Garin Dadi 18

Latest Posts

6/recent/ticker-posts

Ad Space

Garin Dadi 18


©️ *HASKE WRITERS ASSOCIATION*

 

*GARIN DAÆŠI…..!*

 

*_NA_*

*_UMMI A’ISHA_*

 

PAID BOOK

 

18

*Ina kuke manyan mata Æ´an Æ™walisa ma’abota son gyara da kece raini, maza ku garzayo ku nemi maman Maryam domin samun lafiyayyu kuma haÉ—aÉ—É—un Lagos lace wanda zaku iya samun É—inkakku da kuma sabbi a ledarsu, kaya iya zaÉ“inki, gefe É—aya muna da GHT product, zaku samu,*

~MAI DA TSOHUWA YARINYA

~FEMALE CARE

~REODEO

~VIGOR MAX

~ LONGZIT

~B CLEAR

*DUK ZAKU SAMU WADANNAN KAYA CIKIN SAUKI DA RAHUSA MAZA KU NEMI MAMAN MARYAM AKAN WANNAN NO 07080222187, SIYAN NA GARI MAIDA KUÆŠI GIDA…..*

~~Drop na ɗauka har masaukin da samz ya sauka kuma ban wani sha wahalar gane wurin ba saboda sanannen wuri ne, har ɗakin da yake na shiga bayan nayi knocking naji shiru, yana kwance cikin blanket, a hankali na ƙarasa shiga na zauna gefen gadon, zaune ya tashi fuskarsa ɗauke da murmushi duk da fuskar ta ɗan faɗa kaɗan haka bakinsa lips ɗinsa duk sun bushe sunyi fari alamun bai ci abinci ba,

“Sannu….. Ya jiki?” na tambayeshi ina kallon cikin É—akin,

“Da sauÆ™i…… Me yasa kika wahalar da kanki kika zo?”

“Na zo inga yanda kake ne kuma in duba ka”

“Na gode, ya training?”

“Babu daÉ—i” na faÉ—a cikin shagwaÉ“a ina É—an turo baki,

“Me yasa?” ya tambaye ni yana kallon cikin idanuwa na amma ban bari mun haÉ—a ido ba,

“Saboda baka nan….”

“Ayya sorry…. Gobe zan zo in dai naji sauÆ™i”

“Allah ya baka lafiya…… Amma me ke damunka?”

“Amin…. Nagode”

“Me ke damunka?” na sake tambayarshi ina kallon gefen da yake zaune sanye cikin fararen jersey,

“Karki damu naji sauÆ™i….” jin abin da ya faÉ—a ya sani É—an É“ata fuska kaÉ—an ina gyara handbag É—ina,

“Shikenan tunda ba zaka faÉ—a min ba”

“Am sorry….. Kaina ne ke ciwo” ya faÉ—a yana murmushi, na san ba hakan bane kawai dai ya faÉ—a ne dan a wuce wurin,

“shikenan Allah ya baka lafiya….. Bari na wuce”

Langaɓar da kai naga yayi yana kallona,

“amma dai ba fushi kika yi ba ko?”

“uhmm ni ba fushi nayi ba” na faÉ—a ina miÆ™ewa tsaye,

“OK bari na zo na rakaki masaukinku” cikin sauri na juya ina kallonsa yana Æ™oÆ™arin saukowa daga kan gadon,

“a’a ni bana buÆ™ata dan Allah ba sai ka fita ba kayi zaman ka”

“kina ganin babu matsala zaki iya zuwa ke daya?”

“insha Allah zan je lafiya kawai kayi zaman ka Allah ya kara sauÆ™i amma idan baka warke ba Allah nima zan kwanta” daga haka na fita daga cikin É—akin ina murmushi ni kaÉ—ai, murmushin shima yayi bayan fita ta yana mai shaÆ™ar Æ™amshin turare na da na bar masa shi kansa bai san wanne irin al’amari ne wannan ba amma yana jina acikin ransa fiye da komai da ya mallaka ahalin yanzu sannan bai taÉ“a ganin yarinyar da ta burgeshi yaji jininsa ya haÉ—u da nata tun akaron farko ba kamata, sai dai jikinsa da tunaninsa na bashi cewa akwai tarin Æ™alubale a tarayyarmu wanda nima sau da dama ina tuna hakan.

