Daudar Gora Book 1 Page 50

Latest Posts

6/recent/ticker-posts

Ad Space

Daudar Gora Book 1 Page 50


Part 1 End_*

*_(50)_*

 

……..Dire kofin da ke empty a hanun Tajwar Eshaan dai-dai da komawar Iffah daÉ“as zaune Æ™asan lallausan kafet É—in kamar wadda aka zarema dukkan numfashi. Ta matse jikinta tana mai Æ™oÆ™arin riÆ™e tsumar da takeyi tare da miÆ™ewa zumut. Ya kafeta da ido lips É—insa na É—an motsawa alamar son cewa wani abu amma jin kai da Æ™asaita ya hanashi yin hakan. Sai kawai yay Æ™oÆ™arin janyewa cike da basarwa amma hakan ya gagara. Shi kansa bai san yaya akai ba, bai san tayaya ba kawai ya samu kansa ne da riÆ™o hannunta. A tare suka rumtse ido bisa mabanbanta dalilai. Karan farko na fara tasirin dafin macizan da suka gama gauraye jininsa ya matsota a hankali garesa. Babu zato Iffah tajita saman jikinsa da ke fitar da wani irin sirrintaccen Æ™amshi mai karya zuciya. Numfashinta ne ya fisga da Æ™arfi kamar mai cutar Asthma, ta buÉ—e ido da sauri dan gaba É—aya hankalinta ya dawo jikinta. Zumbur ta mike jikinta na wani irin kaÉ—awa ta fara jan Æ™afafunta da baya-baya siraran hawaye da batasan na minene ba na rige-rigen sakkowa. Cikin son danne tashin hankalin dake cigaba da gauraye jijiyoyi da tsokar jikinsa ya É—ago idanunsa da launinsu har ya fara canjawa ya zuba mata, gab taci tuntuÉ“e da centre table, kaifin idanunsa da tasirin su gareta a wannan gaÉ“ar ya sata zubewa gaba É—ayanta akan tebirin…
Wata irin zufa ce ta fara keto masa a dukkan Æ™ofifin gashinsa, yayinda tun yana iya ganin Iffah a kusa da shi har ta fara masa nisa. (Tabbas a kwai matsala) ya ayyana a zuciyarsa yana mikewa da Æ™yar. Da kallo ta bishi zuciyarta na wani irin mahaukacin bugu tamkar zata buntsiro ta bakinta. Ganin ya shige ta miÆ™e itama cikin sassarfa, harta nufi Æ™ofa ta dakata, tamkar an janyo idanunta suka sauka kan computer É—insa, janyewa tai dan burinta tabar sashen kawai amma sai zuciyarta ta dinga ingizata ga computer É—in. Bayanta ta É—an waw-wai-gawa irin dai na rashin gaskiya kafin ta koma da baya ta zauna a kujerar tasa ta dasama rubutun fuskar computer É—in ido. A karan farko Æ™irjinta yay wani irin masifar motsawa. Tsabar kaÉ—uwa batama san takai hannu ga computer É—in ba har rawar jikinta na bayyana. Babu tantama saÆ™on data turama Ajmaal ne na karshe, kaÉ—an ya rage zuciyar Iffah ta É“aro waje a wannan gaÉ“ar, babu shiri ta fara sama dukkan saÆ™onin data tura masa ne babu ko É—aya daya goge, kowanne kuma babu canji a date É—in data tura ne. Ai babu shiri ta fito ta shiga settings É—insa na WhatsApp. A Profile É—insa, dp pic.. É—insa, da komai na dai Ajmaal É—in data sani ne… “Allahumma ajirni fi musibati wa’akhlifni khairin minha”. Iffah ta ambata a karon farko numfashinta na barazanar barin gangar jikinta, computer É—in tai Æ™oÆ™arin singumowa gaba É—aya dan maidata cinyarta akai rashin sa’a ta danna abinda bata sani ba kamar Æ™iftawar ido suuu ta shige cikin table É—in. ƘwaÆ™walwarta neman bugawa tayi tsabar rikicewa, ta shiga leÆ™e-leÆ™e a wajen sai dai babu abinda ta gane. Babu shiri ta zabura hanyar da Tajwar Eshaan ya bi tana haÉ—a hanya…..

