Ikraam 79

Latest Posts

6/recent/ticker-posts

Ad Space

Ikraam 79


Ikhram~ By Khaleesat Haiydar 79….. Wasa wasa
wani watan ya kusa xagayowa Ikram bata bar
Khaleel ya taba ta ba, har ya ma hakura duk da
ssae yake sha’awarta kuma ita ke takalo masa,
mugun shakkar masifarta yake, ko kadan bae son
jaraba da tsiwar Ikram ji yake kmr kansa xae rabe
biyu idan tana yi don bae son hayaniya shi kam,
gashi fa xaman lfya suke amma da ya kawo mata
batun sae tayi kwana biyu tana gaba da shi tana
xumbure xumbure. ran thursday ta fara ciwon
marar nata da safe, kuka take tana juye juye kmr
xata mutu, bae ko tanka ta ba sae da ya gama
shirinsa na office snn ya kai ta gida, Mami xata fita
office knn ita ma, da mmki tana kallonsu tace “lfya
kuma” ba tare da ya kalleta ba yace “ciwon ciki
wae” bae jira me Mami xata ce ba ya juya ya nufi
kofa yana cewa “ni na tafi office Mami” Mami da
Jummae dake tsaye falon suka juya suna kallon
Ikram dake ta rusa kuka. Kwananta biyar a gida
Mami ta kirasa ya xo ya dauketa don tun da ya
kawo ta bae sake komawa gidan ba, bayan sun
gaisa da Mami ya koma cikin mota yana jiranta, ba
a dau lkci ba ta fito jummai na biye da ita a baya,
ta bude mata motar ta shiga snn tayi masu sae da
safe, sae da suka fita daga gidan snn ya juya yana
kallonta, sae a snn ya lura da idonta da yyi jajur
sbda kuka, bae ce mata komai ba don bae san
abinda aka mata ba har suka isa gida, as usual a
fusace ta fice daga motar bayan ya gama parkin,
yyi murmushi ya bude motar ya fito ya kulle snn
ya bi bayanta, goma da rabi tana kwance daki ya
shigo, ya xauna gefen gado yana kallonta yace “me
aka maki kike kuka?” ta mike a fusace kmr jira
take, tana huci tace “daga yau idan marata na
ciwo idan baxa kaini asibiti ba ka barni in mutu a
gida, kar ka sake kaini gidan Mami na gaya maka”
tana kai wa nn ta fice daga dakin tana huci. Hka
xaman nasu ya kasance har na wata da watanni
bbu abun arxiki har tana neman shiga ss2, da ta
fara al’ada dama sae dae ya kai ta asibiti ba gun
Mami ba kmr ynda ta gaya masa, ita ko tausayinsa
ma bata ji, bata ma san wahalar da yake ciki ba,
duk ya rame abun tausayi, a watansu na takwas
ranar wani saturday suka je gida gun Mami, Mami
taji ddin ganinsu ssae, ga Ikram tayi kyau ta kara
murmurewa abunta, amma sae ta ga Khaleel dinta
kmr ba shi ba duk ya rame, Ikram dae nata murna
da jin ddin ganin Maminta ta makalkaleta, don har
sun fi xuwa gun Ammi kan wajenta, rabonta da
Mami wata kusan uku knn, kiri kiri yake kin kaita
sae dae kusan kullum suna waya. da yamma tana
dakin Jummai tana gyara mata gashi, Khaleel ya
shigo dakin Maminsa yace xae fita xuwa anjima
xae dawo, Mami tayi shiru tana kallonsa snn tace
“xauna mu yi mgna Khaleel” ba musu ya xauna
yana kallonta, a hankali tace “ka gaya min meke
damunka Khaleel?” yyi shiru har sae da ta
maimaita tambayar snn yace “bbu abinda ke
damuna mami, me kika gani” ta girgixa masa kai
tace “haba Khaleel, to idan baka fada min
matsalarka ba wa xa ka gaya ma, kana da wanda
ya fi ni ne” a hankali ya sakko kasa kusa da ita nn
da nn hawaye ya cika idonsa ya sunkuyar da
kansa murya can kasa yace “mami kin dae san ni
ba maxinaci bane, kuma….” shiru yyi ya kasa
karasawa hawaye na sauka daga idonsa, Mami ta
kasa cewa komai sae kallonsa take, mikewa yyi a
hankali ya bar dakin ta bi sa da kallo.

Post a Comment

0 Comments