Daudar Gora Book 1 Page 6

Latest Posts

6/recent/ticker-posts

Ad Space

Daudar Gora Book 1 Page 6


……Baki ta murguÉ—a da juya idanunta farare tas tamkar madara cikin nasa da ya kafeta da su. “Inma kai mayene to wlhy bazan ciyu ba, Babiy kullum addu’a yake min shi da Ummu”. Tana gama faÉ—a tabar wajen.
Yaransa na waccan ranar ne dai yau ma a tare da shi. Kuma suma sarai kalaman Iffah da bazasu manta muryarta da wuri ba ta shiga cikin kunnuwansu. Dama sune suke dubama yaran dake tare da su books ɗin, shi ko yana biye da su ne kawai da binsu da idanu. Ɗaya daga cikin yaranne ya nuna littafin da Iffah ta ɗauka, su kuma kasancewar suna ɗakkoma sauranne sai shi da kansa yay yunƙurin ɗakkowa kafin su suyi hakan. Yunƙurin zagayowa wajen Iffah ɗaya daga cikin yaransa yayi, dan yay alƙawarin yau sai ya daddala mata mari, amma sai ya dakatar da shi ta hanyar yima ɗayan alamar ya tsayar da shi da ido. Da sauri wancan da shima yake jin kamar suje su haɗu su faffasa mata baki ya kira sunan wancan.
“Azaan!”.
Cak ya tsaya tare da rumtse ido da cije baki dan yasan dai ogane zaisa Fakhir ɗin ya dakatar da shi. Gashi harya hango Iffah dake gaban mai biyan kuɗi. Dole ya haƙura badan yaso ba, amma yaci alwashin duk randa suka sake haɗuwa da yarinyar can babu oga sai ya mata karyawar gasashshiyar masara danta tabbatar itace zata gujema haɗuwarsu ba su ba kamar yanda ta faɗa.
Iffah dai tuni ta biya kuÉ—in littafi daya cinye mata duka kuÉ—inta babu ko na bawa mai Mototaxi (napep). Sai mita take a ranta Littafin yayi tsada, koda ta fito ta iske mai Mototaxi ya cika yayi taf. Tana isowa inda yake hannu kawai ya miÆ™a mata alamar ta bashi kuÉ—insa ya wuce. Fuska ta Æ™yaÉ“e ta cikin niÆ™ab É—inta tana wani kif-kif da idanunta da kawai yake gani. “Oh oh kaiko duk daÉ—in asara ai ta jira samu ko? Idan mukaje inda zani nace maka bazan biyaka bane?”.
A fusace yana mai dalla mata harara yace, “Na fasa kaiki, dalla malama bani kuÉ—ina kije ki hau wata. Kuma har na zaman danai anan sai kin haÉ—amun”.
“Lallai sannu shugaban É“arayin Ruman. Saboda Babiy yamun baki ko? Idan kaga zaka É—aukeni muje na baka kuÉ—inka ka daukeni, in kuma zaka zauna wage baki kana ihu ne na tare wata na hau ka biyoni a baya dan bani da shi anan sai naje gida”.
“Baki da hankali”. Mai Mototaxi ya faÉ—a a matuÆ™ar fusace yana fitowa. Harga ALLAH Iffah ta tsorata, dan tasan wannan mai zubin samudawan Æ™arnin farkon fyaÉ—a daya zai bazar da itane a titin nan sai dai a kaima su Ummu gawarta. Amma tsabar Æ™arfin hali sai faman fiki-fiki take da idanu da faÉ—in, “To sai kayi duk abinda ma zakayi mana”.
“Hakama kika ce?”. Ya faÉ—a yana matsota. Jikinta taja baya tana wani zazzaro masa manyan idanunta masu matuÆ™ar sheÆ™i tamkar ta tara ruwan hawaye a ciki, “Idan hanunka ya taÉ“a koda abayar jikina sai na É“allashi! Idan kuma ka isa ka gwada”.
“Kan uban can kayyasa, ke yarinyar nan kin san wanene ni kuwa? To dan ALLAH gwada É“allamin hanun nagani”. Ya faÉ—a yana yo kanta da gaske. Securitys É—in dake a bakin bookshop É—inne sukai saurin taresa, dama dai ganinsu yasa Iffah wannan hura hancin, ganin ta samu yanda takeso baki ya Æ™ara buÉ—ewa ta buÉ—e baki zata cigaba da tsiwa idanunta suka sauka a kan mutumin nan. Yanayin takunsa na isa da Æ™asaita kawai saka rawa a zuciyar Iffah yake, sai dai kasancewarta yarinya mai Æ™arfin halin tsiya da rashin son a ga gazawarta yasa baka isa ganin wannan tsoron ba a kan fuskarta. Janye idanunta tayi tamkar bata gansa ba, shima sai ya cigaba da takowa tamkar bai ganta É—in ba yaransa da tawagar yara kusan goma sha biyar biye da su. Kamar waccan ranar yau ma sanye yake cikin suit da sukai matuÆ™ar fidda Æ™yawun halittarsa ta tsayayyen mutum, saÉ“anin ranar na yau baÆ™aÆ™e ne, sai dai sunyi matuÆ™ar dacewa da lallausar farar fatarsa mai matuÆ™ar sheÆ™i da É—aukar idon mai kallo. Ga mayataccen Æ™amshinsa irin na ranar mai saka zuciyar mai shaÆ™a raunana da nutsuwa. Harya gotasu zai wuce a binsa sai kuma ya tsaya cak, hannayensa duk biyu ya zuba a aljihun wandonsa tare da juyowa. Ita ya fara kallo, sai kuma ya janye lulu idanunsa masu tabbatar da kwarjininsa da kamewarsa ga duk wanda ya kallesu ya maida kan securitys É—in nan dake riÆ™e da mai Mototaxi É—in har yanzu. Azaan daya fahimci mi ogan nasu ke nufi yay saurin faÉ—in “ku sakesa” duk da har cikin rai baiso hakan ba. Babu musu suka sakesa, shiko sai huci yake idonsa akan Iffah data juyar da kai gefe irin bata sanma mi’ake É—in nan ba. Hanunsa É—aya ya zare daga cikin aljihunsa ya É—an É—aga rigar suit É—in tasa. KuÉ—ine masu yawa ya zaro ya miÆ™ama mai Mototaxi É—in. Cikin rawar jiki ya kai rissine kamar gwiwarsa zata taÉ“a Æ™asa ya amsa yana godiya kamar zai haÉ—iye harshensa. Kansa kawai ya É—auke zai juya suka sake haÉ—a ido da Iffah. Baki ta tura gaba tana fiki-fiki da idanu da sake É—auke kanta…
Takaici kamar ya kashe su Azaan. Babu wanda a cikinsu bai harari Iffah ba kafin subi bayan ogansu da tuni yabar wajen. Mai Mototaxi da bakinsa ke washe uwa gonar audiga ya kalla Iffah. “A to hajjaju taho na kaiki koda karshen Daular Ruman ne ma”. Wata banzar harara ta balla masa da jan tsaki tabar wajen. Cike da takunta na nutsuwa ta gitta motarsu dake Æ™oÆ™arin barin wajen. Azzan yay Æ™aramar Æ™wafa, a ransa yana raya shine zai zama sanadin nakasa yarinyar nan kuwa wataran. Mai gayya mai aiki kam da gaba É—aya zuciyarsa ta gama tabbatar masa yarinyar nan aljanar ce idanunsa ya lumshe a hankali yana mai Æ™ara gyara zamansa na Æ™asaita tamkar ba’a mota yake ba….

