Ikraam 57

Latest Posts

6/recent/ticker-posts

Ad Space

Ikraam 57


[2/25, 08:35] Zjy: Khaleesat Haiydar ~Ikraam~ By Khaleesat Haiydar 57…. Light make up Mami tayi mata snn ta dan goga mata wet lip a lebbanta, ta mike ta dauko dan kunne na fashion da sarka sae bangles masu kyau ta saka mata su, snn ta dauki dankwalinta tayi mata dauri me kyau kmr headtie, ya xauna das das a kanta gwanin sha’awa, Mami tayi murmushi tana kallonta tace “Masha Allah my dota” Ikram ta wara manyan idonta tace “nayi kyau ko Mami” Mami ta rungumeta tace “ssae ma dota, amma kin san me nake so da ke” ikram ta girgixa mata kai Mami ta dafa ta tace “kinga anguwa xaku ikram, kar ki kuskura kiyi magana da kowa kawae gaishe da mutanen da kika gani xaki yi, snn kar ki xauna masu kan kujera a kasa xaki xauna sae ance ki hau kujera kin ji ko, kuma bance kiyi kallo ba idan kika je don na sanki da shegen kallo kmr bakauyiya, kar ki kuskura ki kallan masu TV, lemo ma idan aka baki kar ki sha sae ance ki sha” Ikram ta bata fuska tace “sbda me Mami” Mami tace “kice min to kawae dota” Ikram ta dan marairaice tace “to Mami” turarurruka kala kala Mami ta dauka ta feshe ta da snn ta dauko mata takalmi mai dan tudu don doguwa ce Ikram don ma bata gana girma ba, kalan shaddar jikinta ne takalmin amma light, tayi fasten din mata belt din takalmin da igiya snn ta dauko mayafi kalar takalmin ta daura mata a kafada ssae Ikram tayi kyau kmr wata ba indiya, Mami ta kasa daina kallonta don ita kam mmkin irin kyan Ikram take yi tun kan ba aje ko ina ba, kyakkyawa ce ikram ta karshe da ka ganta ka ga asalin fulani, wayarta ta dauka ta shiga daukarta hotuna snn tace “je ki ki kira min Aliyu” Ikram ta fita da sauri kmr jira take, dakin jummai ta fara shiga ta na juye juye tace “Mama jummai nayi kyau?” sakin baki jummai tayi tana kallonta, Ikram ta bata fuska tace “banyi kyau bane Mama,” jummai ta rike haba baki bude tace “ikram” Ikram tayi kmr xata yi kuka tace “kice nayi kyau mana” Jummai ta girgixa kai tace “Masha Allah yar mami, kin ganki kmr balarabiya kuwa” dama abinda Ikram ke jiran ji knn ta fice da gudu tana dariya, kasa ta sauka ta tadda Aliyu xaune falo ya dafe kansa, ta karaso kusa da shi da sauri ta dafa shi tace “yayana” dagowa yyi yana kallonta, tayi murmushi tace “nayi kyau yayana?” kasa ce mata komai yyi ya tsura mata ido sae kallonta yake, ta bata fuska tace “kace nayi kyau mana yayana” nn ma bae ce komai ba, idonsa na cikin nata yana mata wani irin kallo, jijjigasa tayi tace “yayana” sae a snn ya dawo, ta bata fuska ta mike xata bar wajen ya riko hannunta a hankali yace “kinyi kyau kanwata” murmushi tayi tace “to ngdd yayana, mami tace in kiraka, bari in je in tambayi yaya Khaleel ko nayi kyau” kallonta kawae Aliyu ke yi kmr bae taba ganinta ba, ta juya da sauri tayi waje snn ya sauke ajiyar xuciya ya lumshi idonsa, a hankali take tafiyar nata cikin sanda kar yaji karan kon kon shoe dinta, yana xaune yana danna wayarsa, ta rungumosa ta baya hade da yin yar kara da nufin ta tsorata shi, tura ta yyi a fusace yace “wae ni abokin wasan ki ne aka ce maki” rigijib ta xube kasa ta mike tsaye da sauri tana kakkabe jikinta ya juya yana kallonta xae yi mgna ta makale a throat dinsa, cikin muryar kuka tace “kuma Allah ya isa na, dama ba xuwa nayi in tambayeka ko nayi kyau bne” tana fadin hka ta fashe da kuka, ta juya xata bar wajen ya kamo hannunta da sauri, har lkcn yana kallon fuskarta a hankali yace “srry, kin yi kyau” handkerchief ya ciro yana goge mata hawayen fuskarta yace “Aliyu ya xo knn” ta murguda masa baki tace “eh” yyi murmushi yace “idan kun je can sae kiyi ta murguda masu kaxamin bakin nn naki da ba kya brush” ta mike da sauri tana xare ido cikin muryar kuka tace “wllh ina brush kullum da safe da daddare, sae dae idan kai ne baka yi” tana kai wa nn ta juya ta bar garden din, ya bi ta da kallo yana murmushi har tayi corner snn ya mike ya bi bayanta. Har bakin mota Mami ta rakosu bayan ta gama yi ma Aliyu mgnr da xata yi masa a daki, Ikram ta xauna gaban mota tana daga ma Mami hannu baki har kunne, Khaleel ya xagayo ta inda take don tare suka fito yana kallonta yace “saura kije kiyi ta washe masu hakora, ko kuma ki je kina murguda masu katon bakin ki kiga idan baxa su koro ki ba” fitowa tayi daga cikin motar da sauri har tana neman faduwa cikin muryar kuka tace “Mami kina ganinsa ko” da sauri ya shige gida yana dariya, Mami ta bi sa da kallo snn tayi kwafa tace “kyaleni da shi Ikram, shiga mota ku tafi, kuma karki yi misbehave kinji dota, kin dae ji abinda na gaya maki daxu ko” Ikram ta gyada mata kai snn Aliyu ya tada motar suka bar gidan Ikram na daga ma Mami hannu. Like · 9 · Reply · Report · 1 hour
[2/25, 08:35] Zjy: ~Ikram~ By Khaleesat Haiydar

Post a Comment

0 Comments