Daudar Gora Book 1 Page 9

Latest Posts

6/recent/ticker-posts

Ad Space

Daudar Gora Book 1 Page 9


9_*

………..Kasancewar wajene daba kowa ke shiga ba anyhow yasa sai da Iffah tai kiran Sir Fawzan bayan saukarta a bakin gate. Umarnin bama security É—in wajen wayar ya bata. Bayan yayi magana da security É—in suka bata damar shigewa batare data san miya faÉ—a musu ba. Tafiya take a nutse tana É—an kallon wajen da tsarinsa. Dan babban garden ne mai cike da ababen kallo da ni’imtattun korayen ciyayi da Æ™awatatun filawoyi. Ta taÉ“a shiga sau biyu a dalilin taron makarantarsu ta Islamiyya da aka gudanar a wajen. Ya riga ya faÉ—a mata inda zata samesa, dan haka kanta tsaye take nufar wajen ranta fes da nishaÉ—i tamkar ance mata ga wuÆ™a ga maÆ™oshin Tajwar Eshaan ta yanka.
Sai da taje kusan Æ™arshen garden É—in ta tsaya, sai kuma ta shiga canki in canka na number wajen daya bata kasancewar akwai rukuni-rukuni na É“oyayyun wajen hutawa da manyan mutane sukafi tu’ammali da su idan basa buÆ™atar wata hayaniya. Cikin É—an É—age kafaÉ—a ta nufi na farkon da zuciyarta tafi karkata. Ƙawatuwar wajen takai mai kallo shagala harya iya manta abinda ya kawoshi, kamshin firanni da wani iska mai busawa a hankali kaÉ—ai na dabanne. Jitai kamar da shakku na shigowarta wajen, amma sai ta dannesa a Æ™asan zuciya ta cigaba da takawa tamkar mai sanÉ—a tana leÆ™e-leÆ™e. Ta isa kusan tsakkiya zuciyarta ta shiga gargaÉ—inta ganin babu alamar akwai mutum mai numfashi a wajen, cak ta tsaya tare da ciro wayarta domin neman sir Fawzan.
“Ya ALLAHU”.
Ta faÉ—a jin ana sanar mata bata da kati kona sisi a wayar. Kamar zatai kuka ta sauketa daga kunenta tana É—an Æ™ara danne-danne da cigaba da takawa a hankali batare data san mike a gabanta ba. KaÉ—owar iska da sassanyan Æ™amshin turare mai daÉ—in gaske ya sakata tsayawa cak Æ™irjinta na harbawa da Æ™arfi. Fararen idanunta ta janye daga kan wayar tare da É—ago kanta gaba É—aya, a kan mutumin dake kishingiÉ—e bisa wani lallausan jan darduma daya haÉ—u da kalar korayen ciyayi ya bada Æ™yaÆ™yÆ™yawan tsari ta sauke. Rabin jikinsa akan tum-tum yake. Kansa a risine yana kallon lap-top Æ™irar kamfanin apple dake akan wani Æ™aramin tum-tum É—in itama. Gefensa kaÉ—an wani Æ™yaÆ™yÆ™yawan bowl ne fari na tangaran, sai butar shayi kalar golden akan tray dake tabbatar da set ne dan harda Æ™ananun cups nashan shayi. Sanye yake da Æ™ananun kaya farare tas da suka fidda ainahin suffarsa ta masu ta’amalli da Æ™arafuna, gashi sun sake fidda ainahin hasken fatarsa da sheÆ™inta irin na masu jin daÉ—i. Duk da tana a gab da shi aikinsa yake hankali kwance baiko nuna alamar yasan da zuwanta ba.
“Mi kake buÆ™ata?”.
Sassaanyar muryarsa mai zurfi da kamewa ta daki kunenta da alamar akwai wanda yay tsammani ba ita ba. Ƙirjinta ne ya sake harbawa har tanaji kamar jininta daya tsinke na neman biyo hudojin gashin fatarta ya fito. Bata da niyyar cewa komai, gata tsaye tamkar an dasata ta gagara É—aga ko Æ™afa É—aya tabar wajen duk da haka zuciyarta tafi buÆ™atar da tayi. Jin shiru ba’a amsa masa ba, ga tsaiwar mutum yanaji har yanzu a gabansa ya sashi É—ago lulu idanunsa masu haske da baiwar bakin Æ™wayar tsakkiyarsu ya sauke a kanta. Komai tsayawa yay daga garesa, kamar yanda Iffah ma hatta kaÉ—awar iskar wajen ta tsaya mata cak… Fuskarsa dake a kame da kwarjini ya sake tsumewa yana sassauta girman idanunsa tamkar mai son lumshesu da gayya.
