Ikraam 83

Latest Posts

6/recent/ticker-posts

Ad Space

Ikraam 83


Ikraam~ By Khaleesat Haiydar 83…… Bude kofar da aka yi yasa Ikram ta mike xaune da sauri tana share hawayenta, Mami ce ta shigo dakin tana kallonta tace “kukan me kike” ta fashe da wani sabon kukan tace “ba kuka nake ba” Mami tace “to yyi kyau, daxu wa kika gaya ma xaki bar gidan nn” shiru ikram tayi kanta a kasa, Mami tace “yyi maki kyau” snn ta juya ta fice daga dakin. Hka Ikram tayi ta xama ita daya a dakin kmr mayya taki fitowa, har aka fara iska alamar hadari, ta mike da kyar ta kulle windows din dakin ta koma tayi kwanciyarta, kan kace me ruwa har ya sakko, karfe tara Jummai ta shigo dakin tace “Ikram ki je Mami na kiranki, wae yau kuma miskilancin naki ne ya tashi, kin je kin debi abinci kuwa ma” Ikram ta gyada mata kai kawae, jummai tace “to maxa ki je Mami na kiranki” mikewa tayi ta sa Hijab dinta don sanyi taji take taji, ta bi bayan Jummai, Mami na xaune tana duba wani littafi Ikram ta shigo dakin, kallo daya tayi ma Sudais dake bacci kan gado Mami ta lullubesa ta xauna kasan tiles tace “gani Mami” Mami tace “tashi daga gun nn, kin ci abinci?” mikewa tayi ta koma kan kujera ta gyada mata kai, Mami tace “karya kike” kmr xata yi kuka tace “ni na ci” Mami tace “meyasa kika bar gidan nn daxu” Ikram tayi shiru bata ce komai ba, Mami tace “magana nake maki” ta sunkuyar da kanta tace “dama na xo in maki sallama ne xan tafi hutu gun Ammi, kuma na ga kina da baki shi yasa muka tafi gida kawae” muryarta na rawa ta karasa mgnr, Mami tayi shiru tana kallonta, jin shirun yasa Ikram ta daga kai tana kallonta, Mami tace “to kukan me kike daxu” ta kuma sunkuyar da kanta tace “ya Khaleel ne ya ki kaini gun Ammi kuma” nan ma Mami bata ce komai ba na kusan minti biyar snn tace “tashi ki debo abinci a dinnin ki xo nn ki ci” ba musu Ikram ta mike ta fita ta debo abincin snn ta dawo dakin, da kyar ta iya cin abincin Mami na kallonta don ji tayi kmr ta amayo shinkafar, duk ta rasa me ke damunta, tana kai plate din Kitchen ta dawo Mami tace “dauki sudais ki kai sa gun mamansa” Ikram tayi kmr bata ji taba, sae da ta maimaita instruction din snn ta mike tace “ae ban san inda take ba” Mami tace “dakin Aliyu” fuskarta a daure ta nufi gadon ta dauki yaron ta fice daga dakin, ko sallama bata yi ba a tura kofar ta shiga dakin, suna xaune kan gado yana danna laptop, tana jingine jikinsa tana kallon abinda yake yi, karasa Ikram tayi kusa da gadon ta kwantar da yaron hannunta da ya farka a tsorace sbda ynda ta ajiyesa kan gadon, snn ta juya ta fice daga dakin, Rukayya da ta bita da kallo ta dawo da dubanta ga mijinta tace “ni ban san me nayi ma Ikram ba naga kmr bata so na, kuma ni ba wae na taba ganinta bne” banxa Aliyu yyi mata ya ci gaba da abinda yake, ikram na komawa dakin Mami, Mami tace “kinyi wanka ne” ta dan yi shiru snn tace “ni baxan yi akwae sanyi” Mami tace “akwae ruwan xafi a bayi” bbu ynda ta iya ta shiga tayi wankan snn ta fito, ta dauki kayan baccinta tasa ta dan yi shafe shafenta ta haye kan gadon Mami tana game da wayarta, goma dae dae Khaleel ya shigo dakin kallo daya yyi ma Ikram ya dauke kansa, Mami tace “daga ina kke cikin ruwan nn Khaleel” ya xauna gefen gado yyi shiru kmr baxae ce komai ba, Ikram dae sae kallonsa take fuskar ta a tamke, yana shafa kansa yace “gun frndx dina naje” Mami tace “cikin ruwan nn?” yace “no kafin a fara ruwan na fita ae” Mami tace “to kaci abinci” ya mike yace “ehh na ci, sae da safe Mami” Mami tace “to Allah ya kai mu” ya fita ya rufo masu kofar ya nufi dakinsa, Mami ta juya tana kallon Ikram tace “baki ga mijin ki bne” Ikram ta dauke kai bata ce komai ba, Mami tace “to tashi ki ban waje sae da safe” mikewa xaune tayi kmr xata yi kuka, ba tare da Mami ta kalleta ba ta mike ta shige bathroom, a fusace ta fice daga dakin ta nufi dakinsa, yana xaune sanye da singlet yana sip din tea, ta kashe wutan dakin ta koma can karshen gado tayi kwanciyarta tare da rufawa da bargo, yace “kina da hankali kuwa? Tashi ki kunna min wuta kar in bata maki rae” a fusace ta mike xaune tace “an ki din” sae kuma ta fashe da kuka, yyi murmushi ya ci gaba da shan tean sa.
[2/25, 08:43] Zjy: ~Ikraam~

Post a Comment

0 Comments