Daudar Gora Book 1 Page 8

Latest Posts

6/recent/ticker-posts

Ad Space

Daudar Gora Book 1 Page 8


_8_*

……….Zaune takai a kujerar dake duban tasa tana mai kallon agogon hanunanta. Ya saki murmushi cikin kafeta da idanu. “Daga zuwa sai duba agogo?”.
“Hakan dolene Sir, domin ko lokacin islamiyya zan cinye anan. Kaga kenan sai da tsantseni”.
“Okay”.
Ya faÉ—a yana gyara zamansa. “Ba buÆ™atar maimaita abinda ya faru baya, na gaba kawai yanzu shine zanyi iya Æ™oÆ™arin ganin na haÉ—u da abokin nawa koda ta waya ne, kin san aikin nan nasu yana hanasu samun isashen lokaci matuÆ™a kasancewarsu manya dake tare da babbar kafar yaÉ—a labarai mai aiki da kamar duniya gaba É—aya. Ke yanzu a gareki miye shirinki?”.
KafaÉ—a Iffah ta É—an É—age cikin jan iska da hurowa. “Kusan dukan shirina a kammale yake, burina kawai nasamu yin hira da African Aye️‍”. “Indai hakane haÉ—uwa da abokina kawai ya rage mana, fatana dai bayan ni kar wanda yasan wannan hatta a gidanku, inba hakaba zamu iya shiga haÉ—arin da har burin rayuwarmu ma bazai cikaba bayan wannan. Nikuma zanyi duk yanda zanyi insha ALLAHU wajen hana wannan sirrin fita daga gareni….”
“Shi abokinka É—in fa?”.
“Baki da matsala da shi domin shi aikinsa ne”.
Kai ta jinjina masa fuskata cike da murmushi. Sai kuma ta rissinar da idanunta alamar jin kunyarsa saboda kallon daya kafeta da shi. Kunyar nada nasaba da tuna yanda ta dinga wancakalar da shi da manufarsa a sanda yake malaminta. Sai gashi shine na farko data fara tunkara da matsalata a yanzu duk da kuwa tana kallonta a kan matsalar data shafi kowa na ƙasar Ruman ne. Sautin murmushinsa ya sakata ɗagowa ta ɗan kallesa, sai kuma ta sake kauda kanta gefe itama tana murmushin.
“Hummm!”
Ya faÉ—a yana miÆ™ewa. Itama miÆ™ewar tayi batare data yarda sun sake haÉ—a ido ba. “Kije gida zamuyi waya”.
“Nagode sir, ALLAH ya tsare gabanka da bayanka”.
Jin sautin murmushinsa ya tabbatar mata jin daÉ—insa, amma sai tai gaba da sassarfa tunkan ya sake cewa komai……..