A É“angaren Tajwar Eshaan kam da kyar ya iya kai kansa É—aki, dan jefa kafar kawai yake batare da yasan inda yake takawa ba. A Æ™asan lallausan carpet É—in É—akin ya zube yana mai jingina jikinsa da yay sharkaf da zufa jikin gado, duk wata addu’ar da tazo bakinsa ambata yake, a haka Iffah data gano É—akin da Æ™yar ta shigo a É—imauce. Idanunsa dake a lumshe ya buÉ—e a hankali suka sauka a kanta. Dukkan Æ™arfin halinsa da jarumta ya tattaro ya adana tashin hankalin da ke tattare da shi. A É“angaren ta itama ruÉ—anin da take ciki ya bada gudunmawa wajen makantar da ita yanayinsa, cikin rawar harshe idanunta dake tsiyayar hawaye a kansa ta durÆ™ushe É—an nesa da shi.
“Dan ALLAH na roÆ™eka ka faÉ—amin wanene kai? Miye alaÆ™ar ka da Ajmaal?!”.
Babu alamar zai tanka mata, sai dai idanunsa dake sake rinewa jajur na tsaye a kanta ƙyam. Tsahon wasu mintuna ya lumshe su da sake buɗe su a kanta yana cije lips ɗinsa. Ya kauda fuskarsa cike da ƙarfin hali, da son saisaita muryarsa, a maimakon ta samu amsar tambayarta sai saɓaninta ya fito da ga garesa.
“Ki canja madarar da kika bani da wadda ke akan dining. Hatta kofin da na sha daga cikinsa karki bari”. Ya Æ™are faÉ—a a wahale cikin cije baki da rumtse idanunsa.
(Iffah ki nutsu karki tonama kanki asiri) zuciyarta ta ayyana mata. Idanunta ta rumtse da karfi tana gyaÉ—a kai kamar wadda ake faÉ—amawa a cikin kunne. Sai kuma ta shiga goge hawayen nata da maida kallonta garesa a yanayin son kare kai.
“Ni ba batun madara na tambaye ka ba. Wanene Ajmaal?!!!”. Ta faÉ—a a matuÆ™ar tsawace.
Birkitattun idanunsa ya rumtse da Æ™arfi dan sam baya son hayaniya, balle ma a irin wannan halin da yake ciki a yanzu. Ya buÉ—esu kanta shima a fusace har sai da kallon cikinsu ya sakata zabura. Shima cikin tsawar da fisgar numfashi ya ce, “Babu abinda zai amfanar da ke a jin amsoshin da kike buÆ™ata a yanzu. Kije kiyi abinda nace!! Kije!!!!”.
Ba Æ™aramin firgici Iffah ta shiga da yanayin nasa ba. A zabure kuwa ta miÆ™e, batama san taya ta nufi Æ™ofa ba ganin kanta kawai tai a falo, harta nufi Æ™ofar lifter ta dawo da baya, tambulan É—in madarar ta É—auka, ta nufi dining wajen wanke hannu ta juyeta, kofin ta É—auraye jikinta nata Æ™yarma, gaba É—aya ta nema jarumtarta ta rasa, sai da ta tabbatar ya fita ta dawo kan dining É—in inda aka shirya break fast, madarar dake a jiye a wani tambulan ta É—aga ta juye a wanda ta wanke É—in, ta sake komawa ta wanke wannan, sai kuma ta rasa ina zata É“oyesa kamar yanda zuciyarta ke bata shawara. Da kyar ta samu nutsuwar samun wajen makalasa, ta dawo harta sake nufar hanyar fita ta sake dawowa da baya, kofin da ya sha madarar ne, shima É—auka tai ta wanke ta zuba sabuwar madarar ta kauraya ta maida inda ya sha. Sake nufar Æ™ofa tayi sai kuma ta sake dawowa ta nufi É—akin dai da ka ganta kasan tana a cikin halin É—imuwa….

A É“angaren Tajwar Eshaan kam tana fita tari ya sarkesa, jin saukar abu a tafin hannunsa da yake tare bakin ya sashi saurin kallon hannun. “Jini..” ya ambata a hankali saman lips, sai kuma ya saki wani irin wahalallen murmushi da mai da kansa ya kwantar jikin gadon yana ambaton “Sunci nasara, sun sami nasara ta dalilinki *_My Sohaa_*….” tari ya kuma sarÆ™esa a hankali, sai dai murmushin na nan maÆ™ale a fuskarsa har yanzu, sai faman lumshe idanunsa da suka birkice yake yana Æ™oÆ™arin buÉ—esu da Æ™yar fuskar Iffah da hawayenta ne tsaye Æ™yam a cikinsu. Ba mutuwa yake tsoro ba a yanzu, baya da Æ™urar da zai barta a ciki, ya tabbatar itace zata sha wahala, wahala irin wadda ba ita yay mata tanadi ba. Hakanne ya zaburar da shi, yaja jikinsa da ke saki gaba É—aya da Æ™yar zuwa telephone..
Ana É—agawa ya fara magana cikin son É“oye yanayin da yake ciki. “Duk wani cctv footage na safiyar yau zuwa yanzu na sashe na ka kwashe sa, amana ko kai na haramta maka ganinsa ka ajiyesa gareni, idan kuma na rasa raina ka damÆ™ashi ga Zawja Fareedah….”
Bai bada damar cewa komai ba ya yanke kiran, da Æ™yar ya maida akalar wani zuwa Malikat Bushirat….

