Garin Dadi 17

Latest Posts

6/recent/ticker-posts

Ad Space

Garin Dadi 17


©️ *HASKE WRITERS ASSOCIATION*

 

*GARIN DAÆŠI…..!*

 

*_NA_*

*_UMMI A’ISHA_*

PAID BOOK

17

*Ina kuke manyan mata Æ´an Æ™walisa ma’abota son gyara da kece raini, maza ku garzayo ku nemi maman Maryam domin samun lafiyayyu kuma haÉ—aÉ—É—un Lagos lace wanda zaku iya samun É—inkakku da kuma sabbi a ledarsu, kaya iya zaÉ“inki, gefe É—aya muna da GHT product, zaku samu,*

*MAI DA TSOHUWA YARINYA

*FEMALE CARE

*REODEO

*VIGOR MAX

* LONGZIT

*B CLEAR

*DUK ZAKU SAMU WADANNAN KAYA CIKIN SAUKI DA RAHUSA MAZA KU NEMI MAMAN MARYAM AKAN WANNAN NO 07080222187, SIYAN NA GARI MAIDA KUÆŠI GIDA….*

~~~Hannu na sa ina murza idanuwa dan samun tabbacin shin dagaske ne ko kuma sune suke yimin gizo? Tabbas da gaske ne hakan ya sanya naji jikina ya fara rawa wadda ban san ko ta mecece ba,

“uhmm……. Kin yi shiru” ya sake turo min, cikin kasala na koma na kwanta sannan na bashi amsa da,

“Babu abin da ke damuna kawai dai na gaji ne….”

“Gajiya? Wacce irin gajiya?”

Murmushi nayi araina ina jinjina ƙwaƙwarsa da gani zai yi tambaya,

“Na gaji da zama ne wuri É—aya kuma ina fama da ciwon kai” na bashi amsa ina murmushi ni kaÉ—ai,

“ayya sorry…..”

Murmushi kaɗai nayi kafin na buɗe saƙon da ya sake turo min,

“Zan iya zuwa in duba ki yanzu?” É—an jimm nayi na kalli gefen da anty Salma ke zaune tana duba manual,

“Kar ka zo pls…..”

“Why?” ya sake tambaya ta,

“Idan ka zo za ayi min faÉ—a”

“OK na gane, amma ina buÆ™atar wata alfarma daga gareki”

“Allah yasa zan iya”

“Ki turo min pics É—in ki ina son ganin ki ban taÉ“a ganin fuskarki ba”

Ajiyar zuciya na sauke araina ina cewa idan wannan ne babu matsala abune mai sauÆ™i, pics É—ina na tura masa guda biyu nace shima ya turo min nashi, turo min yayi sama da guda biyar a Æ™asan ya rubuta wai shi bai iya rowar pics ba, murmushi nayi na fara buÉ—esu É—aya bayan É—aya ina kalla, gaba É—aya hotunan yayi bala’in kyau kamar ka sace shi ka gudu,

“Zan iya kiran ki yanzu?”

Shiru nayi kafin na bashi amsa da “ehh” yana buÉ—e saÆ™ona sai ga kiran sa, nan naji gabana ya shiga faÉ—uwa, to ni yanzu me zan ce masa ni Maimunatu? Na shiga tambayar kaina ba tare da na É—auki wayar ba har sai da na jiyo muryar anty Salma tana cewa ba kirana ake yiba? Cikin sanyin murya da tsoro wanda ban san ko na menene ba na É—aga kiran,

“Hello….” na faÉ—a ina lumshe idanuwa na,

“Hello…….. Ya jikin?” ya tambaya cikin harshen turanci,

“Da sauÆ™i…..” na amsa ina sake gyara kwanciya ta,

“Kin sha magani?” kai na girgiza masa kamar yana kallo na,

“Meyasa baki sha magani ba?”

“Babu komai….”

“kin ci abinci?? “

” Ehh ”

” Ban yarda ba….. Duk da baki son in zo dole zan zo zan kawo miki maganin headache É—in”

“ka bar shi kawai…. Na gode” tun kafin in Æ™arasa naji ya katseni da cewa,

“Zamu fara faÉ—a ba daga fara wayarmu yau, ki jirani nan da 5 minutes”

Katse wayar yayi nikuma na sake mirginawa É—aya É“angaren ina mamakin wannan al’amari, har 5 minutes É—in tayi ta gota ban sani ba saboda ina can ina tunani, mamaki da al’ajabi sun taru sunyi min rubdugu har sai da naji Æ™arar wayata alamar kira sannan na tuna,

“Zo ki karÉ“a…..”

“kana ina?”

“Ina harabar hotel É—in”

Tashi nayi zaune na kalli anty Salma nace mata ankawo min magani zan karɓo, ita duk tunanin ta Samir ne saboda taji muna hira da turanci nikuma bance mata ba shi bane na barta ahaka, a yadda nake haka na fita babu abin da na sauya ina sanye da dogon hijabi mai hannu har ƙasa. Irin faɗuwa da bugawar da gabana ke yi ba zata kwatantu ba, haka dai na daure na fita harabar hotel ɗin, caan na hango shi tsaye shi kaɗai dan haka cikin sassarfa na ƙarasa jikina yana ɗan rawa,ko da naje dab dashi sai na rasa me zanyi, shin zanyi masa sallama ne ko yaya?