★__________________★

*_DAULAR RUMAN (MASARAUTA)_*

Katafaren É—aki mai É—auke da Æ™ayatattun kayan more rayuwa, kwance take bisa lafiyayyen gado da dukkan nau’in shimfiÉ—unsa suka kasance na alfarma. Sautin dariyar dake tashi cikin kunnuwanta tamkar mafarki ya sata buÉ—e idanu, cikin tsumar jiki ta ture lallausan bargon da take ciki, tamkar walÆ™iya ta dire Æ™asan lafiyayyen kafet É—in dake malale gaban gadon tai kneel down tamkar mai neman gafara, kanta a risine alamar nuna tsantsar girmamawa…..
Tamkar shirin film ko labaran almara tsohuwa tukuf sanye cikin jajayen kaya ta bayyana bisa baÆ™ar kujerar Æ™arfe mai É—auke da adon gold a cikin É—akin. BaÆ™ace matuÆ™a mai tsananin muni da jajayen idanu, yanda ta zauna Æ™afa a harÉ—e kai ka É—auka itace Shahanshan É—in…..
“Lafiya da tsahon rai su Æ™ara kasancewa a rayuwar *_Uwa_* mai share kukan masu kuka”. HamshaÆ™iyar matar ta faÉ—a cikin tsantsar girmamawa ga tsohuwar dake harÉ—e saman kujerar tata tamkar sarauniyar ingila.
Cike da isa da Æ™asaita tsohuwar taja wani kakkauran numfashi da sake faÉ—aÉ—a girman Æ™ofofin hancinta ta hanyar hurashi, Æ™ara harÉ—e Æ™afafunta tai tana mai motsa yatsun hanunta, idanunta jajaye kafe akan matar. Cike da isa da Æ™asaita mai É—auke da rashin daÉ—in muryarta ta tsufa ta fara magana. “Ta-Æ™urya kin kusa cin nasara wajen cika sharaÉ—i na biyu akan alÆ™awarinmu. Na tayaki murna, saura sharaÉ—inki na Æ™arshe, mafi wahala a cikinsu”.
Ƙasa ta Æ™arayi da kanta cike da girmamawa a gareta, da dukkan Æ™arfin zuciyarta ta furta, “Kece madubin nasarata Uwa!, duk inda akaga naje da jagorancinki na isa. Yanda na cika na farko shima na biyu zan cika sa, nayi alÆ™awarin cika na Æ™arshe ma fiye da yanda kike tsammani…..”
Jajayen idanunta masu kama da garwashin wutar gidan biredi ta É—ago tana kallon Æ™yaÆ™yÆ™yawar kuma hamshaÆ™iyar matar dake gurfane a gabanta. Ta Æ™yalÆ™yale da wata dariya mara daÉ—in saurare ga kunen kowa, sai kuma ta gimtse tamkar ba ita tayi ba tana zaro manyan jajayen idanunta kamar na dodanni. “Ta-Æ™urya nasan zaki iya, sai dai akwai wani babban Æ™alubale dake tunkaro cikar nasararki ta biyu, kuma gab yake da cimmawa, idan baki gaggauta datsesa ba, zakiyi biyu babu”.
A razane ta É—ago tana kallonta cikeda bushewar zuciya, sai kuma ta maida kanta da sauri ta rissinar “A gafarceni Uwa, a kawar da ko miye mai son yima cikar burina kutse. Na rantse da ALLAH daya halicceni, koda cikin yankin ahalina ne bana buÆ™atar numfashinsa Uwa!!”.
Dariya ta sake Æ™yalÆ™yalewa da shi sai kuma ta gimtse fuska. Kanta ta shiga girgiza mata da dukkan isa. “Ta-Æ™urya wannan karon akwai banbanci da koyaushe, dama na taÉ“a faÉ—a miki bayan cikar nasararki ta farko akwai Æ™alubale dana gani akan cikar ta biyu, sai dai ba’a buÉ—e mun komaiba a wancan lokacin, alamar haka na nuna Æ™arfin taurarin mai yunÆ™urin, amma a daren jiya dana tsananta bincike akan mafarkinki na gano wani yanki da Æ™yar. Ƴar shilar suda na Æ™oÆ™arin yin cara irin ta gawurtattun zakaru a kunnen bututu da taimakon wata zuciya mai son kusantar tata.”
“A taimakeni a kawar mun dasu gaba É—ayansu Uwa. Ko a bani damar kawar da su da kaina”.
“Hhhhhhh!!!! Ƙaddarar Æ´ar shilar bata mutuwa bace cikin sauÆ™i. Tana kuma da Æ™arfin taurarin da zata iya cin nasarar dusashe naki”.
Bugawar da Æ™irjinta yayi ta zata zuciyarta ce zata fito ta bakinta dan tsabar razana. Ta kafeta da idanu cikin wani irin yanayi mai wahalar fassara. Sai kuma tai saurin maida kanta Æ™asa ta rissinar tana faÉ—in, “A gafarceni Uwa”.