*_MALIKAT BUSHIRAT_*

Yanayin tashin hankalin da masarautar ke ciki koma a ace Æ™asar baki É—aya dan yau mutanen da suka fito zanga-zanga akan murabus É—in Tajwar Eshaan sunfi na kullum yasa ko fita batayi. A kallo É—aya zaka iya Æ™irga damuwarta saman Æ™yakykywar fuskarta data koÉ—e matuÆ™a a cikin kwanaki ukun nan. Tayi duk wani Æ™oÆ™arin ta iya iyawa domin ganin gudan jininta amma al’amarin ya gagara. Kuka bata san iya adadin da tayi ba ba kuma ta san wanda zatayi a gaba ba, dan anzo gaÉ“ar da ko’a mafarki bata taÉ“a sakata a lissafin Æ™addararta ba…..
Shigowar kira a landline É—in É—akin barcin nata ya sata zabura dan yazo mata ne a bazata, dole ta ambaceshi da bazata dan Tajwar Eshaan ne kawai ke da wannan hurumin. Har tuntuÉ“e taci amma bata damuba ta caÉ“i kan wayar tunkan ta karasa gareta da Æ™yau. Rawar jikinta dana harshe na faruwa ne a lokaci guda, sai dai muryar data doki tsakkiyar dodon kunnenta ta saka numfashinta tsaiwar wucin gadi….
“Ammie!…”
Aka faɗa da ƙyar cikin kuma rawar harshe mai fidda sautin nakasashshiyar murya mai tabbatar da amon razani ga mai saurare.
“Saiful-malik!!…”
Ta ambata itama tare da fisgar numfashinta dake kaikawo a iya maÆ™oshinta zuwa cikin baki kawai. Shi bai sauka a huhu ba, bai kuma fita ta hanci ba. Bata ma san ta saki wayar ba ta fice…
“Ya ALLAH Akia!…”
Jasrah dake shigowa ta faÉ—a da sauri tana riÆ™o Malikat Bushirat da gaba É—aya idonta ya rufe da ruÉ—ani. Son Æ™wacewa take tana ambaton “Eshaan.. Jasrah Eshaan.. Eshaan zasu kashe min shi”.
Sam Jasrah bata fahimci inda Æ´ar uwar tata ta dosa ba, dan haka tai saurin katseta da faÉ—in, “Na shiga uku Akia dan ALLAH nutsu kimin bayani, mi ya dakesa?”.
Ina Malikat Bushirat ta kasa amsata, dan numfashinta ma har ya fara fisga. Bata haÉ—a soyayyar Tajwar Eshaan da komai ba a duniya. Tana masa wani irin makahon so mai wahalar fahimta. Duk yanda Jasrah taso tanÆ™warata ta kasa, sunan Eshaan kawai take ambata da son fisgewa ta fita. Bazai yiwu ta barta ta fita a haka ba, dan haka tai saurin danna Æ™ofar bedroom É—in da Æ™afa. HankaÉ—ata Malikat Bushirat tayi, duk da taji zafi dama gata ba wani Æ™warin jikin take ji ba amma haka ta daure ta murza key. Da Æ™yar ta iya zarewa ta sake riÆ™o Malikat Bushirat tana mai fashewa da kuka. “Akia dan ALLAH ki sanar min, fitarki a haka ba itace mafita ba, idan ma akan masu zanga-zanga É—in nan ne ki kwantar da hankalinki jami’an tsaro bazasu barsu su É“alla koda gate na farko ba……..”
“Jasrah ki fahimceni…..!!!”
Malikat Bushirat ta katseta cikin Æ™araji sai kuma ta fashe da kuka. Tabbas babu lafiya, Æ´ar uwarta a haka lallai akwai matsala. Har taune harshe take wajen ambaton, “Zan fahimceki faÉ—amin ko a taÆ™aice ne Akia dan ALLAH”.
Da Æ™yar Malikat Bushirat ta sanar mata a dunÆ™ule, nan fa hankalin Jasrah ya tashi itama babu shiri ta zabura ta buÉ—e Æ™ofar……

★★….

