a shirme”. Shima Miran Arshaan É—in ya karÉ“a masa a nasa zafin.
Shiru Miran Jasim yayi da dafe kansa yana murza goshinsa dan ya tuna tabbas anyi hakan. Amma wannan aikin na cikin gida da rashin sanin mi Tajwar Eshaan ke ciki ya É—auke hankalinsa bai nutsu yayi nazari kan batunba kasancewar akwai abubuwa da yawa da bawai yana buÉ—ema Miran Arshaan É—in bane, kamar yanda shima Miran Arshaan É—in ba komai yake yarda ya buÉ—e ma Miran Jasim É—in ba. Sai dai a yanzu dukansu sun fahimci yin kuskure, dan haka kowanne ya ajiye É“oyayyar manufarsa suka fuskanci juna.
“Ni ina ganin in har an yarda da aikin Barrister É—in nan shawararsa ba abar yardawa bace. Sannan dole ne fa mu gaggauta ganawa da yarinyar can in ba hakaba aikinmu zai iya buÉ—ewa. Dan idan ya kasance Barrister Aas na raye bazai samu É—aki bane ya kulle kansa domin hutu kaima ka sani”.
Miran Jasim ya gyaÉ—a kai da faÉ—in, “Hakane maganarka na kan gaskiya. Yanzu minene abinyi?”.
“Abinyi É—aya ne bama Barrister Akeem damar shigewa gaba kafin kwana biyun nan na cikar aikinmu abar Æ™asar nan da mutanen. Bayan ka haye karagar mulki shi kuma shegen duk inda yake zamu nemishi ne ya É—an-É—ana kuÉ—arsa”.
“Ina sake godema ALLAH da kasancewar ka kusa da ni, dan kana farkar da ni a duk sanda kaina ya shiga duhuwa É—an uwana”.
Murmushi Miran Arshaan ya saki a zahiri, a zuciya kam faɗi yake, (Banza ka gama cusamin ƙayar a rumbu na rufeta da ɗan boto ina daga kwance).
ÆŠaukar wayar Miran Jasim dai-dai da kammala wayar Iffah da Daneen Ammarah daga can……

★★…..

Tana ajiye wayar wani kiran ya sake shigowa, kamar zata share dan bata san number ɗin ba sai kuma dai ta ɗauka da tunanin ko Sir Ajmaal ne kasancewar a saƙonta na ƙarshe ta roƙesa idan ya gani ya kirata. Daga can aka amsa sallamarta kai tsaye, hakan ya sata Ciro wayar a kunenta ta kalla tamkar mai son gano muryar. Miran Jasim da kamar yana ganinta yay gyaran murya, hakan ya sata sake maida wayar.
“Kina magana da Jasim Ibn Abdull-Majeed Aliy”.
Kai tsaye Iffah ta ganesa, dan haka ta fara gaidashi da girmamawa. Hakan ya masa daÉ—i, dan yanda yake amsa mata da kulawa zai baka tabbaci. Shiru ne ya É—an biyo bayan gaisuwar, kafin ya katsesa da faÉ—in, “Ibnati inata zaman jiran ji daga gareki amma shiru. Ko baki amince da abinda kika gani bane ba dai?”.
Iffah da ke jin an taÉ“o mata inda ke mata Æ™aiÆ™ayi hawaye suka shiga rige-rigen sakko mata. Hannu tasa ta sharesu da É—an jan hanci. “Ba yarda ne banyiba ranka ya daÉ—e, kawai dai zuciyata na kaikawo ne na son sanin dalilinka na yin hakan a gareni. Idan ban manta ba kai fa Ammi ne garesa, mizaisa ka zaÉ“eni sama da shi? A barshi ma zaka iya hakan kasancewar ka mai gaskiya ko Æ™yamar abinda yake. Amma miyasa su na baya da aka rasa bakuyi wani yunÆ™uri ba sai ni a kaina bayan akwai Æ´aÆ´an Tajwar mafi rinjaye a cikin wanda ya halaka?”.
(Kaga ibilishiyar yarinya) ya ayyana a zuciyarsa. A zahiri kam sai yay gyaran murya cike da dattako yana kallon Miran Arshaan da shima ke sauraren komai. “Wato Ibnati duk yanda zan miki bayani a wayar nan ba lallai ki fahimta ba. Amma zan tura miki lokaci da adireshi mu haÉ—u zai fi”.
Jimmm Iffah tayi kamar mai shakku, sai kuma ta nisa cikin gyaÉ—a kai tace, “Okay babu damuwa ina jira”. Daga haka sukai sallama kowa ransa na masa kaikawo…

★★….