Tunda ta samu wata Mototaxi É—in ta shiga zuciyarta ta tafi tunani. A karan farko take tambayar kanta waye wai wannan mutumin a garin nan?, da ganinsa dai kasan É—an masu farcen susu ne ko shi a karan kansa ne mai farcen susar. A Æ™asan zuciyarta taji tana buÆ™atar sanin shi É—in wanene badan wani abu nasa ya birgeta ba. Hasalima haka kawai haushinsa takeji tun akan bige yaron nan da suka kusa yi a waccan ranar da Æ™oÆ™arin guduwa da sukai. Ko kuma ma dai aljanin ne?, dan inba aljani ba taya zata dinga ganinsa duk inda taje gashi har karo biyu.. Tasha ji a bakin mutane ana faÉ—in ita É—in Æ™yaÆ™yaÆ™yawa ce, tafi kowa Æ™yau a gidansu, amma Æ™yawun wannan bawa da dirarriyar halittar jiki data fuska mai cike da kwantaccen gashi tamkar shiya zaÉ“ama kansa komai sai dai aljanin kam….. Isowarsu anguwarsu ya sata ture tunanin ta nunama mai Mototaxi inda zasu Æ™arasa ta amso masa kuÉ—insa. Cikin sa’a suna isa Æ™ofar gidansu sai ga Babiy da Hanash suma an saukesu da alama yanzun ne suke dawowa. Su suka biya mai Mototaxi É—in kafin su shige cikin gidan bakinta washe tana jera musu sannu da zuwa…