Wani irin kakkauran numfashi mai cike da gargaÉ—i tsohuwar taja, cike da Æ™asaita tana yamutse mummunar fuskarta ta cigaba da faÉ—in, “Zamu iya samun mafita sai dai akwai ruÉ—ani a cikinta. Har zuwa yanzu kuma ban samu buÉ—ewar ruÉ—anin ba kai tsaye. Dan haka kina da zaÉ“i biyu. Kodai ki Æ™ara yin duk yanda zakiyi igiya ta Æ™ullu tsakanin Malik-alMuluk da wannan Æ´ar shila muyi duk yanda zamuyi tazama cikamakin aikinmu na biyu, ko kuma ki barta ta cimma burinta…….”
Idanunta da suka kaÉ—a jajur tai Æ™oÆ™arin É—agowa, sai dai ta maidasu da sauri zuwa Æ™asa. “Uwa amma kin faÉ—amin na cinye jarabawa ta biyu da zarar ya aura cika makin matansa shine matakan nasarata, yanzu haka akwai su su biyu da suka rage É—auke da aurensa a kansu, zasu miÆ™asu garesa a karshen watannin nan kamar yanda na samu tabbaci. Taya zamu shigo da wata bayan aikin ya cika. A yanzu ya rage kawai samun cikar burina na Æ™arshe ne a kansa. Miye dalilin shigowar wannan yarinyar abinda bai shafeta ba? Mizai hana ai mata wani hukuncin daya dace da ita?…”
Hannu ta É—aga mata cikin tarar numfashi da Æ´ar hasala-hasala, da kakkausar murya tana mai nunata da É—anyatsa “Amma har yanzu ban sanar dake wadda ta dace ba, kuma damun san cutarwace na umarninmu gareki bazamu ce ta shigo ba”.
“Hakane Uwa, a gafarce ni. Sai dai Mahaifiyar Zak…….”.
Ta faɗa da alamun shiga tashin hankali mai girma, amma kallon da Uwa ta watso amata ya hanata ƙarasawa.
Bata tanka mata ba, sai dai yanayinta ya nuna a hasale take, dan cikin kaushin murya da zunzurutun jin zafi ta kaÉ—a Æ™ahon hanunta mai kama da kwarkwaron gidan dodon koÉ—i. A take haske ya gilma, sai ga farar takarda a hanunta. “Ƴar shila burinta shine É—aukar fansa, domin biyu a cikin masu É—akin Malik-alMuluk da suka shuÉ—e jininta ne. Burinta shine bin kadin jininsu ta hanyar bayyanama duniya ko kawar da shi. Bayyanawar tata kafin cikar burinki faÉ—uwarki ne, a yanzu haka kuma ta haÉ—u da mai taimaka matan harma sun gama magana”.
Sosai zuciyarta ta Æ™ara harzuÆ™owa. Amma sai batace komai ba saboda ganin Uwa a hasale take da ita. Cikin yin Æ™ara Æ™asa da kai tace, “Da ace bayan cikar burina ne kauÉ—i da Æ™udirin É—aukar fansar wannan yarinya ya shigo haske ne ga cikar burina. Dan zata Æ™arasamin aikin Æ™arshe da zanyi. Amma tunda ta shigo a tsakkiyar labarina dolene ta fuskanci hukuncin daya dace da ita. Idan ita bazata mutun ba shi a kawar min da shi mana Uwa”.
“Hakan mai sauÆ™i ne, sai dai shima babu buÆ™atar mutuwarsa, dan zai iya mana amfani a gaba. Sannan shi rabata da shi shine mafi Æ™ololuwar hukuncinsa. Dan haka daga nan zuwa safiyar kowace juma’a ta Æ™arshen shekarar nan ki tabbatar an zarga igiya tsakaninta da Malik-alMuluk, a dakatar da kai masa matan da suka rage a kaita garesa bayan tarewa, dan da ita zamu cigaba da amfani har samuwar cikar burinmu ga kowa!!.”
Da sauri ta É—ago kai jin muryar nayin nesa da ita, sai dai kafin ta iya furta wani abu Uwa ta É“ace daga É—akin tamkar guntun girgijen hadari a tsakkiyar fararen gizagizai. Zumbur ta miÆ™e tana mai dafe kanta dake sara mata, wani irin tuÆ™uÆ™i da Æ™aiÆ™ayin mai zafafa ruhi zuciyarta ke mata. Sai dai sanin wacece Uwa ya sata jin É—an sassauci kaÉ—an, amma ruÉ—ani mai É—auke da abubuwa masu matuÆ™ar yawan gaske da fassarasu a É—auka shekara dubu bisa dubu ba’a kammala ba na neman danne wancan Æ™warin gwiwar. Taya ruhin Æ´aÆ´an sarakunan Æ™asar Ruman basu bata matsala ba sai Æ´ar talakawa Æ™asÆ™antattu? Dolene yarinyar nan ta É—anÉ—ana kuÉ—arta na hukuncin shiga gonar daba tata ba Æ™warai da gaske, sai tayi wasa da ita a tsakkiyar titi wasa irin na É“era a hanun mage, dan ko ita Malikat bata isaba…..

