Ikraam 9

Latest Posts

6/recent/ticker-posts

Ad Space

Ikraam 9


~Ikraam~ By Khaleesat Haiydar 9….. Mami tace
“dawo inda kike kar mu bata ynxun nn” ba musu
ta dawo, shi kam tada motar kawae yyi yana
murmushi suka bar wajen, tana jikin Mami suka
iso dae dae inda Mami ke shiga mota idan ta fito
daga kasuwa Mami na kallonta tace “ina ne
hanyar gidan naku Ikram” Ikram tace “A’a a nn
xaku ajiye ni ae” Mami tace “aa gun mamarki xan
je Ikram,” da sauri Ikram tace “A’a ni dae a nn
xan sauka nace maki bbu kowa a gidanmu” Mami
tayi shiru tana kallonta snn cikin lallami tace “to
Ikram ae Mamanki dukanki xata yi idan kika
koma gida ynxu ke kadae, kinga dare ya kusa,
xata ce daga ina kike” ikram ta girgixa kai alamar
bata yrda ba tace “A’a ae a xaure xan tsaya har
Abbana ya dawo, baxae bari ta dokeni ba” Mami
ta rasa me kuma xata ce mata, can dae tace
“baki son in mayar da ke gidana ki xauna dani ina
sa maki cartoon ina baki naman nn mae dadi
muna tafiya yawo kuma ina siya maki sabon
kaya” da sauri Ikram tace “ehh ehh ina so” Mami
tayi murmushi tace “to ae sae naje na gaya ma
mamarki kar ayi ta nemanki” Ikram ta girgixa kai
tana tabe baki alamar bata yrda ba tace “A’a ni
dae baxan kai ki ba dukana Ammi xata yi da
waya ko muciyan tuwo maman altine ta taya ta,
kinsan maman Altinen nan bata sona” Aliyu da ya
tsura mata ido har lkcn yyi murmushi yana kallon
mami cikin harshen turanci yace “bar ta kawae ta
tafi Mami, xan rakata da kafa sae in ga gidan
nasu, idan yaso ko gobe ne sae in kawo ki” Mami
ta galla masa harara tace “sannunka, to ban yrda
ba” yyi murmushi yace “to ae dats d only option
ynxu Mami” ya maida dubansa ga Ikram yace “to
ni in raka ki gidanku Ikram” Ikram ta juya tana
kallonsa xata yi magana yace “to ae ba shiga
xanyi ba, kawae raka ki xanyi” tace “to” snn ta
shiga tura motar xata bude, a hankali Mami ta
bude mata motar snn ta sakar mata murmushi
tace “to ki gaida min mamanki Ikram” kai kawae
Ikram ta gyada mata ta fice, shi ma ya fito, Mami
ta mika masa ledan tsarabar da tayi mata ya
karba snn ya bi bayan Ikram, ita ko ta dawo
driver seat tana binsu da kallo, tafiya suke yana
rike da hannunta yace “wani class kike Ikram”
Ikram tace “ae primary 5 nake ynxu, amma fa da
a primary 4 nake kawae sae naga an mayar dani
5, kuma ina son makarantar mu ssae don ana
siyar da alawa da madara da ice cream, Ammi
tace baba ne yace a sa ni a makaranta don shafa
da altine ma sun fara xuwa, amma ynxu shafa ta
daina xuwa wae babanta kawu na lado bashi da
kudi, nima kasan wa ke biya min, to ba babana
ke biya min ba don shima ba shi da kudi, malam
habu ne ke biya min,” matse hannunta da ta ji yyi
yasa tayi shiru, yace “ca nayi wani class kika ban
ce ki ban lbri ba” ta fixge hannunta tana huci
tace “shine xaka cunkule ni baka san akwae xafi
ba” yyi yar dariya yace “to rama” ta dago
hannunsa ta dage ta shiga yi masa abinda yyi
mata, sae taga dariya kawae yake, bae ankara ba
yaji ta gatsa masa wani mugun cixo, yyi yar kara
ya fixge hannunsa ya saki ledan hannunsa yana
yarfe hannun yana kallonta da mamaki, ta fashe
da dariya ta kanne ido tace “gashi nn na rama”
ya daga hannun yana kallon inda ta cije shi, ta
duka ta shiga kwashe abinda ya xubar snn ta
mika masa ledan tace “ungo” ya fixge yace “wllh
ba ruwana dake daga yau” tayi narai narai da ido
kmr xata yi kuka ta mika masa hannunta tace “to
rama” ya kama hannun ya durkusa gabanta ya
daura hakoransa kan yatsunta, ta rumtse ido tana
yarfe dayan hannun ya gatsa mata cixo shi ma
snn ya sake, ihu ta fasa ta shiga yarfe hannun ta
fashe da kuka tace “wllh sae na gaya ka da
babana” ya fashe da dariya yace “to ae ke kika
ce in rama” rikota yyi ganin guduwa take son yi
tana kuka, don ba karamin xafi cixon yyi mata ba,
da sauri yana dariya yace “srrry kanwata kema
rama kuma” ta fixgo hannunsa ta gatsara masa
wani shegen cixo, yyi kara yana yarfe hannun ya
mike ya dauki ledan yace “to mu tafi” suka ci
gaba da tafiya tana tsotsan inda ya cije ta sae
kallonta yake har suka iso anguwarsu, ta juya
tana kallonsa tace “oya ka tafi to ga gidanmu
can” yace “baki son in gaida mama Ikram” kmr
xata yi kuka tace “to ae dukan mutane take yi,
nima ynxu nasan dukana xata yi” ya tsura mata
ido yace “mu je in roketa kar ta dokeki” da sauri
tace “A’a ae sae ta dokeni, ta bayi na yi tsalle na
fita daga gida daxu don ta rufe kofar xaure wae
baxan fita ba ni kuma ina son in fita” ya xare ido
yana kallonta da mamaki, kan yace komai tace
“lahhh ga Abbana can ya dawo” da gudu ba tare
da ta kuma kallonsa ba tayi gaba, ya shiga
kiranta ta karbi abinda mami ta siya mata amma
ina, dae dae kofar xaure suka ci karo da Abbanta
ta rungumesa tana masa oyoyo yace “daga ina
kike Mamata” tana washe hakori tace “can” jan ta
yyi ba tare da ya lura da kayan jikinta ba suka
shiga ciki, Aliyu yyi murmushi ya juya ya bar
wajen don Magrib yyi. Suna shiga tsakar gida
Ammi ta fito da wayar rediyonta Ikram tayi waje
da gudu tana ihu, Abba yace “wae meye hka kike
Aisha me tayi maki” Ammi tace “ae wlh ta koma
ta shigo gidan nn ta inda ta fita idan ba hka ba
wllh sae na faffasa mata jiki yau”

Post a Comment

0 Comments