Auren Gado 9-10

Latest Posts

6/recent/ticker-posts

Ad Space

Auren Gado 9-10


9⃣&🔟

………… Khaleel yabar gidan bayan ya gama breakfast shima domin shikadai yasan damuwar shi, bayajin zai Amince da wannan Auren tareda ci gaba da zama a Nija yana ganin irin wainnan Abubuwan, he can’t take it. Saida Ahmed ya nemeshi a waya yafada mai inda yake a can suka hadu, dafashi yayi “why kafita bayan nafada maka zamuje gaisuwar surukai? “Yaya tunda na duba naga baka gidan I know you’re hurt shiyasa nafita, and please Yaya don’t just sit down and watch things ka dauki Action mana. Yafada yana kallon shi cikin damuwa, murmurshi Ahmed din yayi tareda cewa “my brother, a wurin wa zandauki Action? Don’t forget she is our mother dole mubi ta duk yanda takeso. “Its unfair”, haka zakaci gaba da kallon Abubuwa nafaruwa till when? “Ko zuwa yaushe ne Am ready inyi mata biyayya khaleel am ready to obey what ever she said, can’t you do that for your mother? I can’t Yaya gaskiya am seeing everything you need privacy with your wife amma an tauye ka, yakamata tunda ka rabota da y’an uwan ta ka bata kulawa, itama tanada right akan ka fiyeda mommy don haka dole ka kula da yarinyar nan, kasan yanda kukayi and you disappoint her daka boye mata gaskiya I know she is in pain, please Yaya she needs your comfort.

“Hmmm my brother has grown up, yafada yana rungume shi gam gam tareda jin dadi, “khaleel kasan how hard am trying? Banda zabi ne, Amma Inna fada maka bana damuwa k’arya nayi, “I needs my wife like any other man da yayi sabon Aure I want her very badly, yazanyi in iya Cire idanuna akan matata bayan she is closer to me, this is the hardest time for me. Yafada yana tunano yanda yaganta dazu without hijab, her shape her chest her hair, oh God! he has the most beautiful girl as his wife.

Rungume shi khaleel yayi tareda cewa “I will help you through this brother. “Thank you”. Daga nan suka wuce gidan kawun su tareda godiya akan hidimomin shi, ya musu Allah yasanya Alkhairi, tareda nasiha mai zafi akan zaman Aure, kafin ya dawo kan Khaleel, “kai balkisu Tafada min komai akan Y’ar gidan mai Nasara, and am happy da zakayi Aure kaima, kuma ni bazan hanaka Auren zabin kaba, zankuma shige maka gaba har kaima Allah ya cika maka naka burin, Amma Ahmed kayi sa’ar surukai nagari Allah ya kad’e fitina, kunje kun gaida su? ” yanzu zamuje kawu friends dina ma na jirana daga nan can zamuje. “To to to, kuje Allah ya muku Albarka, zan Dauki Abokina mu samu ganin mai nasara, idan komai yayi dai dai zanfada muku. “Mungode sukafada baki daya, Wanda itace kalmar farko da ta fito daga bakin shi bayan gaisuwa domin Allah yagani Fauzy saidai idan Allah yayi baida ta cewa, fuskar shi kawai zaka kalla kasan baya farin ciki. “Relax brother, bakasan me zai faru gobe ba, kayi hakuri may be haka Allah ya tsara dole zaka yi Rayuwa da fauzy, don haka ka nemi zabin Allah, inba Alkhairi bace sai ya baka wata. “Mata biyu Yaya? “Yes kaiba namiji bane? ” no please kai kace bakason biyu nida nake kanin ka inyi biyu, ni mace daya is OK for me. “You can handle two wife’s nasan kanina, I believe in you. Yafada yana Dariya, haduwa sukayi suka tafi jakara tareda Abokan Ahmed din. Wanda khaleel ya daure har cikin gidan da Akwai Sauran mutane suka shiga suka kwashi gaisuwa cikin mutunci da girma. Wanda idanun shi nakan Inna kulu wadda yasani ba tantama kyanta Naziya ta dakko, haka yabi Shukrah da kallo yana ganin tsantsar kamar su tareda yayyin ta masu Aure duk Suna Kama, Amma no one like Naziya she is more beautiful a cikin su.

