Adandi 24

Latest Posts

6/recent/ticker-posts

Ad Space

Adandi 24


*24*

 

Washe gari tunda yayi sallar asuba bai koma gdan sarautar ba kasancewar tun dare ya hada kayansa yakai gdan Manson qarfe takwas zakara ya bashi saa yabar garin Katsina inda ya dauki hanyar Abuja zuciyarsa cike da zulumi yanabin address din da Rahmah ta bashi harya isa layinsu Samha amma saidai kashhh yana zuwa sojojin da suke gadin gdan suka tabbatar masa da sun tafi garinsu bikin Samhan saura kwanaki uku a daura mata aure rashin sani da akace yafi dare duhu ashe gda dayama suka kwana da ita kasancewar shigar dare sukayiwa birnin Dikko.

 

Ba qaramin girgiza yayi ba da yasamu wannan mugun lbr ya jima a zaune a cikin motar yana tunanin abinda ya dace yayi zuciyarsa na bugawa da qarfi yana Kiran sunan tare da neman agajinsa cikin gaggawa saura kwana uku auren Samha da Mus’ab? Ya tambayi kansa tare da juyawa ya nufi airport saboda baiga amfanin zamansa a 9ja ba da yake dama yayi booking bai samu matsala ba jirginsu ya tashi bayan ya kira yayansa Farooq yace yazo ya dauki motarsa a filin jirgin saman Abuja wannan kenan.

*****

A bangaren amarya Samha kuwa hidima ta kankama ta biki duk wani abu da akeyiwa amaryar gdan sarauta fulani Amina tasa anyi mata sunje lalle ita da Yasmin tare da gyaran gashi Rahmah ma tazo tare suketa kaikawon bikin qasan zuciyar Samha fal da zulumi Allah ya sani don dai shima mahaifinta umarni yakebi ne amma da babu abinda zaisa ta auri Mus’ab mutumin da ya boye mata wasu bangarori na rayuwarsa daya kamata ace ta sani.
Da wannan tunanin akaci gaba da shagalin biki itadai Samha bata wani nuna farin cikinta da auren nata Yasmin ce takeyi mata tsiya takance “wai saikace ba auren soyayya ba Princess Aysha duk kin wani takurawa kanki da koke koke ai kawa ki saki jikinki abune daya zama dole a gurin kowacce mace keda zaama keta hazo dake abar qasar dake kodai kinada wanda kikeso ne?”

 

Takan kada mata kai tace “aa kawai dai inajin zuciyata bata na’am da auren nan ne Yasmin” hakadai zasuyita tausarta harta dan saki jikinta aketa hidimar da ita Mamy kam tananan sai quncin rai takeyi ita a dole Gidado Sa’ad yayi mata laifi ya dauko biki ya kawo garinsu yan’uwansa sai wani gani-gani sukeyi mata shidai bai kulata ba duk da lura da rashin walwalarsa da tayi bata tambayeshi baasi ba shima bai fada mata ba.
Ana gobe daurin aure ne fah salon biki ya canza bushe² da kade kade suka qaru a gdan daga Samha har uwarta har fulani Amina da Yasmin babu wanda yasan meke faruwa kawai dai hidima suketa yi Mamy kam ko bangaren fulani Amina bata taba zuwa ba tunda sukazo fulani Amina dake mace ce me sauqin kai ko a jikinta saidai idanma wani abune ta karya billenta taje ta tambayi Mamy tana yatsina tanashan qamshi zata bata amsa bata wani damuwa tunda dama tasan ba dasawa sukeyi ba fulani Hadiza itace makira irin Mamy saboda haka tunda Mamy ta iso suka jorner kasancewar me martaba matansa biyu Fulani Amina itace babba kuma itace me Yaya hudu Mainah Abubakar shine babba sai Mainah Farooq sai Mainah Abdullah wanda suke Kira da Abdu sai kuma Gimbiya Yasmin sai fulani Hadiza itace Mata ta biyu bata taba haihuwa ba hakan ne yasa ta dauki karan tsanar duniya ta dorawa yayan gdan musamman Mainah Abdu wanda shi yafi kowa fada gurin ubansu saboda miskilancinsa da izzarsa ga uwa uba rashin barin ta kwana baya daukan raini a cikin masarauta shiyasa ya zama gagarabadau na masarauta kowa ya debo raininsa a waje yake zubarwa ciki kuwa harda Fulani Hadiza baya raga mata ko kadan shiyasa take mugun tsoronsa wannan yasa data fahimci tsananin qiyayyar Mamy gareshi dalilin marin daya taba tsinka mata tun yana yaro saboda ta zagi babarsa yasa fulani Hadiza shigewa jikinta saboda su samu damar gamawa dashi cikin sauqi.

