Ikraam 101

Latest Posts

6/recent/ticker-posts

Ad Space

Ikraam 101


~Ikraam~ By Khaleesat Haiydar 101…. Tana
sauka stairs yyi saurin karasawa kusa da ita
suka shiga saukowa tare yace “kin ci abinci
kuwa” banxa tayi masa kmr bata ji ba, yace
“Ikram” ta juya a dan fusace tace “to wae meye
in naci ko ban ci ba haba” shiru yyi ya tsaya
kallonta, bata jira me xae ce ba tayi gaba da
sauri, ya bi ta da kallo har ta shige kitchen, snn
juyawa yyi ya koma dakin Mami, tana shiga
kitchen jummai ta mika mata faranti dauke da
kular shinkafa da plate sae spoon tace “tafi min
da wnn sama Ikram, ina tahowa da miyar” Ikram
ta karba tana kallon Maryam dake goge goge a
kitchen din tace “sannu da aiki” Maryam tace
“yauwa, kin karbi abinci kuwa Ikram” Ikram tace
“xan xo in karba ynxu” bata jira me Maryam xata
ce ba ta juya ta fita daga kitchen din rike da
farantin da Jummai ta bata, ta nufi dakin Mami,
gaban Mami ta ajiye farantin Mami tace “ba
nawa bne na Aliyu ne, ina jumman take” Ikram
tace “wae tana tahowa da miyan” mikewa tayi
rike da farantin ta nufi inda Aliyu ke xaune Khaleel
na daga gefensa, ta durkushe gabansa ta ajiye
farantin, tana daga kai suka hada ido yyi saurin
sauke idonsa, ta sunkuyar da kanta da sauri xata
mike Jummai ta shigo dakin rike da wani trayn
me dauke da miya da cokalin diban miyar da cup
sae lemo da ruwa ta ajiye gaban Aliyu, Ikram ta
juya tana kallonta tace “in xuba masa Mama
jummai” Jummai tace “in xa ki iya xuba mana”
Ikram ta dauki plate ta bude shinkafar ta shiga
deba a hankali, Jummai ta fita daga dakin, kmr
ance ta daga kai taga kallonta Khaleel yake, yana
gnin ta daga kai yyi saurin dauke idonsa, ta
sunkuyar da kanta ta ci gaba da abinda take, da
kyar ta daga kai tana kallon Aliyun da ya mayar
da hankalinsa kan TV tace “ya isa hka” yi yyi kmr
bae ji ba ganin ynda Mami da danta ke kallonsu,
tace “nace ya isa hka” yace “ehh” ba tare da ya
kalleta ba, ta bude kular miyar ta xuba masa kan
shinkafar snn ta dauka ta mika masa tace “gashi”
ba tare da ya kalleta ba still yace “ki ajiye mana”
a hankali ta ajiye abincin snn ta mike taga Mami
ma kallonta take, juyawa tayi da sauri ta fice
daga dakin, dakin Mama Jummai ta wuce tayi
kwanciyarta, can karfe sha biyu Mami ta shigo
dakin ganin bata ganta ba ta tada ta don har tayi
bacci dakin tace “tashi ki wuce sama ki kwanta”
ba musu ta mike tana murxa ido ta nufi sama
dakin Mami taga sudais kwance inda take son
kwanciya ta koma can nesa da shi ta kwanta,
Mami ta shigo dakin tace “ae ba nn xaki kwana
ba, kije dakin Khaleel Maryam na can ku kwanta,
Ikram tace “Mami ni nn nake son in kwanta”
Mami tace “to je ki ce mata nn xaki kwana ban
son kananan mgna” Ikram ta mike ta nufi dakin
Khaleel har Maryam ta kwanta, tace “ni dakin
Mami xan kwana fa” Maryam tace “to Allah ya
tashe mu lfya” Ikram ta juya ta koma dakin Mami
tayi kwanciyarta bayan ta canxa kayan jikinta
xuwa na bacci don tayi wanka dakin Jummai.
Can cikin dare Sudais ya tashi ya dinga kuka yaki
shan Madararsa, Ikram dae na xaune sae kallonsu
take, Mami na ta fama da shi, can dae tace “to
Mami idan tana da yaya da tayi aure sae a kaisa
ta dinga basa nono mana” kmr xata yi kuka ta
karashe maganar, Mami ta mika mata shi tace
“rikesa in kara masa madaran kila ya sha” Ikram
ta karbesa ta rungumesa tana jijjigasa, ynda yyi
mata daxu da rana hka ya dinga yi yana lalubar
kirjinta, da sauri tace “Mami kinga wae nono yake
son sha” Mami tace “da’alla ki rike min shi da
kyau” xaunar da shi tayi kafarta kmr xata yi kuka
yana ta kuka abun tausayi, ganin Mami ta juya
masu baya yasa ta sa masa yatsanta a baki taga
ya fara sha da sauri, cire yatsan tayi ya saka
kuka ta dagasa a hankali ta sa masa lip dinta a
baki nan da nn ya fara tsotsa da sauri ta kura
masa ido bakinsa na nata tana kallonsa, bude
kofar dakin aka yi Aliyu ya shigo ta sauke sa da
sauri duk da ya gansu, yaron ya fashe da kuka,
Aliyu ya karaso cikin dakin yace “ya hanaki bacci
ko Mami” Mami tace “bari ynxu xan masa allura”
ya karasa kusa da Ikram ya mika mata hannu ta
basa shi ya shiga lallashinsa. Kwanansu biyu a
gidan bayan anyi ukun Rukayya suka fara shirin
komawa gida ran Wednesday da daddare ,
Maryam ta gama shirinta don Khaleel na jiransu
amma Ikram taki tashi daga kan gadon Mami, da
kansa ya shigo dakin yace “ke fa muke jira Ikram”
Mami tace “yau naga ikon Allah, wae baxa ki
shirya bane ana jiranki Ikram” Ikram tayi shiru
kmr baxata ce komai ba ta hade rae, ganin ynda
suke kallonta yasa tace “Mami ni bbu inda xa ni a
nn xan tsaya.”
Like · 4 · Reply · Report · 8 minutes ago

Post a Comment

0 Comments