“Princess……” naji ya faÉ—a cikin husky voice É—insa, É—an murmushi nayi na sadda kaina Æ™asa,

“ya jikin?”

“da sauÆ™i”

“ina yi miki fatan samun sauÆ™i cikin gaggawa”

“na gode”

Shiru ne ya É—an biyo baya dan na lura shi É—inma ba wai mutum ne mai surutu ba sau da yawa shi kaÉ—ai zaka ganshi zaune shiru sai ko wayar shi da zaita latsawa ko laptop É—in shi,

“Ga maganin kije ki kwanta ki huta….”

“nagode”

“nima haka”

KarÉ“ar ledar nayi duk da na ganta Æ™atuwa haka kuma naji ta da É—an nauyi wannan ke tabbatar da ba wai iya maganin ne kaÉ—ai aciki ba, sallama yayi min ya tafi nabi bayan sa da kallo yanzu ma Æ™ananan kaya ne a jikinsa jeans da t shirt, ciki na koma ina jin wani al’amari yana ratsa birnin zuciya ta,

Fruits ne cikin leda sai ko maganin ciwon kai, apple kaɗai naci nasha magani na kwanta bayan nayi sallar isha, bargo na shige na cigaba da chaten ɗina dan itama anty Salma na jiyo ta tana waya da mai gidanta da yaranta, samz ne ke tambaya ta wai waye saurayi na, murmushi nayi nace masa babu, cewa yayi wai bai yarda ba ya za ayi ince ba ni da saurayi, wani murmushin na sake yi nace masa ban samu type ɗina bane, tambaya ta ya sake yi wai shi type ɗina ne? Shiru nayi na rasa amsar da zan bashi dan a zahirin gaskiya shine type ɗin nawa, duk yanda nake son mijina ya kasance haka samz yake sai dai akwai ƙatuwar matsala dan ko mun fara soyayya tofa babu inda zata je tunda shi ba musulmi bane, sake tambaya ta yayi, bani da zaɓi wanda ya wuce in faɗa masa gaskiyar lamari nan nace masa ehh dariya naga ya yi sannan yace wai in kara tura masa pics ɗina guda biyun da na tura sunyi kaɗan, tsokanarshi nayi nace to dai idan matarshi ta gani kar ya kira sunana dariya yayi kafin yace min ai bai da aure, zaro ido nayi nace dagaske?

“Dagaske mana, ko dan kin ganni na fara tsufa?”

“a’a ni bance ba…… Kawai na tambaya ne”

Hira muka cigaba da yi har Æ™arfe 9, shi da kansa yace wai in ajiye wayata haka in kwanta in yi bacci amma kafin in yi baccin bari ya kirani yaji jikina, sallama muka yi na kashe wayata gaba É—aya na yi addu’ar bacci, da tunaninsa nayi bacci da asuba kuwa ina buÉ—e wayata da message É—insa na fara yin tozali kuma hakan ba Æ™aramin daÉ—i yayi min ba, sake komawa bacci nayi wanda bani na tashi ba sai wurin 9, wanka nayi naci abinci na sake komawa na kwanta na faÉ—a yanar gizo,ina shiga WhatsApp da massage É—inshi nayi arba, murmushi nayi na fara karanta saÆ™on kamar haka, _As you rest and heal, know that you are thought of warmly and wished a quick recovery._, reply nayi masa ina tura masa sai gashi online, hira muka fara yi wadda tayi mutuÆ™ar É—ebe min kewa ta sani na manta komai da duk wata damuwa wacce nake tare da ita sai dariya kawai nake yi wanda hakan yasa Anty Salma tsokana ta, har azahar tayi muna hira da shi sai lokacin nace masa zan yi salla sannan muka yi sallama. A cikin weekend É—in mun É—an saba da juna saboda kullum sai ya kirani da safe da rana da yamma da kuma dare ga chaten da muke yi wuni za muyi muna abu É—aya shiyasa har na matsu Monday tayi in ganshi dan tun lokacin da yazo ya kawo min magani bai sake zuwa ba sai dai waya, shima a nasa É“angaren kamar ya fini matsuwa da Monday tayi ya ganni duba da irin yadda yake ta maganar yana cewa weekend É—in wai baya sauri yaÆ™i ya Æ™are kuma shi babu inda yake zuwa kullum yana gida sai ko wani lokacin ya kan je filin Æ™wallo, murmushi nayi araina nace “ai saida exercise É—in kai kam ko ka É—an rage nauyi…….”.