Kamar É—azu yanzu ma drop na É—auka ina kallon yanda cikin garin yake wanda ya amsa sunansa birni, wayata na ciro cikin handbag dan ganin wanda ke kirana, Anty na gani nan na É—aga bakina É—auke da sallama,

“Salma tace min kin fita, ina kika je?”

“Anty bafa nisa nayi ba, kinma ganni a hanya na kusa komawa hotel É—in da muka sauka”

“Har yanzu fa baki amsa min tambaya ta ba nace ina kika je?”

“Dubiya naje….”

“waye bashida lafiya?”

“Tare muke training”

“to daga yau karki sake fita dab da magriba, kin ji abin da nace?”

“To anty, agaida su Sultan”

“Zasu ji”

Kiranta na katsewa na Samz na shigowa, cikin sanyin muryarsa naji yace,

“Inata kira kina waya…”

“ehh, anty ce, elder sister É—ina”

“Ayya, ya hanya?”

“Mun kusa mu Æ™arasa…..”

“kuna ta ina yanzu?”

ÆŠaga idona nayi na kalli waje nan naga wani symbol na wani restaurant,

“Perfect kitchen restaurant…..”

“ok to Allah ya kai ku lafiya”

“amin, ya jiki?”

“ai na warke, tun da na ganki naji na samu lafiya”

Murmushi nayi nace, “da gaske?”

“Da gaske mana”

“Ba dai ka Æ™i ka faÉ—a min abin da yake damunka ba?”

“No baby…. Ba Æ™in faÉ—a miki nayi ba ai na samu sauÆ™i”

“to Allah ya baka lafiya”

Har na koma masauki muna waya dashi sai da nace masa na shiga É—aki sannan muka yi sallama.

Washe gari  tun sassafe naga kiransa video call ta Imo, murmushi nayi na É—auka ina kallonsa, yana kwance cikin bargo da rigar sanyi a jikinsa,nima Æ™udundune nake cikin bargo da hijab a jikina saboda sanyin Lagos,

“Good morning baby…..”

“morning….. Ya jikinka?”

“Naji sauÆ™i…… Just want to see your beautiful face”

“Na gode, zaka zo?”

“yeah, zan zo in ganki cutie”

“Ka daina faÉ—a min haka, kar kasa in fara É—aukar kaina sahun masu kyau”

“Ni awurina kinfi kowacce mace kyau…..”

Lumshe idanuwa na nayi ina murmushi kafin na buÉ—esu akan shi, “nima awurina kafi kowanne namiji kyau…..”

“are you serious baby?”

“Am serious”

“Thank you queen”

“you are welcome king” na faÉ—a cikin tsokana,

“Kamar dai kinfi sakewa dani a waya ko?”

“uhmm kusan haka ne gaskiya” na bashi amsa ina rufe fuskata,

“shy girl”

Sallama muka yi na ɗan sake komawa bacci zuwa wani lokaci naji anty Salma na tashi na wai inyi sauri dan har mun so mu makara saboda itama baccin ta koma, cikin hanzari na shirya muka fita, koda muka je mune kusan na ƙarshen zuwa dan sai da aka tare mu ma, ina zama ya taso yazo kusa dani ya zauna juyawa nayi na kalle shi yana sanye da blue black ɗin wani yadi yasha hula itama kalar yadin nasa,