A fisge, tamkar an jawo furucin daga bakin Iffah ta yamutsa fuskarta da Æ™anÆ™ance manyan fararen idanunta da tun a kallon farko ta kaudasu da ga kansa alamar kunya irin ta mace, “Idan ma kai aljanine wlhy nafi Æ™arfinka. Wace irin jaraba ce duk inda nai saina ganka”. Ta Æ™are maganar da hura bakinta.
Kamar yanda bai motsa daga yanda yake ba haka bai ce mata komai ba, bai kuma janye idanunsa a kanta ba har yanzu. A zuciyar Iffah fa ta fara tsorata dajin tabbacin mutumin nan fa Æ™ila aljani ne. Amma sai taga idan ta nuna tsoronsa fa zai ma iya kasheta, saboda a yanzu haka ma Æ™arfin hali take, tana matuÆ™ar jin kaifi da tasirin idanunsa a dukkan É“argon jikinta da jijiyoyi da gudanar jini. Amma sai ta dake a Æ™asan ranta tana karanto addu’ar neman tsari da aljanu.
Kusan tunani iri É—aya ne a zukatansu. Dan shima dai zuciyarsa ta Æ™ara yarda wannan abar aljana ce kawai, yana ganin kuma ya kamata yasan miyasa take bibiyarsa ne?. Nisan data fara masa a idonsa ya fahimci tabar wajen, ilai kuwa can ya hangota tana tafiya cikin sassarfa ta nufi Æ™ofa. Cin karo data kusan yi da mutum ya sata ja gefe da sauri. ÆŠaya daga cikin matasan datai masa gani biyu da su ne, cikin nuna alamar mamaki da tsuke fuska yake kallonta. Harara ta balla masa ta Æ™yaÉ“e fuska da raÉ“ashi ta wuce, danji take Æ™afafunta tamkar ba’a kansu take takun ba…..
“Fareedah!”.
Da sauri ta juyo jin muryar Sir Fawzan daya sauke numfashi da dafe kansa na tabbacin ya jima yana nemanta. “Ina kika shigane wai? Tun É—azun sai faman zagaye garden É—in nan nake ni da securitys nemanki, ga wayarki ma taÆ™i shiga sam”. Maimakon ta bashi amsa sai ta zube a kujerar dake a kusa da ita ragwaf. A wahale tace “Sir ka bani ruwa nasha Please”.
Sosai yanayinta ya sake neman firgitashi, amma fahimtar ruwan tafi buƙata ba tambaya ba ya sashi barin wajen da ɗan hanzari. Mintuna ƙalilan ya dawo da robar ruwa. Miƙa mata yay bayan ya ɓalle murfin. Tunda ta kafa kai bata koja numfashi ba sai da ta sha fin rabi, ta sauke robar tare da dafe goshinta tana sauke ajiyar zuciya a jajjere. Lokaci ya bata sosai ta samu nutsuwa kafin ya kai zaune a kujerar dake facing ɗinta.
“Fareedah miya faru wai? Ina kika shiga? Duk kin tadamin hankali saboda security sun tabbatar min kin shigo”.
A hankali ta É—ago manyan idanunta da launin farinsu ya sirka ta zuba masa. Sai kuma ta janye da sauri tana girgiza kanta dan fuskar mutumin nan kawai ta gani a tare da shi saboda ta sakama ranta aljani ne. Idanunta rumtse tare da yakice tunanin ta sake buÉ—esu akansa. “Sir lokaci ya Æ™ure ina abokin naka?”.
Ya fahimci bata son bashi amsa, sai kawai ya girgiza mata kai. “Rashin ganinki ya sakani a ruÉ—anin da har ya kira waya ban sani ba, sai daga baya na lura na kirashi shima kuma bai É—aga ba”.
“Ya ALLAH, shike nan itama wannan damar ta kufce min!”.
“Bazamuce haka ba sai munji ta bakinsa, a yau ne dai kawai nake ganin bazai yuwu ba gaskiya, kodan ke a karan kanki ma. Kinga saura baifi mintuna arba’in ayi magrib ba. Kije gida, insha ALLAHU zanbi duk hanyar data dace domin ganin kin haÉ—u da shi”.
Kallonsa take kamar zatai kuka. Sai dai saka zantukansa a ma’aunin hankali ya sata kasa cewa komai.
“Kiyi haÆ™uri”.
Ya faÉ—a cikin sake sanyaya murya yana mata wani lallausan kallo. Kauda nata idon tai daga kansa, taja iska ta fesar da jinjina masa kanta kawai. Dan ta tabbatar inhar tai magana kuka ne zai iya Æ™wace mata ma…..

