Ikraam 62

Latest Posts

6/recent/ticker-posts

Ad Space

Ikraam 62


Ikraam~ By Khaleesat Haiydar 62…… Mami tayi shiru na dan lkci snn ta ci gaba “Naji mutuwar mahaifin Khaleel ssae, don Allah ya gani duk iya xamana da shi bamu taba samun matsala ba, mutum ne me saukin kai da kirki ga yawan kyauta, ina gama takaba na koma gun Mahaifiyata da Khaleel, ko kadan yan uwansa basu nuna mana bakin cikin dukiyar da ya mutu ya bar ma Khaleel ko kuma ince ya bar mana me yawa ba don kowa na da nasa, duk family dinsu bbu me karamin karfi, mahaifin Aliyu kuwa ina fita da wata biyu dama ya kuma aure abunsa, kuma kusan a tare muka haihu da amaryar tasa ita ta haifi danta Mujaheed ni kuma Khaleel, makarantar da yaransa maxa ke xuwa na secondary shi Khaleel ma ke xuwa don makaranta ce me kyan gske, lkci daya kwatsan Alhaji ya fara hada sch fees dinsu gaba daya har da na Khaleel ya biya, ni dae ko sau daya ban taba masa gdya ba kuma ban taba nuna na sani ba ma, ana hka dae ya fara xuwa gidanmu yana nuna min Interest dinsa na son na dawo gidansa a matsayin matarsa kuma, har ga Allah ina sonsa, amma ssae nake tsoron xama da matar nn tasa duk da nasan da sabuwar Amaryar da yyi, amma dama Allah ya rubuta dole sae na kuma komawa gidansa, hka kuwa aka yi, ko kadan matan nasa basa shiri da na shiga gidan, amma sae me ina shiga da wata biyu Hajiya ta hade kai da Aishar suka dawo suna shiri ssae, duk suka sani gaba, in takaice maki lbri wllh a daddafe nayi shekara uku a gidan na haifi Seeyama, nn na bukaci ya sallameni bana auren kuma, to dae na wahala kan ya ban takardata, amma kuma yaki bari in tafi da Khaleel da seeyama, ban masa musu ba na bar masa su, na mayar da hankali na ga aikina duk da nasan Khaleel ba jin ddin Hajiya yake a gidan ba, through out stay din yarana a gidan basu yi rashin uwa ba don Mahaifiyar Mujaheed bata taba canxa masu ba, ita ta rike seeyama tun tana karamarta, kuma har yau Seeyama bata sake dani kmr ynda ta sake da ita ba, mun rabu da Alhaji da yan watanni Aliyu ya dawo wajena duk da ba tare da amincewar Mahaifiyarsa ba, ni na rikesa har ya gama karatunsa na likita, su kuma suka rike Khaleel can, to kinji me ya hadani da Aliyu Mmn Ikram, kinga baxan ce maki ba da na bne, ynxu dae abinda nake so daku kuyi hkuri don Allah, iyayensa ne suka takurasa kan aure kuma yace shi Ikram yake so, shine fa ta xo har nn tayi tijarar da ta saba,” Ammi tace “bkm Hajiya, Allah yasa mu dace, amma gobe xa’a daura auren Ikram da wani dan uwanta” Mami tace “ban gane ba” ammi ta dan yi shiru snn ta gaya ma Mami ynda suka yi da Hajiya da kuma hukuncin da Abban Ikram da yayansa suka yanke, Mami ta mike da sauri tace “innalillahi wa inna ilaihi raji’un, anya matar nn xata ga annabi kuwa,” ta koma ta xauna da kyar tace “don Allah mmn Ikram kar ku lalata rayuwar yar ku ku bar ta tayi karatu, wllh bata isa aure ba ynxu, irin wnn auren da ake ma yara ke sa xaka ga yarinya na fama da ciwon yoyon fitsari, gasu nn da yawa muna ganin cases irin hka a hsptl ” Ammi ta share hawayen dake bin kuncinta tace “to ya xanyi Hajiya, ni ynxu banda abun cewa a nn, ca fa tayi xata daure mu da wnda xae tsaya mana” Mami tayi murmushin takaici tace “ae tana takama mijinta soja ne, yayanta ma hka, amma kyaleni da ita mmn Ikram xan dawo anjima da yamma” Mami na kai wa nn ta fice da sauri, Ikram ta mike da sauri ta fashe da kuka xata bi ta, Ammi ta fixgota ta rungumeta tana kuka ssae. Mami na isa gida ta kira Khaleel tace ya bar abinda yake ya xo tana nemansa, bae mata musu ba cikin minti sha biyar ya dawo gida, ssae Hankalinsa ya tashi ganin mode din Maminsa, ya xauna yana kallonta cike da damuwa yace “baki da lfya ne Mami?” Mami ta sauke ajiyar xuciya tace “lfyata qlau Khaleel, magana xa muyi ne” ya dawo gefenta ya xauna yace “na me fa Mami, hope lfya?” a hankali Mami ta fara masa mgna ba tare da ta kallesa ba “nasan baka taba min musu ba Khaleel, kuma idan na sa ka abu ko bae maka ddi ba kana respectin dina kayi” Khaleel bae ce komai ba sae kallonta yake, a hankali tace “wnn karan ma baxan so ace ka min musu ba Khaleel” Khaleel ya sunkuyar da kansa bae ce komai ba sae dae gabansa faduwa yake, ganin tayi shiru yasa da kyar yace “me kike son in maki Mami” Mami ta sauke wani ajiyar xuciyar tace “so nake in hada ka aure da Ikram Khaleel……” saukowa kasa yyi da sauri cikin tashin hankali yake girgixa mata kai “no Mami kar ki min hka don kinga bana miki musu Mami plss,” nan da nn hawaye ya cika idonsa muryarsa na rawa yace “ki bari plss Mami kar kiyi min hka” Mami tayi shiru tana kallonsa, hawayen dake makale idonsa ya gangaro, ta sauko kasa ta dafa sa tace “y son?” ya daura kansa kan kafadarta cikin rawar murya yace “she is nt meant 4 me, snn ni baxan iya aurenta ba sbda abu biyu, na farko na dauketa a matsayin kanwata na biyu kuma, baxan iya cin amanar brotherna ba, plss Mami karki ce min wnn ba reasons bne consider me” hawaye ssae yake yi, Mami ta shafa kansa tana murmushi tace “ya isa son kar ka sake xubar min da hawayenka, i wont force yhu kuma na gamsu da reasons dinka,”
[2/25, 08:35] Zjy: ~Ikhram

Post a Comment

0 Comments