Adandi 10

Latest Posts

6/recent/ticker-posts

Ad Space

Adandi 10


*10*

 

Komawa tayi ta kifa kanta saman pillow taci gaba da rera kukanta tana fadin “ Innanillahi wa innah ilaihirraji’un” Rahmah ce ta dafa bayanta tace “kiyi hqr Samha ki sanyawa zuciyarki dangana insha Allahu zaki samu wanda ya fishi….” Saurin zabura tayi tace “ a Ina Rahmah waye shi? Babushi duk duniya Rahmah shi na fara so kuma shi zanci gaba daso har bugawar numfashina ta qarshe” Jan hanunta Rahmah tayi ta zaunar da ita lkcn da Mansoor ya miqe ya gaji da ganin wannan abin tausayin ji yakeyi dama shine ya samu wadda take sonsa haka da gsky da bazai taba wasarairai da rayuwarta yayi kantafi da soyayyarta haka ba.

 

Fita sukayi Ja’afar yanajan motar suna sauke numfashi kowa da abinda yake saqawa a ransa.
Saida ta qara kwana daya a asibitin sannan aka sallameta jikinta ya warke amma zuciyarta bata warke ba saboda kullum cikin Kiran wayar Abdullah take amma baya dagawa saida ta kuma kwana uku a gda sannan ranar Monday ta shirya domin zuwa makarantar cikin wani blue black din hijjab take dogo har qasa daga takalminta har safarta duk blue black ne glass din idonta medical shine kawai fari tayi kyau sosai abinka da kyakkyawar asali kallo daya zakayi mata ka fahimci ramarta.

 

Tana shiga dakin daukar karatun aka rinqa yi Mata sannu ciki harda su Zainab da suka raba gari dasu saboda Abdul yace bayason mu’amalarta dasu guri ta samu ta zauna tana nazarin littafin philosophy Dr Sa’ed shine zaiyi musu lecture ta farko har gda yaje dubata kuma yaje asibitin shigowa yayi ya fara gabatar da darasinsa harya gama ya fita batamasan me yayi ba wani dalubi ne yazo ya tsaya kusa da ita yace “Mrs Samha Dr Sa’eed yana nemanki yace ki sameshi a office dinsa.

 

Kamar kar take sai kuma dai ta tashi ta dauki Jakarta ta fita ta nufi office din nasa ta mursa handle din yayi Mata izinin shiga sannan ta shiga zama tayi inda ya nuna mata nutsuwarsa ya tattara gaba daya ya bata yace “Samha mgn nakeso muyi dake me muhimmanci don Allah ki tsaya ki fahimceni sosai kafi ki yankemin hukunci”cikin qosawa tace “ina sauraronka Sir” ajiyar numfashi yayi ya sake bata hankalinsa yace “lkc naga yanata tafiya batare dana bayyana miki sirrin zuciyata ba wlh Samha tun ranar dana fara dora idona akakin naji ina sha’awar rayuwa dake rayuwa ta aure ta har abada ki taimaka ki dorani a mizani ki aunani idan nayi daidai da mijin da zaki iya aure toni a shirye nake dana tura gdanku ayi mgn don Allah Samha kada kicemin a’a”

 

Wani lalataccen kallo ta rinqa yimasa har ya gama fadar abinda zai fada ta tattara yawun bakinta ta hadiya daqyar tace “ok shikenan abinda zaka fadamin” daga mata kai yayi cikin zaquwa dason jin abinda zatace amma ga mamakinsa sai yaga ta miqe tana shirin fita da sauri ya riqe hijjab dinta ya zagayo gabanta yace “ki fahimceni Samha wlh bada wasa nake miki ba tunda harna kasa daurewa na fada miki inasonki aduk yanda kike inasonki da halinki ki amince dani zakiyi farin ciki…” a fusace ta juyo ta kalleshi tana nunashi da yatsa wanda yasashi saurin jada baya cikin rawar murya tace.

 

“Dama iyakar tunaninka Dr kana tunanin qaddarar haduwa dakai ce ta kawoni B.U.K matsayin dalubar Spychology? Uhm to kayi saurin sake hasashe domin falsafarka ta fada maka qarya nace qarya zuciyarka take fada maka mallam so dayane tak kuma na riga na bayar dashi ga wanda ya cancanta saboda haka kayi gaggawar mayar da kalamanka inda ka fito dasu na barka dasu basu da guri a zuciyata”

 

Tana kaiwa nan ta juya ta fice da sauri tana hada numfashi kusan a makance take tafiyar har tazo daidai faculty dinsu Abdul din haka kawai zuciyarta ta rinqa umartarta data shiga koda zai daketa batare da tsayawa shawarar me hakan zai haifar Mata ba ta nufi cikin gurin zuciyarta na bugawa da qarfi kan wata kujera ta hangeshi shida abokansa ya dora hanunsa a kansa kamar wanda ya tafi duniyar tunani.
A nutse ta qarasa tare dayi musu sallama suka amsa mata tare da kallonta ta fahimci kallon da sukeyi Mata na tausayi ne amma banda Nasir data fahimci kallon mara zuciya yakeyi mata murmushi tayi saboda ita kanta batasan bata da zuciya ba sai akan Abdul tace “kuyi hqr ko zaku iya bani aron abokinku don Allah” murmushi Ja’afar yayi yace “keda mijinki waye zai shiga tsakaninku yaji kunya”

 