SuÉ“ucewar kan wayar a hannun Tajwar Eshaan dai-dai da sake faÉ—owar Iffah É—akin a birkice. Gaba É—aya ma ta mance matsayinsa da nata, tai kansa babu alamar hankalinta na tare da gangar jikinta. Tana zubewa gabansa yana faÉ—owa jikinta hannunsa dafe da kansa yana ambaton “Ammie…” a hankali, ga wata irin zufar da tai masa sharkaf kai kace wanka yay a lokacin.
“Na shiga uku ni Fhareedah!”. Da Iffah ta faÉ—a cikin kuka ya saka shi É—ago idanunsa dake matukar jazur zattashin hankali. Akanta ya tsaidasu a wani irin bahagon yanayi, ya lumshesu da Æ™yar ya sake buÉ—ewa a kanta. Lips É—insa da suka koma jajur saÉ“anin pink a da suna motsa a hankali ya saki wani wahalallen murmushi da har Iffah ta koma ga ALLAH bazata taÉ“a mantawa ba, dan ya zauna a allon zuciyarta tamkar rubutu akan dutse. kafin idon nasa ya koma ya lumshe gaba É—aya tattausan hanunsa na dama saÆ™ale cikin nata da bata san sanda ya riÆ™o ba………..✍️

*_ALHAMDULLAHI!!_*

Ina godiga ga ALLAH daya bani ikon kawo ƙarshen littafin DAUƊAR GORA CIKI KA SHATA kashi na farƙo. Ina roƙon UBANGIJI ya bani tsahon rai da lafiya ni da ku har zuwa bayan salla da zan ɗora kashi na biyu insha ALLAHU. Ina mai baku haƙuri da ƙari saman haƙuri da tangarɗa da jinkiri da aka samu duk da Alhamdullah ban taɓa fashin posting ba, sai dai labarin yayi tafiyar hawainiya saboda yanayi, hakan ta samune dalilin babban dalili daya shafi uzirin rayuwata. Insha ALLAHU bayan salla zakuga canji ayi haƙuri amin afuwa dan ALLAH yau da gobe kenan kun san Bilyn taku ba haka takeba a da..

Himmm!! Ban san ma mizan ce mukuba daga Æ™arshe, amma ku sani DAUÆŠAR GORA part 2 zai zama na musamman ne da salo mai….. (hummm badai sai nace komai ba..)

★Yaya kuke tunanin rayuwar Iffah zata kasance ne?.

★Mizai faru da Tajwar Eshaan zai mutu ne kokuwa?.

★Waye saurayin daya kwamushe su Kaka?.

★Taya Tajwar Eshaan ya zama Ajmaal?.

★Wacece ta Æ™urya?.

★Miran Jasim da Miran Arshaan zasu ci nasara?.

★Anya Æ´an Æ™asar ruman akwai mai iya kwantar da fushinsu a wannan gaÉ“ar?.

★Yaya makomar su Babiy da Barrister?.

Kai tambayoyin da yawa suke karna cikaku da zance Ni ban baku cigaba ba. Kudai kawai muyi addu’ar ALLAH ya kaimu a gama azumi lafiya. Ya rabbi kasa muyi karÉ“aÉ“É“iyar ibada.

Ina ƙaunarku masoya, zan cigaba da ƙaunarku kuma. Duk wanda ya soni domin ALLAH shima ALLAH ya soshi haka.

Taku Bilyn Abdull ce.

 

*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*

*DAUDAR GORA Billyn abdul*

*KI KULANI hafsat xoxo*

*A RUBUCE TAKE Huguma*

*RUMBUN K’AYA Hafsat rano*

*IDON NERA Mamuh ghee*

_LITTAFI DAYA: 400_
_LITTAFI BIYU: 600_
_LITTAFI UKU: 800_
_LITTAFI HUDU :1000_
_LITTAFI BIYAR: 1200_

_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_

_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_

_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_

_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_

_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_

_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_

ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN

MARYAM SANI
ACCESS BANK
0022419171

SAI A TURA SHAIDAR BIYAN

09033181070

IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA

09166221261

ÆŠ ✨
( )

 

 

Post a Comment

0 Comments