Ikraam 93

Latest Posts

6/recent/ticker-posts

Ad Space

Ikraam 93


93….. Da kyar Khaleel ya iya dagota ya kwara mata ruwan da ya debo ya juya xae bar wajen, ba shiri ta dawo ta fasa ihu a tsorace muryar ta na rawa take cewa “don Allah don annabi kar ka min komai ya Khaleel wllh tsoro nake ji plsss ka tausaya min” komawa can bakin gadon yyi a hankali ya sauke kafafuwansa kasa ya dafe kansa, jikinta na rawa har lkcn bata fasa kukan da take ba ta shiga kkrin sauka daga kan gadon tana yi tana kallonsa, fixgota yyi cikin xafin nama ta fado kansa xata saka wani ihun ya rufe bakinta da sauri murya can kasa ba tare da ya kalleta ba yace “bbu abinda xan maki, koma ki kwanta” cikin kuka mae ban tausayi tace “kace wllh ya Khaleel” a hankali yace “wllh” shiru tayi jikinta bae bar rawa ba har lkcn tana sauke ajiyar xuciya, sun fi minti biyar a hka ya kwantar da ita a hankali snn ya mike da kyar ya shiga bathroom, ta shige cikin bargo ta shiga rusa kuka kmr ranta xae fita, yana fitowa daga bathroom bae ko kalleta ba ya nufi daya side din gadon yyi kwanciyarsa tare da juya mata baya. Washegari hasken rana ne ya tada Ikram don bae tasheta ba, ta mike xaune da sauri tana kallon agogo taga bakwae da kusan rabi da sauri ta fada bathroom tayi wanka snn tayi alwala ta fito, tana cikin sllh ya shigo dakin, kallo daya yyi mata ya kwashi wayoyinsa dake gaban Madubin dakin yyi ficewarsa, tana idar da sllh ta tabe baki ta mike ta bude jakarta ta ciro brush dinta ta koma bayin ta wanke bakinta ta fito snn ta ciro kayan da xata sa, atamfa ce riga da skirt an mata dinkinta dai dai jikinta, ta gama shafe shafenta tasa under wears tana cikin sa riga Khaleel ya shigo dakin ta mayar da xaninta kirjinta da sauri, yana kallonta bbu yabo bbu fallasa yace “ina jiranki a falo idan kin gama xamu tafi gida” ta bata fuska tace “wani gidan?” bae tanka ta ba ya fice ta dan yi tsaki ta gama sa kayanta snn ta sauko falo don jin wani gidan xa su, yana kallonta yace “ina jakar taki, ko nn xaki bar shi” tace “to wae nn ba gida bne ko ina xa mu? Ni fa bana son ganin yarinyar da kace min ka aura don ni xan iya fasa mata kai idan na ganta, don hka gwara kawae ka bar ni a nn” ta karashe mgnr tana murguda baki, Khaleel ya mike yana rike da makullin motarsa ya nufi kofar fita, da sauri ta bi bayansa ta saka kuka tana cewa “au tafiya xaka yi, to ni baxa ka tafi ka bar ni kadae a gidan nn ba” tana isowa inda yake ya fixgota suka fito daga gidan ya kulle kofar da key, fuskarsa a daure ya ja ta ya nufi mota da ita ya bude bayan motar ya jefata ciki ya rufe ya xaga ya shiga driver seat yyi horn maigadi ya fito ya bude masa gate ya fice daga gidan, har suka isa gida bata bar kukan da take ba bayan mota kmr xata fasa masa kunne, ssae kukan nata ke bata masa rae amma ya danne xuciyarsa ya gama parkin ya bude motar ya fita ya nufi kofar shiga gidan, fitowa tayi ita ma da sauri ta bi bayansa dae dae bakin kofa ya juya ya shaketa yana huci yace “ki dinga kiyaya na ikram, na maki wani abu ne xaki sa ni gaba kina min kuka don uwarki” ya karasa mgnr cikin tsawa ya turata a fusace har tana neman faduwa yyi cikin gida abunsa, sae da ta gama cin kukanta nan tsugunne a balcony snn ta mike tana share hawayenta ta shiga cikin gidan, bbu kowa a falon ta gama kalle kallenta fuskarta a tamke snn ta haura sama ta tsaya corridor din dakunan xuciyarta na bugawa tana neman ina ne dakin amaryar, dakin dake kusa da nata ta bude, xuciyarta ya kusan shigewa cikinta ganinta xaune cikin wani leshi mae shegen kyau bbu dankwali kanta gashinta har kusan bayanta, shi kuma yana xaune dab da ita suna facin juna ya dago kanta ya kafa mata ido yana kallo ko me yake ce mata oho, kyakkyawa ce maryam ta karshe, ssae Ikram ta gane ta, ta shigo dakin kmr mahaukaciya ta fasa ihu tayi kan maryam tana cewa “la ila ha illalahu, keee me ya shigo dake gidana har da kwalliyar ki, wllh yau sae na fasa maki kai” Maryam ta mike tana kallon Khaleel dake bin Ikram da kallo baki bude, a fusace ya fixgota ya kifa mata mari mae rae da lfya ya yyi waje da ita ya wurgar snn ya rufe kofar dakin, Maryam tace “kaga ka ja mata kunne ta daina shigo min daki hka Khaleel don ni ban ciki da halin jakanci, ita wnn yaushe ta balaga da har xata san wani kishi, to in kanta rawa yake ni hauka nayi, kaji min dae” shiru Khaleel yyi yana kallonta snn yace “hka muka yi dake Maryam, ban gaya maki irin warce xa ki shigo ki tarar ba” tace “to ae wnn ba yarinta ke damunta ba samun waje ne kawae” tana fadin hka ta dauki dankwalinta ta daura xata fita yace “ina xaki?” tace “breakfst xan kawo maka mana” yace “A’a ki bari ba ynxu ba sae ta bar falon” wani kallo ta watsa masa snn ta fice abunta, Ikram na durkushe falo sae rusa kuka take kmr xata tsaga gidan Maryam ta sakko, tana ganinta ta mike da sauri tayi kanta tana huci tace “ina kike tunanin xaki, ance maki gidan ki ne nn” Maryam ta watsa mata wani mugun kallo tace “kika kuskura ki iso gabana wllh sae na nakada maki shegen duka”
[2/25, 08:43] Zjy: ~

Post a Comment

0 Comments