Adandi 7

Latest Posts

6/recent/ticker-posts

Ad Space

Adandi 7


*7*

 

Taji an kira sunanta dagowa tayi da sauri saboda ta gane muryar malamin nasu ta sauke idanunta akansa yayi mata murmushi yace “ina tayaki murnar gane bambamcin gsky da qarya qimarki da kika zubar a baya yanzu kin samu damar kankarota don Allah ki dawwama a haka zanyi farin ciki sosai”ajiyar zuciya tayi lallai iska tana wahal damai kayan kara tana ganin mutuncin Dr Mus’ab amma tunda yayi Mata nasiha akan sanya hijjab ta tattarashi a bolar rashin mutuncinta.

 

Mayar da kanta qasa tayi saboda kallon da yakeyi mata tace “na gde Sir” daga haka bata kuma cewa komai ba ya sake sauke mata murmushi ya jima a tsaye akanta yanajin qaunar yarinyar tana qaruwa a ransa yana burin samunta da mallakarta a matsayin matar aurensa, juyawa yayi ya fara darasinsa ta hanyar yin gwaji cikin abinda bai wucce 15 minutes ba ta gama ta miqe cikin takunta na isa taje ta miqa masa takardar fuskarta babu yabo babu fallasa saida ta fita sannan ya dauke kansa daga kanta ya sauke idonsa akan takardar kullum yana yabawa da brain din yarinyar.

 

Kai tsaye department din su Abdul ta nufa fuskarta sake cikin niqabi kamar jiya yauma yana zaune shida Mansoor ta tako wasu cikin daluban sun ganeta wasu kuma suna tunanin wacece shikuwa Abdul bai ganeta ba saida ta qarasa ta dage niqaf din sannan ya ganeta ya zuba mata ido tare da fadada fara’arsa cike da farin ciki yace “kyakkyawar shiga gsky kin shammaceni madalla dake daluba ta gari” murmushi tayi me sauti da har yabawa wushiryarta da dimples dinta damar bayyana tace “nayi farin ciki da yabawar malamina” dariya abin ya bawa Mansoor yace “au ashe ka zama malami tab amma kuwa munyi farin ciki da wannan ci gaban malamin malamai”
Yasan da shaqiyanci yake mgnr saboda haka ya miqe yace “tashi muje qyale wannan mutumin bashi da aikinyi ne daluba ta gari” ajiyar zuciya tayi saboda tunda ta tsaya shi take kallo tana qissima irin yayan da zasu haifa idan sukayi aure tabi bayansa suka fita suna fita taja ta tsaya shima ya tsaya yiyi yace “yadai?”

 

Qasa tayi da kanta ta dafe cikinta cikin wata murya datasashi jin wani yarrrr a jikinsa tace “My Abdul inajin yunwa fa” lumshe idonsa yayi ya langwabar da kansa yace “ok” ya juya akalar tfyr zuwa capteriar suna tafe suna hira yana fada Mata irin kyan da tayi cikin hijjab din suna zuwa suka zauna ya qara kallonta da qananun lumsassun idanunsa yace “wlh Samha a duniya babu abinda yake burgeni da mace kamar naganta cikin hijjab inason macen da tasan darajar kanta tasan cewa ita dukiya ce me daraja kuma abar kawwamewa da alkintawa” kafesa tayi da manyan idanunta a sanyaye ta furta “da gaske hakan yana burgeka Abdul?”

 

Yanda tayi masa tambayar ne yasashi saurin hadiye yawun bakinsa tare da qoqarin saita nutsuwarsa batare da ya iya furta komai ba ya daga mata kai alamar “Eh” ajiyar zuciya tayi ta dora hanunta saman table din gabansu ta tallafo habarta ta zuba idanunta akansa tace “zan kasance cikin sanya hijjabi a gaban idonka da bayan idonka Abdul ni kadai iyayena suka haifa shiyasa na taso cikin gatan daya zamemin tawaya a rayuwata bansan ya zanyi na aikata daidai ba duk abinda nace zanyi shi iyayena sukeso bani da wanda zai tsawatar min ya nunamin wannan daidai ne wannan ba daidai bane nasani Abdul da ace inada dan’uwa kamarka qila da hakan bata faru dani ba Abdul Ina neman amincewarka tunda bazaka dukeni qawa ba ka riqeni a matsayin qanwarka don Allah idan nayi ba daidai ba ka sanar dani kuma ka hukuntani badon niba ka amince da Samha wlh zanbi umarninka sau da qafa fiye dana Iyayena saboda nasan kai bazaka dorani a gurbatacciyar hanya ba Abdul ka zama haskena kuma madubina ka mayemin gurbin gibin taya zama naqasu ga rayuwata don Allah kayimin hukunci daidai da wanda zakayiwa qanwarka ta jini don girman Allah Abdul inada rauni ni mace ce Ina buqatar jagoranci a rayuwata kuma inada qaramar qwaqwalwa duk abinda ya burgeni shi nake aikatawa sai bayan nayi sannan na rinqa neman ma’auni domin auna girmansa da nauyinsa a ma’aunin zunubi don Allah kada ka qara barina na zama sasakai My Abdul please…..”