*_MASARAUTA_*

Gurfane take a gaban Uwa kamar yanda dokar take ga duk wanda ke binta. Duk da matsayinta da girmanta a cikin daular ruman a gaban uwa ita ba komai bace face mai neman biyan buÆ™ata (Wa’iyazubillah). Kamar ko yaushe tsohuwar da suke kira uwa sanye take cikin jajayen kaya, sai dai saÉ“anin waccan ranar yau inuwarta kawai ake iya gani a jikin bangon É—akin. Amma abin mamaki babu tsoro ko wata shakkar hakan a idanun hamshaÆ™iyar matar. Inuwar uwa ta kece da mumunar dariyarta mara daÉ—in saurare, kai kace za’a iya jinta a duk faÉ—in masarautar, sai dai abin mamaki iya ita É—in kawai take jinta. Sai da tayi mai isarta kafin ta tsagaita tamkar ba’ita tayin ba.
“Ta-Æ™urya alÆ™awarina ya cika, zaku iya tunkarar kowa a yanzu da maganar auren Malik-alMuluk babu mai musa miki hatta Malikat da shi a karan kansa balle duk wani mai faÉ—a masa yaji. Sai dai akwai banbanci a wannan karon da baya. Hhhhhhhh!!”.
“Umarninki shine abin jira Uwa mai share kukan mai kuka”.
“Hhhhh Ta-Æ™urya shiyyasa bana baÆ™in cikin taimakonki, zan kuma cigaba da taimakonki kiyita na sara keda duk mabiyanki. Ragamar kasancewar gida a hanun wasunki bashine zai sa su zama masu Æ™arfin ikoba sama da naki. Ki shiga ki fita a haÉ—a gagarumin aure na bajinta tsakanin wannan yarinya da Malik-alMuluk. Hakan zaisa su shagaltu da tunanin komai ya canja musamman shafe watanni tara da Zawjata-almilki da suka rage suka kwashe gidan nan batare da ko ciwon kai ba. Ina son ki nuna bajinta irin wadda ko Malikat bazata yiba, Daular ruman zata cigaba da kasancewa a tafin hanunki a baÉ—ini koda a zahiri kinada wanda suke nuna sunfi Æ™arfinki. Ranar mako zata zama ranar sa’a Hhhhhhhh!!!”.
Sautin dariyar ya cigaba da nesa da kunuwanta har inuwar uwa ta É“ace. Nannauyan numfashi ta sauke tare da murmushi mai nuna tsantsar farin ciki. Ta dubi Æ™yaÆ™yÆ™yawan farin tafin hanunta da jini keta kaikawo tana sake maimaita kasantuwar daular ruman a tafin hanunta da uwa ta ambata mata. Tabbas ita É—in mai sa’a ce, sa’ar da zata iya nunata a gaban duk wasu sa’ointa koma wanda suka É—arata. Fatanta kawai ALLAH ya kaita ranar cikar burinta gaba É—aya domin tabbatarma kowa dake cikin Ruman ma ba daular ruman kawai ba *Saka Æ™wan kaza bashi ke nufin mallakar akurki ita É—aya ba* sannan zuwan *mai guri bashi ke tabbatarda naÉ—ewar mai tabarma ba*…….