“you are late…..” naji ya faÉ—a bayan ya zauna,

“Good morning…..” na ce dashi ina Æ™okarin saka wayata a silent,yana nan zaune kusa dani har aka tafi break, yinin ranar gaba É—aya a kusa dani yayi shi idan nayi magana nace ya tashi sai yace wai gadina yake,haka lamarin ya cigaba da gudana tsakanina dashi sai dai har yau babu wanda na sanarwa cewa muna soyayya da samz dan ko Æ™awalli ban faÉ—awa ba haka kuma har yau muma ajunanmu nida shi ba mu furtawa juna kalmar so ba amma dai duka alamomi sun gama bayyana, kulawa muke da juna yana riritani kamar wani Æ™wai, duk abin da zai saka ni farin ciki ya sanshi kuma ya iya shi ina jin wannan shi ne dalilin da yasa bai wani sha wuya ba wurin samun zuciya ta. A kwana a tashi ba wuya a wurin Allah domin har mun fara lissafin tafiya gida nan da kwana shida, text massage samz ya turo min wai in shirya mu fita hang out wannan weekend É—in, da yake da yamma zamu fita shiyasa banji wata fargaba ba na faÉ—awa anty Salma na shirya na fita inda yake jira na, sanye nake cikin gown maroon colour na yane kaina da farin gyalen rigar, shi kuma Æ™ananan kaya ne ajikinsa jeans da t shirt sai p cap, daga ni har shi munyi kyau ajin Æ™arshe, wurin shaÆ™atawa ya kaimu can kusa da wani ruwa kai idan kaga wurin kamar ba a Nigeria ba dan haÉ—uwarsa da tsarinsa ga mutane nan tsilla tsilla masu yawon buÉ—e ido da shaÆ™atawa wasu har É—an cikin ruwan suke shiga daga baki baki ana yi musu hoto yayin da wasu suke shiga jirgin ruwa wurin dai gwanin sha’awa, zama muka yi nida shi muna fuskantar juna,

“Maimunatu…….” ya faÉ—a bayan ya riÆ™o hannu na guda É—aya wanda har sai da naji wani yarrr saboda rashin sabo,

“Na’am…” na amsa ina kallon hannayenmu dake maÆ™ale wuri É—aya,

“ki faÉ—a min gaskiya karki yaudare ni….. Dagaske baki da saurayi?”

Kai na É—aga masa alamar ehh, ajiyar zuciya naji ya sauke kafin ya sake É—ora É—aya hannun nasa kan nawa ya haÉ—e,

“Ni inada budurwa…… Harma relationship É—inmu yaje gida wurin iyayen mu….”

Wani ras ras naji gabana ya fara faɗuwa babu ƙaƙƙautawa,

“Amma yanzu lokacin da na haÉ—u dake sai na ji ra’ayina ya sauya, naji a yanzu babu wadda ta dace dani sai ke….. Maimunatu na faÉ—a kogin sonki…..”

Shiru nayi na rasa amsar da zan bashi, abin ka da Lagos kowa harkar gabansa yake babu wanda ya ko kallemu,

” Nima ina son ka….. Amma ita budurwar taka ya zaka yi da ita? ”

Murmushi yayi ya É—an sunkuyar da kansa alamun tunani,

” amma bakya ganin akwai matsala tunda ni ba musulmi ba ne?”

“Banda matsala da addininka… A yanzu dai kayi naka in yi nawa” na faÉ—a ina yi masa murmushi saboda ba abu ne mai sauÆ™i karon farko ka faÉ—awa mutum ba akan daidai yake ba musamman irin su samz da sunfi shekara 30 cikin abun dole sai a hankali cikin hikima da dabara duk da nasan zai yi wahala muyi aure amma har ga Allah nidai zuciya ta a yanzu shi take so kuma take muradi………….

*Garin dadi littafin kudi ne ga mai bukatar cigaban labarin sai ya tura 500 ta 0774712835 Aisha Ibrahim Access Bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko a tura katin waya da shaidar biya wannan no 07044644433*

_*Ummi Shatu*_

Post a Comment

0 Comments