Labarin alkairin da aka samu na kayan da suka kai kasuwa su Babiy ke basu ita da Ummu, amma ita rabin hankalinta naga abinda take yunÆ™urin yine kawai. Ta matuÆ™ar Æ™agara ai kiran sallar magrib su Babiy su fice masallaci Ummu ta shiga É—aki. Ana kwaÉ—a kiran salla kuwa itace farkon miÆ™ewa yin haramar alwala. Hakan da tai baisa wani yaji daban ba dan kowa yasan Iffah da himmar yin salla. Komi take aka kira salla, ko’a ina take inhar wajen zaiyi ibada zata ajiye abinda takeyi kuwa tayi sallar. Wannan halin nata na Æ™ara sakama iyayenta da Æ´an uwanta sonta, dan tunsu Arfa na raye ma sukansu Ummu takan zaburar dasu akan halin Iffah É—in na kiyaye ibada da Æ™oÆ™arin yinta akan lokaci. Koda ta shiga É—akin bayan tayi alwala bakin gadonsu takai zaune dan tana fashin salla ne, sai da taji tsakar gidan yayi tsitt sannan ta É—an leÆ™o, babu kowa kuwa Ummu ta shige su Hanash sun fita massallaci. Da sanÉ—a ta fito ledar maganinta na É—azu da taketa É“oyo riÆ™e a hanunta. Wuff ta afka É—akin Babiy, cikin sa’a bata wani sha wahalar ganin tulunan da aka cika da zuma ba sabbi Æ™al. Ta saki murmushi dajin kamar tai ihu dan farin cikin da takeji a zuciyarta. Amma sai ta kanne cikin rawar jiki da É—an yin leÆ™e-leÆ™e irin na mai tsoron a kamasa yana laifi tana Æ™oÆ™arin buÉ—e kwalbar. A tulun farko ta zuba kusan rabi, sai kuma ta dakata bisa shawarar zuciyarta akan ta zuba duka tunda bata da tabbacin dukansu Tajwar É—inne zaiyi amfani da su. Ƙaramin sandan data shigo da shi tasa ta motsa da Æ™yau har saida ta tabbatar ya gauraye sannan ta sakama É—aya, tana tsaka da juyawa ta tsinkayo muryar Ummu na kiranta. Ido ta rumtse da sauri tana ambatar sunan ALLAH, da hanzari ta shiga rufe roban sauran maganin saboda jin kamar Ummu na nufi É—akin, cikin riga ta saÆ™a maganin da sandar sannan taÉ—an leÆ™o. Can ta hango Ummu ta nufi kitchen É—insu, aiko tai wuff ta fito ta faÉ—a É—akinsu. Ummu data juyo saboda jin kamar motsi ta sake Æ™wala mata kira. Yanzu kam amsawa tai da fitowa tana gyara mayafin abayarta.
“Yi haÆ™uri Ummu ina karatune”.
“Shine kuma bazaki mun ko gyaran murya ba zaki barni ina wage baki”.
“Kiyi haÆ™uri to Ummuna”.
Ummu ta fito daga kitchen É—in tana gyara mayafin jikinta itama. “Jeki ki cigaba da karatunki dama motsi naji kamar, amma fara duba kosu Hanash sun bar mana Æ™ofa buÉ—e ne”.
Da to Iffah ta amsa tana nufar hanyar soro da sauke ajiyar zuciya…

