Adandi 11

Latest Posts

6/recent/ticker-posts

Ad Space

Adandi 11


*11*

 

Ana cikin wannan badaqalar suka fara jarabawar zangon karatu na farko itadai Samha pepar kawai take zanawa amma batasan me take rubutawa ba saboda haka ta cire tsammani da samun sakamako me kyau kamar yanda ta sana samu haka sunkayi exams din sukayi hutu zuciyarta cike da kewa da tunanin rashin abinda takeso ta tattara ta dauki wannan a matsayin qaddararta saboda duk yanda taso shawo kan Abdul abin ya faskara har yanzu sun kasa komawa normal sometimes ko wayarta baya dagawa idan kuwa tayi saa ya daga to gaisuwa ce kawai zai kashe wayarsa takanyi kukan zuci harda na fili a bangare guda kuma ta dage wajen neman sauyi gurin buwayi gagara misali mai Rahmah a duniya me jinqan muminai a lahira amma abin mamakin bata tabajin wani yanki na qaunarsa ya ragu a zuciyarta ba koda second daya.

 

Satinsu uku a hutun suka dawo itama akayita ta qare lkcn da suka dawo semester da zasuyi project lkcn ne aka kafe musu results bata da carry over amma point dinta yayi qasa sosai lamarin da yake sabo a gurinta da duk wanda yasanta a baya duk sanda aka kafe results itace take samun point mafi rinjaye a Department dinsu sai gashi wannan karon ta samu point din dabai gaza biyu ba al’amarin daya sosa zuciyar masoyanta ciki harda malaminta da yake burin mallakarta a matsayin mata.

 

Tana zaune a gerding wayarta tayi tsuwa alamar tana neman agajinta sanya hanunta tayi ta dauka wayar tare da karawa a kunnenta batare data damu da ganin sunan me Kiran ba “salam” ta furta cikin sanyin muryarta da take qara narkar da zuciyarsa yace “My love idan babu damuwa kizo inason ganinki” miqewa tayi ta dubi Rahmah daketa yimata mitar faduwar baqar tasar da tayi a jarabawa tace “tashi ki rakani Dr Mus’ab ke nemana” miqewa tayi suka nufi office din nasa da sallama suka shiga inda idonsa dake cikin tabarau yake kanta zama tayi tace.

 

“barka da rana Sir” ajiyar zuciya yayi tare da rufe laptop din dake gabansa ya miqe ya nufota cikin nazarin yanayin abar qaunartasa ya dade da fahimtar tana cikin damuwa amma bai taba tunanin damuwarta takai wacce zatayi kantafi da makomar karatunta ba cikin dakiya irinta mazajen fama yace “Samhatu menene yake damunki dahar yasa kikayi riqon sakainar kashi da rayuwarki ta hanyar rusa plan dinki na zama cikakkiyar masaniyar halayyar dan adam meyasa My love don Allah ki fadamin gsky ban sanki da qarya ba kuma bazan taba yafe miki ba natsawar kikayimin qarya”

 

Ajiyar zuciya tayi cikin so da qoqarin aro juriya ta sanyawa kanta ta taqarqare ta fara yimasa bayani kamar haka “riqon sakainar kashi kace ko Sir? Ina roqonku daku daina zargina bani na zabawa kaina hakan ba qaddarata ce ta zabamin haka kunsan kuwa ita qaddara hade take da bugawar numfashi babu yanda zanyi da ita dole na karbeta ayanda tazo mani” duk kalaman nata bai fahimci komai ba saison goge laifinta ta hanyar alaqantashi da qaddara qara tattara nutsuwarsa da hankalinsa yayi yace “kiyimin bayani yanda zan gane My love ko zan iya taimaka miki Samha son gsky baya buqatar ki fahimceni zan karbeki a duk yanda kika zomin”

 