Cikin Æ´ar dariya Miran Arshaan yace, “Amma shegiyar yarinyar nan fa da zata samu dama a masarautar nan ba Æ™aramin hatsabibiya za’ai ba. Kaji murya cauy-cauy bata ko tsallaken kalma ga shegen wayo”.
“Shiyyasa dolene tana kammala aikin nan a kaudata kawai, ai tunda har tana da Æ™arfin halin shigowa masarautar nan da Æ™udiri irin na kashe Shahan-shan dama nasan zamuga fiye da hakan tattare da ita. Irin waÉ—an nan yaran masu taurin zuciya a cikin mata basu da yawa, amma kuma kasancewar su mata ga mai mulki ba karamin Æ™ara samun power bane. Badan-badan ba babu abinda zai hanani tabbatar da ita abokiyar tafiyata. Dama yarinyar ga shegen Æ™yau da Æ™ira tamkar ita ta zana kanta…”
Ƙaramar dariya Miran Arshaan yay idonsa akan É—an uwan nasa. “Wato dai Jasim Akh har yanzu bazaka canja ba, na É—auka tuni ka jingine batun son matan nan naka kodan kujerar da ke gab da zama taka”.
“Bazaka gane bane Arshaan Akh”. Miran Jasim ya faÉ—a yana tasa Æ´ar dariyar shima da komawa jikin kujera ya lafe Æ™yaÆ™yÆ™yawar surar Iffah da bata wuce sa’ar autarsa ba na masa kaikawo. Shima dai Miran Arshaan É—in hakance a ransa, dan tun randa suka haÉ—u da Iffah a wajen wasan takobi da Tajwar Eshaan yarinyar ta kasa barin ransa. Duk da dai shi yanzu kam ya É—an rage bin mata tun aurensa da Jasrah.
Humm masu karatu Bara na É—an tsakura muku wata gulma dai karna wuce. (A baya Æ™iyayyar Æ´an É—akin su Miran Jasim da Miran Arshaan a bayyane take fiye data Æ´an É—akinsu Tajwar Haysam (mahaifin Tajwar Eshaan kenan) amma a wasu shekaru bayan hawa mulkin Tajwar Haysam sai aka wayi gari sun É—inke, Æ™iyayyar da sukema juna ta koma ta Æ™arÆ™ashin Æ™asa. Wannan haÉ—in kai nasu kuwa ya samo asaline a dalilin kasancewar halinsu da yazo É—aya. Awani lokacin bikin al’ada kamar yanda duk suka saba sun baza yaransu samo musu yara matasan Æ´ammata masu jini a jika da basu gaza sha bakwai zuwa ashirin ba. Karku É—auka da yardar yaran wai ake kai musu su, ko É—aya, ta karfin tsiya za’a É—aukeki bayan an shaÆ™a miki abu ko an yaudareki, bazaki tashi tsintar kanki ba sai a É“oyayyen gurin da in zaki kwana dubu ihu babu mai jinki. Idan sun gama lalata rayuwar yaran kuma a jefar da su. Alokacin da labarin yaje ga Tajwar Haysam hankalinsa ya tashi, dan a shekarar an samu gawar yara Æ´ammata kusan biyar da waÉ—an da aka jikata, iya bincike kuma na jami’an tsaro ba’a sami komai ba. Da shekara ta dawo kuwa yasa tsatstsauran tsaro akan kaikawon mata fiye da maza, aka kuma sake sabon tsarin yanda bikin al’ada zai kasance. Ransu Miran Jasim ya É“aci matuÆ™a, dan Æ™arshe sai a yaran masarauta suka huce haushinsu Æ´aÆ´an talakawa sun gagara É—auka. Duk da ba tare suke aikatawa ba sai shirunsu yazo É—aya a lokacin, har ya kasance yaransu dake sato musu Æ´ammatan sunyi haÉ—aka akan yarinya rigima ta kaure, kowanne ya sanarma ogansa, a zafafe Miran Jasim da Miran Jasim suka buÆ™aci sanin juna kowanne da tunanin shike da Æ™arfin iko, sunko haÉ—un a yanayin da hantar kowanne ta kaÉ—u dan mamaki, amma Æ™wallafa rai da kowannensu yayi akan yarinyar ya sasu amincewa juna yin tarayya da ita a tare Wa’iyazubillah . Haka suka haÉ—u suka lalata rayuwar yarinyar daga Æ™arshe ta rasa ranta, a cikin masarautar suka bizneta har a yau kuma babu wanda ya san hakan sai É—auka da ake yarinyar ta É“ata ne a taron bikin al’ada. Wannan shine sanadin zamowarsu inuwa É—aya dan wannan ya basu Æ™ofar dinga kawoma juna mata, sai dai Miran Jasim yafi Miran Arshaan Æ™warewa a harkar, dan shi har order mata yomasa ake daga wasu Æ™asashen ma). Wanda ya gane na tayasa murna, wanda bai ganeba ya tsallake kawai.