 

Ranar asabar ta kama ranar daurin auren Samha da Mus’ab kamar yanda kowa ya sani qarfe 12:00pm akasa saboda dangin ango da suke da nisa ilai kuwa kamar yanda aka tsara din hakace ta kasance sha biyu daidai maroqan fada suka fara shela suna fadin “Alhmdllh zumunci yayi albarka rayuwa tai albarka a yau mun shaida daurin auren Mainah Abdallah Sa’eed Dandoki da Gimbiya Aysha Sa’ad Dandoki akan sadaki mafi daraja…”

 

Tashin hankali wata uwar zabura da Mamy tayi ta miqe ta qunduma wata uwar ashar tace “idan na yarda Allah ya tsinemin albarka wlh bazai taba yuwuwa ba ni Lubabatu ni zaayiwa rashin mutunci a rasa wanda zaa aurawa yata sai dan iskan fitsararren yaron nan wanda uwarsa tai cikinsa da rana aa bazai taba yuwuwa ba dole da sake bama fa zai yuwu ba” babu kunya saiga fulani Hadiza nan ta shigo da gudunta ta riqe kafadar Mamy da taketa mazari saboda bala’i tace “wai da gaskene abunda nakeji Abdallah suka bawa Ayshatu…” Cikin qunar zuciya tace “barni dasu Hadiza zanyi maganin matsiyata da daidai duk munafurcin na shegiyar matar nan ne itace take shirya komai nikam makircinta bazaiyi tasiri akaina ba da yata wlh ni Lubabatu ban haifawa Mainah Abdu matar dazai kwanta da itaba ina qaryane wlh”

 

Daidai lkcn Dad ya shigo parlourn yanda yaga ta nufoshi gadan² yasashi tsayawa ya zuba mata ido tana zuwa ta damqi kwalarsa tana girgiza qugu tana fadin “baka isaba Gidado wlh kayi kadan Samha yatace nice na haifeta saboda haka bazata zauna da dan iskan tujararren yaron ba dolene a warware auren nan kafin na gwada maka kalar haukana” murmushi yayi ya cire hanunsa daga wuyansa yace “to Lubabatu bismillah haukanki wanne irine ban sani ba auren Aisha da Abdullah ne yariga ya dauru babu abinda ya isa ya rabashi saboda haka kiyi hqr kawai haka Allah ya tsara” ficewa ya juya yayi ya nufi bangaren fulani Amina saboda tunda sukazo Samha tabar bangarensu ta koma can yana shiga ya tarar da ita a jikin fulani Amina a kwance tanata gursheqen kuka tana cewa “meyasa Dad zaiyimin haka meyasa bazai barni na kawo wanda nakeso da kaina ba Fulani kice su janye aurennan don Allah banaso wlh banaso bansan wacce irin karba Mainah Abdu zaiyimin ba bazai taba yarda dani ba kuma bazai taba aminta da abinda zan fada masa ba…” Dagota taji anyi ta fada jikin Dad tace Dad meyasa haka meyasa zakayimin haka Dad banasonsa meyasa zakuyimin auren dol…” Rufe mata baki taji anyi ta baya ta sake bude idonta tar ta saukeshi akan Abdul dake gyara tsaiwarsa cikin hawaye yace “qarya kike Samha kina sona don Allah ki daina furtamin wannan kalmar haka ki fahimceni ki fahimci iyayenmu”……..

 

 

*UMMUH HAIRAN CE…✍*
[2/14, 3:50 PM] UMMUH HAIRAN CE…✍: *_AD_*

 

*_Dont read this book if you are not married. Mature content contained in it. Reader discretion is advised. You read at your own risk._*

Post a Comment

0 Comments