Ikraam 2

Latest Posts

6/recent/ticker-posts

Ad Space

Ikraam 2


~Ikraam~ By Khaleesat Haiydar 2…… Mami ta bi ta da kallo tana girgixa kanta snn tayi murmushi tace “Mu tafi son,” ya mayar da wayarsa da yake dannawa cikin aljihu snn ya shiga motar ya tada yyi reverse yana kallon Mami ta Madubi yace “ina kika samo yarinyar nn mami,” Mami tace “wlh kawae biyo ni tayi daga cikin kasuwa fa, ban santa ba,” bae ce komai ba ya mayar da hankalinsa ga tukin da yake. Karfe kusan biyar na yamma Ikraam ta isa gida rike da kubewar da Ammi ta aiketa, bakin xaurensu ta tsaya ta dan buda labulen buhun dake jikin kofar a hankali tana lekan tsakar gidan, ido hudu suka yi da Ammi dake xaune bakin murhu tana kwashe tuwo a tsakar gidan, Ammi tace “xaki ci ubanki ki lekoni da kyau, ae yau me raba ni dake a gidan nn sae Allah,” da gudu tayi waje ta fasa wani shegen ihu tare da xubewa kasa tana cewa “wayyo Allahna,” tana birgima hade da shure shure, me tredan dake karshen layin yana xaune yana kallonta don ba nisa tsakaninsu ya daka mata tsawa hade da yi mata dakuwa yace “kinci uwarki, kwana biyu kin rabu da iskancin nn shine xaki dawo dashi ynxu,” mikewa tayi ba tare da ta kallesa ba ta kara gaba da gudu don tasan yana iya tasowa ya kakkwade ta, can kofar gidansu altine ta koma ta fada kasa ta ci gaba da birgimar ta, mamar altine ta leko tace “Au kin dawo da wnn iskancin naki ne ynxu Ikram, to tashi ki koma gidanku ja’ira kawae,” Baba mai nama ne ya xo wucewa da tasan namarsa yace “wa ya doke ki Rabi,” cikin kuka tace “Ammi ce,” ya kamo hannunta yace “kai, Aisha ma dae wallahi, ynxu ina abun duka jikinki,” maman altine tace “wllh baba idan an bibiya ma bbu abinda aka yi mata, tsabar iskanci ne na Ikram, ae ta kwan biyu bata tara mana mutane a anguwa ba,” Baba na rike da ita suka yi hanyar gidansu yana cewa “ae hakuri ake da yara barin wnn yar malaikan Allahn me ta sani,” sallama ya shiga kwadawa bakin xaure, Ammi ta fito yafe da mayafi tace “ina yini baba,” bae tsaya amsa gaisuwar ba yace “Haba Aisha me yarinyar nn tayi maki haka,” Ammi tace “wllh baba ban mata komai ba, tun karfe biyu na aiketa nan bakin kasuwa bata dawo min ba sae ynxu, daga nace xanyi maganinta fa tayi waje da gudu,” Baba yace “to ae Rabi yarinya ce kiyi Hkuri ki kyaleta,” Ammi tace “to baba ngd,” Baba ya juya yana kallon Ikram yace “maxa ki shiga ciki kuma ki dinga jin magana,” ta gyada kai tana goge guntun hawayen fuskarta ta bi gefen Ammi ta wuce sanin baxa ta yi mata komai ba kuma, Ammi ta kuma masa gdya ta shiga gidan, xaune taga Ikrama bakin murhu ta kwaso wasu sababin itace tana tura su cikin wutan, duk hayaki ya cika gidan, ikram na ganinta tace “Ammi kinsan me, yau naga wata yarinya me kirki, ta bani….” Ammi tace “ta shi ki ban waje kar na maki shegen duka da icen nn,” ikram ta mike tana xumburo baki ta shiga dakinta, kudin da mami ta bata ta shiga kallo tana tunanin inda xata boye shi kar Ammi ta gani ta mata duka, wani dan rami dake jikin window ta tura sa, snn ta fito tana kallom Ammi tace “ba kin ce idan kina girki in dinga xama ina kallo ba,” Ammi bata tanka ta ba, ta dauko kujera karami ta xauna tana ta kallon tukunyar kan murhu, hka ta dinga sa Ammi magana daga xaunen da take a wajen don da ta faki idonta sae ta jefa duk me ta gani cikin wutan yyi ta hayaki, da rankwashi Ammi ta koreta daga wajen, ta koma ca bakin kofar dakinta ta xauna tana matsar kwalla, Ammi ta gama miyarta ta shiga dashi dan kitchen dinsu ta fito tana kallonta tace “maxa ki tashi kije kiyi wanka kan kice min dare yyi,” bata yi musu ba ta mike ta tube kayan jikinta ta rataye jikin igiya, Ammi ta juya tana kallonta tace “na shiga uku da wnn yarinyar, wae ikram ban hanaki cire kaya kafin ki shiga wanka ba,” xumburo baki tayi tace “na manta,” ta shige dakinta ta fito da kwandon sabulunta snn ta dauko bokiti ta bude randa ta shiga diban ruwan wankanta, Ammi sae kallonta take kmr ta kwade ta, ruwanta rabin bokiti ta dauka tayi hanyar bayinsu, Ammi ta kwala mata kira ta fito da gudu a tsorace, cikin tsawa Ammi tace “kin wuce kin dauki xanin ki a daki ko sae na make ki, kullum ina koya maki abu amma wawancin ki ya ki bari ki dauka, ni ban san wace irin yarinya bace wnn,” kmr xata yi kuka tana bubbuga kafa ta shiga daki ta dauko xaninta tayi hanyar bayin.ko da ta fito daga wanka Ammi ta xuba mata tuwonta don ya huce, alwala Ammi ta sa ta tayi don lkcn sllhn magrib yyi, Ammi ta shiga daki ta fito mata da karamar riga da dogon wando ta sa, kmr xata yi kuka tace ni ba wnn nake so ba, Ammi ta watsar mata da su tace “to kar ki sa,” snn tayi ficewarta, sae da ta gama xumbure xumburenta snn ta sa tayi sllhn ta fito, kan tabarma ta xauna kusa da tuwonta da kofin ruwa, yarfe hannu ta shiga yi tana cewa “Ammi tuwon da xafi,” Ammi bata tanka ta ba har ta gama gyaran dan tsakar gidan ganin taki cin tuwon yasa ta wanke hannu ta xo ta xauna ta bubbuda mata snn ta mike tace “sae ki bari ya huce.” Ammi na shiga wanka ta tura tuwon gabanta ta mike a hankali ta wanke hannunta snn ta dauko slippers din ta ta fice daga gidan da gudu, sae hanyar kasuwa.

Post a Comment

0 Comments