Ikraam 4

Latest Posts

6/recent/ticker-posts

Ad Space

Ikraam 4


[12/30, 10:39 PM] ‪+234 903 250 7176‬: Ikraam~ By Khaleesat Haiydar 4….. Mamar Altine ta fixgo Ikram ta shiga dukanta da dan icen hannunta, bbu wanda ya bata hkuri, Baba Habu sae ca yake karamata mamata, Ammi ta juya ta yi cikin gida kawae, Abban Ikram dake bakin kofa tsaye yana kallonsu ya shige gida shima, har maman Altine ta gaji dan kanta ta shiga jan ta tana huci tayi cikin gidansu da ita, sae ihu Ikram take tana tsalle tsalle ta bar ta nn tsakar gidansu tayi ma Ammi dake xaune ta rafka tagumi sae da safe tayi gaba, Abbanta ya mike shima daga kan tabarmar da yake ya kamo hannunta ya xaunar da ita gefensa yana kallonta yace “meyasa baki jin magana ikram, ina kika tafi da daddaren nn” Ammi ta mike ta tabe baki tace “hka ka iya malam, wae daga ina take, yarinya ta xama abinda ta xama kayi mata fada baxa kayi mata ba, wllh tun farko kai ka lalata yarinyar nn,” ya hade rae yana kallonta yace “wani dukan kike nufin na sake mata bayan wanda saude tayi mata ynxu,” Ammi bata ce komai ba ta shige daki abunta, ya maida dubansa ga ikram yace “ki dinga jin magana kin ji mamata, kuma daga yau kar ki sake fita da daddare, ko kina son na fara dukanki ne” ta girgixa masa kai yace “kin ci abinci,” ta juya tana kallon inda ta bar abincinta tace “gashi can,” yace “je dauko,” ta mike ta dauko tana yatsine fuska tace “ni baxan ci ba Abba datti ya shiga ciki,” ya shiga kwala ma Ammi kira ta xo ta xubo mata wani abincin, daga cikin dakin Ammi tace “ban da shi,” mikewa yyi ya dauka nasa, suka shiga ci tare ya sa ta wanke hannu tayi alwala tayi slln isha snn ya rakata daki ta kwanta ya tofa mata addu’a ya fito, ya shiga nasu dakin, Ammi na xaune ta hade rae ya xauna gefenta yace “haba Aisha, ikram yarinya ce duka duka shekarunta nawa, wani yaro ne baya kin ji? Sannu a hankali duk xata daina ta nutsu, ki dinga hakuri da ita don Allah, Ammi dae bata tankasa ba tayi kwanciyarta kawae. Washegari da safe Ammi ta shiryata ta tafi sch bayan Abbanta ya fita gun aikinsa, ta hada ta da naira ashirin tace “kuma saura ki ki xuwa makarantar ko kije kiyi dambe a kawo kararki tunda ke kince kin xama jaraba a gari,” tana xumbura baki ta fita daga gidan a xuciyarta tana cewa ni bbu makarantar da xan je malama ta dokeni ban ga littafina ba, kmr abun arxiki ta kama hanyar makaranta da yara tana kusa makaranta ta yanke wata hanya daban da sauri da sauri take tafiya kar mutane su ganta har ta isa wata katuwar bishiyar mangwaro, ta haye ta samu branch me dan karfi ta kwanta kai tana ta kallon mutanen dake wucewa wajen, a hka bacci ya dauketa bata farka ba sae karfe goma da rabi, tafara kalle kallen inda take, can tayi hamma ta tsinko wani mango da bae nuna ba ta shiga ci, har ta gama snn ta duro kasa tana waige waige tayi hanyar Canal da saurinta, wasu almajirae yara ta tarar wajen suna kama kananan kifi da karamin hook dinsu da earth worm a jiki, ta bude jakarta ta ciro nata hook din naira ashirin ta siye shi da ddewa, bbu ranar da bata xuwa canal din kama kifi, ta nannade uniform dinta ta shiga tona rami tana neman earthworm har dae ta samu ta dauke shi da dan tsintsiya tayi gun almajiran tace “ku, ku sa min don Allah,” ba musu suka karba suka saka shi bakin hook din suka mika mata ta koma can bakin katon canal din ta shiga tsoma hook din cikin ruwa tana jiran kifi ya kama ta fito dashi ga gwangwaninta a gefenta, har ta fara ganin yaran makaranta na wucewa gida bata kama komai ba, tayi tsaki ta jefar da earthworm din ta nannade hook dinta ta mayar cikin jakarta snn ta kama hanyar gida da sauri, bata bi ta kofar gidansu altine ba kar ta ganta tace bata je makaranta ba, Ammi ta kai mata ruwan wanka taje tayi kafin ta ci abinci ta fito ta sa doguwar rigarta Ammi ta ajiye mata abincinta tsakar gida ta xauna tana ci a hankali tana kallonta, gani take kmr xata gane bata je sch ba, tana gama ci ta shiga neman littafinta na xuwa makaranta don gobe xata je kada Altine da mamarta su xo su ca ma Ammi bata je ba. Yau kmr kullum Ikram ta dawo daga sch bayan Ammi ta sallameta ta bata abinci ta dauki hijabinta ikram tace “ina xaki Ammi,” Ammi tace “kasuwa xanje siyo yakuwa, kina gama cin abincin ki wanke kwananon kije kiyi bacci, saura ki karar min da ruwan randan,” da sauri Ikram ta mike tace “Ammi ni meyasa baki aikeni ba ai ni kike aika,” Ammi tace ai ni ynxu na yaye aikenki Ikram, na dinga xuwa da kaina in siyo abinda nake bukata,” Ikram ta fashe da kuka tace “wllh Ammi ni se kin aikeni, malamar mu tace mu daina barin mamarmu tana fita siyo abu da kanta bbu kyau, bad children ne ke yin hka,” kuka ssae take, Ammi tace “to ai ke din ce ba kya ji Ikram,” tana share hawayenta tace “kiyi hkuri Ammi Allah xan dinga ji,” da kyar dae Ammi ta bata naira talatin din taje bakin kasuwa ta siyo yakuwar bayan ta ja mata kunnen kar tayi tsokana kuma kar ta dde, ta saka dan hijab dinta ta fita tana share hawayenta, har wani bari jikinta yake kawae ita dae ta ganta a kasuwa, a xuciyarta tana raya kila ma yau xata kuma ganin matar nn ta daukar mata kaya, sae tace ta kai ta yawo a katuwar motarta.

Post a Comment

0 Comments