 

Yanda take mgnr cikin kuka yasashi mugun jin tausayinta dan qaramin bakinsa ya motsa a hankali yace “duk abinda Allah ya tsara shine daidai zanyi iyakar qoqarina wajen sauke nauyin amanar da kika doramin insha Allahu zaki sameni Yaya me adalci ga qanwarsa” ajiyar zuciya ta rinqa saukewa gami da share hawaye lkc zuwa lkc tissue ya zaro a aljihun sa ya sanya hanunsa ya share mata yace “banason ganin hawayen qanwata” batasan lkcn data saki wani kyakkyawan murmushi ba shima murmushin yayi tare dayi mata order abincin itaka nata ita kadai data tambayeshi sai yace mata azumi yakeyi dole ta qyaleshi.

 

 

Tana gama cin abincin suka miqe suka nufi wani gurin hutawa suka zauna a saman kujerun suna zama yace Mata “yanzu dame zamu fara?” Murmushi tayi tace “kasan qanwar taka sai a hankali izu talatin ne dani a qur’ani Ina ganin mu fara dashi ko?” Kallonta yayi sosai yace “izu talatin ai kinyi qoqari yanzu zaki iya kawomin izu ashirin daka” daga masa kai tayi tace “ina fatan hakan tunda ina muraji’ah kullum” murmushin jin dadi yayi yace “ok to mu ajiyeshi akwai lkcn da zan hanaki baccin dare saikin kawomin izu talatin din nan dindin ko a zahiri ko a waya yanzu mu fara da harisai da sauran litattafai ko?”

 

Gyada masa kai tayi tare da janye idonta daga nasa tace “yanda kace malam” sun jima suna karatun kafin su tashi da Arba’una Hadith suka fara yasha mamakin yanda take sauri dauke abinda duk ya koya Mata tare da sarrafa larabcin kamar tayi zaman madina saida sukakai hadisi ta goma yanayi mata bayani dalla² sannan suka tashi tayi masa gdy har zasu rabu tace “yi hqr My Abdul ban karbi number kaba saboda lalurar rayuwa” batare da tunanin komai ba ya karbi wayarta ya rubuta mata number sa ya fito da tasa qirar i IPhone 11 ya Kira da duka layukanta biyu yayi murmushi ya miqa mata ta miqa hanu zata karba ya janye tayi wani farr da idanunta da yasa gabansa faduwa ya miqa Mata da sauri saboda ya lura yarinyar neman karya masa azumi takeyi” bye-bye tayi masa tare da juyawa ta cike da farin cikin kasancewar ta da namiji daya da take jin zata iya rabuwa da komai saboda farin cikinsa.

 

Haka rayuwa taci gaba da tafiyarwa Samha cikin jin dadi gefe guda da fargaba zuciyarta na azalzalar kan cewa ta sanar da Abdul sirrin zuciyarta amma ta kasa da haka har lkcn exam dinsu yazo suka gama ranar da suka gama exams din zaa kulle makarantar kuka ta sanyashi a gaba tanayi masa wanda ya alaqanta da sabo daqyar ya shawo kanta tare dayi Mata alqawarin duk sanda wani Abu ya kawosa Kano zai ziyarceta nan take sanar dashi Abuja zata tafi gurin iyayenta dama karatune ya kawota Kano asalin mahaifinta dan Katsina ne sai a lkcn ya tuna da abinda Ja’afar ya fada masa game da ita ya shafa kansa tare da cewa “karki damu qanwata muna tare a waya ko na network insha Allahu”

 

Haka suka rabu kowa zucciyarsa babu dadi saida ya kaita airport tahau jirgi shida Manson sannan suka juya suka nufi garinsu zuciyarsa cike da kewar qanwar tasa da tausayinta yafi komai tasiri a zuciyarsa tunda suka rabu yakejin zuciyarsa babu dadi zuwa yanzu yarinyar ta shiga ransa fiye da sosai yanayi mata so irin na dan’uwa da dan’wansa na jini.
A hankali ya furzar da wata iska me zafi tuqin ma kasawa yayi sai Manson ne ya karba yanda ya mayar da hankalinsa wajen kallon titin lkc zuwa lkc yake jefawa Mansoor kalamai daidai cikin hirar da yake masa jinsa shirune yasa shi kallonsa tare da cewa “na lura yarinyar nan ta samu mazauni a zuciyarka ina hango soyayyarta da kuma kishinta a qwayar idonka kamar yanda na dade da sanin Samha tana sonka….”

 

Wata uwar harara da yake jifansa da itace yasashi sauya akalar zancen da cewa “ka manta kawai Mainah Samha dabance wlh zaka gasqatani duk ranar da gsky ta fito nidai nasan akwai qauna tsakaninku” kawar da kansa yayi yana shafa wayarsa lkc zuwa lkc yana duban agogo ya rasa meyasa kowa cikin abokansa suke fadin kalmar so tsakaninsa da Samha bayan shidai ya haqiqance ba sonta yake ba tausayinta yakeyi”………..

 

 

 

*UMMUH HAIRAN CE…✍*
[2/11, 2:59 PM] UMMUH HAIRAN CE…✍: *_AD_*

 

*_Dont read this book if you are not married. Mature content contained in it. Reader discretion is advised. You read at your own risk._*

 

 

Post a Comment

0 Comments