“Shiru yayi kawai yana nazari har suka gama gaishe gaishe suka fita waje domin gaida Malam dake dakin zauren tareda manyan Almajiran shi, a nan khaleel ya Amince yes yayan shi yayi Aure inda ya dace, dattijo na gari mai mutunci, nasihar farko itace “sai kayi hakuri da duk wani shiririta ta mata zakaci ribar zama a duniya ka rike gaskiya kabi maganar mahaifiyar ka kagama lafiya, Allah ya kade fitina ya kuma baku zuri’a tagari. Wani irin girman tsohon khaleel yagani tareda tsantsar mutuncin shi, tabe bakin shi yayi tareda kada kai kawai Wanda shikadai yasan meke zuciyar shi.

Saida sukabar gidan sukaje harabar katon gidan nasu ya dafashi “Yaya I don’t know much about Al Ada, Amma nagani Ina yaro idan Ana Aure a familyn mu idan ankai Amarya the next day y’an uwan ta nazuwa, why your bride basu zoba kuma sun san zata bukace su? “Hhh Khaleel mutunci kenan da gudun Abin duniya na gidan su Naziya bakaga komai ba ma Indai zuri’ar malam Abubakar ce, “but Yaya naga younger sister d’in ta ko ita batazo wurin Y’ar uwar taba. “Kasan Abinda momy tayi musu jiya shima zai iya sawa su hana wani zuwa gidan nan. Yafada fuskar shi na canzawa,
“Is OK muje ciki yau dai zaka tare dakin ka enough of the budan kan. “Hmm Allah yasa. Anyi la’asar koda suka shiga gidan, Wanda tana takaiwa da dawowa daga kitchen zuwa falo domin shirya Abincin Dare, duk Abokan hirar nata suntafi, gashi momy tace tayi tuwo miyar kubewa da kuma farfesun kan rago.
Tana cikin Adon ta sosai haryanzu tareda baza kamshi kamar Amarya. Har zata fito cikin kitchen din taji muryar su Suna Dariya ta koma, wani irin zafi takeji a kirjin ta she thinks kamar da gangan ma Ahmed ya Aurota ya kawo cikin gidan su domin ta wulakan ta, toh yayi kuskure, kuma zata nuna mai Abinda Aka koyar da ita daga gidan su, zai gani tarbiyar Inna bazata taba faduwa kasa banza ba, she cried yerstaday, kuma bazata kuma zubar musu da hawaye ba, aiki kuma Alhamdulillah, bazai gagare taba domin ta horu girki ma zatayi Amfani da nata salon domin gujewa damuwa, da izinin Allah zata basu mamaki.
Da taimakon mai Aikin take Amfani da kayan wutar, tsab tuwon shinkafa ta dora Wanda tasa mai ruwa wadatacce da zai dahu lugub, sai kan ragon data wanke tas ta zuba a wuta tareda neman kayan kamshi na gargajiya ta daka ta watsa, tuni kamshi ya cika ko Ina.
Tayi dai dai kuma hankalin ta kwance tana aikin ta, ya shigo ciki, turus yayi yana kallon ta cikeda mamaki domin dai bai kamata ta shiga kitchen ba, tana Amarya kuma kwana daya a gidan miji a ce tafara aiki bayan ga maids cike da gida, wucewa yayi wajen firij saida ya bude taji motsi tareda Saurin juyowa tagan shi ya daga gorar ruwa sama yana sha, Saurin juyawa tayi tana cigaba da aikin ta, domin ta lura ya cika girman kai, and she promise zata kiyaye shi tunda baice Mata ba itama bazata taba yimai magana ba.
Har ya Ajiye gorar ya juya Abun shi yana mamakin halin ta, ko kallo bai ishe taba Wato? Hmmm”.