Tana shiga É—aki wani uban tsalle tai ta dirga saman gadonsu dan farin ciki. Mulmula take tana dariya irin wadda ta jima batayi ba, wauta da Æ™uruciyarta tafi hango mata nasararta na É—aukar fansar Æ´an uwanta fiye da tunanin idan wani abu ya faru Babiy ne na farkon wanda za’a tuhuma kasancewar zumar daga hanunsa ta fito. Haka Iffah ta Æ™arasa wannan dare cike da zumiÉ—in ganin wayewar gari Babiy ya kai zuma masarauta.
Bayan ta idar da salla yau ko fama da ita Ummu batai ba akan shirin tafiya makaranta, a da kuwa saita tasota daÆ™yar kasancewarta mai son barcin safen tsiya da tayi salla take komawa barci. Babiy kansa saida yay mamakin wannan sammakon tashi nata yau, Hanash kam kasa haÆ™uri yay saida yay magana. Sai cewa tai ai sunada program ne a makaranta yau… Koda taje makaramtar ma dai bawai ta nutsu bane, rabin hankalinta ne kawai ga duk malamin daya kasance da su har aka tashi.

★A É“angaren Babiy kam duk da tabon da masarauta daular ruman ta bar masa a zuciya bai taÉ“aji koda wani zai bari ya cutar da su ta hanyarsa ba ko shi ya aikata hakan ta damar dake hanunsa na kai musu zuma. Tsaf yay shirinsa kasancewar yau juma’a ce ya É—iba tulunan zumar nan guda uku ya nufi daular ruman. Idan yaje ba kaitsaye yake É—aukar zumar nan ya kai ga Tajwar ba, dan ganin Tajwar kam babban abune da sai wanda ya cika ya tumbatsa keda wannan damar. Akwai wanda keda alhakin amsarta shi ya isar da ita inda ya dace har ta isa ga sashen Tajwar É—in. Bayan Æ´an bincike a kansa na kullum da basa Æ™arewa ya shiga daular ruman iya Æ™ofa ta biyu. Dattijo da kamanni da suturar jikinsa kawai ta isa tabbatar maka da shima wanine ya iso ga Babiy bayan zaman jiran kusan mintuna goma da yayi. Cikin girmamawa Babiy ya gaidashi duk da zasu iya zama kusan sa’anni da shi. Shiko ya amsa yana hura hanci irin na masu dama ta mulki a hannu. Umarni ya bama Babiy akan ya É—anÉ—ana zumar, Babiy da yasan babu wani abu na razani ko shiga dogon tunani kafin É—anÉ—anawar kansa tsaye ya kai hannu ya É—auka cokali dake bisa tire a hanun hadimin dake biye da dattijon nan. Tunda dama haka ba sabon abu bane garesa duk sanda ya kawo sai ya É—anÉ—ana É—in. Tulun farko ya kwancema baki kasancewar a É—aure bakin yake da ganyen ayaba, yasa cokalin nan ya É—ibo zumar da bismillah ya nufi bakinsa………✍

*_Iffahhhhhh!!!!._*

*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*

*DAUDAR GORA Billyn abdul*

*KI KULANI hafsat xoxo*

*A RUBUCE TAKE Huguma*

*RUMBUN K’AYA Hafsat rano*

*IDON NERA Mamuh ghee*

_LITTAFI DAYA: 400_
_LITTAFI BIYU: 600_
_LITTAFI UKU: 800_
_LITTAFI HUDU :1000_
_LITTAFI BIYAR: 1200_

_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_

_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_

_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_

_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_

_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_

_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_

ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN

MARYAM SANI
ACCESS BANK
0022419171

SAI A TURA SHAIDAR BIYAN

09033181070

IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA

09166221261

*ƳAN ƘASAR NIGER. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*

+2290165991

Books biyar 1250CFA
Books hudu 1050CFA
Books uku 850CFA
Books biyu 650CFA
Bookk daya 450CFA

KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.

MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.

 

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*

✨ÆŠ ✨
( )

 

Post a Comment

0 Comments