Ikraam 51

Latest Posts

6/recent/ticker-posts

Ad Space

Ikraam 51


Ikraam~ By Khaleesat Haiydar 51….. Aliyu ya karaso gefen gadonta ya xauna yana kallonta yace “ina yini Mami” ta mike xaune tace “lfya qlau, ya gidan” yace “Alhmdllh” daga nn bae kuma cewa komai ba ita ma hkn, can bayan kmr minti biyar yace “gani kinyi kira na Mami” Mami na kallonsa tace “dama ba wani abu bane tambaya kawae nake son maka” yace “ina ji Mami” tana kallonsa tace “A gidan ku kana da tabbacin xa su bari ka auri Ikram Aliyu?” yyi shiru yana kallonta snn yace “idan nace ita nake so i am sure xa su barni in aureta” Mami tayi murmushi tace “har da Mum dinka Aliyu” ya girgixa kai yace “ae ba ita xata xauna min da saleemah ba Mami, kuma na tabbatar dad dina baxae min abinda bana so ba” Mami ta gyada kai snn tace “shknn, xan baka Ikram amma da sharadi biyar Aliyu, though ba masu tsauri bane kuma its Nml” ya tsura mata ido yana kallonta a sanyaye yace “to ina ji Mami” ta girgixa kai tace “A’a ba ynxu xaka ji su ba, ynxu dae me kace iyayenka suka ce kayi nn da sati biyu?” yace “suka ce in kai masu mata su gani” Mami tace “gud yaushe xaka kai masu ita?” yyi shiru na wani dan lkci snn yace “duk lkcin da kika ce in kai ta Mami” Mami tace “to duk randa ka shirya ka xo ka dauketa, Allah ya shige mana gaba” yace “Ameen ngd ssae Mami, Allah bar xumunci” tace “Ameen, amma Momy tasan da wnn mgnr ne?” ya girgixa mata kai alamar “A’a” tace “to idan ka koma gida ka sanar mata, xama muyi waya da ita, don bana son abinda xae sa raina ya baci Aliyu” Aliyu yyi shiru snn a sanyaye yace “Mum don Allah kiyi min favour daya” ta na kallonsa tace “na me knn” ya dawo gabanta yace “plss mum ki kira Abba kice masa kece ke son hadani da Ikram, nasan Abba xae ji mgnrki, kinga komai xae xo min da sauki knn” Mami ta girgixa masa kai tana murmushi tace “A’a kasan wnn baxae yiwu ba, kai dae kayi ta addua kawae nasan Momy ma idan ta sa baki komai xae xo maka da sauki ba sae nayi mgna ba” yace “to shknn Mami, i am greatful” tayi murmushi tace “Allah yyi maka albarka son, Allah na tare da kai” Aikin da take yi a computer jiya ta bar masa ya karasa snn ta fita downstairs taga me Ikram ke yi duk da tasan baxae wuce kallo ba, hkn kuwa ta tarar tana yi, ta kashe TVn tana hararanta tace “kinyi assignment dinki ne” Mikewa tayi kmr xata yi kuka tace “A’a” snn taje dauko jakarta a sama. Har dare Aliyu na dakin Mami, sllh kadae ya fita da shi, ya dawo ya ci gaba da abinda yake a computer, Karfe takwas Khaleel ya shigo dakin, ya gaida Mami dake kan darduma ta amsa tace “yau baka dawo da wuri ba son ina ka tsaya” ya xauna kan kujera yace “to Mami naga fushi kike dani, yau fa ko gaisuwata baki amsa ba, shiyasa nayi xamana a office” bae jira me xata ce ba ya juya yana kallon Aliyu yace “Hi Brother” Aliyu ya juya suka gaisa snn ya ci gaba da abinda yake. Mami tace “Aliyu ka je ku ci abinci ka bar shi xan karasa” Ikram ce ta shigo dakin ta tsaya daga bakin kofa rike da buk dinta tana hawaye tace “Mami kina ganin yaya Khaleel ya watsa min ruwa ya tsallaka min buk ko” Khaleel ya xaro ido yace “lah yaushe na watsa maki ruwa” tace “wllh Mami ya watsa min, kalli buk dina inda ya jike fa” Mami tace “yau ni nashiga uku da jaraba” Khaleel ya mike tsaye da sauri yace “wllh Mami karya take min daga na wuce ta gabanta sae tace na xuba mata ruwa, ke wae meyasa kika fiye karya ne” Ikram ta karaso cikin dakin ta dauki table water din dake gaban Aliyu ta bude ta karasa gabansa ta watsa masa ruwan ciki a jiki tana murguda baki tace “na rama, kuma wa ennan files din dake cikin dakinka ma duk sae naje na xuba masu ruwa wllh” juyawa yyi baki bude yana kallon Mami yace “kina gani ko Mami” Mami ta galla masa harara tace “ku fice min daga daki kar in bata maku rae” Ikram tayi masa gwalo ta fice da gudu, ya bi bayanta da sauri, Mami tace “dawo nn” juyowa yyi yana kallonta fuskarsa a daure tace “dawo nace” dawowa yyi cikin dakin, Aliyu ya mike ya kashe system yana kallon Khaleel yace “mu je mu ci abinci Khaleel” ba musu Khaleel ya mike suka fita daga dakin a tare.
[2/25, 08:35] Zjy: ~

Post a Comment

0 Comments