Karfe shida ta kammala tuwon tareda miyar kubewa lafiyayya da taji namomi a ciki, maid tace”Aunty Saura Abincin master karami. Kallon ta tayi “da daren ma bayacin Abincin mutane? “Yes saidai Ana dafamai ruwan tea ya hada ko coffee. Shiru tayi kafin tace ta kwaso shrimp d’in da su crabs, da kanta ta gyara ta wanke tas tasa ta gyara Mata Y’ar citta dasu garlic tace ta daka mata su da Albasa da tarugu saida suka daku ta d’an sa ruwa ta shafe su tsab harda spices, ta saka a oven, ta saka lowest yanda bazai kone ba kafin tayi wanka, maid din ta yanka mai salat ta wanke su tumatur.
Dakin ta ta koma ta tube tareda shiga wanka, cikin Sauri Sauri, ta dauro Alwala domin ankira magrib, bata tsaya yin dogon Azkar ba ta mike cikin Sauri ta canja zuwa wata doguwar rigar Atamfa mai flay cikin dinkin da malam ya Mata, tayi kyau sosai,
ta daura dankwali ta fito. Yanzu duk sunfito Suna falon momy dasu Ahmed harma da Khaleel, yana Rungume da katuwar tab yana dannawa, Suna hira kasa kasa su duka. “Toh hamshakiya abamu Abinci yunwa mukeji. Mommy ta fada. Muryar ta a kwance tace na gama momy zan shirya ne kawai a dining. “Noo ki sa maid ta shinfida mana dadduma anan bazamu hau saman ba,.
Bakomai yasa tace hakan ba saidan kar su zauna kusa itada Ahmed. Domin sa idawan ta dazu sun tsegunta Mata kamar yana rike Mata hannu ta kasan table, Wanda bazaka taba gane munafukan sungan suba.
Tunda ta fito Ahmed ya zuba Mata ido wani irin numfashi yakeja a ciki, domin Allah yagani shiba dutse bane, idanun shi ko kyaftawa basayi akan kirjin ta da yake gani, tareda Ayyana irin cika mai Hannun da zasuyi, har wani irin Aunawa yakeyi, he know dai dai Hannun shi ne. Kallo ta yakeyi sosai har mommy ta lura. Tareda Ayyanawa a ranta “Ahmed Indai ni Balkisu ce na haifeka bazaka taba hadamin iri da yar matsiyata ba muje zuwa.
Tayi k’wafa, Saida ta jera komai tareda turawa khaleel nashi cimar ta koma gefe ta zauna itama, gaba daya kamshi ya gama cikasu, ita kanta mommy miyon ta ya tsunke, wani irin murmurshi Ahmed keyi na jin dadi, domin yana ganin yanayin Abincin yasan zaiyi dadi sosai.
Khaleel ma kallon Abincin shi yakeyi, domin ba ataba hadamai shi da komai ba yana ganin yanda yayi wani irin kyau ga Aroma na tashi. Momy kallon yanda yake kallon Abincin tayi tace “idan bazaka iyaci ba ayi maka wani? “No is OK, yafada yana daukar fork yafara ci. Wani irin test yaji tareda dadin da baitaba jin yayi ba, domin ta yimai hadin da kowama zai iya ci. Kallon shi Ahmed yayi “yadai brother its good? “Of cos Yaya she is a wonderful cook. Batareda ya kalli side d’in ta ba.
Shiru kakeji a wurin kowa na zuri, saida taga kowa baiyi complain ba itama ta debi kadan tafaraci, Ahmed sai aika Mata da sakonni yakeyi ta gefen ido, ta dukar da kanta dama suna facing juna itada shi.
Saida mommy tayi nak tace “next time idan zaki tuka tuwo ki tabbatar yayi sulbi sosai. To kawai tace domin idan dai ba tuwon masara takeso ya koma ba, tasan ko hasidin iza hasada yasan tuwon nan ya tuku. Maid din ce ta tayata suka kwashe komai zuwa kitchen, tayi daki domin yin sallah. Suma fita sukayi masallaci.

