Ikraam 17

Latest Posts

6/recent/ticker-posts

Ad Space

Ikraam 17


By Khaleesat Haiydar 17….. Ikram na ganin Mami tayi bayan Kawu na lado da gudu tana cewa “wayyoo don Allah kawu ku boyeni, wllh yakumbo tace min kaina xata yanke, wayyoo Ammina” Shatu ta fixgota tace “kaji min shegiya na lado idan tana yanke kan mutane da bata yanke namu ba,” Aliyu ya kamo hannun Ikram ya xaga da ita ta daya side din motar sae bari jikinta yake, ya shiga yi mata magana a hankali a kunnenta, shiru tayi tana kallonsa, ya sakar mata murmushi snn ya share mata hawayen idonta da hannunsa ya bude bayan motar ya sa ta ciki, Shatu ta juya tana kallon Na lado da ya saki baki yana kallonsu, ta dan tabe baki a xuciyarta tace “can dae,” snn ta juya ta shige gida tana tattaba kirjinta ko kudin na nn har lkcn, Mami kam kasa motsi daga inda take tayi, don tabbas tasan karya shatu da mijinta suke, ba da ixinin iyayen ikram suka bata ita ba, maganganun da taji Ikram nayi yasa jikinta yyi sanyi, Muryar Na lado ya dawo da ita daga tunanin da take, yace “to Hajiya ni dae nayi ciki, kuma kuyi ku bar kofar gidan nn don naga yan gulma har sun fara fitowa kallo” yana kai wa nn ya juya ya shige gida. Mami ta sauke ajiyar xuciya ta xaga bayan motar ta bude, kanta na kafadarsa tayi lamo yana bude mata chocolate din hannunsa tana kallonsa, da harshin turanci Mami ta shiga yi masa magana “i dis lyk dis undecent behaviour of yhurs Aliyu, wat’s dat yhu think u re doin 4 Godsake” bae ko kalleta ba yana kallon Ikram yace “bude bakin kanwata” ta bude kuwa ya saka mata, sanin ba kulata Aliyu xae yi ba yasa cikin nutsuwa ta fara masa magana da turanci kuma, “bana tunanin xan tafi da ita ynxu Aliyu, bari in kai ta gun mamarta kawae, idan Allah yyi xan rike Ikram xan riketa, nasan 4 sure karya wa ennan mutanen suke, son kudi ya rufe masu ido nd i assume don ba yar su bace yasa suka yi hkn, kuma ko ni aka ma hka baxan ji ddi ba a rabani da ‘da na without my knowledge, its beta i take her back 2 her parent, may b sum odza tym” ya daga kai yana kallon Mami yace “to in baki son daukarta ne ni xan dauketa in kai ta gidanmu, don Ikram ba kalar Suleja bace” Mami tace “gidan ku wajen wa?” yace “koma wajen wa” Mami tace “amma nasan ba wajen uwarka ba dae ko” murmushi yyi bae kuma cewa komai ba, ta koma driver seat ta bude ta shiga snn ta tada motar, ganin hanyar gidansu Ikram ta kama yasa Aliyu yace “plss Mami, don Allah ki tafi da Ikram, wllh nasan iyayenta xasu ji ddi daga baya, ynxu kina komawa da ita gida baxa su kuma baki ita ba, but kinga ko da kwana uku tayi gun ki kika kawota taga iyayenta xasu ji ddi ae” da kyar Aliyu yyi convincin din Mami suka kama hanyar Abuja don da gida tayi niyyar maida ikram. Shidda saura suka isa gidan Mami, tana gama parkn Aliyu ya bude motar suka fito da Ikram, Ikram ta jawosa tana yafitosa alamar tana son masa magana ya duka ta shiga masa magana a hankali a kunnensa, Mami dae sae kallonsu take, Aliyu yyi mata murmushi ya gyada mata kai, tana kallon Mami kmr xata yi kuka tace “kice wllh baxa ki yanka ni ba” Mami tayi murmushi ba tare da ta shirya ba, ta dafa ta a hankali tace “sbda ina sonki yasa na dauko ki dota” tana fadin hka ta kuma yi mata murmushi snn ta kama hannunta suka shiga gidan Aliyu na biye da su a baya, sama Mami ta haura da ita ta bude mata dakinta ta shiga bathroom ta hada mata ruwan wanka snn ta fito ta tarda ta tsaye gaban madubi duk ta birkice kayan make up din dake wajen, Mami ta kamo hannunta ta shiga da ita bayi tace maxa ga ruwa nn kiyi wanka ki daura towel ki fito, kuma kar ki taba komai sae soso da sabulu kawae kina ji na, Ikram ta gyada mata kai snn Mami ta fita ta dauki Atm card ta sauko falo, Aliyu ya fito daga kitchen knn ta mika masa tace “kananan kaya xaka fita ka siyo mata don Allah,” bae yi musu ba ya karba yace “ok, don Allah Mami ki min cous cous kafin in dawo” tace “in kaje gida nasan baxa ka rasa ba ni kam a gajiye nake” tana kai wa nn ta haura sama, ya girgixa kai ya fice daga falon. Ikram ta fito daga wankan daure da towel amma bata ga Mami a dakin ba, gaban Madubi ta xauna ta dauko wani shower gel ta shiga shafawa, jin budewar gate da shigowar mota gidan yasa tayi gun window da gudu tana lekan ko meye wnn, tana ganin mota ne ya shigo ta bude kofa ta sauka falo da gudu tayi bakin kofar, kasa bude kofar tayi sae turasa take da karfi ita dae taje taga motar, taji an bude kofar ta dan koma baya da sauri, Khaleel ne ya shigo yana danna wayarsa sanye da suit ga briefcase a dayan hannunsa duk da daga aiki yake amma kmr lkcn yyi shirin don yyi kyau har ya gaji, bae lura da ita ba ya shigo falon tare da kullo kofar ya dan tsaya ya gama danne dannensa snn ya mayar da wayar cikin aljihunsa, Ikram dae na tsaye gefensa rike da dan farin tawul dinta sae kallonsa take baki bude xae ci gaba da tafiya tace “kai!” juyawa yyi da sauri tare da komawa baya yana kallonta, bae san lkcn da ya saki briefcase din hannunsa tare da sakin wata yar kara ba yana kiran “mami” ba karamin tsorata Ikram tayi ba ita ma ta fasa Ihu a tsorace tana kwala ma Anty kira ita ma.
Like · 1 · Reply · Report · 4 minutes ago

Post a Comment

0 Comments