Adandi 23

Latest Posts

6/recent/ticker-posts

Ad Space

Adandi 23


23*

 

Miqewa tayi ta nufi cikin gdan yayi saurin shan gabanta yace “ki fahimceni Samha kada kiyi fushi saboda gudun irin wannan yasa na boye miki gsky” tsaya ta saurareshi ba ta shige gdan daidai lkcn da Dad da Mamy suke sakkowa daga sama Dad ya tareta da sauri yace “lfy meye ya faru Aishatu?” Cikin kuka tace “na hqr da dauren Dad wlh bazan aureshi ba Dad ya yaudareni ya munafurceni dama Abdul ya fadamin Mus’ab yana boyemin wasu abubuwa Dad kabashi kudinsa don Allah Dad kada ka takuramin na aureshi….”

 

Riqeta Mamy tayi tace “Waime yake faruwa ne meye ya faru tsakaninki da Mus’ab din?” Cikin kuka tace “yanada aure Mamy kuma wai mu biyu zaya aura yanzu Dad Mamy Mus’ab bashida gsky” wata uwar zabura Mamy tayi tace “yana da Mata kuma ku biyu zai aura kambu wannan rashin mutuncin ba anan ba wlh bazai yuwu ba” shikam Dad zama yayi yana nazarin abun bai iya cewa komai ba ya miqe ya fita ya tarar da Mus’ab a tsaye ya kama hanunsa yace “Aishatu tazomin da wani zance na yarinta Mus’ab mene gskyr lamarin nan?” Sunkuyar dakai yayi alamun rashin gsky ya fara sosa kai yana zayyano masa kamar yanda ya fadawa Samha gwauron numfashi Dad ya ajiye ya jinjina kai yace “shikenan kaje zan nemeka”

 

Yana fadin haka ya juya ya shiga gdan lkcn Samha ta shiga daki so Mamy a tsaye tanata huci ta tareshi tace “ya kukayi dashi?” ajiyar numfashi yayi yace “abinda ke akwai kenan” kallonsa ta kumayi da sauri tace “kawai ka mayar masa da kudinsa tunda dama gobe ake shirin kawo lefe sai kawai ya hada ya kaiwa waccan din amma yata bazata iya wannan auren ba Mata biyu ita ta uku ina laifinma daya ita ta biyu Ina da sake wlh da sake Dad bafa zai yuwu ba nifa idan babu dama yaronnan Na’im ya dawo satin daya wucce ma har tsaraba ya kawomin da kuma atamfofi har uku kawai ka bashi dama ya turo ayi mgnr amma wlh yata bazata taba auren irin Gdan sarautar Katsina ba na tsani ahlin Sa’eed kuma azan taba hada jinina dasu ba…”

 

Dafe kuncinta tayi da sauri saboda baqon abinda bata taba sani ba a gurin mijin nata ya nunata da yatsa yace “kina haukanki Lubabatu nine da dangina muke da iko da Aishatu bakeba kuma daga rana irin ta yau zan fara gwada ikona akanta bandama rashin kara irin taki harni zaki kalli tsabar idona kice bakyason dan dan’wana wanda mukazo duniya tare to bari kiji da Sa’eed da Sa’ad abu dayane kuma dole ki hqr da tsarin masarautarmu don bans tare da masarauta ba yana nufin nabarta kenan ba so Samha ta Mainah Abdu ce kuma tunda abin naki yazo da rashin mutunci wlh babu abinda zaa canza yanda akasa da Mus’ab haka zaayi da Abdu ko kinaso ko bakyaso ni dake maga wanda zaibi wani” juyawa yayi ya fice daga gdan zuciyarsa na tafasa yana fita ya kira Mai martaba ya sanar dashi abinda ke faruwa ya tura masa number waliyin Mus’ab a take Mai martaba ya kirashi ya sanar dashi shine waliyin Aishatu yanason ganinsa washegari kuwa sukaxo garin Katsina sosai sukayi mgn ta manya dole Mai martaba yace to babu komai amma fah yarinya tana neman canza raayi saboda haka suzo sati me zuwa zai daura auren Samha da Mus’ab wannan abu ba qaramin citta yabawa Mus’ab ba nandanan ya fara shirye²nsa.

 

Shikuwa Abdul tunda ya rasa Samha ya shiga wani hali lamarin har tsoro ya fara bawa Mai martaba duk ya susuce bashi da aiki sai kuka yaje garin Abuja yafi sau goma haka zai gama yawonsa ya dawo duk ya rame yayi baqi bashi da aiki sai tunani yakan kulle kansa a daki ya bai leqo ko farfajiyar gdan sarautar ba Fulani Amina ta shiga damuwa da lamarin dan nata da soyayya take azabtar dashi gashi baimasan inda zai samu yarinyar da yakeso ba yauma suna zaune ta kawo masa ziyara dakinsa kansa yana saman cinyarta tana shafa sumarsa tana share masa hawayen fuskarsa yace “Fulani Samha tasoni fiye da duk yanda kike tunani ta dauki amanar kanta ta bani ta yarda dani kuma ta nunamin qauna amma naqi yarda da soyayyarta gareni naqi gasqata gskyrta yanzu gashi ta tafi ta barni wlh fulani da nasan inda Samha take zanje tayimin duk hukuncin da take ganin ya dace dani indai zata aminta ta aureni wlh bazani iya rayuwa da kowacce mace ba idan ba Samha ba ita nakeso itace burina fulani naqita saboda ina tunanin bazan taba samun budurcinta ba sai gashi da kaina na rabata da budurcinta a lkcn dabai dace ba na cutar da ita yanzu kallon danakeyi mata a baya shi mijinta zaiyi mata idan ya gane itadin ba varging bace meyasa taqi ta bani damar gyara barnar da nayi da kaina?” Numfashi Fulani ta sauke tace “na fada maka kaci gaba da addu’a idan Samha rabonka ce zatazo gareka ko kai kaje amma kayi qoqarin fitar da mata kasan halin mahaifinku tunda yariga ya sakoka a gaba to saiyayi maka garama ka kawo da kanka kafin ya waiwayeka nasan yanzu hidimar bikin Gimbiya Aysha ne ya dauke masa hankali amma tabbas zai waiwayeka” ajiyar zuciya yayi ya share hawayensa yace “gobe zan sake komawa Abuja idan na dace na sameta zan dawo idan ban sameta ba zan wucce England zanyi wani aiki na wata takwas bazan fadawa Mai martaba ba saboda nasan bazai barni ba zaice sai nayi aure sannan na tafi”……

 

 

_Don Allah kuyimin hqr kaina ke ciwo Allah ya bamu alkhairi_

 

 

 

*UMMUH HAIRAN CE…✍*
[2/14, 9:08 AM] UMMUH HAIRAN CE…✍: *_AD_*

 

*_Dont read this book if you are not married. Mature content contained in it. Reader discretion is advised. You read at your own risk._*

 

Post a Comment

0 Comments