Sai yanzu kukan da take qoqarin hadiyewa ya kwace mata cikin tashin hankali yace Mata “ya salam Samha me nayi miki kiyi hqr don Allah…” Bata ankara ba saijin hanunsa tayi saman fuskarta yasa harshensa yana lashe hawayen nata ta rintse idonta da qarfi duk yanda takeson tsayar da kukan takasa tausayin kanta da tausayin malamin nata suna qara fasa bargonta suna shiga jikinta sukuma qaddararsu kenan yana sonta tanason waninsa son maso wani daqyar ta iya janye fuskarta daga hanunsa ta miqe tana har hada hanya tace “qaddararmu kusan iri dayace malam kana sona inason waninka na dade da amincewa kokawar zuwa in tadda qaddarorina ya hanani bin zabin iyayena na tafiya qasar England domin yin karatuna na nace sai nazo B.U.K nayi karatu Sir qaddara uku itace take wahalar dani dakai da duk wani masoyina”

 

Cikin mugun tashin hankali yace “wadanne su Samha guda uku tak fadamin su please kada ki heading dina komai” yana kaiwa nan ya saketa inda ta koma ta zauna qasan tiles Rahmah kuwa ficewa tayi saboda gaba dayansu tausayi suke bata.
Dubansa tayi bayan ta saisaita nutsuwarta kadan tace “qaddara ta farko shine haduwa da mugayen qawaye wadanda suka rinqa bugamin gangar shaidan suna fadamin ni babbar yarinya ce wanda hakan ya hadu yayi tasiri a cikin rayuwata mara foundation din kyakkyawar tarbiyyar nunawa duniya wanda hakan ya zamomin tawayar da qaddarata ta biyu take guduna da qoqarin nisanta kanta dani Sir Abdullah shine qaddarata ta biyu shine namiji na farko dana faraso a duniya sonsa shine yake wahalar dani yaqi karbata yaqi gasqatani yaki yarda da cewa Samha ba karuwa bace Samha ba mazinaciya bace samhan yanzu batada nace Sir inaji a jikina soyayyar Abdul itace zatayi sanadin katsewar numfashina Sir kai kaine qaddarata ta uku kana sona ka yarda zaka rayu dani aduk yanda nake ka dauki matsalata ka mayar taka amma kash zuciyata tayi nisan da bazataji kiranka ba wlh da ina da yanda zanyi dana cire Abdullah a zuciyata na maye gurbinsa dakai a hakanma na gde da results din da kuka bani musamman kai daka banj A bayan nasan ban shuka tsiyar da ko D zan samu ba Suma sauran malamaina sunyi qoqari sosai wajen yimin adalcin dana kasa yiwa kaina da rayuwata ta gaba.

 

Miqewa tayi ta dauki Jakarta ta fice daga office din baiyi yunqurin hanata ba saboda yasan ko ya tsayar da ita bashi da sauran kalma daya data saura dazai iya furta mata ta gama daureshi da jijiyoyin jikinsa jan qofar da tayi ne ta rufene yayi daidai da zubowar wasu zafafan hawaye a idonsa ya jima a zaune yana tunanin abinda ya kamata yayi yasan shima yana yana cikin matsalar rayuwa domin bashine ya dorawa kansa sontaba shima qaddarar tasa rayuwar ce tazo da haka “waye Abdullah din da take iqirarin tanaso? Shikuwa wanne irin mara saa ne a rayuwa da yakewa soyayyar mace irin samha Sa’ad Dandoki riqon sakainar kashi?” Tambayar da yayiwa kansa kenan ya miqe ya fara zagaya office din lallai shima ya tabbata mara saa daya kasa samun zuciyarta meyasa ta kasa bashi guri koda bazai wucce fadin qaramin yatsaba a zuciyarta? Ya sake tambayar kansa amma babu amsa a wajensa.

 

 

*UMMUH HAIRAN CE…✍*
[2/11, 2:59 PM] UMMUH HAIRAN CE…✍: *_AD_*

 

*_Dont read this book if you are not married. Mature content contained in it. Reader discretion is advised. You read at your own risk._*

Post a Comment

0 Comments