Asubar farko ta ranar Litinin na tashi na shirya cikin ɗoki da farin ciki, babu komai araina face murna da tarin farin ciki haka fuskata ƙunshe take da annurin zallar farin ciki, nasha kyau har na gaji cikin simple makeup ɗin da nayi dan dama daga powder sai kwalli da lip glow shikenan kwalliya ta amma duk da haka na haɗu iya haɗuwa cikin doguwar rigar atamfar da na saka ash colour mai ratsin green coour, mayafi nasa green nasa baƙin takalmi, ni kaina na san weather ɗin garin Lagos ta karɓi fatar jikina duba da irin yadda nayi wani fresh dani kamar me shafa mai, nayi kyau nayi haske fatata sai sheƙi da ƙyalli take, yau kama kaina nayi naja class ɗina sosai dan ko inda trainers suke ban kalla ba tun bayan da muka yi signing lokacin da muka shigo,

Kaina yana ƙasa ban ɗago ba naji wani shegen ƙamshi yana ratsa ƙofofin hancina duk da cewa akwai face mask a fuskata,

“Good morning…..” naji daga bayana saitin kunne na, juyowar da zan yi na jini cikin jikinsa domin dab dani ya duÆ™o ya dafa kujerar da nake kai, kamar wani mayen Æ™arfe wanda ya haÉ—u da É—an uwansa mayen Æ™arfen daÆ™yar na iya janyewa,

“Good morning….” na fada murya ta can Æ™asa,

“Morning….. How was your night and how do you feel now?” ya faÉ—a saitin kunnena cikin raÉ—a,

“I feel much better…..”

Bai Æ™ara cewa komai ba ya juya ya tafi, Nana dake kusa da ni ta juyo ta kalle ni dan yanzu ba sosai muke zama tare da Anty Salma ba cikin Aunties take shiga nikuma nake shiga cikin sa’annina, duk Æ™waÆ™war Nana na son jin me ke tsakanina da Samir da kuma Samz Æ™in faÉ—a mata nayi,

Lokacin breakfast da lunch duk sai da ya kirani awaya wai yana kallo na inci abinci da yawa, ga mamaki na muna hira awaya ina cin abinci sai gashi na cinye da inata mitar an zuba min da yawa dan shinkafa ce jalop da fried rice itama a gefe sai alala guda É—aya da farfesun kayan ciki sannan ga pepper chicken akai, muna hira inata nishaÉ—i ban san lokacin da na cinye ba gaba É—aya sai guntu na bari,

“Kaga yadda naci abinci yau? Rabon da na ci abinci irin haka har  na manta”

“Tunda hakane na gane logic É—in yanzu duk lokacin da zaki ci abinci zan rinka kiranki har sai nasa kin ci da yawa” dariya nayi na tashi na mayar da flates É—in sannan na wuce toilet ina jin cikina dam kamar zai fashe, bayan na fito kuma sai ban ganshi ba wurin zaman su, har kusan lokacin tashi baya nan text massage na tura masa _Where are you?_ babu reply har kamar 5 minutes zuwa can sai gashi ya shigo kai tsaye wurina yataho, É—an ranÆ™wafowa yayi yace min,

“Gani na dawo…. Lafiya Lau nake”

Murmushi nayi na É—aga masa kai, juyawa yayi ya wuce wurin zamansa, har aka tashi ba mu sake magana ba sai bayan da na koma masauki, lokacin da zan ci abinci kamar da rana cemin yayi wai in cika flate hakan kuma nayi ina ci muna hira na cinye, waje na fita dan nayi bala’in Æ™oshi, wurin 9 muka yi sallama da shi na kwanta raina fari tas babu damuwar komai, tun daga lokacin kusan kullum muna waya dashi nake cin abinci yanzu abinci nake ci sosai dagaske bada wasa ba, yau dai tunda yashigo naga he looks somehow, after kamar 30 minutes ya É—auki jakar shi ya fita, wayarshi nayi ta kira amma a kashe, abincin ma yau ban wani iya ci da yawa ba, bayan an dawo daga lunch trainers É—in ke sanar damu wai muyi haÆ™uri  training da za ayi mana yanzu Samuel ne kuma bai da lafiya sai zuwa gobe idan yazo,

Bayan mun tashi na sake gwada kiran sa sai lokacin naji da ta shiga, muryarshi sanyi Æ™alau muka gaisa sannan na tambayeshi address É—in inda ya sauka zan je in duba shi, sallama muka yi bayan ya faÉ—a min, faÉ—a ma Aunty Salma nayi zan je cikin gari, bata hanani ba amma tace dai kar in jima in tabbatar na dawo before dare, side handbag É—ina na É—auka na fita………….

 

*Garin dadi littafin kudi ne ga mai bukatar cigaban labarin sai ya tura 500 ta 0774712835 Aisha Ibrahim Access Bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko a tura katin waya da shaidar biya wannan no 07044644433*

*_Ummi Shatu_*

Post a Comment

0 Comments