★★ BARRISTER ★★

Kamar yanda su Barrister ke zaman tsammani a yau sai ga kira daga Sayeed Harun Al-rashid, sun tattauna sosai ciki harda yarjewar fita da su Babiy zuwa wata ƙasa da kuma tsananta bincike wajen gani maɓoyar Barrister Abdallah Aas kamar yanda Barrister suka tsara musu. Abu mafi saka Barrister a ƙololuwar farin ciki shine damƙa fita da su Babiy ɗin a hannunsa, amma a zahiri sai ya nuna hakan ba aikinsa bane, shifa ya bada shawara ne kawai.
A ɓangaren su sun nuna masa sufa sun yarda da shine, bayan shi kuma bazasu iya bama wani aikin ba gudun abinda zai je ya dawo. Bayan dai ɗan cigaba da tirjewa da ga ƙarshe Barrister ya amsa. Hakan ya musu daɗi suma, dan a nasu ɓangaren sun bashi aikinne domin ƙullama rayuwarsa, acewarsu koda ta tashi salin alin zasu zare hanunsu su barsa a ciki.
Barrister da ya gama fahimtar su da Æ™udirinsu duk da basu fito sun faÉ—a ba yay murmushi yana mai girgiza kansa da mamakin mutanen wannan duniya mai cike da rikici. “Son kai shine tushen rugujewar kawunan mu a wannan duniyar. Mai mulki kansa kawai ya sani. Mai arziÆ™i kansa kawai ya sani. Talaka kansa kawai ya sani. Mai ilimi kansa kawai ya sani. Jahili kansa kawai ya sani. Iyaye kansu kawai suka sani. Matasa kansu kawai suka sani. Yaro kansa kawai ya sani. Kowa akan buÆ™atarsa kansa kawai yake iya kallo. Duk shaÆ™uwa irin ta ma’aurata akan son kansu kowanne zai iya aikata komai. Duk shaÆ™uwa irin ta É—a da iyaye akan son kansu zasu iya komai. A wannan duniyar yanzu samun cikakken amini sai an tona, ka gama yarda da mutum amma akan son kansa zai iya komai. Son kai dai! Son kai dai ya rabbi. Ƴan uwa son kai fa na kawo abubuwa da yawan gaske. Yana gina hassada a zuciya, Æ™yashi, zalunci, raunana imani, Æ™arya, munafunci, kai komai ma wlhy, hatta shirka tana iya shiga a cikin son kai batare da mun sani ba. Ya rabbi ka ganar damu gaskiya tun kan ta nisanta a kunnuwanmu da idanunmu…….✍️

(Wannan zance haka yake Barrister, ALLAH dai ka shiryar damu).

*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*

*DAUDAR GORA Billyn abdul*

*KI KULANI hafsat xoxo*

*A RUBUCE TAKE Huguma*

*RUMBUN K’AYA Hafsat rano*

*IDON NERA Mamuh ghee*

_LITTAFI DAYA: 400_
_LITTAFI BIYU: 600_
_LITTAFI UKU: 800_
_LITTAFI HUDU :1000_
_LITTAFI BIYAR: 1200_

_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_

_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_

_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_

_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_

_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_

_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_

ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN

MARYAM SANI
ACCESS BANK
0022419171

SAI A TURA SHAIDAR BIYAN

09033181070

IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA

09166221261

*ƳAN ƘASAR NIGER. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*

+227 96 09 67 63

Books biyar 1250CFA
Books hudu 1050CFA
Books uku 850CFA
Books biyu 650CFA
Bookk daya 450CFA

KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.

MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.

 

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*

✨ÆŠ ✨
( )

 

Post a Comment

0 Comments