(Tofa masu karatu, ita kuma wannan wacece ita? Iffah fa ta taro match É—in da babu players. Kumuje zuwa dai muga yaya wasan zai kaya…)

★__________________★

*_IFFAH_*

A ɗan firgice ta buɗe idanunta tare da tura hannu ƙarƙashin filon data tada kai ta sake danne wayar dake faman ɓurari cike da tsoron kar Ummu ta jiyo, dan tasan Babiy da Hanash basa gidan. Ajiyar zuciya ta sauke mai matuƙar ƙarfi da zaro wayar, cikin rawar jiki ta dannata a silent. Tamkar jira kiran ya sake shigowa kuwa. Idanunta masu matuƙar girma da haske ta waro sosai ganin mai kiran, ai batama bari tayi ring na biyu ba taa ɗaga tare da kaiwa kunnenta tana direwa a gadon.
“Kina jina?”.
Aka faɗa daga can. Kanta ta jinjina masa tamkar tana gabansa dai-dai tana leƙawa tsakar gidansu. Daga can gefen da Babiy ke kiwon tsuntsaye ta hango Ummu, dan haka ta sauke ajiyar numfashi da fara magana cikin raɗa.
“Ina jinka Sir! Ta samu ne?”.
“Babu lokacin dogon magana Iffah, kiyi Æ™oÆ™ari daga nan zuwa awa É—aya ki sameni, dan kuwa mun tsinta dami a kala Ajmal ya shigo Ruman, kuma a yanzu haka mun gama magana da shi sai dai ban sanar masa ainahin zancen ba, ya kuma buÆ™aci haÉ—uwa dake…..”
“Ya ALLAH! Alhmdllhi. Naji daÉ—i matuÆ™a wlhy Sir. Insha ALLAHU duk yanda zanyi kuwa zan fito ka saurare ni”.
“Okay”.
Kawai ya faÉ—a yana mai yanke wayar. Itama shiri ta shiga faman yi a gaggauce, tare da tattare takardun dukkan bayanai data tattara waje É—aya. Bakinta É—auke da addu’ar samun nasarar amincewar Ummu abisa Æ™aryar data shirya akan fitar ta fito. Daga inda Ummu take tako zubomata ido na alamar tuhuma. Gareta ta Æ™arasa cikin danne komai da karsashin data aro. “Ummu kiran gaggawa na samu daga Ikram. Inaga dai abinda muka jima muna jirane ya fito”.
“Amma Iffah….”
“Ummu dan ALLAH kar kice a’a”. Iffah tai saurin tarar numfashinta cike da marairaicewa. “Ni ba hanaki zanyiba, sai dai wannan yawan fitar taki a kwanakin nan bana zuwa makaranta ba ya fara damuna Iffah. Shin kin manta halin da muka shiga da wanda zamu iya shiga a yanzu? Ina jin tsoro wlhy, matuÆ™ar tsoro a duk sanda kika fita koda makaranta ne”.
Sosai tausayin Ummu ya sake mamaye zuciyar Iffah, ta haÉ—iye hawayen da suka taru mata a ido tana Æ™aÆ™aro murmushi. “Insha ALLAHU Ummu babu abinda zai faru, wanda ya farun ma a baya bazamu taÉ“a mu yafe ba. Fita ta kuma ta daina baki tsoro, tunda kinga duk sanda zan fitan ina suturta dukkan jikina”.
“Shike nan ALLAH ya tsareki, dan ALLAH kiyi maza ki dawo kafin Abbin ku ya dawo gidan nan ko É—an uwanki”.
“Insha ALLAHU Ummuna”. Iffah ta faÉ—a tana rungumeta. Shafa kanta Ummu tai tana murmushin Æ™arfin hali itama, dan ba wani zuciyarta ta samu nutsuwa bane ita dai, ta bartane kawai saboda tace fitar ta shafi karatunta. Amma zata cigaba da rakata da addu’a harta dawo………✍

*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*

*DAUDAR GORA Billyn abdul*

*KI KULANI hafsat xoxo*

*A RUBUCE TAKE Huguma*

*RUMBUN K’AYA Hafsat rano*

*IDON NERA Mamuh ghee*

_LITTAFI DAYA: 400_
_LITTAFI BIYU: 600_
_LITTAFI UKU: 800_
_LITTAFI HUDU :1000_
_LITTAFI BIYAR: 1200_

_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_

_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_

_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_

_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_

_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_

_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_

ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN

MARYAM SANI
ACCESS BANK
0022419171

SAI A TURA SHAIDAR BIYAN

09033181070

IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA

09166221261

*ƳAN ƘASAR NIGER. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*

+22 90165991

Books biyar 1250CFA
Books hudu 1050CFA
Books uku 850CFA
Books biyu 650CFA
Bookk daya 450CFA

KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.

MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.

 

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*

✨ÆŠ ✨
( )

 

Post a Comment

0 Comments