Mommy ce zaune a falon tana waya da Zarah “So nakeyi Auren khaleel ayishi cikin Sauri, don haka zanturo miki kudi kifara yomin odar Kaya na gani nafada, domin bikine zamuyi shi na kece raini.
Shigowa sukayi tayi Saurin Sallama, ta Ajiye wayar, zama sukayi tareda gaidata, tace tom dare yayi ku wuce ku kwanta Allah ya tashemu lafiya. Taci gaba da latsa wayar ta, “mommy in tafi dakina? “Ahmed yafada cikin sanyin murya mai hade da lallashi. “Saurin uban me kakeyi? Da da bakayi Auren ba uban me ya sameka? Kaga Ahmed ka fita idona in rufe, saboda aji dadin Asirce ka shiyasa kake kokarin shige Mata, to kabari sai nan da sati daya idan Agumun da aka kullo Mata ya sirace ehem. Saurin kallon ta khaleel yayi tareda cewa “Haba momy haka ake Aure fisabilillahi? Ai da kin hana kawai yayi Auren wannan irin kwalelen ya isa Haba. “Toh ubana ai kai nasani zaka iya dukana ma, to dak’ar ni kaji, ku tashi ku wuce kubani wuri kafin in canja shawara.
Khaleel ya fara mikewa fuuu ya wuce saboda takaici, Ahmed ya tsaya tareda zamewa kasa ya dafa kafarta “don Allah momy in laifi nayi miki ki yafemin don Allah, kibarni in sauke hakkin Y’ar mutane ko lekata inyi infito minti biyar ya isa don Allah. Yafada yana zubo da kwalla, tace “minti biyar idan ka wuce hakan zan shigo kuma wallahi bazakaji da kyau ba.
Tashi yayi da sauri yana share kwalla “na gode mommy, ya nufi dakin yana Ajiyar zuciya, a zaune take tana waya da Shukrah a wayar Inna, tanajin motsi ta kashe tareda mikewa tana jan hijabin data Cire ta Ajiye a gefen gadon nashi. Rufe jikinta tayi a cukurkude tareda daburcewa ta rasa Ina zata shige ma, “Hmmm yayi doguwar Ajiyar zuciya. Ya fara takowa cikin natsuwa tareda zuwa gaban ta. Hannayen ta ya riko. “Naziya”Am sorry please kinji komai zai wuce please don’t be angry with me I love you, hannu yasa ya zame hijabin dake kafadar ta ya fadi kasa ya zuba Mata ido tundaga sama har kasa.
“I don’t know you baby, yanzu nake sanin God gift da nasamu batareda sani na ba, you are beautiful baby, yafada idanun shi na kadawa kamar zaiyi kuka, cikin natsuwa ya bude hannayen ta yajata saman kirjin shi, jikinta na wani irin rawa domin wannan ne karon farko da namiji ya rungume ta, shikuwa jin kirjinta a nashi tuni yajishi a sama, Abunka da pure man da bai saba da cakuduwa da mata ba, Saura kiris su zube kasa, yana fesar da iska bakinshi domin samun sauki ya dago fuskar ta tareda dora lips dinshi kan kyakkyawan bakinta yaji kiran momy, ” Ahmed karka Bari inshigo ciki ranka zai baci nafada maka. Saurin janyewa tayi domin a tsorace take dashi tanajin yanda yake murza jikinshi a laps dinta she can feel his hardness, da bata kawo komeye ba ma. Muryar shi a shake yaja baya “please kibiyoni Anjima Kinga mommy tace infita anan please wife kifito ko kitchen ne muyi magana. Yafada yana fita cikin hanzari da Sauri, wasu irin kwalla ne suka taru a idanun shi.
Zamewa tayi kasa ta zauna tanajin wani irin yam yam a jikin ta, Allah yagani tana son Ahmed, Abinda ya boye mata Wannan ta fahimci dalilin shi domin ita ta nunamai batason namiji mai hali, Sannan yanzu ta Kara fahimtar shi Waye daga jiya zuwa yau, yana matukar son familyn shi yana bin umarnin mahaifiyar shi mai cikeda matsaloli Wanda ta daura damarar zata yi mata biyayya muddin ranta domin Ahmed, wani irin tausayi yabata yanzu, hawayen data hango akan kyakkywar fuskar shi kawai ya karya mata zuciya, me zatayi da zai sanyaya mai rai?
Daukar wayarta tayi ta Kira yayar ta bayan ta kulle kofar ta, Aunty Raliya, itace babbar yayar su ita ma tana Auren mai d’an hali saidai kamar yanda Al Adar su take suba masu yawon gidajen y’an uwa bane, “Aunty Raliya Ina wuni. “Amarya yadai kina kirana Karfe goma lafiya ko? “Lafiya kalau Aunty yasu Abba? Duk sunyi bacci, Ina fatan ba Matsala ko? “Um um, “Ina mijinki kike Kira na by this time? ” baya nan yana dakin su. “What bangane ba, kodai kinki yarda dashi ne? “Aa. “Naziya, ki fadamin damuwar ki Kinga ke ba kawaye gareki ba da zaki fadamusu ni yayar kice bazan so ki cutu ba, bakomai Aunty. “OK listing to me kije ki dafamai ruwan tea mai kayan hadi ki shirya ki kaimai dakin nashi, kinsan wasu maza basa son shiga dakin mata saidai mata su bisu, “Aunty sai inje? “Karkije kinji, ki tsaya shirme wawuya kawai. Ta datse kiran kit, domin tanada zafi, tasan duk Abinda ke faruwa kuma sunada labarin uwar mijin Naziya domin Zarah kusa da ita take kuma haryau batasan Naziya kanwar tabace don haka ko dazu tashigo tana bata labarin Hajiya bilkisu da yanda take juya Ahmed, tana dariya da jin dadi,