Maye gurbin inda Ja’afar ya tashi tayi tare da saisaita muryarta tace “My Abdul” sauke hanunsa yayi tare da sakin ajiyar zuciya ya zuba fararen qananun idanuwansa a kanta qasa tayi da idonta wasu hawaye nasu zafi suka zubo mata tayi qarfin halin cewa.
“Ya jikinka dazu Rahmah take fadamin kayi fama da ciwon kai” a gajarce ya amsa da cewa “da sauqi yana qoqarin tashi ta ruqo hanunsa bata damu da irin kallon da yake Mata ba tace “bazanyi maka dole kasoni ba My Abdul amma nasani ko bayan Raina idan soyayyarka tayi nasarar halakani zakake tunawa dani a matsayin masoyiya ta haqiqa wadda ta qaunaceka domin Allah na yarda da naqasun tarbiyyata daya zamemin katanga da samun farin cikina na yarda ban cancanci zama matarka ba kamar yanda ka fada amma inaso koda zaka yanke alaqa dani din girman Allah ka cireni daga matsayin daka ajiyeni wlh niba karuwa bace bantaba zina ba ka yarda dan….”

 

Fuzge hanunsa yayi yana qara maida hankalinsa ga kallonta yace “taya zan gasqataki Samha bayan kina shaye² nasani kuma maye babu abinda baya sanyawa shiyasa aka haramtawa duk wani musulmi na qwarai shan wani abu da zai gusar masa da hankali Samha kiyi gaggawar cire mgnr so tsakanin mu idan ba hakaba zan yanke igiyar zumuncin dake tsakanina dake kuma kamar yanda na fada miki a farko abokaina sune suka roqeni naci gaba da zama a matsayin yayanki kuma malaminki kamar yanda kika buqata” cikin kuka me ciwo tace “hakan ma na gde indai zan sanyaka farin ciki to zanyi biyayya ga umarninka koda kuwa zan rasa duk wani haske na rayuwata amma Ina neman alfarmar kaci gaba da zama a matsayinka na malamina kuma yayana My Abdul jahilcina ga abinda ya shafi addinina shine ya haifarmin da shiga halin da nake ciki a yanzu don Allah kada kabada qofar da wannan tawayar zaisa wani yaqi qanwarka kamar yanda kaima kaqini My Abdul please…”

 

Sosai kalaman nata na qarshe suka daki zuciyarsa zuba mata ido yayi yanason gano aibin yarinyar da zuciyarsa taqi amsarta a matsayin abokiyar rayuwa yanda take kukan riqe da qafarsa ya sanyashi jin wani mugun tausayinta baisan sanda ya sanya hanunsa ya dagota ba yasa yatsansa ya share mata hawayen yace.
“Insha Allah bazan gaza ta wannan bangaren ba kinji qanwata” daga masa kai tayi tace “na gde da hakanma”

 

Tana fadin haka ta juya ta fice daga faculty din yabi bayanta da kallo zuciyarsa na bugawa da qarfi yanajin ninkin tausayin yarinyar a zuciyarsa tabbas da zai iya daya daya karbi soyayyarta amma yasan bazai taba iya auren macen da tasan maza ba yanada yaqinin qaryane abinda take fada masa na cewa bata taba zina ba.
Daqyar ya iya daga qafarsa ya nufi teather din da zasuyi lecture ya zauna Mansoor ya kalla yace “tausayin yarinyar nan yana neman karyamin burget Manson wlh dazan iya dana karbi soyayyarta amma bazan iyaba bazan iyaba Manson” Khamal ne ya magantu da cewa “tausayi matakin farko ne na so Abdul na tabbata abinda kakeji game da Samha ya wucce tausayi ko ka yarda ko kada ka yarda zuciyarka ta kamu da son yarinyar nan” miqewa yayi zai fita Khamal ya ruqosa yace “ba dole nace ka yarda ba amma ni na sani kanasonta….”

 

Daga masa hanu yayi yace “ya isa Khamal nagaji da sauraron wadannan yan iskan kalaman naka me zanyi da ita Khamal idan na amince da wannan ballagazar yarinyar me zata bani me zan karba a gurinta da zai zamemin abinda zanke dubawa nayi farin ciki a darenmu na farko babu ta rabar muku komai Khamal qila kaima ka taba dandana ko dolene a gurina na zabawa yayana uwa tagari mezan fada musu idan suka taso sukaji tarihin uwarsu karma akai ganan wlh tallahi Khamal ba Samha danasan halinta ba ko watace da bansanta ba na aura nakai mata samartaka ta nikuma najita ba budurwa ba wlh a daren saina yanke igiyoyin aurena uku a kanta ko wacece ita to kuma menene zaisa nayi abinda zai dameni ina sane”

 

Yana fadin haka ya juya ya zai fice daga Hall din Ja’afar ne ya daga murya yace “dama nasan tunaninka kenan Abdullah amma ka sani sona gsky baya duba cancanta akan dauko mace ADANDI ma a sata tayi istubura’i kuma a aureta a zauna da ita zama na soyayya balle Samha da duk wanda ya kwana ya tashi a skull dinnan yasan bata zina”……

 

 

 

*UMMUH HAIRAN CE…✍*
[2/11, 2:59 PM] UMMUH HAIRAN CE…✍: *_AD_*

 

*_Dont read this book if you are not married. Mature content contained in it. Reader discretion is advised. You read at your own risk._*

Post a Comment

0 Comments