★★_______★

Kwanaki biyu kenan Iffah bata sake neman sir Fawzan ɗinta ba, ta kuma kashe wayarta ta yanda shima koya nemeta bazai sametan ba. Ita tasan dalilin zaɓar yin hakan, duk da yanayinta ya nuna tana da damuwa dan babu walwala tattare da ita sam tun baro garden ɗin da tayi. Yau ma data kasance bazataje makaranta ba kamar yanda ta saba ta tashi taya Ummu aiki, sai dai yanda take komai kamar mara laka a jiki yasa Ummu nutsuwa a nazartar ta..
“Wai lafiyarki kuwa Iffah? Tun dawowar fitar da kikai shekaran jiya duk kin wani canja. Ko jikin naki ne?”.
“A’a Ummu, kawai dai kaina na É—an mun ciwo ne Æ™asa-Æ™asa. Amma na san barci ne da bai isheni ba”.
“Barci kuma? To miya hanaki barcin?”.
In’ina ta fara na rashin sanin abinda zata faÉ—a. Sai kuma tai Æ™asa da kanta ganin yanda Ummu ta kafeta da idanu. Ummu mace ce mai yawan tsantseni wajen tarbiyyar Æ´aÆ´anta. Komai tana binsa a sannu babu garaje ko gaggawar akan tafida yaranta tun kafin sukai haka, shiyyasa cikin sauki take iya sanin matsalolinsu da saurin fahimtar sabuwar hanya da suka É—auka saÉ“anin wadda ta sansu da shi. Yanzu ma dai É—auke kai tai ga Iffah ta cigaba da hidimar gabanta batare data sake magana ba. Daga baya ma saita Æ™irÆ™iri jan Iffah da sabuwar hira da bata da alaÆ™a data farko. Tun Iffah na É—ararewa har ta saki jikinta…

★Washe gari ta É—an danne kaso sittin cikin dari na damuwarta dan kar Ummu ta hanata zuwa makaranta. Sai dai koda taje makarantar ma dai zaune kawai ta kasance badan ta nutsu a fahimtar komai ba har aka tashi. Kanta tsaye ta fito domin samun abin hawa a bakin gate kamar sauran É—alibai. Da Æ™yar ta samu tare da wasu da suke kusan a anguwarsu, sai dai zasu rigata fara sauka…
A hankali wata baÆ™ar mota dake fake É—an nesa da makarantar tasu ta fara bin bayan mai Mototaxi É—in da sam shi hankalinsa baima kai ba. Haka suma su Iffah babu wanda ya kula da motar. Da mai motar ya fahimci zasu zargesa sai ya canja salon bin nasu. A haka har aka sauke abokan tafiyarta. Motar ta cigaba da binsu har titin anguwarsu, anan aka dakata har mai Mototaxi É—in ya shiga ya kai Iffah ya juyo zai fita suka tsaidashi……….✍

_To ke kuma baƙar mota daga ina?._

*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*

*DAUDAR GORA Billyn abdul*

*KI KULANI hafsat xoxo*

*A RUBUCE TAKE Huguma*

*RUMBUN K’AYA Hafsat rano*

*IDON NERA Mamuh ghee*

_LITTAFI DAYA: 400_
_LITTAFI BIYU: 600_
_LITTAFI UKU: 800_
_LITTAFI HUDU :1000_
_LITTAFI BIYAR: 1200_

_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_

_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_

_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_

_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_

_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_

_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_

ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN

MARYAM SANI
ACCESS BANK
0022419171

SAI A TURA SHAIDAR BIYAN

09033181070

IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA

09166221261

*ƳAN ƘASAR NIGER. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*

+227 90165991

Books biyar 1250CFA
Books hudu 1050CFA
Books uku 850CFA
Books biyu 650CFA
Bookk daya 450CFA

KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.

MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.

 

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*

✨ÆŠ ✨
( )

 

Post a Comment

0 Comments