Shiru Naziya tayi tarasa ta Ina zata fara, tashi tayi cikin Sauri, saida ta leka falon taga bakowa domin mommy nada nauyin bacci tana shiga dakin ta ta bingire, kitchen ta shiga ta dafamai ruwan tea harda na’a na’a, yana tashin kamshi, ta samu tea jug da cup ta zuba ta fita tana tunanin Ina zata ganshi harta bashi tea din takoma dakinta, jitayi anriko Hannun ta, tayi Saurin juyawa zata Sa ihu yace “Shhhhhh, nine, ware idanu tayi, jikin ta na rawa tace “ga tea Dama shi zankai……… Rikota kawai yayi ya nufi hanyar dakin khaleel da ita, yana kan computer yana duba harkokin company dinsu da Ahmed ke gabatar mai yanzu, ganin su yayi kawai ya sauke kanshi. Saida ya zaunar da ita ya koma gefen Khaleel yace “brother please excuse us. Dago kai yayi tareda kallon yayan nashi cikin idanun shi kuma yasan sarai me yake nufi yace “Ina zanje Yaya nida dakina? “Go to my room please, “zan tsaya a falo idan kungama magana indawo but I can’t go to your room yanzu na Matar ka ne, “OK tanks ten minutes kafin mommy ta farka,.tashi yayi tareda daukar wayar shi ya fita yana “quick brother kaga Ina aiki na ka tsayar dani,
Kulle kofar yayi tareda nufar inda take tsaye cikin hijabin ta,……. ðŸ–Å 

 

*Matar Soja*
10/20/21, 7:33 AM – Fiddausi Yunus: 🌻🌻AUREN GADO🌻🌻

 

*Matar soja ce*

 

Daga marubuciyar
KUSKURE NA
BARIKI AUREN SOJA
MUK’ADDARI
WANAKE AURE
ZANYI BIYAYYA
And now AUREN GADO,

Ga masu son su biya ga account details dina, *NAFISA HASSAN SANI 7304736012 @ FCMB* sai ku min magana ta wannan number 09069200154

 

 

🆓 page

 

Post a Comment

0 Comments